Showing 27001 words to 30000 words out of 42080 words
sannan ya cire glass din shi ya daura saman hannun dayan ya na fadin " na gode , amma na san hanya , zan ci gaba da ga nan , see you next time " ya kai karshen ya na shiga Daular ya bar su nan sun yi sumar tsaye
sai da ya shiga sannan ya su ka juyo su ka kalli junan su baki sake su na zaro idanu , wata yar karamar kara su ka saki da dariya a tare kafin Adel ya ce " sai da na ce muku Malik ne amma ba ku yarda ba "
wani dan karamin murmushin geffen fuska Malik ya saki dan ya jiyo abun da ya ce , da ga haka ya ci gaba da tafiyar shi har ya iso part din MALIKAT HOUDA
bakin shi da sallama ya shigo parlourn MALIKAT HOUDA , nan ya tardo ta zaune tare da MALIKAT AL'UMU da mama da Nesrine , MALIKAT AL'UMU na rike da Nailah , MALIKAT HOUDA kuma ta na rike da Junior ( π€£π€£π€£β gaskiya sai dai mu kira shi da Junior dan ni mutum guda na bawa wannan sunnan wato MALIK NAWFEL HICHAM BIN JAABAR , MY NUMBER ONE π€£β ) MALIKAT INAS kuma ta na rike da Nayel
bai ce musu komai ba ya nufi corridor ya shige , kai tsaye bedroom din da Inaya ke ciki ya nufa dan dama ita ya zo nema
ya na shiga ya gan ta konce tsakiyar gado , ta dunkule waje guda , idanunta na bude
da sauri ya nufi gadon dan a nashi tunanin wani abu ya same ta , ya na isa ya zauna a baki ya na fadin " my Cutie , me ya faru ? ciwo ki ke ? "
a hankali ta dawo da kallon ta gare shi , ta saki wani dan karamin murmushi ta ce " yanzu fa na tashi da ga barci , ko one minute ba a yi ba da na bude ido "
a hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce " to me ya faru ? ko wani abu ki ke so ? fada min zan je na kawo miki "
girgiza mishi kai ta yi ta na fadin " yaya Zayd ba na bukatar komai a yanzu , kawai ina son na huta , jikina duk a mace ya ke "
a hankali ya sunkuyar da kai ya manna mata kiss saman forehead ya na fadin " okay my Cutie , konta ki huta , dama na zo na fada miki ran Friday za mu tafi Makkah , da ga nan mu koma gidanmu na US "
wani dan karamin murmushi ta saki murya a sanyaye ta ce " da gaske yaya Zayd , za mu tafi Makkah ? "
gyada mata kai ya yi a hankali ya na cewa " har Madina sai mun biya , da ga nan mu tafi DubaΓ― mu yi shopping sannan mu komawar US "
har ta saki wani dan murmushi sai ta marairaice fuska ta na fadin " baby , please tell me , baby nawa na haifa ? don Allah ka fada min , wlh hankalina duk ya ki konciya , da na lumshe idanu sai na dinga jiyo Muryar shi "
wata yar karamar ajiyar zuciya ya sauke , a sanyaye ya ce mata " Cutie , me ki ke so na ce miki yanzu ? "
a hankali ta mike zaune , ta jingina bayanta a jikin forehead din gadon , ta riko hannunshi ta na fadin " ka fada min gaskiya mana , zan fi jin dadin ka fada min gaskiya ko me zai faru hakan zai sa na ji sanyi a zuciya ta , ko dai babyn bai zo da rai ba ? " ta fada ta na dan marairaice fuska
sai da ya dauki lokaci kafin ya ce mata " i'm sorry my Cutie , na yi tunanin in na boye miki hakan ba za ki ji zafin rashin ba , amma gaskiya ne Triplets mu ka samu , sai dai namijin na biyu bai zo da rai ba , I'm sorry "
wata nanauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta lumshe idanunta , ta fara zubar da hawaye
da sauri ya fara goge hawayen ya na fadin " kin gani ko , shi ya sa na ki fada miki , ga shi yanzu ki na kuka "
a hankali ta girgiza mishi kai ta na fadin " ba komai baby , Allah zai ba mu wani , ko ba komai yanzu zan daina wannan tunanin , amma please ina son na ga Nayab , ina so na ga in ya na kama da Nayel din mu " ta kai karshen ta na ware idanunta a sanyaye
