Showing 12001 words to 15000 words out of 42080 words
" no , kar ka yi nadamar lokacin da ku ka samu na farin ciki kai da ita , na san da ka san hakan za ta faru ba za ka tafi ba , amma tsotsayi ne , in ya wuni ba zai kwana ba , haka Allah ya rubuta za ta faru , kuma ta farun ni dai kawai fata na Allah ya sa ka yi nassara "
" ko ban yi nassara ba don Allah ina son ka koma Qatar da family na , specially Cutie da Babyn mu , na bar maka amanar su don Allah kar ka bari wani abu ya same su ko da ba na raye "
da sauri Diya ya ce mishi " in sha Allah kai za ka yi nassara , Allah ya na tare da ma su gaskiya , ba zai bari zalunci ya yi nassara ba "
shi da Malik ya yi shiru bai ce komai ba amma har cikin zuciyar shi ya na fargaba a je bai yi nassara ba , shi ba ta saudiyar ya ke ba ta Cutie din shi ya ke , yanzu a ka je ya mutu ya za ta yi , babu wanda zai kula da ita da babyn su
ya yi nisa duniyar tunanin shi ya jiyo Muryar Diya ya na fadin " ka san General Abdallah har US ya je neman ka ? "
slowly ya bude idanun shi ya kalli Diya ya na daga gera ya ce " ya a ka yi ya san ina US ? "
" ni na fada mishi , har General din US army General Aylan Jalaludeen su ka hada kai dan neman ka , musaman General Aylan ya ba da tukuyicin one million of American dollars ga duk wanda ya gan ka , amma shiru "
cikin nitsuwa Malik ya katse shi da cewa " wait , General Aylan fa ka ce ? ina General Abdallah ya san shi ? "
" ni ma ban sani ba , but ya ce mahaifin shi ya sani a DubaΓ― shi ya sa ya yarda ya taimaka wajen neman ka "
" Diya , na hadu da General Aylan , har mu ka yi hira da shi "
dan zaro idanu Diya ya yi ya na fadin " ban gane ba , ka hadu da shi kuma bai fada maka a na neman ka ba ? "
shiru Malik ya yi dan ba shi da amsar da zai ba shi , kenan Aylan ya na sane a neman shi a Saudiya amma bai ce mishi komai ba , ta wani bangaran ta sanadiyar Aylan ne ya samu ya rage zafin da ya ke ji cikin zuciyar shi har ya karbi babyn shi , to why bai fada mishi abun da ke faruwa ba ?
π€π€ NI MA ABUN NAN YA DAURE MIN KAI , YA NA SANE KUMA YA YI SHIRU BAI CE KOMAI BA ? π€π€
su na zaune a haka kawai su ka ga wata mota baka kirin ta nufi hanyar fita masarautar
a tare duk su ka tsare motar da ido har sai da ta fita sannan Diya ya kalli Malik ya ce " Malik , Aymane ne fa , ina za shi je cikin wannan daren ? "
cikin ko in kula Malik ya ce " shi ya sani "
" a ka je wani abu kuma ya ke shirya wa ? please tashi mu bi bayan shi "
" no , kyale shi , duk abun da ya shirya shi dan cutar da ni Allah ba zai bari ya yi nassara ba , kyale shi kawai "
" amma M...... " bai kai karshen maganar shi ba Malik ya katse shi ya na daga mishi hannu allamun ya yi shiru
ba musu Diya ya ja bakin shi ya yi shiru amma cikin zuciyar shi ya na jin ba abun kirki ba ne Aymane ke shirin yi ba , in abun kirki ne why zai fita a irin wannan lokacin ?
