Showing 1 words to 3000 words out of 23161 words

Chapter 1 - Bakar Akida Part 1 Complete Hausa Novel

M SHAKUR   

21 Oct 2025

416

BAKAR AKIDA🏻


©TASKAR NABEELA DIKKO

®PEN WRITERS ASSOCIATION




GABATARWA_ :"DUKKAN YABO DA GODIYA SUN TABBATA GA ALLAH UBANGIJIN BAYINSA,SALATI MARAS ADADI GA SHUGABAN HALLITA MANZON RAHMA DA ALAYENSA BAKI DAYA."



TSOKACHI: "WANNAN LITTAFI NA BAKAR AKIDA LABARI NE KIRKIRARRE KAGAGGE BANYI DOMIN WANI KO WATA BA."


SADAUKARWA:"GAREKU MASOYA DANGINA DA ABOKAINA INA MAKU FATAN ALKHAIRI😍





Page 1/5



Bismillahir rahmanir rahim



_____________________________

"Billahillazi!Salman kayi kadan ka auro salma ka kawo gidan nan a matsayin surukata!"Can dai inji su gada!"Ga yar arziki wacce ta gado shi tun kaka da kakanni kamar kai!Amma sai ka nacewa waccan mayyar yarinya yar gidan mayu masu shegen shiga ran tsiya!"Na rasa me ka gani ga salma wanda minal batada shi!"Ace karasa abin so sai wannan kodaddiyar yarinya yar matsiyata da kaf danginsu ba wanda ya taba mallakar keke bare babur!"To wallahi idan ni hjia mai gado ce na haife ka!Bazaka auri salma ba kaji na gaya maka!" Minal ce zabina kuma ita ce zaka aura tashi ba fashi kuma ka b'ace min da gani tun ban sassaba maka ba."Kar ka qara yimin zancen ta!"


"Salman dake gurfane gaban mahaifiyarsa ne ya dago kansa idonsa jajir kmr barkono ya ce,Allah ya huci zuciarki Ammina in shaa Allah zan ga nayi kokarin hana zuciata abinda ta ke so zanbi umirniki(Umurnin Uwa)ya qarashe maganar cikin kunar rai!"

"Hanyar waje Hjia mai gado ta nuna masa da hannunta cikin bacin rai ta ce Salman tashi ka tafi ko zan samu nutsuwa wato ni zaka fadawa har ynzu salmar ce aranka ba minal bako!?" get out!'

"Very sorry Hajiya in sha Allah hakan bazai sake faruwa ba!"Inji salman cikin ladabi!"


"Tashi yayi sum-sum ya wuce yabar falon saboda yasan halin Hjiarsa sarai fagen iya masifa ta kwarai sosai!"Dakinsa ya nufa yana mai zubda hawaaye ciwon son salma ne ya addabe sa!" da kuma tsantsar tsanar minal ne dauke a qalbinsa!"A gaskiya shi kam bAzai iyA dAina son salma ba har karshen rayuwar sa!"Dan kuwa ita ce zabinsa ba minal ba marar kunya!"Ya rasa a ina wannan BAK'AR AK'IDA tasamo asali acikin afamly dinsu!"Da har suke cigaba da Assasata!."Fatan shi Allah yasa su gane gaskiya!"






"Zaune ta ke a Dan madaidaicen tsakar gidansu mai kama da kango tana jika gari da suga domin Karin safe."

"A gefen ta wata dattijuwa ce ke daka Tim tin tuuum in banda sautin karar turmi da tabarya ba abinda ke tashi,wurin!"


"Wacce ke shan gari da sugan ce ta taso ta qaraso gurin da matar nan mai dakan ta ke."

"Ta ce Inna kawo in idar da surfen kije ga naki gari can na rage maki."Kinga dakan nan baki ko iya yinsa sosai."


"Matar wacce aka kira da inna ta ce kibarshi kawai salma wannan dakan sai ni naga ke gabaki daya kirarki ta fita daban da takowa agidan nan kamar yanaynki da jikinki basa jure wahala!" Wallahi ina tausayin ki salma!"Inna ta karashe maganar tana mai zubda hawayen da take gogewa da gefen zaninta."

"Murmushi Wanda yafi kuka zafi Salma tayi tace,Haba Inna ki daina damuwa da halin rayuwar mu haka Allah ya so kuma hakan ya ke son ganinmu karfa ki manta kaf danginmu ba mai arziki kedai mu godewa Allah da yayi mana arzikin samun rai da lafiya masu arziki nawane adunia suna da dimbin dukia amma sun rasa rayukansu da lafiyarsu kinga basu da anfani Innata saboda haka Allah yai mana komai arayuwa.!"Kawo tabaryar jeki ki karya zan cigaba!"

