Showing 18001 words to 21000 words out of 42080 words

Chapter 7 - Exiled Prince Book Four Complete Hausa Novel

Meerah   

24 Oct 2025

139

saman forehead

sannan ya dago ya kalli Doctor ya ce " ba na son maganar nan ta fita da ga dakin nan , kar Wanda ya san MALIKAT Triplets ne ta haifa , ko ita kanta kar ku fada mata , ki dauki babyn cikin sirri ki bizine shi "

dan zaro idanu ta yi ta na fadin " ran ka shi dade , ba za a yi mishi jana'iza ba ? "

bai ce mata komai ba ya juya a hankali ya kontar da babyn saman gadon da ke bayan shi sannan ya juyo ya kali doctor ya ce " zan yi mishi jana'iza , amma ba na son kowa ya san da maganar nan , da ga ni sai ku ukun nan , na roke ku don Allah , dan son annabi kar ku fitar da maganar nan , na san ba za ta iya jure wa ba idan ta ji wannan maganar , ni na godewa Allah ma da ba ta cikin hayacin ta ya shigo duniya , na roke ku don Allah kar ku bari wani ya san wannan maganar , ya zama sirrin mu na mudu hudun nan sai Allah "

a hankali Doctor ta gyada mishi kai kafin ta juya ta karbi dayan babyn ta ce " in sha Allah , Twins ne MALIKAT ta haifa , nurse ? "

a tare su ka ce " twins ne ta haifa "

wata boyayyar ajiyar zuciya Malik ya sauke , ya na shirin magana Doctor ta riga shi cewa " za ka rike shi , ko mu tafi ? "

bai ce mata komai ba ya dago hannayan shi a hankali ya mika mata
ba musu ta daura mishi babyn a sama
nan take ya kara sautin kukan shi ya na wuntsila Kafafu kadan ya kubcewa Malik
da sauri Doctor ta karbe shi ta na fadin " Nurse , ku je a yi wa mai martaba dress , ya samu rauni a jikin shi , ku kontar Da hankalin ku , zan kula da komai " ta fada ta na juyawa da babyn hannunta , gudar nurse din ta na rike da namijin

sai da ya sunkuyo ya mannawa Inaya kiss a saman forehead din ta , sannan ya kai bakin shi saitin kunnen ta ya yi mata rada kafin ya mike ya juya
ya bi bayan nurse din nan su ka baro dakin , ya ma kassa kallon dayan babyn nashi dan ya na jin zafi cikin zuciyar shi ba kadan ba , amma ba komai haka Allah ya so kuma duk abun da ya yi dai'dai ne



❀⚘ EXILED PRINCE ⚘❀

( LOVE MEETS POWER ) πŸ‘‘πŸ”₯




( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )




STORY & WRITTEN BY : MEERAH βš˜πŸ•Š


【THE ROYALTY LOVE β€πŸŒΉγ€‘



【 BOOK ________ 4 πŸ“šβœπŸ’Œ 】





_______________________β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘______________________




ο½› P A G E ________ 13 & 14 βœπŸ’•πŸ”₯}



su na fitowa kawai ta ga Malik ya yi gaba abun shi , ya nufi su MALIKAT AL'UMU da ke zazzaune sun yi zugum

su na ganin shi su ka mike a tare su na tambayar ta sauka lafiya
gyada musu kai kawai ya yi kafin ya ce " za ku iya komawa part din ku , doctor ta ce ta na bukatar hutu " ya kai karshen ya na shirin takawa

da sauri MALIKAT AL'UMU ta taro shi ta na fadin " me ta samu ? mace ko namiji ? "
slowly ya juya ya kalli MALIKAT INAS , cikin sanyin murya ya ce " Nayel & Nailah "

wani kyawatencen murmushi MALIKAT INAS ta saki har hawaye na zubo mata
da sauri RIANNA ta ce " Akhie Twins ne ta samu ? "

gyada mata kai ya yi a hankali kafin ya juya ya fice word room din ran shi fari tas kamar an yi mishi albishir da gidan Aljanna

a haka su ma su MALIKAT INAS su ka baro Word room din , kowace ta nufi part din ta na asali

