Showing 15001 words to 18000 words out of 42080 words
Abyad ki koma , idan wani abu ya same ki dukka mu uku ba za mu rayu ba "
girgiza mata kai Abyad ta yi ta na fadin " Aswad , ba za ki iya yin fada da shi ba ke kadai , ki bari na taimaka miki "
" Ki fara fitar da Malik da ga wajen nan " Aswad ta fada
gyada mata kai kawai Abyad ta yi , kafin ta tako da gudu ta nufo Malik da ya yi sumar tsaye , ta riko hannunshi ta bace bat tare da shi
sai ga ta tsaya gaban su MALIKAT AL'UMU rike da Malik
sakin hannunshi ta yi , ta na shirin juyawa ya riko hannunta ya na fadin " Cutie , kar ki tafi "
a hankali Abyad ta juyo , ta kwace hannunta a hankali , wannan karan da harshen Hausa ta ce " kar ka damu ba abun da zai same ta , ka zauna a nan , idan wani abu ya same ka , ita ma za ta cutu "
ta na gama fadar haka , ta yi taku uku baya , ta na fuskantar su , ta fara motsa lips din ta a hankali
a hankali wani farin hayaki ya fara tashi tsakanin su , ta dago hannun ta , ta fara yin sama da shi , shi ma hayakin nan ya fara yin sama
sannan ta daina motsa lips din ta , ta sauko hannun ta kafin ta juya da gudu
ta na juyawa Malik ya tako da sauri ya na fadin " Cutie ! " , sai dai ya na iso wajen hayakin nan ya yi baya da sauri ya ji kamar ya bugi bango
a rude ya tsaya ya na kallon hayakin nan , ya mika hannun shi , kawai sai ya ga ya tabo abu kamar ya taba bango
cikin fitar hayaci ya fara kai wa hayakin nan bugu , ya na fadin " Cutie ! Cutie ! " da sauri Diya ya riko shi ya na fadin " Ka kontar da hankalin ka , ba abun da zai faru da ita
bangaran Abyad kuwa , kai tsaye geffen Aswad ta dawo ta tsaya ta na fadin " ya za mu yi da shi ? "
a hankali Aswad ta yi sama da hannu ta , sai ga wata katuwar Sword baka kirin ta fito a ciki , ba tare da ta kalli Abyad ba ta ce mata " kar ki damu , zan yi maganin shi "
ta na gama fadar haka ta nufi macijin nan da gudu
da sauri ya juyo da wutsiyar shi zai kai mata bugu , kawai sai ta bace bat
sai ga ta tsaya a bayan shi , ba tsaya bata lokaci kawai ta caka mishi sword din hannun ta a baya
wani irin razanannan kuka macijin nan ya yi , a dubu dari ya sa wutsiyar shi ya buge ta , wata yar karamar kara ta saki ta na yin cen gefe ta fadi
" Cutie ! " Malik ya fada da karfi ya na zaro idanu lokacin da macijin nan ya buge ta , sa karfi ya shiga kai wa hayakin nan bugu amma ina , ba kuma zai iya zagaye shi ba dan hayakin ya raba masarautar biyu , babu ta hanyar wucewa
lokaci guda Abyad ta bace , sai ga ta tsugune geffen Aswad ta na fadin " ba ki ji ciwo ba ? "
" a'a " Aswad ta fada ta na kokarin tashi
da sauri Abyad ta mike tsaye , ta na kallon macijin nan ya na kokarin cire sword din Aswad da ke bayan shi
a hankali ta mika hannunta , kamar da ga sama wata farar bow ta fito cikin hannunta
a hankali ta kai dayan hannunta , ta fara jan zaren bow din nan kamar ta na shirin tilla kibiya
sai da ta ja shi har karshe kafin ta saki , kawai sai na ga wata farar Arrow ta fito ta nufi macijin nan da mugun gudu ta soke shi a jiki
wani marayen kuka macijin nan ya saki dan ba karya ya ji zafin hakan
lokaci guda Abyad ta bace bat , ta koma gaban macijin , ta kara jan bow din nan ta harba mishi kibiya , ta sake bacewa ta koma bayan shi , ta harba mishi wata arrow a baya , yanzu ma ta sake bacewa ta koma dayan geffen ta sake harba mishi arrow , sai da ta harba mishi har guda hudu kafin bow din hannunta ta bace
