Showing 24001 words to 27000 words out of 42080 words
, ya a ka yi ta san da Nayab , bayan ya na da tabbacin ba ta cikin hayacinta lokacin da ya shigo duniya , in ma doctor ce ta fada mata ya a ka yi ta san sunan shi Nayab bayan shi bai fada mata ba
ya yi nisa duniyar tunanin shi kawai ya jiyo Muryar mama ta shigo dakin ya na sallama
a hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya juya ya na amsa mata sallamar ta
Inaya na ganin ta ta saki kuka ta na fadin " mama , ki ce mishi ya fiddo min babyna , ina jin shi ya na kira na , amma wai ya ce shi bai san maganar me na ke ba , ni baby uku na haifa ba guda ba , ku medo min da babyna "
a hankali Mama ta rungume ta ta na fadin " Auta , duba ki gani " ta fada ta na nuna mata Malik da ke rike da Nayel
cikin rudu Inaya ta kalle su kafin ta juyo da kallon ta kan mama
cikin sanyin murya mama ta ce mata " kin dai gani , mijin ki ne kuma ya na rike babyn ku , ga guda kuma a konce , ki na tunanin da a ce uku ne ba zai fi ki farin ciki ba , amma kin gani baby biyu ne , kawai tunanin ki ne ya ba ki hakan "
cikin kukan nata ta katse mama da cewa " amma mama ina jin kukan shi , ina jin shi ya na kira na "
a hankali mama ta girgiza mata kai ta kai hannu ta fara goge mata hawayenta ta na fadin " tunanin ki ne kawai , please ki kontar da hankalin ki kin ji auta ? wannan su kadai ne babyn ku a yanzu sai wanda za ku samu a nan gaba , ai ki na so ko ? "
wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " mama da gaske biyu ne ba ? ba uku ba ? "
" no biyu ne Allah ya Albarkaci auren ku da su , ko ba ki son su ? "
da sauri ta ce " mama ina son babyna mana , fiye da komai "
" har ni ? " su ka tsinci Muryar Malik ya na fada
a tare su ka juya su na kallon shi , ya tsare su da ido
wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " ina son ka fiye da tawa rayuwar "
gyada mata kai ya yi a hankali kafin ya mike ya kontar da babyn saman gadon shi dan ya yi barci , sannan ya dago ya ce musu " yanzu na dawo " ya kai karshen ya na juyawa zai fita
har ya kai bakin kofar mama ta ce mishi " tsaya don Allah ina son na yi magana da kai , auta yanzu na dawo " ta kai karshen ta na sakin Inaya
ta mike ta bi bayan Malik su ka fita ita kuma Inaya ta koma ta konta
sai da su ka yi dan nisa da dakin sannan su ka tsaya mama ta ce mishi " na sani Triplets ne ta haifa , ban ga laifin ka ba dan ka boye mata dan kar ta cutu , amma ina jin wani abu wanda ba zan iya fada maka ba "
cikin rudu ya ce mata " ta ya a ka yi ku ka san uku ne bayan ni da doctor da nurse biyu ne kawai mu ka san triplets ta haifa , ko ita na yi mamakin yadda a ka yi ta san Triplets ne "
" Muryar shi ta jiyo , haka ni ma na jiyo Muryar shi ta haka ne na gane su uku ne ta haifa , but zan so ka koma wajen doctor ka tambaye ta ina babyn ka ya ke in ba ta gan shi ba za ta iya samun sukuni ba , haka za ta yi ta jin Muryar shi "
wani dogon nunfashi ya ja ya na saukewa a hankali kafin ya ce " ki yi hakuri mama , ba zan iya ba , na san in ta ji labarin shi ba za ta iya jurewa ba , shi ya sa na boye wannan maganar , ke ma ina rokon ki don Allah kar ki fada mata "
" amma ya ka ke so ta yi Muryar shi da ta ke ji ? "
" zan san yadda zan yi " ya na gama fadar haka bai jira amsar ta ba ya raba ta geffen ta ya wuce
a hankali ta juya ta bi shi da kallo na dan lokaci kafin ta juya ta sauke wata yar karamar ajiyar zuciya sannan ta koma dakin Inaya
❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
STORY & WRITTEN BY : MEERAH ⚘🕊
【THE ROYALTY LOVE ❤🌹】
【 BOOK ________ 4 📚✍💌 】
_______________________♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡______________________
{ P A G E ________ 17 & 18 ✍💕🔥}
▪AFTER TWO DAYS
wani katon waje ne cike da chairs red color dukkan su , su na kallon wani hall
