Showing 15001 words to 18000 words out of 23161 words

Chapter 6 - Bakar Akida Part 1 Complete Hausa Novel

M SHAKUR   

21 Oct 2025

420

kuna kulla mata gadar zare!"Ni bani wurin in wuce!"


"Juyawa tayi cikin bacin rai ta ce dan uban ku kuzo muje!"Minal!!!!"



"Nidal da ke kuka tana sharar hawaye tace muje minal ko!"tare da kamata domin ta tashi tsaye dan takoma kamar hoto."



"Minal tuni bakinta ya rufe!" kukan ma ta neme shi ta rasa!"Bugun zuciyarta sai qara tsananta yakeyi!" komai ganinsa takeyi kamar a mafarki!"Tashi tsaye tayi suka fara tafiya hajiya zainab ta wuce gaba Nidal rike da hannun minal abayanta sai dai basuyi aune ba sai jin minal kawai sukayi tayi suuuuluuu sai qasa!"Ta fadi tuiii!"Tamkar matacciya tuni numfashin ta ya tsaya!"


Da gudu Hajiya zainab ta dawo tanw fadin Innalillahi wa inna ilaihir raju'un!!!!!!!" minal na Shiga uku Nidal ta mutu ne!"Cikin kuka take fadin maganarta jikinta na rawa!"Da gudun su suka karaso wurin suna cewa INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJU'UN!!!!"MINAL!!!!"






BAKAR AKIDA!



©TASKAR NABEELA DIKKO


®PEN WRITERS ASSOCIATION





Page 71/75




_SADAUKARWA:" GA K'ASATA NIGERIA INA ROKON ALLAH DA SUNAYENSA TSARKAKAH DA YA SADAMU DA SHUWAGABANNI NAGARI MASU TSORON ALLAH WADANDA ZASU TAUSAYAWA MUTANEN K'ASATA ALLAH YA QARO ARZIKI DA CIGABA ACIKIN K'ASATA NIGERIA AMEEN, DA FATAN ANYI ZAB'E LAFIYA ALLAH YA SA A KAMMALA LAFIYA FATAN ALHERI JAMA'AR K'ASATA MAI GIRMA NIGERIA."🇳🇬_




________________________________

"Kaga malam dan Allah ni ka wuce kabar kofar gidanmu tun kan nasa ai maka wulakanci!"


"Ko kuwa ana so dole ne Dan ummaru!"tunda can kasan ni ba wani sonka nikeyi ba Zainu Dan gudun hijira nikeso!"Rashin sa ne saboda ya koma cikin sauran danginsa yasa nafara kula ka!"Yanzu kuma anyi walqiya gari ya haska na hasko rayuwAr tsaf nace banyi kuma bazan taba yi ba!"Wallahi bari kaji daga yau kar naqara ganinka kofar gidan nan kuma sunan karime ya fita daga bakin ka!"Bani ba kai...!"Dole mu rabu...!"Inji karime da ta riqe kugu sai masifa take zubawa saurayinta cikin bacin rai da rashin mutunci!"


"Haba karime ban cancanci ki wulakanta ni hakan ba!"Ki sani ina sonki kuma ina kaunarki domin Allah!"na miki alqawarin zan maye maki gurbin Zainu Dan gudun Hijara....!"


"Wallahi har ka mutu bazaka iyaba!" koh ba maye gurbin zainu ba?Ai yayi maka zarra!"Domin gari da madara suna da bambanci, kalar su ce dai iri daya amma dandano ba guda ba Dan ummaru!" yau ina kai ina Zainu jarumin maza!"Mtwssss shin wai kai ma idan ana babbakar giwa wama zai jiyo kaurin zomo!"Ai da iya takun mutum akan gane shi gwani ne!"Ni Dan Allah ka fice kabarni da bakin cikin da ke damuna....!"


"Karime kisani shi arziki na Allah ne kuma wannan *BAK'AR* *AK'IDA* ce da kika daukarwa kanki!"Ki debeta acikin rayuwarki!"kice sai mai kudi zaki aura!? sai naga tufin asirinki shi ne kisamu talaka kamar ke domin ruwa ba sa'an kwandon ba ne!"