sai dai kawai na ce Allah ya tsare Malik da ga sharin Aymane
β€β EXILED PRINCE ββ€
( LOVE MEETS POWER ) ππ₯
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
STORY & WRITTEN BY : MEERAH βπ
γTHE ROYALTY LOVE β€πΉγ
γ BOOK ________ 4 πβπ γ
_______________________β‘β‘β‘β‘β‘β‘β‘β‘β‘β‘β‘β‘______________________
ο½ P A G E ________ 9 & 10 βππ₯ο½
βͺAYMANE πΊ
Tuki ta ke yi cikin nitsuwa da ga gani akwai abun da ya shirya
ya yi wajen one hour ya na wannan tafiyar kafin ya iso wajen wani kasurgumin Daji , babu motsin mutum bai rai sam sai dai tsintsaye da namun daji , har kukan tiger na ke jiyo wa amma shi ko tsoro babu ya ratsa ta dajin nan cikin motar shi
ya yi ten minutes a haka kafin na ga ya tsayar da motar bakin wani katon dutsi
a hankali ya bude kofar motar ya fito , kai tsaye dutsin nan ya nufa , nan na ga wata yar karamar kofa kamar cellar da ga kasan dutsin ko digon haske ba ya fitowa
babu ko tsoro ya nufi kofar ya shiga babu ko sallama
kamar da wassa kawai sai na ga wajen da mugun haske kamar safiya , wajen zallar dutse ne an yi zanen macizai a sama da mutane , ga wata wuta na tashi tsakiyar dutsen da wasu kwalabe zagaye da wutar hayaki na tashi da ga cikin su
kai wajen ba zai iya kwatantuwa ba dan bai yi kama waje holy ba , da ga gani wajen tsafi ne in ba haka ba ya za a ce da ga waje na ga wajen duhu babu digon hasken da ke fitowa ta kofar
ga shi kuma cikin da mugun haske kamar da safe , kai ni dai zuciya ta ba ta amince da wajen nan ba
a hankali Aymane ya karaso gaban wutar nan
ya sa hannu daya bayan daya ya fara cire kayan jikin shi ya na ajiye wa gefe
sai da ya rage da ga shi sai short sannan ya zauna gaban wutar nan , ya yi irin zaman cin tuwo
ya kai hannu ya dauki gudar kwalba ya sa yatsun shi biyu a ciki
kafin ya fiddo su da wani abu ja a sama kamar jini , kai tsaye saman forehead din shi ya shafa wannan abun
ya na shafawa ko ya shanye kamar bai shafa komai ba , a hankali ya meda kwalbar ya ajiye
ya lumshe idanunshi ya fara karanto wani karatun mara dadin ji ,
a hankali wani dan karamin iska ya fara tashi a wajen
a dubu dari ya ware idanunshi , ba karamar razana na yi ba ganin yadda idanun shi su ka koma na maciji , ma su ban tsoro ya tsare waje guda da ido
kamar a film haka na fara ganin zanen macizan nan da ke saman dutsen nan sun fara fitowa kamar na gaske , daya bayan daya su ka nufi Aymane kawai sai su shige jikinsa su bace bat
su na bacewa ko zanen ke fitowa saman fatar jikin shi , sannu sannu har sai da jikin sa ya cika da wadanan zanen sannan na ga ya ja wani dogon nunfashi ya lumshe idanunshi kafin ya sulale a wajen ko motsi ba ya yi
ya na faduwa ko wutar nan ta gaban shi ta mutu ita kan ta , wajen ya koma duhu kamar ba a taba yin haske a wajen ba
π€§π€§π€§ NI DAI BA ABUN DA ZAN CE SAI DAI ALLAH YA KARE MANA MALIK , AYMANE YA WUEC ABUN DA YA KE TUNANI , MUGU NE NA GIDAN GABA , YANZU NI WANNAN ABUN DA YA YI BAN MA SAN KO MINENE BA , SAI DAI RANAR DUEL DIN MU GANI AMMA NA SAN BA AL'HERI NE BA , SAI DAI KAWAI NA CE MALIK ALLAH YA KARE KA DA GA SHARIN AYMANE DA MACIZAN SHI
βͺAFTER TWO DAYS π€§π₯
yau ta kama ranar Friday , tun karfe 6 a ka fara shiryeΒ²n duel din Malik da Aymane