a saman hall din akwai wata doguwar table shinfide da wani tissu white color , an jera drinks kala² a sama da Mic guda 11 a gaban kowace kujera , amma na gaban farar chair din nan ya fi kawatuwa
, bayan table din akwai wasu chair guda biyar a geffen , biyar a geffen hagu sai wata babba fara kal ta alfarma a tsakiyar su
wajen duk zagaye ya ke da Sojoji , kowane rike da gun ya daure fuska , ga wasu yan JARIDA zazzaune saman chairs din nan , sai wasu manyan cameras wajen hall din nan
cen na hango Diya zaune saman kujerun da ke saman Hall , da Rafik , da General Abdallah , Idris da Hussein a geffen dama , a geffen Hagu ma akwai wasu biyar zaune saman chair din da allamun wadanan su kuma ministers ne
wajen ya yi tsit ba ka jin komai
su na a haka Malik ya shigo wajen ya na sanye da wasu suit Farare kal ma su mugun kyau , ya saka wasu sneakers farare kal a kafafun shi , ya daure wanan smooth hair din nashi a baya , ya na taku cike da Izza wasu sojoji guda uku na biye da bayan shi
ya na shigowa wajen kowa ya mike tsaye , har su Diya , nan take kowa ya shiga yin tapi , dan duk mutanan wajen ba karamin dadi su ka ji ba ganin shi
a haka har ya karaso saman hall din nan , ya nufi chair din Fara , da sauri wani soja da ke tsaye baya ya karaso zai janyo mishi chair
a hankali Malik ya daga mishi hannu , ba musu ya koma ya tsaya
hannu ya sa janyo chair ya zauna , sai da ya zauna sannan kowane ya koma ya zauna su na kallon shi
cike da nitsuwa ya fara magana cikin wata zazzakar murya ya na fadin " Assalamualaikum wa rahmatullah wa barkatuhu , My name is Nawfel Hicham Bin Jaabar , na ji dadin ganin yadda ku ka hallaci wannan zaman , kafin mu fara abun da ya kawo mu , zan so mu bude taron nan da addu'a , mai girma Rafik , bismillah " ya fada ya na dan kallon Rafik
ba musu Rafik ya mike tsaye ya fara jero musu addu'o'i su na amsa mishi da Ameen , sai da ya kammala sannan ya koma ya zauna saman chair din shi
ya na zama Malik ya ce " Alhamdoulilah , na san kowa a wajen nan ya san matsayina a cikin kassar nan tamu mai albarka , na san kuma kowa ya san abun da ya faru last seven months da ba nan , bayan hawan Aymane Bin Abdoul Mujeeb kujerar Malik , da farko zan so na gabatar da sakon ta'aziyata ga ahalin da su ka rasa 'ya'yansu , ina me kara ba ku hakuri , in sha Allah wannan shi ne na karshe da izinin ubangiji , Tabbas ni na hakura na sauka da ga kujerar Malik , amma ba wanda ya yi tunanin Abun da Malik Aymane zai aikata , a lokacin da na samu labarin abun da ke faruwa a cikin masarautar na yanke shawarar dawowa dan na rushe wannan bakin mulkin nashi , kuma cikin yardar ubangiji na yi nassara , ga duk al'umar Saudiya da ke sauraro na a wannan lokacin , zan so ku sani , ni Malik Nawfel HICHAM bin JAABAR na dawo kan kujerata ta Malik , kuma in sha Allah zan ci gaba da kula da kassar Saudiya kamar yadda mahaifina Malik HICHAM BIN JAABAR ya kula da ita bisa gaskiya da kyakyawar zuciya , da ga yanzu duk wani mai laifi za a yanke mishi hukunci dai'dai abun da ya aikata bayan kwakwaran bincike , mai gaskiya kuma a ba shi gaskiyarshi , duk wasu makarantu da a ka rufe za a bude su , a ci gaba da bawa yaranmu karatun da ya dace , da ga Maza har zuwa Mata , I'm sorry ba ni da isashen lokacin sauraron tambayoyin ku , amma ministers za su amsa muku , ina yi wa kowa fatan al'heri , Allah ya mayar da kowa gidanshi na lafiya , Thanks a lot "
ya na gama fadar haka ya mike , da sauri su ma yan JARIDA su ka mike su na kokarin su nufe shi amma sojoji sun tare su , a haka har Malik ya sa kafa ya fice wajen ,
ya na fitowa sai saman wasu dankareren motoci ma su nunfashi duk black , cike a wajen , na yi kokarin kirga motocin amma gaskiya na kassa sai ka ce companyn buga mota dan wajen cike ya ke da motoci