shi ma Diya da Nesrine su ka koma part din su , haka Abdoul da Tesnim
Rafik kuma ya nufi fada ya bude ta , ya kira duk wani na fadar ya fada mishi ya dawo Ranar Friday za a sake nada Malik Nawfel Hicham Bin Jaabar

bangaran Malik kuwa kai tsaye part din MALIKAT HOUDA ya koma ,
babu ko sallama ya shigo parlourn , nan ya tardo ta zaune , sai faman addu'a ta ke yi
ta na ganin shi ta sauke ajiyar zuciya ta tashi da sauri ta nufe shi ta na fadin " masoyina , ba abun da ya same ka dai ko ? Allah na gode maka "

wani dan karamin murmushin geffen fuska ya sakin mata kafin ya ce " kin ga , ki daina kira na da masoyinki , so ki ke papi ya tardo ni , ya ce na kwace mishi matar shi "

wata yar karamar dariya ta saki ta na fadin " kai dai ka sani , mara kunya kawai "

" shikenan , bari na yi wanka , zan yi miki albishir me dadi "

" shikenan , ina jiran ka , mai martaba " ta fada cikin zolaya
bai ce mata komai ba ya nufi corridor ya shige bedroom din Inaya ke ciki , kai tsaye toilet ya wuce

bai ce mata komai ba ya nufi corridor ya shige bedroom din Inaya ke ciki , kai tsaye toilet ya wuce dan ya yi wanka
jim kadan ya fito sanye da bathrobe
bed din ya nufo ya zauna , ya zauna a baki ya kai hannu ya bude bedside drawer ya fido A box

sannan ya ajiye a sama , sannan ya bude ya fiddo wata yar takarda
hannu ya sa ya rabata gida biyu , ya fido wata yar karamar allura irin ta dinki ta na da wani siririn zare blue

a hankali ya kai allurar nan wajen yankar da Aymane ya yi mishi , ya fara yi wa kanshi dinki , ya na lumshe idanunshi , ya na cije lips din shi na kassa dan ba karamin zafi a dakwai ba
amma a haka ya yi wa kan shi dinki , ya yi dressing wajen , sannan ya tashi ya nufi dressing room

jim kadan ya fito sanye da Trouser black color , da T-shirt sky blue , sai wasu sneakers farare a kafafun shi , ya daure wanan smooth hai din nashi a baya , sai tashin qamshi ya ke , sannan ya nufi kofar fita bedroom din ya fito

kai tsaye part din ya baki daya ya baro , ya nufi hanyar Fada
bakinshi da sallama cen kassan makoshi ya shigo Fadar , nan ya tardo duk mutanan fadar shi , su na zaune
su na ganin shi kowane ya saki murmushi ya na mikewa tsaye su na gaishe shi cike girmamawa

sai da ya karaso tsakiyar fada sannan ya juya ya kalli side din su
tsayawa ya yi ya kare musu kallo na dan lokaci kafin ya ce " na ji dadin ganin ku cikin koshin lafiya "

a tare duk su ka saki wani kyawatencen murmushi su na fadin suma sun ji dadin ganin shi a raye

dan sunkuyar da kai ya yi kafin ya dago ya ce " okay , zan so ku fara shirye shiryen nada sabon Malik ranar Friday , sannan Dalil ( sabon Sarkin bayi ) zan so ka mayar da bayinka part din su , sannan gobe ka sa su je part din Malik su kwashe duk kayan da ke ciki za a zuba sabi , duk wani abu da ke bukatar gyara a cikin masarautar nan har ma wajen ta kawai ku aiwatar , kar ku damu da adadin kudin za a kashe , Idris ( shi ne sabon me kula da dukiyar Daular ) ka bude bankin masarautar , na ba da dama a fitar da kudin da su ka dace dan ganin an kyara masarautar , amma abu na farko da na ke son ku fara shi ne cire min wadanacen banzan status da a ka kafa min bakin Daula , General Abdallah , duk mutanan Fadar Aymane da ke hannun jami'an ka , ku yi executed din su kawai , ita kuma Hafsat a mayar da ita wajen mahaifiyar ta , sannan ku shirya min zama da yan JARIDA a matsayin Mr president ba Malik ba ran monday "