Inna miqawa salma tabaryar tayi tana mai tausayawa rayuwar 'yarta!"Wacce aka Haifa acikin talauci ta girma acikinsa fatan ta Allah ya sa ta mutu acikin arziki!"Saboda batason tasha wuya da azabar rayuwa da suka gani!"


"Salma ko cigaba da dakan tayi da kyar take dakawa saboda ita sam bata iyawa karfin haline takeyi domin ta taimakawa innarta da tsufa ya tasowa sanadin talauci domin tuni tabarya ta tsotse mata kurciya takoma tsuhuwa Dan kuwa wannan ce kadai hanyar cin abincinsu wato surfe."




" Zaune take ta daura kafa daya kan daya cikin shigar wasu mugwayen English wears wando da riga Kore, matsatsun gaske, acikin qayataccen falon ta da in ban da qamshi da sanyi A.C ba abinda ke tashi acikin sa," earpiece sanye a kunnenta tana sauraren waqoqin justin bieber."

"Sai wani bin waqar takeyi tana lumshe ido,A gefe 'yan aikinta ne zaune suna kallon t.v a qasan kafet."

"Falmata ta ce,ranki shi dade lokacin sallaah yayi muje muyi sallah!?

"Mtwsssss ke wace irin jaaka ce bazaki bari idn kinje gidan ubanki ba, kiyi sallolinki ko sallah aka kawoki kimin ne?"

"A ah falmata tace, cikin firgici!"Kiyi hakuri Anty minal!"


"Okay!Meye aciki idan kin koma gida saiki kiyi gabadaya mana."Ni kaina ma nafison in hada uku ko hudun inyi at dsame time yafi sauqi ko ba hakaba."In ji Meenal

"Hakane Anty!"Su ka amsa mata dukan su falmata da lami suna duban junan su."

"Am lami je ki part din mum kice ina kiranta."

"To Anty,
Lami ta ce, ta wuce domin Isar da saqon uwar gijiyarta cikin sauri!"


"Meenal jiyowa tayi wurin falmata tace,Ke jaaka awuni sallah nawa ma akeyi na manta nace Hudu uku ne ko?"

"Cikin ladabi falmata ta ce,A'ah Anty,biyar ne awuni."

"To ya akeyi Dan naga ke kin iya ita waccan banzar kmr jahilace!"(Lami)

"Akwai Subhi ana raka'a biyu,Zuhr,Asr raka'a Hudu,sai magrib 3 da isha itama hudu akeyi Anty."In ji falmata cikin nutsuwa saboda ita tanada dama fagen ibadah."


"Okay"Naji abin ashe da yawa nikam biyu nikeyi kowacce."


"Toh!Falmata tace cikin mamaki azuciyrta duk da tasan cewa ita kanta bawani ilimi ne da ita ba Amman tasan ya zatayi sallah amma ita minal din kmr ba diyar musulmai ba koda yake baza tayi mamaki ba tunda ba a nigeria tayi rayuwarta ba duk a London tayi karatunta harta gama cikin yahudawa tasamo dunia kam amma komai bata sani ba ga me da lahirarta."Allah ya shirya tace azuciyarta."


"Minal ko sai waqa takeyi tana shan shishaa tana rausayawa."





BAKAR AKIDA👸🏻👸🏻👸🏻


©TASKAR NABEELA DIKKO

®PEN WRITES ASSOCIATION




Page 6/10



An karbou daga Abih hurarah(R.A) ya ce,"Manzo Allah_ _(SAW) ya ce, "Kashedin ku da zato domin shi zato zance ne na karya."_
_Bukhari da Muslim ne suka ruwaito._





________________________________
ASALIN SU



DR.SALMAN



"Dr.Salman Tahir Galadima yaro ne matashi kyakkyawa wanda ya ke da shekaru 30 cip a dunia."

"Yayi karatu a qasar India inda ya zama babban likita Wanda ayanzu hakan ya na aiki GENERAL HOSPITAL da ke garin ARGUNGU."

