Showing 30001 words to 33000 words out of 42080 words

Chapter 11 - Exiled Prince Book Four Complete Hausa Novel

Meerah   

24 Oct 2025

136

tafi , ka tashi mu tafiiiiiii "

wani dan nunfashi Malik ya sauke kafin ya sa hannu guda ya sauko shi da ga saman bayan shi ya na fadin " please my Prince , ka bari at least na gama aiki na , sai mu tafi "

ai ko ya na gama fadar haka Prince ya Zube a kassa ya na sakin kukan shagwaba , ya na harba kafafu har sai da sneakers din shi su ka fice , ya na fadin " Ni ice cream na ke so , mu tafi mu sayo ice cream " har da wasu hawayen iskanci ya ke kamar da gaske

sarai Malik ke jin shi amma ya share shi , dan ya saba da rigimar Prince , da ya tashi dauko momyn shi sai da ya wuce , gwara ya share shi , dan in ya ce zai biye mishi yanzu zai yi frog jump , ya san ba karamin aikin Prince ba ne ya ce sai ya yi frog jump sannan zai hakura da ice cream din , dama dama Princess ita ta dauko miskilancinsa , shiru da ita in har ba tabo ta ka yi ba , sai ka rantse ba ta cikin wajen
akwai wata rana da su ka taba fita da PRINCE su ka manta da ita cikin bedroom din ta , amma a haka su ka je su ka dawo ta na cikin bedroom din ta , ta na konce ta na barci

ya na a haka kawai ya ga Prince ya sa hannu ya ture laptop din shi har sai da ta fadi kassa ba tare da ya bar kukan shagwabar shi ba

cak Malik ya tsaya ya na zaro idanu , kamar ya tashi ya yi kuka shi ma ya ke ji dan jarabar Prince

wani dan karamin kukan kura ya yi kafin ya tashi a zafafe , ya dauki Prince ya juya ya na kallon kofar Kitchen ya na fadin " Cutie ! Cutie ! Cutie ! " ya ke kwalla mata kira da karfi

cikin nitsuwa na ga Inaya ta fito da ga kitchen din
Masha Allah , Gaskiya ba karamin kyau ta kara ba
ta cika ta yi bul bul abunta , da ga gani ta samu hutu , har wani haske ta yi kumatu sun fito , gaskiya US ta zauna mata
ta na sanye da wando palazzo pink colour , da wata t-shirt blue , amma da ga gani ta Malik ce dan ta so ta yi mata yawa

a haka har ta karaso cikin parlourn , a sanyaye ta ke fadin " baby , lafiya ka ke min irin wannan kiran ? "

mika mata Prince ya yi ya na fadin " rike yaron ki ! "

cikin rudu Inaya ta kai hannu ta karbi Prince da ke ta faman turo dan bakin nan nashi irin nata
ta na karbar shi ta juya ya dauki laptop din shi da ta fadi , da wayoyin shi , sannan ya juyo ya kalle ta ya ce " na bar muku gidan , na san sai kun kashe ni za ku huta , da ke da yaron ki ku na neman ku saka min hawan jini wlh , da daddare ban huta ba , da safe ban huta ba , gwara na tafi tun kafin ku kashe ni " ya na gama fadar haka ya juya ya nufi kofar fita parlourn ya fice

wata yar karamar dariya Inaya ta yi dan ta san yaron nata ya tsula tsiyar tashi ,
sai da ya fita sannan ta dawo da kallon ta saman shi ta na fadin " me kuma ka yi wa Daddyn naka ? "

cike da shagwaba Prince ya ce mata " Cutie , ni fa kawai na ce mishi ina son ice cream ne , shi ne ya yi fushi ya tafi , ni ke ce mishi ya dawo , na bar ice cream din , ina son zama tare da Daddyna " ya kai karshen ya na sakin kukan gaske wannan karan

ita dai ta tsaya ta zuba mishi ido ya na hawaye bibiyu , kamar ba shi ya tukarawa baban nashi ba har ya tafi , yanzu kuma ya na kuka dan ya tafi ,

ta tafi duniyar tunanin ta kawai ta jiyo Muryar Malik ya na fadin " wa kuma ya taba min babyna ? "
a tare ita da Prince su ka juya su ka kalli saitin kofar parlourn
ya na tsaye ya na sakin wani dan karamin murmushi , dama ba tafiya ya yi ba , laptop din shi ne ya kai cikin motar ya runo ashe ya manta file din shi , shi ne ya dawo zai dauka , ya jiyo Prince na kuka

da sauri Prince ya diro da ga jikin Inaya ya nufi Malik
ya na sa isa ko Malik ya sa hannayan shi biyu ya dauke shi , cikin sanyin murya ya ce " I'm sorry my Prince , bari mun tafi sayan ice cream din , now stop crying please , kai ma ka san ba na son ganin kukan ka "

wani dan karamin murmushi Prince ya saki kafin ya kai hannu ya fara goge hawayen shi , ya kontar da kan shi saman shoulder din Malik , ya lumshe idanunshi , da alamun barci ya ke ji ,