( Idan ba ku manta ba tun farko na ce muku Malik shi ne shugaban kassar Saudiya , kuma duk wata maganar administration a hannun shi ta ke , hakan na nufin shi ne sarki kuma president din kassar Saudiya , mutanan Fadar shi kuma duk yawwancin su ministers ne )

" an gama ya shugaba " su ke fada a tare sannan su ka shiga jero mishi addu'a

cikin zuciyarshi ya ke amsa musu da Ameen kafin ya juya ya sa kafa ya baro fadar
tafiyar shi ya ke cikin konciyar hankali ya na bin Daular da kallo , a haka har ya karaso cikin word room

kai tsaye dakin da ya kai Inaya da farko ya nufa , kawai sai ya ga babu kowa a ciki
da sauri ya juya ya koma reception ya na tambayar matar shi
cikin nitsuwa Wata nurse ta ce mishi " an sauya musu daki , su na cikin room 5 "

bai bata amsa ba ya juya ya nufi room 5 , babu ko sallama ya tura kofar ya shiga
ya na idanunshi su ka sauka saman ta , ta na konce saman gado ta na sanye da wata gown blue irin ta ma su jinya , idanunta a lumshe da allamun barci ta ke ko har yanzu ba ta farka da ga sumar ta ba

kusan gadon ya ga wani dan cradle tsayin shi daya da gadon Inaya
a ciki ya hango babys din su konce a ciki , an dunkule su cikin wani towel , Macen pink , Namiji kuma blue , Ita dai Nailah idanunta a rufe da allamun barci ta ke , Nayel kuma idanunshi na bude ya na kallon ceiling , idanunshi Tak tak irin na Malik wato hazel

wata nanauyar ajiyar zuciya Malik ya sauke kafin ya tako a hankali kamar barawo ya karaso gaban su
tsayawa ya yi ya na bin babys din shi da kallo kamar ya hadiye su

ya na a haka kawai ya ga idanun babyn sun juye kamar yadda a ke juya PAGE din littafi su ka koma farare kal kafin su dawo dai'dai

wani dan karamin murmushin geffen fuska ya yi murya cen kassan makoshi ya ce " idanun momynka ka dauko "
ya na gama fadar haka ya tako a hankali wajen shi , har kai hannu zai daukar babyn ya tsaya cak ya na kallon Tambarin masarautar a wuyan babynshi

ya so ya duba hannun Nailah , amma ya san tunda a ka yi wa Nayel ba makawa ita ma an yi mata

lokaci guda kawai ya ji ranshi ya baci
da sauri ya janye hannunshi ya juya da sauri ya fice dakin
kai tsaye office din doctor din da ta karbi haihuwar Inaya ya wuce
babu ko sallama ya tura kofar office din ya shigo ya na fadin " wa ya ba ku izinin yi wa babyna tambarin masarautar nan ? "

a hankali Doctor ta mike ta na fadin " ranka shi dade b..... "

ba ta kai karshen maganar ta ba ya katse ta da cewa " ki ba ni amsar tambaya ta kawai "

" MALIKAT AL'UMU " ta fada a takaice

bai ce mata komai ba kawai ya juya ya fice office din , kai tsaye word room din ya baro ya nufi part din MALIKAT AL'UMU ya na taku da sauri , duk yanayin face din shi ya sauya da allamun ranshi ya baci

babu ko sallama ya shigo parlourn MALIKAT AL'UMU ya na kiran " momy ! , momy ! momy ! " ya ke fada da karfi ya na tsaye tsakiyar parlourn

da sauri MALIKAT AL'UMU ta fito da ga corridor a rude ta ke fadin " lafiya ka ke min irin wannan kiran ? me ya faru ? "

cikin bacin rai ya ce mata " momy , why za ki ce a yi wa babyna tambarin masarauta ? , why ? "

" zo mare ni Nawfel , mare ni na ce don Allah " ta fada cikin tsare gida

wani dan karamin tsaki ya ja ya na kauda kai gefe kafin ya ce mata " momy , ni fa ban bada izinin yi wa babyna wannan abun ba , why za ki min haka ? "

" saboda yaron Malik ne , kuma dole a yi mishi tambarin masarauta , kar ka ce za ka goge shi , wlh za ka ji musu ciwo ka ga har yanzu ba wani kwari ne da su ba "

