Showing 18001 words to 21000 words out of 23161 words

Chapter 7 - Bakar Akida Part 1 Complete Hausa Novel

M SHAKUR   

21 Oct 2025

418

saka aciki ba!"Dozin akwatuna biyu kalolin kayan sunfi dari su sarka jaka gyale da sauran su tamkar wani kanti har su gwala gwalai ba'a barsu abaya ba!"Kaya dai na arziki."Sai masha Allah."


"Tarba ta arziki da mutunci dangin Inna baraka sukayiwa su Hajiya Raliya."


"Yan uwan malam duk sun zou auren kowa sai murna yakeyi da farin ciki domin salma ta zama tauraruwa acikin yaransu ita kadai ce ta auri mai arziki kaf dangin su!"Domin haka ne sukaji dadi sosai komai an gudanar na al'ada wanda karfi bai fi jiki ba."Da hakan aka kammala komai su Hajiya Raliya su ka koma."


"Yayin da karime da sauran sa'ointa ke ta kaiwa da komowa sai murna sukeyi suna duban kayan na arziki da basu da adadi."A gefe ko Baba larai sai faman cika takeyi tana batsewa tana hararen karime da bata ma san masarda innarta ke toyawa ba dan tuni ta kama salma ta rike gam.''Da dai larai ta fahimci karime bata kulata ficewa tayi daga sashen zuciyarta cike da bakinciki da takaicin wannan kayan da aka kawo ga karime sai wani rawar kai!"takeyi domin rashin sanin ciwon kai!"Amma zata dawo ta sameta sai ta ci mutuncinta.!"


"Salma ko tun safe tabar gidan taje gidan wata qawarta Zara'u, Saboda kada masu kawo lefen su sameta."



"Dr.Salman da jameel da sauran abokan su ne zaune amajalisa yayin da suke ta masa tsiya domin yaki ya amince suyi pre-wedding pics."Sam yaki ya amince saboda yace haram ne ba kyau kuma baya son ya tallata matan sa aduniya yana kishin su!"Da hakan dai suka gama cike ciken Wedding I.v din su suka wuce domin aiwatar da wasu lamurra nasu shi da jameel."






"A gefen minal ko da lauje acikin nadi domin ita kam gaskiya tana son Dr.salman matuka amma *BAK'AR AK'IDA* ta tsanar talaka tayi mata tsirou a zuciya da take ganin bazata iya zama da salma a matsayin kishiyarta!"Ai wannan wulaqanci ne domin tafi karfin tayi kishi da 'yar talakawa!"Domin wannan babban ci baya ne agareta kuma abin kunya ne da fad'a familynsu."



"Tana cikin tunanin ne taji sautin muryar daddynta da ke shigowa acikin falon nata "Da sauri ta tashi daga kwancen da take akan 3siter din tare da gaida daddynta."



"Amsawa yayi tare da zaunawa akusa da ita ya ce my daughter ya jikin ki?


"Da sauki daddy har ka dawo ya office!?"


"Normal!"Dear."Ya bata amsa a takaice."


"Duban royal stool din da ke gabansu cike da magungun nan ciwon zuciya da cup da robar ruwan faro da ke ajiye."sannan ya kalleta yace an baki magani duk ina ma'aikatan naki!?



"Eh,Daddy su bani na sha ni ce na sallame su dan ban son damuwa sai gobe zasu dawo nafi so na zauna nikadai shiyasa!"




"Haba!"Daughter ya kamata ki debe damuwa aranki kin ga idan har kina son salman aure babu fashi komai an shirya har I.v daurin aure an buga ni banga abin damuwa ba aciki!"Yarinyar nan gidanta daban naki daban kuma komai gidanki yafi NATA!"Ba akanki zata zauna ba Dear!"To meye abin tashin hankali aciki!?"



"Haba Dady talaka ce fa matsiyaciya kaima Kasan duk dangin mu basa son talaka amma sai ace nikai ce za'a fara yiwa kishiya kuma talaka gaskiya nikam ina jin takaici da bakin cikin abin!?




"Ina son kiyi hakuri minal wannan yana daga cikin kaddarar ki babu yadda zanyi da nayi wani abu salman yana da kirki kuma dole ne ayi masa adalci shima ya auri zabin shi matukar ba son kai zamu nuna ba!"Domin ke da shi duk abu daya ne kuma muna bukatar rayuwar kowa acikinku!"Kiyi hakuri kiyi watsi da *BAK'AR AK'IDA* irin ta mahaifiyarki kisani shi arziki na Allah ne kuma mai kudi da talaka duk daya ne agurin sa wannan shi ne mafita agareki idan ko kin fasa auren salman zan sanarda su mun hakura adaura aurensa da salma kawai Allah yabasu zaman lafiya."