wani marayen kuka macijin nan ya saki , kafin ya nufe ta gudu , duk da ya galabaita dan har idanun shi sun fara rufewa , jikin shi ya yi sanyi
ya na isa ya sa wutsiya , kafin ta bace , ya matse ta a cikin wutsiyar shi ya daga ta sama , ya buga ga kassa da mugun karfi har kura na tashi
da mugun gudu Aswad ta tasso , ta nufi Abyad ta Zube saman guyiwowin ta , ta talabo ta , ta na fadin " Abyad , Abyad , ki na ji na ? "
murya a disashe ta ce " ina jin ki , ba abun da ya same ni "
da sauri Aswad ta mike tsaye , cike da bacin rai , ta bude baki ta yi wata razananiyar kara ta na kallon macijin nan
nan take wata bakar guguwa ta tashi da karfi ta fara mamaye macijin nan , a hankali Aswad ta daga kafa ta shiga cikin guguwar nan , ta tsaya cak waje guda
a hankali ta mika hannunta , da sauri Sword din ta da ta caka mishi a baya ta fito ta koma cikin hannun ta
wata razananiyar kara macijin nan ya saki lokacin da sword din ta fita da ga jikin shi
da sauri ya nufi Aswad cike da bacin rai , sai dai kafin ya iso gare ta , ta bace bat cikin guguwar nan
cak ya tsaya ya na juyi ya na kuka ya na neman Aswad
sai da ya share one minute a haka , babu Aswad
ya na a haka ya ga kawai ta fito da ga cikin guguwar nan cen sama dai'dai tsawon shi , kamar an tillo ta , ta daga sword din ta sama ta raba macijin nan gida biyu har jininshi ya watsun mata a fuska
nan take ya fadi kassa rabi ya yi gefe , rabi ya yi dayan gefe
non take gudun guguwar nan ya kara , sai kururuwa ta ke yi wani razanannan sauti na fitowa da ga ciki
sai da ta yi wajen good one minute ta na wannan sautin kafin ta bace bat tare da macijin baki daya
wata nanauyar ajiyar zuciya Abyad ta sauke ita da Aswad a tare , ta tashi da gudu ta nufi Aswad
wani dan karamin murmushi Aswad ta saki kafin ta bude mata hannayan ta , ta na isa ta shige jikin ta
a hankali farin hayakin nan da ta tare su Malik da shi ya fara yin kassa har ya bace shi ma
ya na bacewa ko sai ga Inaya tsaye a wajen , ta na sanye da kayan ta na farko , idanun ta sun komo dai'dai har wannan katon cikin nata
a hankali ta fara bin wajen da kallo ta na tambayar kanta me ta ke yi a nan
cen ta hango su Malik tsaye , sun yi cirko² su na kallon ta babu ko kiftawa sun ma rasa abun da za su ce , da a ce wani ne ya ba su labarin abun su ka gani yau , da wlh sai su ce mishi ba shi da hankali , amma da idanunsu su ka gani , kowa ya shiga yi wa Inaya ayar tambaya ban da Malik
ta na ganin shi ta saki wani cool murmushi ta fara takawa a hankali ta nufe shi
ya na ganin ta fara takowa ya sauke wata nanauyar ajiyar zuciya
har zai daga kafa kawai ya ga ta tsaya cak , kawai sai ya ga wajen da ta ke tsaye ya jiqe kamar an watsa mishi ruwa
wata irin muguwar murdawa cikin ta , ya yi mata har sai da ta saki wata razananiyar kara ta na dafe shi da hannayan ta
a dubu dari Malik ya yi kanta ya na fadin " Cutie , me ya faru ? "
amma ko jin shi ba ta yi sai kara ta saki , ta nunfashi sama sama
da sauri su MALIKAT INAS su ka nufe su dan sun ga allamun kamar naquda ce ta ke , ga shi kuma ta zubar da ruwa hakan na nufin haihuwa za ta yi
MALIKAT INAS na karasowa wajen Malik ta ce mishi " mu kai word room , haifuwa za ta yi "
dum ya ji gaban shi ya fadi , tun kafin wani ya yi magana , ya sa hannayan shi biyu ya dauke ta cak sai kara ta ke saki ya nufi word room da ita