misalin karfe 8 kowa ya hallaci wajen da za a gabatar da duel din , a cikin garden a ka shirya yin duel din
kowa na cikin masarautar sai da ya hallaci wajen , da mutanan fadar Malik , da kuma na fadar Aymane , har da su MALIKAT INAS , da Inaya ba rokon da su mama ba su yi mata ba a kan ta zauna , amma fir ta ki ta ce sai ta je
a tsaye Malik da Aymane su ke tsakiyar garden din , su na fuskantar juna , Rafik na tsaye da ga tsakiyar su a gefe
cikin nitsuwa ya fara magana ya na fadin " kun san yadda tsarin fada da takobi ya ke , ban da zalinci "
cikin nitsuwa Aymane ya katse shi da cewa " ka ga don Allah ka ba mu waje mu yi mu wuce wajen , a sani na ka kashe ko a kashe ka shi ne tsarin wannan fadan , dan haka ka wuce ka ba mu waje "
" za ka iya tafiya Rafik " Malik ya fada cikin sanyin murya
gyada mishi kai Rafik ya yi kafin ya juya ya karbi Sword din da ke hannayan Azim da ke tsaye bayan shi
ya mikawa Aymane guda , sannan ya mikawa Malik guda ya na fadin " Allah ya ba mai rabo sa'a " amma cikin zuciyar shi Malik kawai ya ke yi wa addu'ar samun nassara , da ga haka ya bar wajen ya koma wajen da a ka shiryawa ma su kallo
ya zauna saman chair din shi geffen MALIKAT AL'UMU , ya na zama ko Aymane da Malik su ka fara fadan su
a hankali MALIKAT AL'UMU ta juyo ta kalli Rafik ta ce " Rafik , wai fadan minene su ke yi ? "
wani dan karamin murmushi Rafik ya yi ya na fadin " ranki shi dade , wanda ya yi nassara shi zai hau kujerar Malik "
" Wanda bai yi nassara kuma fa ? " MALIKAT INAS ta fada
dan jinkirtawa Rafik ya yi kafin ya ce " mutuwa zai yi "
a tare su ka ce " inallillahi wa'ina illaihi raji'un , ka na nufin idan Malik bai yi nassara ba kashe shi Aymane zai yi ? "
a hankali ya gyada mishi kai ya na fadin " ina jin tsoron hakan ranki shi dade , addu'a kawai za ku yi Allah ya ba shi sa'a , idan Aymane ya yi nassara za mu shiga babban tashin hankali dan babu wanda zai iya yin jayaya da shi a kan kujerar Malik "
kalmar shahada MALIKAT AL'UMU da INAS su ka shiga jerowa , kenan kashe musu yaron su za a yi in dai bai yi nassara ba , nan take zuciyoyinsu su ka fara bugawa da karfi
a hankali MALIKAT INAS ta juya ta kalli su Malik dai'dai lokacin da Aymane ya samu Malik a damtsen shi na dama ya yanke shi nan take ya fara zubar da jini har ya gangaro saman takobin hannunshi
da sauri Inaya ta rumtse idanunta , ta na kauda kai gefe
a hankali RIANNA ta riko ta , ta na fadin " ko mu koma ciki ? "
girgiza mata kai Inaya ta yi ta na fadin " a'a Aunty RIANNA "
da to kawai RIANNA ta amsa mata kafin su ci gaba da kallon su Malik
wata yar karamar dariya Aymane ya yi lokacin da ya ji wa Malik ciwo a hannu ya na fadin " ya ,har ka gaji ? still yanzu ma mu ka fara "
a hankali ya kai hannun shi na hagu ya riko sword din , dan ba karamin rauni ya samu ba , ba zai iya ci gaba da fadan da hannun damar ba
wata yar karamar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya nufi Aymane , shi ma Aymane da gudu ya nufo Malik
sai dai kafin ya kai ga daga takobin shi , Malik ya juya ya ba shi baya ya caka mishi sword din shi a ciki har sai da ta fito mishi ta baya
