Showing 9001 words to 12000 words out of 42080 words
kashe shi ba kai tsaye , dole ka fara kawo karshen sihirin shi , Idan ba haka ba ba zai mutu ba , ni kai na ban san inda ya boye karfin sihirin shi ba , da na je na kawo karshen shi , zabi guda gare ka , da ka samu dama ka cire mishi kai kawai ta haka ne kawai zai mutu idan ba haka ba tashin hankali da za ka gani da ga baya ya karfin tunanin mai tunani "
ta na gama fadar haka ta sauke wata yar karamar ajiyar zuciya , ta ja wani dogon nunfashi kafin ta lumshe idanunta , ta sake bude su a hankali ya ga sun koma dai²
a hankali ta juyo ta kalle shi ta ce " baby me ya faru ? "
wata nanauyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce " ba komai "
wani dan karamin murmushi ta saki sai kuma ta tsuke fuska lokaci guda ta na fadin " sai yanzu ka dawo , ni na yi fushi ma da kai " ta kai karshen ta na kauda kai
" sorry Cutie , na tafi yin wani aiki ne " ya fada cikin sanyin murya
turo dan bakin nan nata ta yi ta na fadin " baby yunwa na ke ji , tun tafiyar ka ban ci komai ba "
" shikenan , me ki ke ki ci ? "
da sauri ta ce mishi " irin abincin da ka ke min a US " ta fada ta na sakin wani dan karamin murmushi
gyada mata kai ya yi kafin ya ce " okay , jira ni ina zuwa "
da to kawai ta amsa mishi , da ga haka ya tashi ya nufi kitchen ya shiga
da kallo ta raka shi har sai da ya shiga sannan ta saki wani dan karamin murmushi
sai da ya dauki one hour a cikin kitchen din kafin ya fito ya na rike da wani tray
kai tsaye gabanta ya karaso ya zauna a kassa saman carpet , sannan ya ajiye tray din a gaban shi ya na ce mata ta sauko
ba musu ta sauko kassa su na fuskantar juna , ya fara ba ta abincin da kan shi
sai da ta kammala sannan ya dauki tray din ya mayar da su kitchen sannan ya dawo parlourn
ta na zaune saman sofa ya tardo ta , ta shafar cikin ta
a hankali ya karaso wajen ta ya zauna ya na fadin " yanzu tashi ki je ki konta "
shagwabe mishi fuska ta yi ta na fadin " ba tare za mu kwana ba ? "
a hankali ya girgiza mata kai allamun a'a
shiru ta yi ta na kallon shi babu ko kiftawa
sai da ta dauki lokaci kafin ta ce " baby , amma akwai abun da ke damun ka ko ? "
" me ki ka gani ? " ya fada a sanyaye
" kawai na ga yanayin face din ka ya sauya ne "
" ba zan miki karya ba , ina cikin damuwa , ba kadan ba , amma duk lokacin da na tare da ke na kan ji damuwata ta tafi , please don't leave me , kar ki tafi ki bar ni "
wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta rungume shi ta na fadin " mutuwa ce kadai za ta raba ni da kai "
a hankali ya zagayo da hannayanshi a bayanta ya rungume ya na sauke ajiyar zuciya a hankali
❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
STORY & WRITTEN BY : MEERAH ⚘🕊
【THE ROYALTY LOVE ❤🌹】
【 BOOK ________ 4 📚✍💌 】
_______________________♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡______________________
{ P A G E ________ 7 & 8 ✍💕🔥}
Sai da ya dauki lokaci rungume da ita a haka kafin ya raba jikinsa da nata ya na ce mata " yanzu tashi ki je ki konta dare ya yi "
marairaice mishi fuska ta yi ta na turo dan bakin nan nata ta ce mishi " please baby tashi mu je ni ba zan iya kwana ni kadai ba " ta kai karshen idanun ta na cikowa da ruwa kamar za ta yi mishi kuka
a hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce " shikenan , tashi mu je " ya fada dan ya san halin ta yanzu za ta yi zaune ta aza mishi kuka duk sai mutanan part din sun fito , gwara ya yi abun da ta ke so ko ya samu ya rabu da ita cikin lalama
wani kyawatencen murmushi ta sakin mishi kafin ta mike tsaye ta na turo katon cikinta
a hankali shi ma ya mike ya riko hannunta su ka shiga corridor , ya shiga bedroom din ta
cikin sa'a ko babu kowa