sai cije lips din shi ya ke dan ba karamin zafi hannun shi na dama ya ke yi mishi ba , ga shi ko sai zubar da jini ya ke
amma a haka ya daure ya nufi word room da ita , tun a reception ya shiga kwallawa su doctor kira
dama cikin word room din akwai mace likita me karbar haihuwar matan masarautar
da gudu wata nurse ta tafi office din ta , ta kira ta
ta na fitowa ta cewa Malik " yi sauri ka shiga da ita dakin cen " ta fada ta na nuna mishi wani daki
da sauri ya nufi dakin , har su MALIKAT INAS sun bi bayan shi , doctor ta ce musu " a'a ku tsaya a nan , shi ma yanzu zai fito " ta kai karshen ta na nufar dakin da Malik ya shiga
ba musu kowane ya zauna saman waiting chair , kowane da addu'ar da ya ke yi cikin zuciyar shi
bangaran Malik kuwa , ya na isa cikin dakin kawai ya kontar da ita saman gadon jinya dai'dai lokacin da doctor ta shigo ta na fadin " za ka iya fita " ta fada dai'dai lokacin da wasu nurse guda biyu su ka shiga da gudu
har ya juya zai fita ya ji ta riko hannunshi
da sauri ya juya ya na kallon ta , a hankali ta girgiza mishi kai hawaye na zubo mata
ya na shirin yi mata magana doctor ta ce " please ranka shi dade ka fita "
ko sauraron ta ba ya yi ya dawo wajen Inayar shi ya sunkuyo ya ce mata " ki kontar da hankalin ki ba abun da zai faru , kin ji ? "
ya na gama fadar haka ya jiyo Muryar doctor ta na fadin " ka fita don Allah "
cikin bacin rai ya dago ya ce mata " babu inda zan je , ku yi aikin ku kawai , idan ba za ki iya ba ki fice min da ga nan "
ba dan ta so ba ta ja bakin ta ta yi shiru
wata yar karamar kara Inaya ta saki , ta na kuka ta ce " kar ka saki hannuna don Allah "
a hankali ya dago hannunta da ke cikin nashi ya manna mishi kiss ya na fadin " ba abun da zai faru , ina tare da ke "
ba ta amsa mishi ba kawai ta saki kara ta na lumshe idanun ta har wani dago kai ta yi kafin ta koma , ga wata uwar zufa da ta karayo mata , kamar an watsa mata ruwa
cikin sanyin murya doctor ta ce mata " ki kontar da hankalin ki , ki dinga jan nunfashi a hankali , ki na saukewa "
ba musu Inaya ta ja wani dogon nunfashi har kirjin ta na yin sama
sai dai maimakon ta sauke kawai sai ta saki kara ta na kara matse hannun Malik a cikin nata
da sauri ya daura dayan hannun nashi saman kumatun ta ya na fadin " Cutie , Dube ni kin ji ? "
ba musu ta juyo ta kalle shi idanun ta duk sun yi ja sai hawaye ta ke ta marairaice fuska
da sauri ya sauke forehead din shi saman nata ya na kallon cikin idanunta , murya cen kassan makoshi ya ce mata " ba abun da zai faru da ke okay ? "
da sauri ta katse shi da cewa " yaya Zayd mutuwa zan yi , da zafi " ta kai karshen ta na kara sautin kukan ta
cikin sanyin murya ya ce mata " ba abun da zai same ki , ki daina cewa mutuwa za ki " ya fada kamar zai yi kuka har wasu hawaye ke zubo mishi wanda shi kan shi bai San da su ba
karan farko da na ga hawayen Malik , ko a lokacin da Daddyn shi ya mutu bai yi hawaye ba
wata yar karamar kara Inaya ta saki ta na janye forehead din ta , ta kauda kai gefe , da karfi ta cije lips din ta kamar za ta fashe su
da sauri Malik ya kalli doctor ya ce " wai har yanzu ba ku fiddo mata wannan abun ba ? "
" don't worry , ga kanshi nan na fitowa , ranki shi dade , last working , ki turo da karfi " doctor ta fada ta na kallon Inaya