da sauri Malik ya juyo ya yi baya ya na kallon Aymane da ke zubar da jini ta bakinshi
wata nanauyar ajiyar zuciya duk mutanan Malik su ka sauke MALIKAT AL'UMU da INAS su na yi wa Allah godiya cikin zuciyoyinsu
da sauri Inaya ta mike tsaye ta na kallon Malik ta ce " ka cire mishi kai ! " ta fada da karfi har sai da hankalin kowa ya dawo gare ta
Malik na jin hakan ya tuno abun da ta tabba fada mishi lokacin da ya ce wa Aymane su yi duel din na ya cire mishi kai ta haka ne kawai zai mutu
tuno hakan ne ya sa shi nufar Aymane da sauri zai zame takobin shi
sai dai kafin ya karaso ya ga Aymane ya zare takobin da kan shi ya tilla gefe ya na sakin murmushi
" ka kashe ni , amma ba za ka iya ja da shi ba " Aymane ya fada jini na fitowa da ga bakin shi
kafin Malik ya yi taku biyu , kawai ya ga skin din Aymane ta koma green scales na fito mishi kamar irin na maciji , idanunshi su ka koma irin na maciji
bayan kalmar shahada ba abun da mutanan wajen da Malik su ke yi
su na kallon Aymane da ya fara girma , ya na girma , ya na girma , ya koma dankareren maciji tsanwa shar , girman shi ya yi biyun macijin da Rouksar ta zama a word room
wani irin razanannan kuka macijin nan ya yi tongue din shi na fitowa waje
duk mutanan wajen sai da su ka saki kara , ma su tserewa na yi , ma su suma na yi
MALIKAT INAS , MALIKAT AL'UMU da Rafik , RIANNA , Diya , bayan kalmar shahada ba abun da su ke yi
da sauri General Abdallah ya kalli Sojojin shi da ke tsaye cen a geffen ya daga musu murya ya na fadin " Fire ! "
da sauri Su ka fiddo gun su ka fara harbin macijin nan , amma ko ajikin shi , bullet din sai faduwa kassa su ke yi
wutsiyar shi kawai ya sa ya buge duk sojojin da ke wajen su ka yi cen gefe su ka fadi
shi dai Malik ya yi sumar tsaye bayan kallon macijin nan ba abun da ya ke yi , sai kalmar shahada da ya ke karantawa cikin zuciyar shi , ya na kallon macijin nan cikin ido dan shi ma macijin Malik ya ke kallon
ya na tsaye a haka kawai ya ga........
β€β EXILED PRINCE ββ€
( LOVE MEETS POWER ) ππ₯
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
STORY & WRITTEN BY : MEERAH βπ
γTHE ROYALTY LOVE β€πΉγ
γ BOOK ________ 4 β€βπ γ
_______________________β‘β‘β‘β‘β‘β‘β‘β‘β‘β‘β‘β‘______________________
ο½ P A G E ________ 11 & 12 βππ₯ο½
ya na tsaye a haka kawai ya ga Inaya kamar ta fado da ga sama tsaye a gaban shi , kayan jikin ta duk sun koma baki kirin , gashin ta ya yi black sosai , ga shi kuma ya yi kwari kamar an yi kitso , idanunta sun koma bakake kirin ko digon fari babu , har wani bakin hayaki ke tashi da ga saman rigar ta da gashin ta , wani abun mamaki kuma cikin jikinta ya bace bat kamar ba ta taba yi ba
a hankali Malik ya bude baki ya na shirin magana ya ga wani haske ya fito da ga jikin ta ya yi cen gefe dan nesa kadan
wata irin muguwar bugawa zuciyar shi ta yi
wata Inayar ce kuma daban , amma wannan kayan jikin ta duk farare ne , har gashin kan ta fari ne kal , idanunta sun koma farare kal har wani haske su ke yi kamar torch , ita ma dai cikin ta a shafe ya ke babu allamun pregnancy a tattare da ita
cikin wani harshe da ban san irin shi ba mai sanye da bakaken kaya ta cewa dayar "