"Daddy wallahi ina sonsa ban fasa ba zanyi kokari naga na hakura!"Amma wallahi Daddy na tsani salma tsana mai tsanani!"Ta Shiga tsarin rayuwata ta bata ta dagargazani yadda banyi zato ba!"Minal ta ce tana kuka!"




"Babu komai Dear ki hakuri kinji Allah yasa hakan ne alheri!"Inji Daddyn minal."




"Ameen Daddy nagodeminal tace tana zubda hawaye!"Daddy ko kara lallabata yayi tare bata haske akan rayuwa sai da yaga ta gamsu sannan ya wuce zuwa sashen su."Minal koh ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi tare da furzo iska mai zafi sannan ta kwanta domin ta dan samu sassaucin Bacin rata!"Ya ragu cikin hakan bacci barawo yayi awon gaba da ita!"





"Hajiya mai gado zaune afalo tana sauraren jawabin da yan uwanta sukeyi domin auren! suna son ita da salman su janye yadda da auren salma ya auri minal kadai ita da a jininsa kuma 'yar masu kudi!"



"Hajiya mai gado kallon su tayi sosai domin tuni ta gano zainab qanwarta ce ta turo su ayi mata taron dangi a hade mata kai!"



"Ta ce nagode da shawarku da kuma korafin ku yan uwana kuma nagode sosai Allah yabar zumunci."



"Amma kusani batun auren salman da salma ba fashi idan har zaku zo kusa ALBARKA kofata abude take!"



"Yadda kuke son minal hakan nima nake kaunarta domin yata ce,Auren su kuma ahakan yazo dole ne mu karbe shi yadda yazo mana domin rubutaccen al amari ne daga Allah"


"Salman ya shiga mugun hali saboda salma yana sonta tana son sa shin meye aibu dan an hade su dukansu har minal ya aura!?"Kun san cewa cinsu da shansu har sutura ba abinda zai gagare shi dan haka kuje gidan zainab ku tayata hidima saboda ni kunce bazaku xou auren tsiya ba salman zai auro muku bare talaka acikin ku ko!?"Ko da ku ko bada ku ba za'ayi harka aqare lafiya ai ni da nan gidan da gidan zainab duk dayane agurina!"Kusani duk abinda ke zuwa yana dawowa ina sane ido ne na zuba muku duk abinda kuke fada ina ji kuma kayan lefe an kai min su lafiya an dawo tunda abokaina suke kashe min kunya!"Ba ku dangina ba!" To nagode da irin sakayyar da ku kai min amatsayinku na jinina! Allah ya bamu lafiya!"Hajiya mai gado ta ce su ta tashi ta shige bedrum dinta tabar su zaune kamar ruwa ya cinye su sai wani fidda ido sukeyi.!



?🏻👸🏻








BAKAR AKIDA!



©TASKAR NABEELA DIKKO



®PEN WRITERS ASSOCIATION




Page 86/90




_Dedicated to my SAHEEBA Rahmah m Sani Ina yinki 0ver Habibarty Allah ya qara damqon zumunchii yabarmu tare Qawalliyya Muna tare Iya wuya Nabeela Dikko taki ce Aminiyatah_ 😍






________________________________

"Saudat ce ta dubi sa'adatu ta ce"A gaskiya yaya sa'adatu kamar bamu kyautawa yaya mai gado ba!"Kinga tayi fushi ta tashi ta barmu anan abinda bai taba faruwa ba!"



"Ke dan Allah ku kyaleta daga fadan gaskiya!"Ya zamu bari gida naso sai akai kasuwa ko ma kasuwar ta talakawa me zata zama dan ta aurawa danta yar talaka!"Taya dunia zata kira sunanta har taji ta amsa!"Ni kunga kutashi mu tafi inji Hajiya sa'adatu cikin fushi!"


"Hafsa ta ce hakane yaya mutafi ai wannan wulakanci ne dan kawai taga munzo gidan ta ai muma muna da gidajen mu!"Tai jira idan har mundawo!"


"Saudat ta dubi yayyen nata cikin rashin jin dadin zantukan su!"Ta ce yanzu wucewa zamui bazamu je mu mata sallama ba!?"Daga nan mu bata hakuriya yaya hafsa!"