"Mahaifinsa Alh Tahir galadima ya rasu tun yana qaramin yaro sunan mahaipiyrsa hajia Bilkisu(Mai gado) sai qañwarsa daya tal adunia wato Rukayya mai sunan kakar su mahaifiyar marigayi tahir wacce sukeyiwa alkunya da (Ilhaam)"

"Salman ya samu so da kauna da duk wani gata awurin iyayen sa,Sai dai hkn baisa shi karya alqawarin da ya daukarwa mafinsa ba na zama yaron kirki kuma da nagari."Saboda mahaifinsu mutumen kirki ne kuma hamshaqen mai kudi Wanda yakeda katafaran gida anan G.R.A ARGUNGU ga shi mutum mai kyauta da ilimi ga taimako da tausayin mutane."Dukkan halayensa na kirki ba Wanda salman bai dauka ba akullum burin shi ya zarce ayyukan alheri da mahaifinsa yayi arayuwarsa."

"Hajia bilkis(mai gado) macece mai son mulki da takama sam batason talaka ya rabeta saboda iyayenta da danginta masu arzikin gaske ne shiysa ita bata son mu'amula da marar shii."Kaf halayenta iri daya daya ne da yarta kuma autarta Ilhaam."Ta gado halayen hajiya mai gado har ta zauce." Shiyasa akullum salman ke kokarin tunatar da su wasiyyar Alh tahir tun kan yavar duniya da su ji tsoron Allah su daina wulaqanta mutane amma ina abin ya riga da ya zame masu jiki."Sai addu'ah."



BARRISTER MINAL


"Minal Maina Sadauki 'yarinya ce mai masifar kyau ga ta da jiki mai kyau sai dai tsabar rama da tayi mata yawa ke sa ta muni."

"Minal 'yar qanwar hjia ce uwa daya uba daya, mama Zainab wacce ke auren Justice Maina sadauki da ke zaune a garin Argungu."

"Barrister Meenal Maina tayi karatun low a london Wanda a yanzu hakan lawyer ce mai zaman kanta da ta ke aiki a high court Argungu."Tana da shekaru 26 a duniya,Sangartacciya ce ta gaske batada ilimin komai da ya danganci addini kasancewar basu wani Dade da dawowa gida Nigeria ba,"Dan tunda aka haifeta suna London har sai da ta kammala karatunta suka dawo."A Yanzu ne ake koya mata abubuwa da dama dangane da addini dan ko sallah bata iya ba!" kuma bata ma wani maida hankali sosai Dan tana ganin tafi karfin malamman na ta."Saboda minal batada kunya ga rashin ji da shigar banza Sam bata da kama da diyan musulmi tun kan halayenta da dabi'arta,suturarta,da maganarta na marasa tarbiya ne komai take so ko ta ga dama shi takeyi kasancewarta 'ya daya da Allah yabawa iyayenta kuma suna sonta sosai shiyasa takeyin duk abinda ranta ke so agidansu da garin Argungu baki daya."





SALMA MAI WALDAH


"Salma Abu sufyan (Mai waldah) yarinya ce Matashiya black beauty ce mai kyaun diri ga ta kamila mai hankali ga ilimin addini da mutunci tasan girma da mutucin manya." kasancewar da kyar ta samu ta kammala karatunta na sakandare dan ko basuda kudi ko kadan bare ta cigaba da karatunta duk da taso hakan amma ba hali!"Ba kowa ba ce,"Ba diyar kowa ba ce face bayin Allah da su ke zaune acikin tufin asirin Allah Sam gidansu salma baiyi kama da in da mutane ke rayuwa ba,tamkar wani kango haka yake kuma a hakan suke tafiyar da rayuwar su da sauran jama'ar gidan saboda lungu biyu ne da na babanta da kanin babanta da iyalensu duka Suna zaune acikin gidan su da ke garin Argungu a unguwar Allugu Wanda idan ba gidan 'yan walda ko surfe akace ba, bama za a gano gidansu salma ba a unguwar.saboda waldah gadon gidan su ne,wanda duk mazan gidan shi ne sana'ar su matan kuwa surfe ne aikin su."



"Malam Abu Sufyan mai walda shi ne babanta sai Innarta Baraka ita kadai ce Allah ya qaddari ta tsaya acikin yaran da suke samu saboda inna baraka wabi takeyi da ta haihu bayan lokaci kadan yaran komawa(rasuwa)sukeyi."A hakan kowa ke tafiyarda rayuwarsa agidan mata suna dakau(Surfe) yara da manya wasu talla,maza ko suna fitaa faci da walda saboda, su ne sana'a ta gadon gidansu salma."