"Ko zan auri talaka ba dai kai ba kwalin kifi a tabe ka asha karnin banza!"Dan bakada amfani bare mamora!"Kullum cikin harkar tsiya da talauci tun ana waje kwakwaf bare na aure ka,"Gaskiya ni bazan iya zaman hakuri ba!"Zaman gani ga sa'anni nah!"



"Cikin kunar raiI!"Ya kalleta ya ce naji nagode karime cin fuskar yayi yawa!"Amma kisani shi arziki na Allah ne kuma da ace ina shi da nayi miki!"



"Kana da shi!Dan ba ka rasa aikin yi ko sana'a ba!"Dan ummaru kace min zuciya ce tayin alherin ne a bakada ita!" ai ita kyauta tanada dadi ga kowa kuma sabo ne abin daga jini ne!"Zainu ma da ba dan garin nan ba, ya nemo yayi min sha tara na arziki da dukkan lalurorina wadanda saurayin kwarai ke yiwa budurwarsa balle kai."Ni alokacin sa komai ban rasa va!"Ba dan ya koma garin su maiduguri ba da banyi maraicin komai ba!"amma gashi nan yanzu banda komai ko powder nan neman gagarata takeyi abinda nafi karfi yana neman yafi karfina!"Gaskiya kayi gaba Allah ya raka taki gona lafiya nagode!"Karime ta cewa Dan ummaru ta juya ta shige zauren gidan su tayi tafiyarta cikin gida tana masifa da kumfar baki!"




"Tsaye yake kamar ruwa sun cinyesa yana kallonta har ta shige cikin gidan da kyar yaja kafafuwan sa ya bar kofar gidan zuciyar cike da takaicin abinda karime tayi masa ya dauki alqawarin zuwa binnin Lagos domin neman na kansa yadda zai korewa bakinsa k'uda kuma ya huce takaicin wulakancin da karime tayi masa da haka har ya isa gidan su rai a bace!"









"Wayyo! Allah na shiga uku minal kada ki mutu!!"Kinsan muna sonki ni da daddynki bamuda wata sai ke dan Allah ki tashi...!!!"



"Da gudunta har tana tuntube da haki ta qaraso wurin hannunta rike da robar faro mai sanyi"Gurfanawa tayi tare da amsar minal a hannun zainab da Nidal da ke ta faman kukah!"


"Kan minal din ta tallafo, ta aza a A jikinta!"tace Ilham ungo bude min ruwan!"Da saurinta ta bude ruwan tare da mikawa Hajiya mai gado da ke cikin tashin hankali!"


"Ruwan ta dinga watsawa minal a fuska!"Hajiya Raliya ko sai faman fifita take yiwa minal da mayafinta cikin tashin hankali!"



"Ilham banda kuka ba abinda takeyi!"Da kyar ta samu ta kira Dr.salman awaya ta Sanarda shi kaf abinda ke faruwa,"Cikin Sauri ya shaida mata suna zuwa yanzun nan....!"




"Numfashi takeyi sama sama tare da Jan doguwar ajiyar zuciya!"Idonta da sukayi mata nauyi ta bude!"


"Minal!Minal!!Minal!!!Ki tashi bazan iya rayuwa babu ke ba ina sonki my daughter!"Hajiya zainab tace kamar zautacciya tare da rungume minal din ajikinta tana zubda hawayen da kowa ke zubarwa a wurin!"


"Minal cikin karajin kuka!"Ta ce mummie mutuwa zanyi matukar ba mafarki nikeyi ba!"Idan gaske ne maganar danaji dodon kunnena ya fadawa kwakwalwata da zuciyata!"Idan da gaske kunnuwa na keyi to babu shakka zuciyata zata Buga nan take!"Kuce min in farka daga mummunan mafarkin da nikeyi ba gaske bane!"