su na shiga ya saki hannunta ya juya ya rufe kofar ya saka mata security kafin ya juyo gare ta ya ce mata " let's go sleeping , i'm very tired "
wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce mishi " baby , mu je na yi maka tausa mana "
" uhm , da ni da ke wa ya fi bukatar tausa da wannan katon cikin naki "
turo mishi dan bakin nan nata ta yi kafin ta nufi gadon ta Haye ta zauna a tsakiya ta yi irin zaman nan na bokaye
shi dai bawan Allah ya na shan rigima , a ka je ta haifi mace kuma ta dauko wannan rigimar ta ta sai ya dinga bar musu gidan da wannan ya ya kare bare ya samu karama irin ta ya san kashe shi kawai za su yi
wata boyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya tako a hankali ya zauna bakin gadon , ya kai hannu ya cire sneakers din shi
sannan ya ida Hayewa ya jingina bayan shi a jikin forehead din gadon ya na kallon bayan ta sai turo baki ta ke
slowly ya dago hannu ya daura saman bayan ta ya fara yi mata tafiyar tsutsa da yatsar shi tsakiyar gadon bayan ta
wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce mishi " ni ka kyale ni fushi na ke da kai "
ba tare da ya daina ba ya ce mata " da gaske za ki iya fushi da ni Cutie ? "
dan jinkirtawa ta yi kafin ta ce " gaskiya ba zan iya ba , sai dai cikin wassa "
cikin sanyin murya ya ce mata " i'm sorry my Cutie "
a rude ta juyo ta na kallon shi ta ce " baby hakurin me ka ke ba ni ? "
" abun da na yi miki lokacin da mu ke US "
girgiza mishi kai ta yi a hankali kafin ta matso baya ta jingina bayan ta a jikin forehead din gadon sannan ta ce mishi " baby ni ba ka yi min komai ba "
da sauri ya ce mata " no , na san na cutar da ke dayawa , kin zubar da hawayen ki saboda ni , na saka ki kukan da ban taba tunanin za ki yi shi ba a rayuwar ki , ga shi kuma nine silar wannan kukan , ban san abun da ya sa na kaurace miki a lokacin da ki ka fi bukata ta a kusa da ke , duk lokacin da na ga murmushi a face din ki sai na tuno wannan lokacin da ki ke zubar da hawayen ki , ban san ya a ka yi ki samu gourbin yahe min cikin zuciyar ki "
wani cool murmushi ta saki kafin ta riko hannunshi , ta kontar da kan ta saman shoulder din shi ta ce mishi " because i love you , kuma na san duk abun da ka yi ka yi shi ne saboda ka na so na kuma ba ka son rabuwa da ni , amma komai ya wuce , saboda ga shi yanzu babyn mu ya girma kuma ba abun da ya same ni "
cikin nitsuwa ya katse ta da cewa " no , har yanzu ina jin tsoro cikin zuciya ta , in a ka je na rasa ki kin san ba zan iya ci gaba ba da rayuwa kashe kai na kawai zan yi "
slowly ta dago kan ta , ta kalli face din shi na dan lokaci kafin ta ce " idan ka tafi wa zai kula da babyn mu ? Diya ? Ammie , Aunty RIANNA , ? momy ? ka na ganin dukkan su soyayyar da za su nunawa babyn mu za ta kai taka ? please kar ka tsane shi a kan laifin da ba shi ya aikata ba , ko da kuwa wani za ka yi wa hukunci ni za ka yi wa tun da ni na ki yarda mi zubar da cikin " ta qarashe maganar idanun ta na cikowa da ruwa
slowly ya girgiza mata kai kafin ya ce " no , laifi na ne , da a ce ban kusance ki ba da ba za ki samu cikin nan ba , da duk wannan ba ta faru ba "
" baby , ka na nufin ka na nadamar duk lokacin da ka ke kusanta ta ? " ta fada a sanyaye kamar za ta yi mishi kuka
da sauri ya juyo ya daura hannun shi saman face din ta ya ce " never , ko so guda , asali ma wadanan lokutan su ne ma fi mahimanci a cikin rayuwa ta , kuma su ke lokutan da su ka fi ko wane farin ciki a cikin rayuwa ta saboda a lokacin ne mu ke zama abu guda ni da ke , na ji kamar babu kowa a duniyar nan sai ni , sai ke "
wani cool murmushi ta sakin mishi kafin ma ta ce mishi wani abu ya matso ya cabko lips din ta ya fara kissing din ta ya San in har ba hakan ba ya yi ba zai samu ta yi barci ba har ya tsere
wata nanauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta lumshe idanunta ta fara biye mishi