"Watarana da salma tayi rashin lafiya ne sai innarta ta kaita asibiti sai Dr.salman ya duba salma sosai harda bata magani da yayi mata allura to irin yadda salma take kuka alokacin da yake mata alluran ne har yaji ta burgeshi daga nan ya sauke su gida kuma ya fara bibiyarta tun bata kula shi har tafara kula shi saboda yanda ya ke ba ta kulawa da tausayinsu tare da taimakonsu da yakeyi har dai soyayya mai karfi ta dunke atsakanin su."Ba yadda baban salma baiso ya raba salman da yarsa ba!" dan kuwa ruwa ba sa'an kwando ba ne" amma abin yaci tura domin salman baya jin kora da wulaqanci idan dai akan abinda yake so ne."A hankali tun salma bata nuna masa so har tafara saboda irin yanda ya ke nuna mata so da kulawa duk da alokacin tanada shekaru 20 ne aduniya amma tasan cewa salman ya ci akirashi da mai sonta na gaske Dan baya dubin yafi karfinsu kasancewarsu marasa hali."

(So ne hana ganin laifi inji yn mgn lol)








"Tun minal na yarinya qarama take son Yaya salman dinta,Dommin ada can baya gidansu take zama tana hutu,yana sonta tana sonsa irin na kurciyar nan to shi ne ita har xuwa girmanta bata daina ba tun iyayensu na daukar abin amatsayin kurciya har aka gano lalle son salman acikin jinin jiki minal ya ke."Hakan ne ya sa iyayensu mata suka shiga cikin zancen saboda masifar son da minal keyiwa salman."


"Amma shi sam da ita da iyayensu basa gabansa kan maganar hadasu auren! saboda shi halaye da dabi'un minal basu yi masa dan kuwa batada kamun kai bare ilimi da tarbiya ga ta sangarta da rashin kunya da yayiwa rayuwarta katutu."


"A rayuwar salman yana son mace mai tarbiya ilimi da alkunya ba watsatsiya kamar minal ba saboda yana son ya samawa yaran sa uwa tagari wacce zata kula da rayuwarsa da ta yaransa."






BAKAR AKIDA


©TASKAR NABEELA DIKKO


®PEN WRITERS ASSOCIATION



Page 11/15



_"Duk abinda ka raina, shi wani ke so aduniya, yi kokari kayi amfani da damarka, domin daya ce, idan ta wuce bazata dawo ba,Zama mai dubin na kasanka da wanda ka fi, domin kallon Wanda ya fika komai Babbar kasada ce."_

NASIHA CE!






"Inna Baraka ce zaune akan wata tsohowar tabarma da ta sha rana kuma ta ga duniya harta rarake!" ita da 'yartah Salma dubanta ta kai gareta ta ce"Salma a kullum ina maki fadan akan yawan tunanin nan da kikeyi!"


"Ina kara horonki da ki debe soyayyar Salman azuciyarki!"Hanyar jirgi daban da ta mota!"Duk kin wani ki rame!"kina damar da kanki kin sani ko Salman na sonki uwarsa ba sonki takeyi ba!"Har nan gidan ta zo kwanakin baya ta zazzaga mana rashin mutunci!"Tayi mana kashedi kuma ta riga ta gina katanga atsakaninki da Salman!"Ba ke ba shi!"


"Kinga ko salma dole ne ki hakura da salman ko kina so!"Ko ba ki so!"Masu kudin nan da kike gani auren kwarya tabi kwarya sukeyi bani gishiri in baka manja!"Kin ga ko gwara kowa ya tsaya inda Allah ya ajiye shi."Ki daure Mu mikawa Allah lamurran mu sai mu ga haske acikin su"Ni kaina ina jin zafi da tausayinki araina!" saboda nasan kin rasa mai sonki wanda baya dubin yafi karfinki Salman yaron kirki ne mai mutunci Wanda ya cancanci ayaba masa."Fatana Allah ya musanya maki da mafi alheri!"


"Salma hawayen da ke zuba tun a lokacin da Inna tafara maganar har yanzu ne ta share a fuskarta azuciyarta ko zafi ne ke ta fita."Ta nisa tace "Inna na hakura kuma In shaa Allah zan cigaba da addu'a Allah ya musaya min da Alheri."Zanbi umurninki!"Daman tsautsayi ne irin na so nasan cewa salman Dan masu kudi ne yafi karfina!"Allah ya yaye min damuwata!"


"Ameen,Salma hakan nike so kinji kiyi hakuri."Yanzu tashi muje mu fara surfen can!"Kar azo amsa ba mu karasa ba!"



"To inna muje!"Allah yasa mudace"

"Ameen."Wurin turmi da tabarya suka nufa dan karasa surfen su."




*********** "Na Shiga uku mummy na rasa me na yiwa Yaya salman!"Ya tsaneni baya sona!"Baya kaunata!"Idan nakira shi wulaqanta ni yakeyi!"Baya kula dani da sonsa da nikeyi!"kamar ni ba jininsa bace qanwarsa kamar Ilhaam !"Mummy Ku aura min ya salman ko da sonsa zai zamo ajalina!"Mummy ko gawata ce ku kai agidansa domin cikar burina!"Son sa zai kashe ni!"Minal ta qarasa zancen cikin kuka da karaji!"


