Showing 33001 words to 36000 words out of 42080 words
da a na neman ka , kuma har da ni cikin neman ka , har kyauta na bayar ga duk wanda ya samo ka , lokacin da na ji labarin halin da familyn ka ke ciki na yi kokari wajen ganin na taimaka musu saboda General Abdellah abokin mahaifina ne , na so na tura jami'an tsaro na Saudiya dan sauke Malik da ga kujerar , sai da ga baya General ke kwatanta min in na yi haka kamar na haddasa yaki ne tsakanin Saudiya da US , nemo ka ne kadai solution din mu , that's why ma na bayar da kyautar ga wanda zai samo ka dan ka koma Saudiya in da a ka fi bukatar ka , a ranar da mu ka hadu na ga damuwa sosai a tattare da kai , ga kuma halin da familyn ka ke ciki , ba zan so na kara maka wata damuwar ba , that's why na yanke shawarar yin shiru , na fara tambayar ka abun da ke damun ka , na ga in zan iya taimaka maka , na san indan ka samu nitsuwa kai da kanka za ka nemi sanin halin da familyn ka ke ciki "
wata nanauyar ajiyar zuciya Malik ya sauke , sai da ya dauki lokaci kafin ya ce " na gode , i don't know how zan yi maka godiya "
cikin nitsuwa Aylan ya katse shi da cewa " please , ba sai ka yi min godiya .... "
" no , in ban yi maka godiya ba na san sai Allah ya kama ni , ko ba komai kai ka kawo nitsuwa cikin rayuwa ta " ya kai karshen ya na rungume Aylan ba shiri
wani dan karamin murmushi Aylan ya yi kafin ya rungume shi shi ma , ya na dan bubuga bayan shi a hankali
sun dauki lokaci a haka kafin su raba jiki
da murmushi a face din shi Malik ya ce " please , mu je na gabatar maka da familyna "
" ka ce ba kai kadai ba ka zo wannan karan ? "
wata yar karamar dariya Malik ya yi ya na gyada mishi kai ya ce " yeah , ni da Cutie da Prince , my son "
gyada mishi kai Aylan ya yi kafin ya ce " okay , ina jiran ku "
gyada mishi kai shi ma Malik ya yi kafin ya juya da sauri ya koma wajen da ya baro su Inaya
ya janyo su su ka dawo wajen da su ka bar Aylan
sai dai ya na dawo ya neme shi sama da kassa ya rasa , ya kalli hagu , ya kalli dama babu Aylan babu mai kama da shi
wani dan murmushi Malik ya saki kafin ya cewa Inaya " ina ya tafiyar shi , mu tafi kawai "
da to kawai ta amsa mishi , shi dama PRINCE bai san abun da ke faruwa ba ya na ta shan halawar shi ,
sai wajajen Magriba sannan su ka baro park din , shi ma sai da su ka biya pastery su ka sayo cake da ice cream sannan su ka koma gida
ko da su ka koma , Malik ya yi sauri ya yi wanka ya yi alwala ya fice ya tafi mosque
Inaya kuma ta ja Prince ta yi mishi wanka , kafin Malik ya fito ita ma ta shirya shi dan kullum tare su ke tafiya mosque
haka su ka tafi su ka bar ta ita kadai cikin gidan , ita ma wanka ta yi ta yi alwala sannan ta fito ta gabatar da sallar ta ,
sai bayan sallar isha Malik da Prince su ka dawo cikin gidan
βͺWASHE GARI β
β
βͺPRINCE πβ€
a hankali ya ke sauko stair , ya na tsalle ,
ya na sanye da wani Trouser black color , da wata sweater Red color , da sneakers farare a kafafun shi , duk in ya yi tsalle sai gashin kan shi ya yi sama
ya na gama sauko stair din Malik ya shigo parlourn ya na sallama
Prince na ganin shi ya nufe shi da gudu ya na fadin " Daddy , tun dazu fa na ke jiran ka , har na yi fushi " ya fada cike da shagwaba
a hankali Malik ya sa hannu ya dauke shi ya na fadin " I'm sorry my Prince , tell me kun gama shiryawa mu tafi ? "
da sauri Prince ya ce " yeah , kai kadai mu ke jira , na matsu na ga Ammie , da mamie , da mama , da Uncle " ya fada cike da shagwaba
( hmmm , ko da ga ina ya dauko wannan shagwabar ? π€π€ )
" okay , where is your mom ? " Malik ya fada