a hankali ya sa hannu ya matso ta jikinsa kafin ya zame bakin shi da ga cikin nata slowly
murya cen kassan makoshi ya ce mata " mu konta please , barci na ke ji "
a hankali ta gyada mishi kai ta na sakin murmushi kafin ta gyada mishi da ga haka ta gyara ta konta
shi ma ya konta ya janyo duvet ya rufe su har zuwa kugu kafin ya kai hannu saman cikinta ya fara shafawa a hankali
wata nanauyar ajiyar zuciya ta sauke ta lumshe idanunta ta na jin wani sanyi cikin zuciyar ta
ya na tsaka da shafa cikin ta kawai ya ji kamar cikin ta ya buge shi kadan a hannu
gaskiya ya dan razana har zaro idanu ya yi kafin ya juya ya kalli face din ta , ta lumshe idanunta ta na sakin wani cool murmushi
a hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ci gaba da shafa cikin ta , a hankali a hankali har barci ya yi gaba da ita shi kuma ya tsare ta babu ko kiftawa
ya na jin barci ya dauke ta ya janye hannun shi a hankali da ga saman cikin ta kafin ya mike zaune ya sauko da kafafun shi
ya kai hannu ya janyo sneakers din shi ya meda kafin ya tashi tsaye a haka ya fara takawa ya nufi kofar fita dakin ya fice abun shi
ya na fitowa parlour ko ya tardo mama zaune ita kadai kamar aljana dan ba karya ya tsorata da ganin ta
a hankali ya karaso tsakiyar parlourn ya tsaya , cike da kula ya ce mata " mama , wani abu ya faru ? ya na ga ki na zaune a ke kadai ? ko wani abu ki ke bukata na kawo miki ? "
a hankali mama ta gyada mishi kai ta na murmushi ta ce " ba komai , kawai ina son yin magana da mahaifin su , amma Abyad ta ki hada ni da shi "
cikin rudu ya matso ya na fadin " mama , ki na lafiya kuwa ? "
" Eh ina lafiya , ko dan na ce ina son magana da malam ne ka tsorata , kar ka ji tsoro ina iya yin magana da mutanan da su ka mutu in har ruhin su bai yi nisa ba , haka ita ma Inaya ta na iya yi , idan Abyad ta janyo ruhin wanda mu ke son yi wa magana , amma yau sam ta ki yarda ta yi abun da na ce "
a dan razane Ya ce mata " mama , ni wlh wannan abun duk ya fi karfin tunani na kawai ina shanye wa ne "
a hankali ta gyada mishi kai kafin ta ce " na sani kar ka damu za ka iya tafiyar ka "
ba musu ya fara takawa ya nufi kofar fita part din
ya yi dan nisa ya jiyo Muryar mama ta na kiran shi
cak ya tsaya ya juyo a hankali ya na tambayar me ya faru
sai da ta saki wani dan karamin murmushi kafin ta ce " akwai sakon da malam ya ba ni na fada maka amma kullum sai na manta "
" wani sako kuma mama ? "
" ya ce ya gode da amanar shi da ka rike , ya na matukar alfahari da kai kuma ya na rokon Allah ya sa ka samu abun da ka ke so tare da matar ka ya na fatan za ku samu zuri'ar da za ku yi alfahari da ita kamar yadda ya ke alfahari da ku "
shi dai kawai ya tsaya ya na kallon ta ya ma rasa me zai ce mata , kawai ya gyada mata kai kafin ya juya ya fice parlourn ya na juya abun da ta fada mishi cikin kwakwolwar shi
ya na fitowa kai tsaye hanyar garden ya nufa , ya na zuwa ya tardo Diya zaune shi kadai kamar aljani
babu ko tsoro Malik ya karaso wajen shi ya zauna ya na fadin " me ka ke yi a nan ? ina ka baro babys din ka ? "
wani dan karamin murmushi Diya ya saki kafin ya ce " sun yi barci shi ya sa na fito na dan huta , takwaran naka mugun jaraba ce da shi sai mutane sun yi kwana ya tashe su da kuka "
" uhm " Malik ya fada kafin ya lumshe idanunshi ya tafi duniyar tunanin shi
kallon shi Diya ya tsaya ya na yi ya na sakin wani dan murmushi
cen kuma sai ya ce " ka sani na yi kewar ka sosai , kullum in na yi sallat sai na saka ku kai da baby cikin addu'a , na godewa Allah da babu abun da ya same ka "
ba tare da ya bude idanun shi ba ya ce " ni ma na gode da ka ceci ahalina a lokacin da su ka fi bukata ta , na san da ban tafi ba da duk wannan abun bai faru ba , wlh na yi nadamar tafiya "