"Mummy kara rungumo minal din tayi cikin jimami da bacin rai!"Ta ce"Kiyi hakuri minal aure tsakaninki da salman kamar anyi an gama!"Ki daina zancen mutuwa idan kin mutu ni da dadynki rayuwar mu taqare saboda son da muke maki bazamu jure rashinki ba!"Yanzun nan gidan Yaya mai gado zani na gaya mata!"Abinda salman ke maki da irin cin fuska da zarafinki da yakeyi yayi kadan ya wulakanta ki!"Dan kawai Allah ya jarabceki da sonsa!"To wallahi yau za'ayi ta takare!"share hawayenki bari kuka domin na marasa gata ne."


"Mummie Har kinsa naji dadi da sanyi araina shiyasa nike sonki!"Idan kinje Ki nuna mata ranki ya baci saboda harke baya girmamawa kar kibar gidan har sai an tsayar da maganar auren mu!"Kuma wallahi cikin satin nan sai na nemo ko yar gidan uban waye yake wulakanta ni akan ta zan shirya komai domin wulaqanta ko wacece!"


"Hakan yayi kyau minal!"Yanzu bari na wuce ki kira su lami su baki abinci ki ci ki koshi ki kwanta ki huta kinji Durlin."


"Okay mum sai kin dawo ki gaisheta."

"Zataji."Sai nadawo ko gobe idan mun hadu kinsan idan kina bacci ba a tashinki!"


"To sai dai naji ki, adawo lafiya."


"To mumy ta ce,"ta wuce abin ta."


"Salman ne da abokinsA Jameel tsaye jingine da motarsa Bugati (Brown colour)a kofar gidan su Salma wanda akalla sunyi 20min a tsayen suna jiran fitowar salma."


"A hankali da sanyin jiki ta ke tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki"Da sallama ta kara so wurinsu da hijab dinta har kasa."Cikin ladabi ta gaishe su."


"Jameel ne ya amsa mata."Dan kuwa tuni salman ya Shiga duniyar tunani ba abinda yake son gani kamar salma da take tsaye agaban sa Kallonta yakeyi kamar madubi."


"Sun dauki wani lokaci ita da jameel suna tattaunawa yana bata baki dangane da yanayin soyayyar su da salman da matsalolin da suke fuskanta." daga bisani bayanin irin son da salman ke mata yaqara jaddada mata."A karshe wuri yabasu domin waqa abakin mai ita tafi dadi."


"Sun dauki mintuna kafin salma ya yiwa salma magana."


"Ya ce salma kin daina so na yanzu!? kin daina kulawa da ni!"kin daina amsa kirana!"Meyasa!"Shin kinsan yadda hankalina ya tashi!"Na shiga tashin hankali mai yawa saboda duk wata kafar da zamu ga juna kin kulleta!"Ko yanzu nasan alfarma ce nasamu kika fito!"Me nayi maki ne?"Salman ya ce cikin kunar rai yana kallonta!"


"Idon ta yacika taf da hawaye ta daga idonta ta dube shi kana ta ce,Salman ba kai min komai ba amma *BAK'AR* *AK'IDA* ce tayi komai arayuwar mu!"Ita ce ke kokarin gina Katangar karfe atsakanin mu!"Muyi hakuri ka nemi zabin iyayenka daidai kai!"Nima na samu iri na talaka na aura, kwarya tabi kwarya kowa ya tsaya in da Allah ya ajiye shi!"Ko yanzu Inna ce tabani umurnin in zo in gayamaka kabi zabin mahaifiyarka da umurnin ta domin tazo har nan tayi mana kasheki akanka dan haka nima iyayenah sun Gina Katanga atsakaninmu dole mu bar junanmu domin bin umurnin iyayenmu!"Ba domin ranmu yaso ba!"Kai hakuri Salman ka fita harkata....Kuka ne mai tsanani ya kufcewa Salma da gudunta ta shige gidan su ta rufe kofa."


"Salman awurin da salma ta barshi ya durkushe yana kuka!"Da hanzari jameel ya zo wurin tare da taso shi zuwa cikin mota yana bashi hakuri duk da bai San dalilin kukan nasu ba!"Amma yasan tatsuniyar gizo bata wuce k'oki."Nan take suka bar unguwar."




"Hello Nidal.."Kina jina?
"Eh

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login