"Saboda Ina son yaya salman son da ba'a taba yimasa ba a duniya!"Ashe sonsa ne ajalina!''Ban sani ba!" meyasa baya sona!?Meyasa ya tsane ni!?Mummie ku fada masa ni qanwarsa ce ni jininsa ce!Ni ce Minal din Aunty Zee dinsa!"Wallahi na tsani wannan salma sai nazama ajalinta.....!!!"



"Subhannallah kiyi hakuri minal ki daina wadannan zantuka marasa dadi mana!"Inji Hajiya mai gado!"Cikin damuwa da tausayin minal."


"Duk zantukan da takeyi Dr.salman da jameel suna tsaye a kofar falon suna saurarenta kamar yadda jama'ar falon ke saurarenta."Sai dai abu guda da ya tsaya masa rai! kuma ya kara jin yana haushinta da tsanarta Yakama shi duk da ta bashi tausayi shi ne"Kalmar na tsani wannan salma!"Sai nazama ajalinta!"


"Da kyar yabawa zuciyarsa hakuri ya karasa wurin su ya gaida su cikin Sanyin murya Hajiya mai gado da Raliya suka amsa masa."Yayinda Aunty zainab ko kallo bai ishetah ba!"Nidal ko sai harara take watsa masa!"


"Zubura tayi sanadin jin muryarsa ta karaso gareshi cikin kuka!" tace"Yaya salman wallahi ina sonka kaine rayuwata da farin cikinah idan narasa ka mutuwa zanyi matsanacin Sonka shi ya haifar da tsananin kishinka na tsani kishiya dan Allah ka fasa auren salma ka zauna tare da ni har abada!"Zan zame maka fiye da salma zan koma kalar macen da kake so zan daina duk wasu halayena da bakaso!!!"Kai min rai....!



"Duk naji zantukanki minal amma har gobe ba'a canjawa tuwo suna!"Kamata yayi kifara jin tsoron Allah ki gyara halayenki domin Allah ba domin saboda ni ba!"Kiyi hakuri ki yarda da kaddararki Nima salma ita CE kaddarata bazan iya rayuwa babu ita ba!"matukar tana Raye!"Allah ya halatta min auren mace Hudu saboda me zaki haramta min minal!?Bakida dalili bakida hujja!""Son da kike min yasa nike sonki ko ba komai ke jinina ce, salma kuma rayuwatq ce!"Dukkan ku bazan iya rayuwa babu ku ba!"Ki daina zancen mutuwa kowa yanada lokacin sa!" kuma kishiya ba akanki aka fara ba!"Ko ban auri salma ba bazan zauna da mace daya ba dole nai miki kishiya minal!"Dan haka kiyi hakuri kinji!"Hawayenta yake share mata tare da bata ruwan sanyi ta sha!"



"Aunty zainab ya kalla cikin sanyin murya yana bata hakuri amma firrrr...!!!"Tak'i ta sauraren shi saima ruwan masifa da takeyi masa tana ce masa macuci mayaudari sunci amanar zumunci!Kuma an fasa auren!" ba ita basu har abada!"A karshe Nidal da minal ta tasa agaba suka bar gidan!"Cikin matsiyacin gudu @360 suka iso gidan su dan tuni takira daddyn minal tace masa yadawo gida su hadu ba lafiya.!'"


"Hajiya mai gado sam bata ji dadin abinda ya faru ba duk da kasancewar daman tasan halin qanwarta zainab da masifa domin tun can ita ce aqasa koyaushe tana lallabata dan kawai burinta azauna lafiya!"Amma yau ta kaita makura,"Hakuri Hajiya Raliya da Dr.jameel suke basu domin ganin an shawo kan matsalar
Dr.salman kam ko ajikinsa tafi nono fari!"Gaba takai shi gobarar titi!"Abinci ma yasa ilham takawo musu su ci shi da Dr.jameel ."










BAKAR AKIDA!