" momy ba na son abun da zai hada babys di na da wannan masarautar , that's why na yanke shawarar komawa US da su bayan nadin Malik "

dan zaro idanu MALIKAT AL'UMU ta yi ta na fadin " what ? ban gane ba , kamar ya za ka koma US da su ? ka na nufin ba za ka zauna ba ? "

cikin sanyin murya ya ce mata " yeah , ba zan zauna ba , ni dama ban dawo da Niyar zama ba , kuma in sha Allah Next Friday zan koma US , dalilin da ya sa ban bada izinin yi mishi tambarin masarautar nan ba , amma kin je kin ce a yi mishi , gaskiya momy ban ji dadin haka ba "

a hankali MALIKAT AL'UMU ta nufi Sofa , ta zauna ta na kallon shi fuska a marairaice ta ce " yanzu tsakani da Allah Nawfel komawa za ka yi , tun da komai ya wuce ka zauna cikin familyn ka mana "

a hankali ya tako wajen sofar ya zauna geffen ta murya a sanyaye ya ce " momy , ba zan yi miki karya ba , these months that I spent there were the best of my entire life, I felt free, without any pressure, just her and me , na ji dadin zamana a cen fiye da komai , please kar ki ce za ki tsayar da ni , i promise duk bayan sallar Azumi za mu dinga dawowa mu yi babbar sallat a nan , just let me go please "

shiru MALIKAT AL'UMU ta yi ta rasa abun da za ta ce mishi , ita ta na farin cikin komai zai dawo dai'dai , amma ya ce zai koma , zai sake barin su

a hankali ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce " kujerar Malik kuma fa ? wa zai hau ta yanzu ? "

" Diya " ya fada a takaice

" ka sani Diya ba zai iya hawa kujerar nan ba , in da ma a ce Abdoul ne da zai iya hawa "

" na sani momy , amma shi za a nada , dan na san Bayan shi babu wanda zai iya rike min ahalina , na san zai kula da masarautar nan kamar yadda ni zan kula da ita , na yarda da Diya fiye da rayuwata , ba dan shi ba da yanzu ban san inda zan tsinci kai na ba , ba dan shi ba da ba zan taba haduwa uncle bare har ya ba ni auren Cutie , duk wani abun al'heri da ya same ni cikin rayuwata shi ne sila , shi ya sa na yarda da shi fiye da rayuwata , he is my best and ONLY friend's , He is my Brother not my Cousin , dan haka ya na da ikon hawa kujerar Malik "

wani dan karamin murmushi MALIKAT AL'UMU ta saki kafin ta ce " ka tabbatar shi ne abun da ka ke so ? "

" na tabbatar momy " ya fada kai tsaye

" shikenan , amma kar ka fadawa kowa maganar nan , har ranar nadin "

" okay momy " ya fada ya na mikewa tsaye

da sauri MALIKAT AL'UMU ta ce mishi " ina kuma za ka tafi ? "

" ina son na ga babyna kafin mu tafi mosque lokacin sallat ya yi "
da to kawai ta amsa , da ga haka ya sa kafa ya fice part din

har ya nufi hanyar word room a ka fara kiran sallat , kawai sai ya juya ya nufi mosque dan ya yi sallat

bayan sun yi sallat , Diya ya ja hannunshi ya nufi part din shi da shi , sai tambayar shi Malik ya ke me ya faru , ya sake shi
amma ko sauraron shi Diya ba ya yi , su ka shiga part din shi

sai da su ka shiga cikin dayar bedroom sannan ya saki hannunshi , ya meda kofar ya rufe , ya saka mata security

Malik na ganin haka ya ce mishi " wai lafiya ka kawo ni nan , ina son na je na ga babys di na , ka wani kawo ni nan har da rufe kofa "

cikin sanyin murya Diya ya ce mishi " please , ka tsaya akwai wata magana da na ke son mu yi "

wani dan karamin tsaki Malik ya yi ya na fadin " magana ba za ka iya yi min ita ba a mosque sai ka kawo ni har nan ? , wlh ba ka da hankali , ban hanya na wuce " ya fada ya na nufar kofar dakin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login