da sauri Inaya ta shiga girgiza mata kai idanunta a lumshe
da sauri Malik ya daura hannunshi saman kumatunta , ya juyo da face din ta , ya sauke forehead din shi saman nata murya kassa kassa ya ce " okay , zan kirga zuwa uku , da ga nan ki ka dogon nunfashi ki sauke , kin ji ko ? "
a hankali ta gyada mishi kai allamun Eh
" Okay , one , two , three let's go "
wani dogon nunfashi ta na sakin wata siririyar kara karfin ta sauke wata nanauyar ajiyar dai'dai lokacin da kukan baby ya gauraye wajen
wata nanauyar ajiyar zuciya Malik ya sauke ya na fadin " Alhamdoulilah " cikin zuciyar shi har lumshe idanunshi ya yi ya na sakin murmushi kamar shi ya yi aikin
ya na bude idanunshi ya ga Inaya ta yi tsit kamar an yi ruwa an dauke
Dum ya ji zuciyar shi ta buga da karfi , a dubu dari ya kai hannu ya fara jijiga ta ya na fadin " Cuti , Cutie , please ki bude idanunki , Cutie , please ki bude kar ki min haka mana "
da sauri Doctor da ke rike da babynsu ta karaso wajen ta na fadin " ka kontar da hankalinka , ba mutuwa ta yi ba , suma ce ta yi " ta na gama fadar haka
ya ga ta sauke babyn hannun ta saman kirjin Inaya ta kontar da kan shi saitin zuciyarta
wani irin sanyi ne ya ji lokacin da idanunshi su ka sauka saman babyn , kyakyawa da shi fari kal kamar ka taba jini ya fito har wani ja ya yi , ya na kama tak da Malik kamar an tsaga kara , sai dai idanun shi a rufe su ke sai in ya bude mu ga kalar su
da sauri Nurse din da ke tsaye a baya ta ce " Doctor , ina ga Twins ne "
cikin rudu Doctor ta ce " Twins kuma ? " ta na gama fadar haka ta dauke babyn ta juya ta mikawa nurse din
ai ko da gaske Twins ne dan ga kafafun shi nan su na son fitowa , ya kuma a ka yi haka bayan baby ta kai ya ke fara fitowa
da sauri Malik ya ce mata " Doctor me ya faru ? Twins ne ? "
Doctor ba ta ce mishi komai ba ta na aikin ta
kawai sai ganin ya yi ta na rike wani babyn a hannun ta amma ko motsi ba ya yi
Dum ya ji zuciyar shi ta buga , kenan da gaske Twins ne ? ga shi shi ma namiji ne
slowly Doctor ta dago ta kalli Malik , cikin raunin murya ta ce " i'm sorry bai zo da rai ba " ta fada dan ta san ba karamin abu zai sa baby ya fito ta kafafu ga shi ko motsi ba ya yi hakan na nufin ya jima da ya mutu a cikin ta ba ta sani ba
Dum Malik ya ji zuciyar shi ta buga har wani lumshe idanu ya yi ya na fadin " inallillahi wa'ina illaihi raji'un " kassa kassa
ta daya bangaran ya ji dadi da ba ta cikin hayacinta ta haihu da yanzu in ta ji babyn ta guda ya mutu zuciyar ta bugawa kawai za ta yi ,
a hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya dago ya mikawa Doctor hannayan shi a kan ta ba shi babyn
ba musu ta daura mishi babyn
a hankali ya dago shi , ya yi mishi addu'a sannan ya yi mishi kiss saman forehead din shi
ya na a haka kawai ya jiyo sautin kukan wani babyn , cak ya tsaya ya na zaro idanu , ga shi dai sautin ba ya kama da na farko
wata nanauyar ajiyar zuciya ya sauke ya na lumshe idanunshi a hankali kafin ya sake bude su , ya dago kai
nan ya ga Doctor rike da wani babyn , sai wuntsila kafafu ya ke , ido a rufe ya na kuka da karfi
bai san lokacin da ya lumshe idanunshi ya na yi wa Allah godiya cikin zuciyar shi
a hankali doctor ta matso rike da babyn ta ce mishi " congratulation it's a girl , ranka shi dade Triplets ne ta samu "
sai da ya sunkuyar da kai ya mannawa babyn hannunshi kiss