girgiza mata kai ya yi a hankali kafin ya ce " i'm sorry my Cutie , amma tun ranar a ka yi jana'izar shi , bayan ni da doctor da nurse biyu sai mama ba wanda ya san wannan maganar , ko je dan kin matsa ne na fada miki , ki yi hakuri don Allah "
a hankali ta sakin mishi kuka ta na fadin " yanzu ka hana ni ganin babyna , why za ka yi haka , da ka bar ni na gan shi mana "
" i'm sorry my Cutie , wlh ban yi hakan dan na cutar da ke , please ki daina kukan nan wlh b....... "
bai kai karshen maganar shi ba kawai ya ga ta koma Aswad lokaci guda ta na daga mishi da karfi ta ce " ka daina ce min na yi shiru , babyna ne ba nata ba , why za ka ce a yi jana'izar shi ba tare da na gan shi ba " ta fada har wani sama gashin ta ya yi kamar a na hura shi da iska
ba karamar razana Malik ya yi ba , har sai da ya mike tsaye ya na karanto kalmar shahada
wasu yawu ma su daci ya hadiye kafin ya ce " please my Cutie, calm down , please , i'm sorry "
ya na gama fadar haka kawai ya ga ta saki kuka , wasu bakaken hawaye na zubo mata , ta na fadin " ka kawo min babyna na gan shi , ka kawo min shi na gani " ta fada a sanyaye kafin ta lumshe idanunta a hankali , nan take jelar gashinta ta zubo saman shoulder din ta
wata nanauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ware idanunta a hankali
shi ma nanauyar ajiyar zuciya ya sauke ganin idanunta sun dawo dai'dai
a hankali ya zube saman guyiwowinshi ya riko kunnuwan shi , ya na fadin " i'm so sorry my Cutie , just na yi tunanin in na boye miki hakan ba za ki ji zafin mutuwar Nayab ba , ban yi tunanin hakan zai cutar da ke ba , i'm sorry , please forgive me , please "
( in na gane wani abu π€π€π€ Nayel shi ya dauko Abyad , Nayab kuma ya dauko Aswad , yanzu da babu Nayab Aswad za ta koma jikin Nailah1 ko kuwa ? )
wani dan karamin murmushi ta sakin mishi kafin ta mika mishi hannu
a hankali ya mike tsaye ya riko hannunta , ya zauna bakin gadon
" babu komai , na gode baby , na san duk abun da ka yi ka yi shi because you love me , kuma ba ka son abun da zai cutar da ni , ko ba komai na so na ga Nayab , amma tunda kai ka gan shi , ni ma kamar na gan shi ne , so it's okay now " ta kai karshen ta na sakin mishi wani dan karamin murmushi
murmushi shi ma ya sakin mata kafin ya kai hannu ya fara goge mata bakaken hawayen Aswad ya na fadin " kin sani , ya na kama sosai da Prince , kamar an tsaga kara , ba abun da ya baban ta su "
murmushi kawai ta yi mishi kafin ta koma ta konta ta na fadin " ni yanzu barci na ke ji baby , kuma in na tashi ina son ka shirya min diner da kanka "
" duk abun da ki ke so sarauniyata "
a hankali ta lumshe idanunta ta na sakin murmushi , ta na a haka ta ji saukar lips din shi saman kumatunta ya manna mata kiss sannan ya mike ya na fadin zai dawo zuwa anjima
gyada mishi kai kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba
da ga haka ya sa kai ya baro bedroom din
har zai fita parlourn MALIKAT HOUDA ta yi saurin ce mishi " da ka tafi da ita ma zai fi , ka zo ka wuce mutane ko sannu babu "
slowly ya juyo ya kalle ta ya ce " ke dai tsohuwar nan kin shiga rayuwata wlh , sai na yi maganin ki nan gama , kar ki damu ki na gani zan zo na dauke ta na tafi da ita ai dama tawa ce ba taki ba , ci gaba da shiga harkata sai na rataye ki , tsohuwa kawai " ya kai karshen ya na juyawa ya fice abun shi
baki sake MALIKAT HOUDA ke kallon shi , har sai da ya fita sannan ta dawo da kallonta kan MALIKAT AL'UMU da ke rike da jikanta ta ce " kin dai ji abun da yaron ki ya ce ko ? kuma ba ki ce mishi komai ba ?