" wait " Prince ya fada kafin ya juya ya kalli Stair ya ce " Momyyyyyyyyy ! " ya fada da mugun karfi sai da Malik ya lumshe idanunshi ya na fadin " Prince slowly mana , ka fasa min kunne "
ya na gama fadar haka Inaya ta fara sauko stair ta na sanye da wata Abaya fara kal mai mugun kyau an yi mata zanen flower kamar rainbow , ta yafa veil din ta fari shi ma , ta na sanye da wasu sneakers pink color a kafa , ta na rataye da wata yar bag pink color ita ma
ta na rike da hannun Princess , gaskiya babyn ta hadu kamar na sace ta na gudu , fara kal da ita har ma ta so ta fi Prince haske , sak balarabiya , ta na kama da Malik kamar an tsaga kara , har idanunsa Hazel , kamar dai Prince
ta na sanye da wata gown pink color har kassa , sai wata yar jacket white color , mai mugun kyau , fuskarta a daure kamar dai ta Malik a baya , sai ka ce ba ta iya dariya ba
tun da ta fara sauko stair Malik ya tsare ta da ido babu ko kiftawa , sai magana prince ke yi mishi amma ba ya jin shi
a hankali Prince ya kai hannu saitin fuskar Malik ya kyasta mishi yatsu ya na fadin " Daddy , tun dazu ina maka magana ka kyale ni , sai kallon momy ka ke kamar ba ka san ta ba "
a hankali Malik ya sauke ajiyar zuciya dai'dai lokacin da Inaya ta karaso gaban shi ta na fadin " mu tafi ko ? "
gyada mata kai Malik ya yi a hankali ya na murmushi kafin ya riko hannun Inaya , ya juya su ka fita parlourn , su ka fito harabar gidan ,
su na fitowa sai saman motar Malik , kai tsaye ya budewa Inaya wajen mai zaman banza , ta shiga sannan ya daura Princess saman kafafunta , ya rufe motar
ya zagayo ya bude wajen driver ya shiga tare da Prince ya zaunar da shi saman cinyoyinshi ya yi tukin a haka har su ka bar gidan su ka nufi hanyar Airport
β€β E X I L E D P R I N C E ββ€
π₯π ( LOVE MEETS POWER ) ππ₯
ππ ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) ππ
STORY & WRITTEN BY : MEERAH βπ
γTHE ROYALTY LOVE β€πΉγ
γ BOOK ________ 4 πβπ γ
_______________________πβππβππβππβπ______________________
ο½ P A G E ________ 23 & 24 βππο½
γ THE LAST PAGE π€§β€π γ
βͺDAULAR SAUDIYA ππ₯
zaune MALIKAT AL'UMU ta ke cikin parlourn tare da MALIKAT INAS sai murmushi su ke saki
su na a haka RIANNA ta shigo ta na sallama ta na fadin " Ammie , momy mu tafi sauran ten minutes jirgin su ya sauka " ba ta jira amsar su ba ta juya ta fice da sauri ta na sakin murmushi
a tare MALIKAT INAS da MALIKAT AL'UMU su ka fito part din , su na fitowa sai saman wasu motoci a jere bakin part din , a tare su ka shiga motar da ke gaban su , su na shiga motocin su ka tada su ka bar masarautar da mugun gudu su ka nufi airport
a jere motocin su ka shiga airport , kai tsaye wajen saukar jirgi su ka nufa , sannan su ka yi parking ,
daya bayan daya su ka fara sauko motocin , Diya da Nesrine su ka fito da ga cikin motar su tare da Junior din su
RIANNA kuma ta fito da ga cikin motarta tare da mama da MALIKAT HOUDA
MALIKAT AL'UMU da MALIKAT INAS kuma cikin mota guda
sannan Abdoul da Tesnim su ka fito cikin mota guda tare da wata kyakyawar yarinya a shekaru ba za ta wuce 3 or 4 years ba , kyakyawa ce gaskiya kamar an tsaga kara da Abdoul dan ta na kama tak da shi , sai dai ta dauko farin Tesnim dan kamar ka taba jini ya fito ta ke har wani ja ta yi
ta na ganin MALIKAT AL'UMU ta nufe ta da gudu
wani cool murmushi MALIKAT AL'UMU ta saki kafin ta durkusa ta dauki yarinyar nan ,
a hankali duk su ka karaso wajen motar su MALIKAT AL'UMU su ka tsaya
da sauri MALIKAT HOUDA ta ce " wai har yanzu ba su iso ba ? "
wata yar karamar dariya duk mutanan wajen su ka yi kafin Diya ya ce " mamie , mu ma duk mun matsu mu gan su "