©TASKAR NABEELA DIKKO


®PEN WRITERS ASSOCIATION_




~Page 76/80~



_*Wannan shafin kyauta ce zuwa gareka DR.ZAINUDDEEN JIBRIL(ZAIN)Ina miqa godiya ta mai tarin yawa, A bisa namijin kokarin ka domin ganin nayi tsaye kyam a duniyar marubuta,Ina maka Fatan alheri, Allah ya saka maka da mafifichin alheri ya sanyawa xuriya albarka Ameen, Gaba dai gaba dai Oga Zain*_ 👍🏼👍🏼👍🏼





________________________________

"Da masifa ta shiga gidan nasu,Sashen su salma ta nufa domin tasan halin mamanta larai sarai!Da zarar ta gano Danummaru ne yazo wajenta to kashinta ya bushe!"



"Da sauri ta isa dakin su,"inna baraka tasamu zaune tana gyaran shinkafar tuwo,Da sallama ta shiga tare da gaida Inna Baraka."



"Yawwa karime kina lafiya?''


"Lafiya qlaw Inna,Salma na nan kuwa?''


"Eh,tana nan yanzu ta kewaya bayi ki zauna mana ko kasuwa za'aje ne?"


"A'ah inna wurin salma dai nazo muyi zumunci.""


"Atou karime kyale ku ne nayi ai,ace kuna gida daya amma baku biya junanku tunda akai fadan nan!Ki tuna ke ce babba ko ba'a yi ba kin baiwa salma shekara d'aya kin ko ga bai kamata ki biyewa qanwarki ba"


"Inna wallahi ba haka bane kasuwa nike zuwa shiyasa ba na shigowa kuma muna gaisawa idan mun ka hadu domin nagane salma na da kirki da mutunci sharrin shaidan ne!"


"To gaskiya ku gyara karime......"


"Salma ce ta katse zancen su ta hanyar shigowa dakin da sallamarta"


"Inna amsa mata tayi kana ta tashi ta fice daga dakin tana cewa yau dai yayarki ta kawo maki ziyara tunda ke baki shiga sashen su, ai idan abu ya wuce barinsa akeyi!"Inna Baraka tace tare da wucewa zuwa aikinta."


"Salma da murmushi ta kalli karime ta ce"Sannu karime yau kece asashen namu?"


"Ni ce Salma dan Allah kiyi hakuri sai yanzu na gane hassada ga mai rabo taki ce!"Wallahi ina sonki salma Innata ce ke ta kitsa min komai duk abinda nikeyi miki ita ke sakani!"Ko yanzu aboye ne na shigo inda kuke,"Amma yanzu nasan cewa "Karya fure takeyi bata 'ya'ya!"kiyi hakuri!Bamu kyauta muku ba ni da iyayena kuna zaune da mu da zuciya daya mu kuma muna jin haushinku!"Salma ki yafe mana"Kinji 'yar uwata!"


"Hannunta ta kamo ta hade da nata, tace babu komai karime na yafe miki komai ya wuce duk abinda kike min ban taba kallonki da ko daya ba!Harma su inna da baba"Nasan Sharrin zuciya ne!"


"Karime murmushi tayi jikinta asanyaye tare da jin kunyar salma ta ce nagode 'Yar uwata!"


"Babanmu ya ce min aurenki za'ayi makon nan mai zuwa?"


"Eh in shaa Allah karime,"Ki tayani addu'ah domin ni har yanzu ina jin tsoro da fargabar shiga gidan Dr.Salman saboda *BAK'AR AK'IDA* Irin ta danginsa kinsan sun tsani talaka ya rabe su!"


"Babu abinda zai faru da ke Salma sai alheri da jin dadin rayuwa."
Allah ya sanya alheri ina tayaki murna domin salman mutumen kirki ne, Allah ya sa ayida mu"


"Ameen,Karime nagode Allah ya nuna mana naku!"Shin Ina Dan ummarunki ne?Ko yayi tafiya ne? na daina ganinsa!""



"Mtwssssa dan Allah ki daina min zancen sa!" Yanzun nan ma na koreshi! domin ni nagaji da gafara sa banga qaho ba!"Mutum kullum ta-tau kamar jijiya!"Nikam gaskiya nagaji bazan iya rayuwa da shi ba ahakan!"baya iya tabuka min komai!"Kinga fa ko irin... !"