"Ke sakarai!Marar zuciya kizo mu wuce!"Ko mu tafi abinmu!"Ke dan rashin sanin ciwon kai muzo gidanta tayi mana wankin babban bargo ta tafi tabarmu da gadin falonta! dan wulaqanci!"Kice zakije ki bata hakuri....!?To Allah ya kiyaye mu mun wuce kuje muje!"


"Hanya suka kama dukkan su suka fice daga gidan!" ba dan ran saudat yaso ba tabi bayansu zuwa motar su!"A hanya ma sai zagin Hajiya mai gado sukeyi wai ta wulaqanta su akan yar talakawa!"Saudat wayarta,Ta ciro daga jekarta ta rubutawa Hajiya mai gado sakon ban hakuri tayi tare da nuna mata sun wuce saboda sunga kamar bataji dadi ba!"Bayan ta tura mata tayi tagumi tana sauraren yayyenta da ke zuba musamman yaya sa'adat dake driving har buga sitarin motar takeyi kan masifa!"Direct gidan Aunty zainab (Maman Minal )

"Suka nufa cikin fushi!"domin basuji dadin yadda yayar tasu tai masu ba!"Yadda sukeji da kansu da kudi!"Ace har an ci mutuncinsu."Ko sallama basuyi ba suka shiga falon, saudat da ke bayansu kadai ce ta shigo falon da sallama!"








"Karime an sha kyau an fara fresh saboda Aikin Hajiya meena yana kyau."Salma amarya ba'a magana domin ta koma kamar balaraba haskenta ya fito fuskar sai kyalli take kamar madubi."Tayi kyau matuka."Acikin napep suke suna fira har da raha."Salma ta dubi karime ta ce"Shin karime ya zancen dan ummaru kin kira shi!?"

"Karime tace"Na kirashi yafi akirga bai daukah ba!"A karshe kashe wayarsa yayi duka salma!"Jiya da yamma naga Indo kanwarsa na tambayeta shi...Hmnnnnn...kinsan me!?

"A'ah sai kin fada!"


"Wallahi indo wani kallon banza!"Tayi min cikin tsiwa ta ce mi wai yaje neman na kansa tunda har diyan gidan laaka da tab'o sun iya faden arziki!"

"Salma ta ce haba! cikin tsoro! yanzu kina nufin indo ce tace miki hakan wacce naga kuna dasawa sosai!"

"Sosai Salma, Indo koh!" Ni kaina abin yabani mamaki amma nasan cewa bai fadawa iyayensa abinda nai masa ba!"Daman Indo ce abokiyar shawararsa akwai aminci atsakanin!"Amma na bata hakuri kuma nace idan ya kirata ta fada masa nace yadawo zan aure shi, ko da baida ko taro!"Na amince domin nayi nadama!"Karime ta karashe zancen tana hawayen nadama!"


"Salma ta ce"kiyi hakuri karime komai zai daidaita in shaa Allah."Yanzu yana ina ne!?"


"To Indo ta ce min yaje lagos gurin nema tun daren ranar da nayi masa wulaqanci yabi hanya!"

"To kiyi hakuri ni zan kira shi anjuma nasan zai saurareni ke kuma ki kiyaye Allah ya tabbatar mana da abinda yafi zama alheri."In ji salma cikin damuwa da tausayawa yar uwarta!"


"Karime tace"Ameen nagode salma!"


"Da hakan har suka kawo kofar gidan su."Bayan sun sauka sukai sai da safe da shi domin Dr.salman ya dauko musu hayarsa yana kai su gyaran jiki yana mayarda su."


"Cikin gidan suka nufa da sallama......sai dai me Gud'ar da Inna lantana Qanwar su Baba,Ne tayi arba da su cikin murnar ganinsu...sai da suka tsorata daga Karime har salma!"Kana tafara kirari iri-iri da habaici wanda kowa yasan da Inna larai (Maman karime)Take wacce ke kunshe a sashenta tana hadiyar yawu da bakinciki dan sai aikace aikace mutane keyi gobe jumma'a ne auren salma."Cikin rashin jin dadin abinda akeyiwa Innarta tayi sallama da salma ta wuce sashen su!"Karime kenan wadda ke ganin duk bakin halayen Innarta ne ke jawo ana mata arashi!"Salma ko cigaba tayi da sabgogin gabanta da sauran yan uwanta da su ka zo aurenta."





"Zaune suka sameta afalon duk abin duniya ya dameta!"Ko amsa sallamar tasu batayi ba!"


"Da sauri Hajia sa'a ta isa wurinta ta zauna tace me yake faruwa Zainab!"Duk kin wani fame!"Tunanin me kikeyi!"