har ta bude baki za ta yi magana su ka jiyo karar jirgi
a tare su ka kai kallon su wajen da su ka jiyo sautin su na fadin Alhamdoulilah cikin zuciyoyinsu
a hankali jirgin nan ya sauka , ya tsaya ya na fuskantar motocin su
sai da ya yi two minutes a haka kafin kofar jirgin ta bude a hankali
a tare Malik da Inaya su ka fito da ga cikin jirgin Malik ya na dauke da Prince duk jikin shi ya yi sanyi allamun barci ya ke
a tare duk su ka nufe su su na yi musu barka da zuwa , da sauri MALIKAT INAS ta kai hannu ta karbe shi nan ta ga ashe barci ya ke , amma duk da haka sai da ta karbe shi , MALIKAT AL'UMU kuma ta karbi Princess hannu Inaya
da ga haka su ka shiga rungumar juna , specially Diya , da ya rike Malik sai da RIANNA ta shiga ce mishi ya sake mata dan uwa ita ma ta rungume shi , ita dai Inaya tun da ta rungume mama ba ta sake ta ba har kowa ya hakura ya bar ta dan sun San yadda kewar uwa ta ke
da ga su ka shiga motocinsu su ka bar airport din su ka kama hanyar Daular Saudiya
ko da su ka isa kai tsaye Diya ya wuce da Malik building din shi tare da Abdoul
MALIKAT INAS kuma ta tafi part din su da Prince tare da MALIKAT AL'UMU da RIANNA da Tesnim
Inaya kuma ta bi mama tare da Nesrine su ka nufi part din MALIKAT HOUDA tare da Junior
βͺMALIK
tsaye ya ke a cikin parlourn part din shi a floor na uku sai bin wajen ya ke da kallo kamar bakwon shi
ya na a haka ya jiyo Muryar Diya a bayan shi ya na fadin " mu tafi ka yi wanka , ka huta , amma gaskiya abokina US ta zauna maka , ka na cen ka na shan dadinka ka kyale ni nan da aiki "
wani dan karamin murmushi Malik ya yi ya na fadin " ai ni zuwan tsaye na muku , dan gobe zan yi gaba da Cutie " ya kai karshen ya na fara takawa ya nufi corridor
cikin rudu Diya ke ce mishi " ban gane ? "
ko sannu Malik bai ce mishi ba ya shige corridor
sai da ya shiga sannan Diya ya juyo ya kalli Abdoul da ke tsaye gefe ya ce " har yanzu dai na miskilancin nan su na nan "
wata yar karamar dariya Abdoul ya yi ya na fadin " ai miskilanci a jininshi ya ke , ba zai taba fita ba , ba banza Allah ya hada shi da wadda ba ta iya rufe bakin ta ba "
" hmmmm , mu tafi mu ba shi wuri " Diya ya fada ya na nufar lift
ba musu Abdoul ya bi bayan shi su ka baro part din , dan Diya nashi part din daban ya ke , ko so guda bayan tafiyar Malik bai taba shiga building din ba , saboda wannan building musaman na Malik nz , shi ya sa ya yi nashi part din daban , amma mai floor biyu , sai in Malik na shirin zuwa sannan ya ke sa a bude shi a gyara part din , amma floor na hudu sai Malik ya zo da kan shi ya bude shi dan babu wanda ya san ya ma a ka rufe shi bare a bude sai Malik , dan a ganin shi sirrin da ke cikin wannan floor na nashi ne shi kadai , saboda a nan ne ya ga dare mafi mahimanci a rayuwar shi , a nan ne ya zama cikaken mutum dan haka ba wanda ke da damar shiga floor din , idan kuma za su koma US ya sake rufe shi , bayan shi da Inaya ba wanda ya taba hayo shi , har prince
kai tsaye Malik kuwa bedroom din shi ya nufa , ya na isa ya wuce kai tsaye Toilet
sai da ya share good one hour a ciki kafin ya fito daure da towel a kugunshi
ya na fitowa idanun shi su ka sauka saman ta , ta na zaune tsakiyar gado , ta jingina bayan ta a forehead din gadon ta na rike da wayar shi ta na latsawa
wani cool murmushi ya saki kafin ya karaso wajen gadon , ya zauna a baki ya kai hannu ya kwace wayar shi ya na fadin " ta ya a ka yi ki ka san ina nan ? " ya kai karshen ya na ajiye wayar shi saman bedside drawer
wani kyawatencen murmushi ta sakin mishi ta na fadin " tracker na saka maka a jiki, ba ka sani ba ? "