"Haba karime!"Salma tace tare da dakatar da ita!"Meye aibun shi!?Sai naga yana da mutunci kirki ilimi da addini!"


"Aibun shi matsiyaci ne!"Salma.''Me akeyi da talauci ai ko mu da ke zaune acikinsa kullum muna addu'ar Allah ya fidda mu daga cuta ya bamu lafiya!"Ke kinyi arziki Allah yayi maki gyadar dogo saura ni da sauran!"Kin isa barkah shiyasa nazo in tayaki murnar barka da arziki salma!"


"Menene na barkah kuma aciki Karime?"Dama ace kin min barka ne kan nasamu miji nagari zanyi aure in tufawa kaina asiri da nafi jin dadin hakan!"Amma ace barka kike min ta samun mai arziki!?Nikam wannan baya cikin tsarina!"Ya kamata Ki gane shi samu da rashi duk na Allah ne!"Yaushe kika koyi wannan *BAK'AR AK'IDA* ta banzah!"Kina yar talaka kice ke sai mai kudi kike so karime!?"To wallahi kinyi babban kuskure dan ba'ayiwa Allah wayo masani ne akan dukkan komai!"Kuma shi ne mai bayarda mulki da arziki ga wanda yaso!"Idan Allah ya tashi jarabtarki sai yabaki mai kudin karshe kisha wuya!"Ni kaina da kike gani wai zan auri salman wallahi Allah ne shaidata ni kudin shi baya agabana!Kuma naso ace a talauce zan aure shi daga baya muyi arziki atare nafi son hakan!"Kuma ko yanzu Allah na iya maida shi talaka kamar mu!"Dan haka kiji tsoron Allah ki so mai sonki da zuciya daya karime!"Salma tace fuskarta a daure cikin rashin jin dadin abinda karime tayiwa Dan ummaru!"


"Cikin yanayin nadama ta dago kanta zuwa gareta tace na fahimceki salma Allah ya yafe min nasan nayi kuskure abaya kudi ne kawai agabana,Tare da rudi na innata,Hakika ta daurani akan tafarki marar kyau!" sai yanzu na gane da kika fargar da ni gaskiya!"Kuma in shaa Allahu zan nemo shi in bashi hakuri!"Amma salma duk da hakan Danummaru ya cika matse hannu sosai ya kamata ace dan mayukan nan su turare da sauran yan kayan nan na makwalashen kanti da naga ana kasowa abokaina nima yayi min inji dadi komai dai rashinsa yafi karfin su dan iya kudin ka iya shagalinka ne karfi baifi jiki ba!"Ai wannan ma wani abu ne!"saboda rayuwa ce da zamani yazo mana da ita salma!"


"Hmnnnn karime kenan awani wurin kina da gaskiya amma ki qara yin hakuri watarana sai labari."Yanzu kiyi kokari ki bashi hakuri saboda baki kyauta ba kuma shawarata ita ce ki damu da wanda ya damu da ke!"Ki roki Allah ya hada arzikin ku."


"To salma zanyi kokarin yin hakan nagode zan wuce kada inna ta nemeni, amma salma nifa kallonki nike tayi tun dazu naga sai wani sheqi kikeyi kinyi kyau hakan...kamar wata sabuwa ba ke ba?"Ko duk amarchin ne wallahi ba karya kin canja sai haske kikeyi kamar tauraruwa?"Karime ta ce harda shafa fuskar salma da ke walwalniya kamar madubi tayi (smooth)"





"Murmushi tayi tare da duban karime ta ce baki rabo da abin dariya ki wani ce kamar bani ba,Nice dai salmarki...."To daman Hajiya Raliya qawar Maman salman ce ta kaini gidan wata Aminiyar su hamshaqiya kuma kwararriya Mai sayarda komai da ya shafi jiki wato Hajiya Amina Na'amore duka yau kwana na Hudu ne ina zuwa amma ni kaina naga canji wato ita aikinta yana kyau, sha yanzu magani yanzu ne"



"Haba gaske dai kice naira ce kwance a fuskar ki."Ke kam kin fara komawa kalar masu kudi!"Yanzu nima ina so in gyara tawa fuskar ko zan haska ranar aurenki!"Zatayi min?"