Inaya na ganin ya lumshe idanunshi ta san to na barcin ne su ka sauko mishi ,
" baby , ina ga barci ya ke ji , ka kai shi bedroom din shi yanzu ina zuwa " ta fada ta na juyawa ta koma kitchen

ba musu ya nufi stair ya Haye , kai tsaye bedroom din Prince ya shiga
bedroom din ta hadu gaskiya , komai na cikin ta blue ne , har gadon , da carpet , ga ta ko cike da kayan wassa , har da su play station , dan wani lokaci tare su ke game din su shi da Malik

kai tsaye saman gadon shi Malik ya kontar da shi , sannan ya zame jacket din shi , ya ajiye gefe , ya sauko ya manna mishi kiss saman forehead , kassa kassa ya ce " i love you my baby "

cikin magagin barcin nashi ya ce " i love you too my Daddy "

wani cool murmushi Malik ya saki kafin ya sake ce mishi " konta ka huta , in ka tashi sai mu tafi sayan ice cream , mu biya park , okay ? "

wani dan karamin murmushi Prince ya saki kafin ya gyada mishi kai , ya juya mishi baya ya kai hannu ya janyo Teddy din shi , ya rungume

janyo duvet Malik ya yi ya rufe shi har zuwa kirji , sannan ya sauko da ga saman gadon , ya kashe lamps din dakin , Sannan ya fito

ya na fitowa ya ci karo da Inaya taa shirin shiga dakin
da sauri ya sa hannu ya toshe mata baki ya yi baya da ita , su ka shiga nasu bedroom din , sannan ya meda kofar ya rufe ya sa mata security

cikin rudu ta ce mishi " lafiya ka min irin wannan janyowar ? "

a hankali ya tako ya tsaya gaban ta , sai dai ya kare mata kallo da kyau sannan ya kai hannu ya ja mata hanci ya na fadin " dubi don Allah yanzu kin bata min yaro da wannan rigimar taki "

hmmm , kamar dama jira ta ke kawai sai ta sakin mishi kukan shagwaba har da bubuga kafafu a kassa
bai ce mata komai ba kawai ya sa hannu ya yi sama da rigar ta ya fidda mata ita , ya hade bakin su waje guda ya fara kissing din ta

ai ba shiri ta yi tsit , ta na karbar sakon shi , nan take ita ma ta shiga mayar mishi da martani , ta zagayo da hannayanta a wuyan shi
a hankali ya yi baya da ita , su ka fado saman bed din su , ya sa hannu ya fara raba ta da kayan jikin ta , har sai da ya meda ta naked , sannan ya zabe bakin shi da ga cikin nata

bai dire shi ko ina ba sai saman nipple din ta , nan take kawai ya gama fita hayacin shi , specially yadda ya ke jin hannun ta saman kanshi duk ta gama birkice mishi lissafi
Ita kanta tuni tuni ta tafi , dan dama a kusa ta ke , ta yi tunanin janyowar nan da ya yi mata dan su buga game ne , wai sai ta ga ya ja mata hanci shi ya sa ta sakin mishi kukan shagwaba

😴😴😴 NI KAM BARI NA JUYA HAR KU GAMA NA DAWO , DAN ABUN YA FARA FIN KARFINA



β–ͺAFTER SOME HOURS πŸ’«


Misalin karfe 5 na yamma , a tare duk su ka shirya su ka tafi park , dan Malik ya san in ba su tafi ba tom Prince ba zai kyale shi ba , ita dai Princess cewa ta yi ba za ta je ba , ta zauna tare da maid din su , ba irin rokon da Malik bai yi mata ba su tafi , da ga karshe ta sakin mishi kuka, ba dan ya so ba ya hakura ya kyale ta

a haka su ka nufi park din Malik ke yawan kai Su , ba kowane ne ba sai park din da ya hadu da Aylan , kullum a zuciyar shi ya na tunanin zai sake ganin shi , amma tsawan shekara hudu yanzu kullum ya zo ba ya ganin shi har ya cire rai ma ,