wata yar karamar dariya MALIKAT AL'UMU ta yi ta na fadin " to mamie ya zan yi ? na isa na shiga tsakanin mata da mijinta , um um ku yi dramar ku cen nawa ni dai kallo kawai "
a tare duk mutanan wajen su ka yi dariya har ita MALIKAT HOUDA , ba karya tun lokacin da Malik ke karami ya saba sosai da MALIKAT HOUDA , dan bayan ita babu wanda ya ke yi wa wassan kaka da jika , ita ma bayan shi ba wanda ta ke yi wa irin wannan wassan , jinin su ne ya hadu tamkar ita ce kakar shi ta gaskiya bayan ba shi da hadi da ita
β€β EXILED PRINCE ββ€
( LOVE MEETS POWER ) ππ₯
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
STORY & WRITTEN BY : MEERAH βπ
γTHE ROYALTY LOVE β€πΉγ
γ BOOK ________ 4πββ€ γ
_______________________πβπβπβπβπβπβπ______________________
ο½ P A G E ________ 19 & 20 βππ₯ο½
Bari na dan takaice labarin , a ranar Friday a ka yi duk wasu shirye shiryen dan sake nada Malik , amma wani abun mamaki kawai sai ya ce shi bai dawo dan ya zauna saman kujerar nan ba , kawai ya dawo ne dan ya kwace ta da ga hannun Aymane kuma ya yi nassara , yanzu kuma zai nada wanda ya cancenta sa wannan kujerar bayan shi , da ga haka ya nada Diya da kanshi a matsayin Malik , kuma babu wanda ya yi mishi ja , har ya kammala , sannan ya nada Abdoul a matsayin na hannun daman Diya , nan ma babu wanda ya yi mishi ja
a haka har a ka kammala taron , kowa ya koma part din shi
a misalin karfe takwas na dare duk ahalin Malik su na cikin parlourn shi na part din shi a floor na uku dan har yanzu bai bude floor na hudu ba
a haka ya sanar da su zai koma US dan dama ziyara ce ya kawo musu yanzu lokacin komawarshi ya yi
RIANNA ta sha kuka ta rokon shi ya zauna amma fir ya rufe ido ya ce ta yi hakuri shi dai sai ya tafi
babu yadda su ka iya haka su ka yi mishi bankwana su na yi mishi addu'a Allah ya tsare shi tare da Familyn shi , su na fadin sun yi kewar shi sosai , ya ce duk ranar Friday su dinga zuwa a nan parlourn a karfe takwas su yi video call ya ga in kowa ya na cikin koshin lafiya
da ga haka har karfe goma sha biyu na dare ya yi kowane ya koma part din shi
bayan sallar asuba misalin karfe 5 , su ka raka Malik da Inaya da Twins din ta har airport , su na yi musu bankwana , da ga nan su ka shiga jet din su ya daga ya nufi US
THE END ............
π€£π€£π€£π€£π€£π€£ββββββ WASSA NA KE
βͺAFTER FOUR YEARS
βͺUNITED STATE OF AMERICA ( WASHINGTON DC )
wani kyakyawan yaro ne ya sauko stair , Fari kal da shi kamar ka taba jini ya fito , ya na da kananan idanu Hazel , ga dan karamin hancin shi a tsaye , da bakinshi , lips din shi red color shape din na sama kamar heart , ya na da smooth hair ya zubo mishi bayan keya , sai wasu kananan da su ka zubo mishi a gaban goshi har zuwa wajen eyebrow , ga tambarin masarautar Saudiya a wuyanshi
ya na sanye da wandon Jeans white color , da T-shirt blue color , ya daura wata jacket a sama White color , kafafun shi na cikin wasu sneakers Navy blue , da gani renon madara da ice cream
da gudu ya ke sauko stair din ya na wata yar karamar dariya
kai tsaye parlourn gidan ya nufa
nan ya tardo Malik zaune saman sofa ya na faman latsa laptop din gaban shi , ya na sanye da wandon jeans Blue da polo white color , ya na nan dai bai sauya ba , sai dai har yanzu bai tara gemu ba , smooth hair din nan nashi ya kara tsawo duk da ya na rage shi , ya bazun mishi a baya , ya na aikin shi cikin konciyar hankali
a haka dan yaron nan ya nufe shi , ya Haye sofar ya na fadin " Daddy , tashi mu tafi , ice cream na ke so " ya fada cike da shagwaba
ba tare da ya kalle shi ba Malik ya ce " Prince , ba ka ga aiki na ke yanzu ba , ka bari har zuwa yamma sai mu tafi , ka tafi ka yi barci please , Princess na cen na hutawarta kai ka na nan "
noke mishi kafada Prince ya yi kafin ya haye saman bayan shi , ya na tura shi wai ya sauka su tafi , ya na fadin " No , No , No , ni yanzu na ke son ice cream , kuma yanzu za mu