"Cikin damuwa zainab ta kalle su dukansu da ke zaune a falon!"Tace basai na fada maku damuwata ba kun sani!"


"Wai akan yaya mai gado da dan nata ne zaki kashe kaki ke da minal!?"To bari kiji wallahi idan bakuyi da kyau ba sai ciwon zuciya ya zama ajalinku!"Saboda duk abinda kukeyi da halinda zaku shiga ba ruwanta!"Mu ma nan da kinka ganmu daga gidan muka fito korar Kare taimana!"


"Cikin mamaki da fidda ido da dukan kirji Hajia zainab tace Ke sa'adatu korar Kare fa kika ce!?Me kukayi mata!?Anya yaya mai gado matsiyatan nan sun barta akanta kuwa!?"


"Yanzu Zee, mu yaya maigado zata duba tace muna munafuntanta!"Menene... kuma akarshe zata barmu afalonta zaune kamar shegu ina gaya miki ta shige bedrum ta rufe!"Domin kawai mun fada mata gaskiya kan auren yaran nan!"Ni badan kinkarani muje ba da bazan he ba saboda banaso ace na shiga cikin zancen nan !"Wallahi bakiji ba babu abinda bata fada ta inda take shiga bata nan take fita ba!"


"Ni kaina nafara nazarin ba a banza suka barta ba!"Daga ita har salman din!"Idan ko haka ne sai mun tashi tsaye domin ganin an fidda su cikin wannan halin!"


"Hakane Sa'adatu ni yanzu komai ya kwance min,Yanzu ace ni da yar uwata uwa da uba daya munyi kare jini biri jini!"Ku abin da sauki tunda ku tobasanmu ne!"Ni fa Har marina sai da tayi akan auren nan!"Shiyasa naso minal ta hakura amma son salman ya hanata ta barshi tare da goyon bayan mahaifinta!"Domin ya ce aure ba fashi sai anyi!"


"To yanzu ita minal auren nan zatayi inji Hafsa cikin mamaki!"Tana duban Aunty zainab!"


"Ya zanyi Hafsa tunda sun ce sunji sun gani zasu iyah! nikam nace ba ruwana da auren....!Haba Yaya zainab kuyi hakuri mana idan kince ba ruwanki da auren ai kamar kin zuba fetur ne awuta kina jiran ta tashi da rayuwar minal!" saboda bazata taba ganin haske a auren ba matukar babu yardar ki alamarin!"Dan Allah kiyi hakura ki saka musu ALBARKA.!"Inji saudat cikin sanyin murya.!"


"Mtwsssssssss!!!"Hafsa ta ce kana ta dubi yaya Sa'adatu da zainab ta ce kunji wannan santobola!"To idan bata nunawa minal ranta ya baci ba ta ina zata gane kurenta ai gatane da yanci ake nema mata!"Ace kamar minal mai ji da kanta da ilimi da kudi zatayi rayuwa da kishiya ko banzar ma 'yar matsiyatw da batasan arziki ba!?"



"Yaya Hafsa ina son ku ajiye wannan *BAK'AR AK'IDA* Kuma ku ajiyeta agefe saboda ba addini bace al'adace irin ta marasa ilimi ba dole sai anyi auren kwarya tabi kwarya ba kowa zabi nagari ya kamata ya nema awurin ubangiji sann.......!"


"Dakata alaramiyya shehiya munji mu jahilai ne!"Kina ganin ke wata mai ilimin addini ce dan kawai kinga ke ce kinka taba sauke alqur'ani mai girma acikinmu!"Shi ne zaki taramu kina mana wa'azi ko said at.!"To Alhamdulilah dan muma mun san wasu surori!"Wallahi idan na karajin bakinki acikin maganar mu sai ranki yayi mummunan baci!"Inji Hajiya sa'adatu cikin takaici!"


"Ta kalli Yaya zainab tace kiyi hakuri kinsan iyayinta da nuna ita takwarai ce!"


"Dan Alllah yaya kuyi hakuri dukan ku!"Inji saudat!"


"Ba komai ya wuce malama sauda!"Inji hjia zainab."



"Daga nan cigaba sukayi da tufka da warwara akan maganar da yadda zasu bullowa al'amarin Hajiya maigado,Minal,da salman da kuma Abban minal!."












BAKAR AKIDA!





© TASKAR NABEELA DIKKO




® PEN WRITERS ASSOCIATION






Page 96/100



LAIFIN DADI KAREWA

ALHAMDULILLAH!