ga kuma motocin sojoji kamar su ci kan su , ga kuma sojoji cike da harabar wajen 200 ma Albarka , kowane rike da gun
Malik na fitowa duk sojojin wajen nan su ka tsaya cak waje guda , da sauri wani ya nufi wata dankareriar mota Fara kal dan duk cikin motocin nan fara guda tak na gani sai motocin yan JARIDA , a haka sojan nan ya sa hannu ya bude mishi gidan bayan motar
hannu ya kai cikin aljihun wandon shi , ya fiddo wasu glass bakake ya saka a idanun shi , maimakon ya shiga motar nan da soja ya bude mishi
kawai sai ya raba ta geffen ta ya wuce , ya ci gaba da tafiyar shi ya nufi hanyar fita wajen , duk inda ya wuce sai sojojin nan sun daga kafa su na sara mishi
ko sannu bai ce musu ba , a hankali ya dago hannun ya cire button din Jacket din suit din , ya fida jacket din ya yadda a kassa ba tare da ya tsaya ba
ya kai hannu ya fido kassan farar shirt din shi da ya soke cikin wandon shi , ya kai hannu cikin dayan aljihu ya fiddo wata bakar face mask , ya saka , ya sa kafa ya fice wajen shi kadai
duk mutanan wajen sai da su ka yi mamaki baki sake , sun ma rasa abun da za su yi , su bi shi ko kuwa ? kawai dai sun tsaya su na bin shi da kallo har ya fice
bangaran Malik kuwa kai tsaye hanyar Daular Saudiya ya nufa da kafa , duk inda ya wuce sai ya jiyo Muryoyin mutane su na ta yabon shi , dan taron da su ka yi yanzu on live ne kowa ya na kallo
ba karamin dadi ya ke ji ba jin yadda mutane ke yabon shi , wasu na jefa mishi Albarka , wasu na jero mishi addu'a kai abun dai Masha Allah , ya amshi sunan shi na Malik dan kowa cikin garin Saudiya ya shaide shi
ya na tsaka da tafiyar shi kawai ya karaso wajen wani plaza , cak ya tsaya ya na bin plaza din da kallo , ya na nan yadda ya bar shi bai sauya ba , lokacin guda ya saki wani cool murmushi ya na kallon plaza din dan a wannan wajen ne ya hadu da Diya for the first time
a haka dai ya ci gaba da tafiyar shi hannayanshi na cikin aljihun wandon shi , har yi dan nisa kawai ya jiyo Muryoyin wasu samari da ga bayan shi su na fadin " ranka shi dade ! " su ka fada da karfi
cak ko ya tsaya , kafin ya ci gaba da tafiyar shi ba tare da ya juyo ba
ya na haka kawai ya ga wasu samari guda hudu a gaban shi kamar sun fado da ga sama sun tare mishi hanya
daya da ga cikin su ya na ce " ku yi hakuri mun tsayar da ku , ni sunana Adel , tun mu na wancen layin ne mu ka hango ku , to na cewa abokai na mai martaba Malik ne , amma sun ki yarda , shi ne mu ka biyo ku dan mu tabbatar "
a hankali Malik ya dago musu hannu ya nuna musu kunnenshi kafin ya yi musu kwatancen shi kurma ne kuma makaho , ba zai iya magana ba
" wayo , ba ka gani kuma ka ke tafiya kai daya ? ina dan jagoran ka ? dama dama yanzu akwai security a masarautar da tuni an yi gaba da kai " daya da ga cikin su ya fada
a hankali ya girgiza musu kai allamun ba shi da
Adel ne ya kalli abokanshi ya ce " kun ga , bari mu raka shi ni da Hadi , kun ga zirga²r da a ke a masarautar nan ya dawo kamar da farko , kar a je mota ta buge shi , ku/ku koma shop , ba za mu jima "
ba musu biyun su ka raba ta geffen Malik su ka koma inda su ka fito
su na barin wajen wanda ya yi magana da farko ya riko hannun Malik ya na fadin " mu tafi "
ba musu Malik ya bi shi su ka tafi tare da wanda ya kira Hadi
sai sun karaso wajen da a dakwai kwana sai su tsaya su tambayi Malik wace kwana za su yi ,
sai ya girgiza musu kai ya na nuna musu gaban su allamun su ci gaba
ba musu su ke yin hanyar , a haka har su ka karaso bakin kofar Daular Saudiya , ba tare da sun kawo komai a ransu ba
sai da su ka zo dab da kofar shigar sannan Malik ya kwace hannunshi ya na fadin " okay , na gode sosai da rakiya , rike wannan " ya fada ya na cire face mask din shi ya daura saman hannun hadi