bayan ya yi parking din motar su , su ka fito su ka shiga park din ,
shi dai prince tun da su ka shigo baki ya ki rufuwa , sai dariya ya ke , ita kuma Inaya ta biye mishi , da allamun na yarintar sun dawo mata

shi dai Malik kallon su kawai ya ke ya na murmushi

su na a haka kawai ya ga Prince ya kwassa da gudu ya nufi wajen wani me sayar da halawar auduga

da sauri Inaya ta bi bayan shi ta na fadin " Prince , yi a hankali don Allah kar ka bace mana "

bin bayan su Malik ya yi ya na kiran sunan Prince
shi dai Prince ko jin su ba ya yi dan halawar ta yi mugun shiga ranshi , sai da ya iso sannan ya tsaya ya na fadin " Uncle , ina son halwar nan " ya kai karshen ya na nuna mishi mai pink color

ya na gama fadar haka ya ji Nihal ta riko hannunshi ta na fadin " Prince , next time in ka na son abu ka fada min ba tserewa za ka yi ba , a ka je ka bace fa ? "

cikin yar shagwaba ya ce " i'm Sorry Cutie , please saya min halawa "

ya na gama fadar haka Malik ya iso wajen ya na fadin " Prince , why za ka tsere ? dubi yadda ka gajiyar da momyn ka "

wani dan karamin kukan shagwaba Prince ya yi mishi ya na fadin " ni halawa na ke so , pleaseeee " ya kai karshen ya na dan marairaice fuska

ya na rufe bakin shi Malik ya ji wayar shi ta fara ringing ,
hannu ya kai cikin aljihu , ya fiddo ta , sannan ya kai hannu cikin gudan aljihun ya fiddo bandir din dollars , ya mikawa Inaya ya na fadin " kar ku bar wajen nan , yanzu na dawo "

da to kawai ta amsa mishi kafin ta kai hannu ta karbi kudin
shi kuma ya juya , kai a sunkuye ya fara takawa ya nufi hanyar fita park din ya na latsa wayar shi

ya yi nisa kadan , kawai ya ji ya bugi mutun da karfi , har sai da ya saki wayar shi , ya yi gaba kamar ya yi tuntunbe sai dai bai fadi ba

wata yar karamar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya duka ya dauki wayar shi , kawai ya ga screen din ya tarwatse baki daya , ta mutu

wani dan karamin tsaki ya ja , kafin ya juyo ya na fadin " I'm sorry na....... "
ai maganar da bai kai karshen ta ba kenan ya dan zaro idanu



❀⚘ EXILED PRINCE ⚘❀

( LOVE MEETS POWER ) πŸ‘‘πŸ”₯




( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )




STORY & WRITTEN BY : MEERAH βš˜πŸ•Š


【THE ROYALTY LOVE β€πŸŒΉγ€‘



【 BOOK ________ 4πŸ“šβœβ€ 】





_______________________πŸ•ŠβœπŸ•ŠβœπŸ•ŠβœπŸ•ŠβœπŸ•ŠβœπŸ•ŠβœπŸ•Š______________________




ο½› P A G E ________ 21 & 22 βœπŸ’•πŸ”₯}






wani dan karamin Murmushi Aylan ya sakin mishi kafin ya ce " kai ma an koya maka tafiya ka na latsa waya ? " ya kai karshen ya na dukawa ya dauki tashi wayar shi ma

wata nanauyar ajiyar zuciya Malik ya sauke kafin ya ce " General , sai yau Allah ya sake hada ni da kai "

" Kennan nema na ka shiga yi " Aylan ya fada ya na meda wayar shi cikin aljihun shi , ya juyo da kyau su na fuskantar juna

wani dan murmushi Malik ya yi kafin ya ce " Eh , dole na nema ka "
cikin nitsuwa Aylan ya katse shi da cewa " Why ?"

" akwai tambayar da ta tsaya min a rai tsawan shekaru , kuma na san kai kadai za ka iya ba ni amsar ta , amma sai yau Allah ya sake hada ni da kai "

wani murmushi mai dan sauti Aylan ya yi kafin ya nade hannayanshi a kirji, ya daga mishi gera guda ya na fadin " me ya sa ban fada maka a na neman ka a Saudiya ba ko ? "

dan zaro idanu Malik ya yi ya na kallon shi , ta ya a ka yi ya san tambayar da zai yi mishi kenan

ya yi nisa duniyar tunanin shi ya jiyo Muryar Aylan ya na fadin " maganar ta na da tsawo "

da sauri Malik ya katse shi da cewa " please tell me "

" shikenan tun da ka matsa , it's true na san

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login