_WANNAN SHAFIN KYAUTA CE GAREKU_ 👌🏼

_'YAN UWA DA ABOKAN ARZIKI INA MUKU FATAN ALHERI_


_MASOYAN LITTAFAI NA BANSAN ME ZANCE DA KU BA A DALILIN SO DA KAUNA KUNA CIKIN ZUCIYATA KWANCE,NI DA KU SAI DAI FATAN ALHERI ALLAH YA BAR ZUMUNCHI MAI DOREWA ATSAKANIN MU AMIN,SO DA QAUNA NI DA KU YANZU AKA FARA, ANA TARE_ 🤝🏻




🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚





"A yau Jumma'a 22/2/2019 ne aka daura Auren Dr.salman Tahir Galadima da Barrister minal Maina akan sadaki naira dubu dari da hamsin."


"Sai kuma na Malama Salma Abu Sufyan akan sadaki naira dubu hamshin."Daurin auren da aka gudanar a sheikh Abbakar gumi Mosque bayan an kammala sallar jumma'a, Auren na su ya samu halarta dinbim manyan mutane da yan boko, kama kan gwamnan Jihar Kebbi manyan yan siyasa har ma abokan marigayi Tahir da justice maina da Jama'ar kauyen su Malam Abu Sufyan da sauran yan uwa da abokan arziki sunzou sun kuma sanya albarka abin ya qayatar,Musamman Abokan Dr.salman na India da U.s duk sun zo,Da sauran likitocin da ke jahohin nigeria,Shi da abokinsa Dr.jameel sunyi kyau matuka domin shigar su irin daya ce,Bama za'a banbamce waye angon mace biyu acikinsu ba,Sai an cinka saboda sun hadu karshen haduwa acikin tsadaddar shigarsu ta alfarma."An kammala lafiya daga nan suka wuce grand fishing park da ke garin na Argungu domin cin abincin liyafar angwaye da aka shirya ta musamman."





"Gefen Hajiya Mai gado sai dai San barkah domin alheri ne ke kwaranyo mata ta ko'ina."Gidanta ya cika maqil da abokan arziki da makota saboda Hajiya mai gado na kyautatawa makotanta."Abin dai ba'a cewa komai HAjiya Raliya uwar kirjin buki sai hadahadar fama da jama'a takeyi cikin shigA ta alfarma domin sunyi kyau matuka ita da Hajiya mai gado cikin shadda gizna kalar ruwan hoda da tasha pent work mai kyau,Gold masu tsada ne awuyan su hannu da kunne sai dai masha Allah Dan sun sha light make-up,Duk falon cike yake manyan mata yan kasuwa ma'aikatan gwamnati sai faman tande-tande abinci da abin sha kala-kala akeyi domin babu ce kawai babu agidan Hajiya Bilkis(Mai gado)."Wacce tuni ta manta da danginta da *BAK'AR* *AK'IDA* Ta hanasu halartar auren ko ba komai abokanta yau sun share mata hawaye!"Domin dimbin jama'ar da ke buki budiri a gidanta said dai ta ce"Alhamdulillah."





"Gidan Malam Abu Sufyan mai walda ne cike tinjim da jama'ar binni da kauye sai kidin kwarya akeyi da gud'a mata na raqashewa."Karime ce tsakar fili da su luba da hure harma umaima sai kwasar rawa akeyi ana kakkaryawa cikin murna da farinciki yan uwa sai liqin goma ashirin sukeyi!."


"Salma an sha make-up mai kyau cikin rantsattsen Material dinta maroon da silver head tasha adon sarka da yan kunne silver masu kyaun gaske takalminta Hill's da yar qaramar jakarta duk silver color."Fadan irin kyaun da salma tayi ma bazai fadou ba."Duk gidan sai faman qamshi yakeyi,"Inna baraka ma ta hade cikin swiss less dinta mai kyau kamar ba ita ba."Baba larai ko tana sashenta kunshe tana taunar bakin ciki kamar ta hadiye zuciyarta ta mutu!"Duk da taso kange yaranta kar sutafi gurin amma INA!"Dukkan su sun wuce suna shan shagali ita kadai suka bari kamar mayya!"



"Yan uwa da abokan arziki sunyi bajinta domin kuwa sun bayarda gudun muwarsu sun inna sun samu alherai da damage."Kowa ya CI ya sha anyi hani'an sai bararrajewa sukeyi cikin jin dadi."





"Gidan Justice Maina cike yake da jama'a maza da mata."A sashensa manyan mutane abokansa da yan uwansa sai fira ake ana raha abinci da abin sha ne ajiye firjit a katafaren falon nasa sai taya shi murnar auren minal akeyi mashi kuma yanata godiya da nuna jin dadin sa."





Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login