"Eh mana ai matar batada matsala!"Ga kayanta da sauki da rahusa, ga aiki kuma ko'ina tana tura kayanta, kedai bari gobe zamuje tare idan aka qare min sai tayi miki ni zan biya kudin naki"


"Yawwa salma nagode."Bari inyi hanzari n shiga gida nabaro inna zata daura sanwa."Niema muje in taya Inna aiki ta fita da jimawa!"To muje sai gobe idan nazo!"To yayi Allah ya kai mu."In ji salma.


"Amin karime tace Nagode Sannan tayi sallama da Inna Baraka ta wuce sashen su cikin jin dadi."







"Bari kawai Abban minal yaya mai gado ta nuna min bani kowa!"Kuma bani bakin komai ni da 'yata a rayuwarta!"Duk fa abinda na labarta maka shi ne ya faru!"Babu abinda bata ce mana ba!"Akan salman ai d'a baifi d'a ba!"Saboda wata can talakar banza marar gata!"Za'a wulaqanta min minal!"Abinda bazai taba yuyuwa ba ne domin bazan dauki raini!"Ba awurin kowa wallahi!"


"Numfasawa yayi bayan zurfin tunanin da yayi akan zantukan Hajiya zainab din."sannan ya ce"Naji kuma dukkan abinda ya faru!" Gaskiya abin ba dadi amma kisani yadda muke kare lafiyar Minal, haka itama kariyar lafiyar salman takeyi!"Ya kamata muyi musu uzuri zainab!Da salman da minal duk daya ne ya kamata abasu abinda suke so aimasu adalci!"Kada zuciya da saurin fushi yasa muyi da na sani...!"

"Haba!Abban minal wane Dana sani kuma!? Ai ana yinsa ne idan ana tare!Kuma ni minal nasani kamar yadda itama da d'anta tafi damuwa!"Na riga na fada mata wallahi bani ba ita kuma minal bazata taba auren d'anta ba"Domin bazata taba zama da ' Yar matsiyatah amatsayin kishiyarta ba!"Dan haka dole ne a fasa zancen auren.....!"



"Dakatah zainab...Bana son shirmen banza!"A fasa auren fa kinka ce!?To Saboda me!? Salman ne ya ce yafasa!?Ko ita minal din tace maki tafasa!?"


"Ai Ko basu fada ba ni na fada!"saboda ance labarin zuciya a tambayi fuska na hango farinciki kwance a fuskar salman Kasan daman shi ba so yakeyi ba!"Kuma yanzu mahaifiyar sa ta goya masa baya!"Maganin kar ayi kar afara!"Dan haka muma zamu ba minal hakuri ta tsaya jiran mai sonta ba wanda ita ke son sa ba!"Yanzu haka da kyar ni da Nidal,muka samu ta kwanta bacci ko zata samu sassauci!"


"Yanzu zainab meye zamu cewa mutanen da da muka gayyata!?Yanzu duk shirin mu ya zama na banza kenan!"A gaskiya dole ne mu samu mafita...........!"








🏻👸🏻


BAKAR AKIDA



©TASKAR NABEELA DIKKO



®PEN WRITERS ASSOCIATION






Page 81/85


_Dedicated to my little princess Mufeeda Ameenu😍 Allah ya nuna min ranar aurenki Amin._




________________________________
"Gidan malam Abu Sufyan ne cike da jama'ar binni da na qauye."


Ba kowa bane face Hajiya Raliya da jama'arta ta arziki da ta gayyato domin kawo kayan lefen salma saboda duk dangi Hajiya mai gado sunce su bazasu iya shiga wannan unguwa ta qauyawa talakawan da wasun su duk mayu ne!"A cewar su wai duk garin cin maganin arzikine talakawan ke komawa mayu!"Dalilin da yasa hajia Raliya ta nemo mutanen arziki suka kawo kayan da yawan su har baya faduwa babu kawai ce a ba'a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login