Showing 1 words to 3000 words out of 19273 words
*TAWA K'ADDARAR 😢*
```TRUE LIFE STORY```
_FREE BOOK_
_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._
```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK...(24) RUHIN JINN PAID BOOK.. (25) JAMI'IN SIRRI C~I~D PAID BOOK 300 ONLY.. (26). SANADIN PARTY HORRO STORY..(27) ASHRAF_LOVE 💞STORY....(28) TAWA K'ADDARAR 😢 FREE BOOK...
loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝```
_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *TAWA K'ADDARAR 😢 FREE BOOK*
_Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._
*Arayuwa zaka burge wasu Kuma zaka bawa wasu haushi, wasu zasu soka Wasu Kuma zasu k'ika wasu zasu yabeka wasu kuma su kusheka, Haka rayuwa take tafiya idan Kama wani wani bazaka masa ba, dukanin Sak'onninku suna zuwa gareni na Yabo da Akasin hakan, ban Damu da zagin wasu ba Domin kuwa nasan cikakkiyar ni'ima tana Aljanna Amma duk da hakan Ni Mujaheedah Matar mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 nakakce Alhmdllh Domin Alk'alamina A tsalkake Yake bana Batsa ko shashanci ko cin zarafin wani ko Aibatawa, Ina Rubutu Kan tsarin tafarkin Ilimi domin bada Shawara nasiha Fad'akarwa Wa'azantar ilimantarwa, kuma Alhmdllh Sak'ona Yana zuwa daidai inda Allah ya nufa Kuma Yana ban Lada daidai da Aikina, kuma Ina Samun Masoya daidai nufin Ubangiji ✨ Inaaa Alfahari daku Masoyana Kuma Ina sonku Tabbas _BASEERARA ITACE ARZIKINA😍_ Allah ya k'ara wadatamu yamuna K'arshe nainyau yasa mucika da imani yabamu Masoya Nagari ya karemu daga Mak'iyanmu, Allah kabama k'asarmu NIGERIA zaman lafiya da Arziki Mai Amfani..... AmeenAmeen......... Mujaheedah Matar mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 HAUSA NOVELS 📚 TAKUCE🥰🥰*
//////////////////////////////
*JINJINATA GADIK ILAHIRIN K'UNGIYAR KING AND QUEEN WRITING CHAMBER 💪*
//////////////////////////
........................................
*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
(Sarki da sarauniya Write's)
*"We Rule The world of Writing"*
https://www.facebook.com/profile.php?id=100063945240173
••••••••••••••••••••••••••••••••••
*INAAA KUKE MATA IYAYEN KWALLIYA DA GYARAN JIKI?? INAA MASU BUK'ATAR GYARA FUSKARSU DAMA JIKINSU? SHIN KINASON RAGE GIRMAN CIKINKI TO KU HANZARTO DOMIN SAMUN NAKU KODA KUD'INKA SAIDA RABONKA MAMAN TEEMA AND MORE 08100100821......... INAAA MASU FAMA DA MATSALAR RASHIN HAIHUWA? INA MASU FAMADA ULCER? INA MASU FAMADA K'IBA ANA NEMAN ARAGE? INAMASU JIKI SIRANTAKA ANANEMAN YIN K'IBAR? INAAA MASU FAMADA SIKILA? INAMASU FAMADA CIWON JIKI?? KAI DUK WANI WANI CIWO DA ALLAH YA HALARTA ADUNIYA TO YAYI MAGANINSA DAN HAKA KU HANZARTO AGUJE DOMIN SAMUN NAKU MAGANINMU BASHIDA MATSALA YASAMU KARRAMAWA DOMIN TINDAGA CHANA YAFITO GHT KENAN KABADA KUD'I MUBAKA MAGANIN MATSALARKA IN SHA ALLAH... HAKA MASU NEMAN MAGANIN MATA KO WANNE IRI AKWAI WANDA HARSAIKIN BADA LABARI HUNNNMMM RIGIJI GABJI WASU KAYA SAI AMALA KAWAI KUYI MAZA KIYI MAZA KAYI MAZA HAD'UWA DA MAMAN TEEMA DOMIN SAMUN MAGANIN MATSALARKI KO WACCE IRI 08100100821 ITACE NUMBER TA DOMIN HAD'UWA DANI KUWA NI MARUBUCIYAR LITTAFAI HAUSA KATUNTUB'I WANNNAN 07064904617 MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 HAUSA NOVELS 📚 CE*
_LABARI MAI TSUMA ZUCIYAR MAIKARATU, YANA KUNSHE DA DARASIN RAYUWA IRI IRI, KUMA LABARIN YAFARU DA GASKE SAIDAI ABUNDA ZAN K'ARA DAGA CIKIN BAIWATA, DALILIN KAWO MUKU WANNAN LABARIN DOMIN YAZAMA DARASI GA Y'AN BAYA, TAWA K'ADDARAR 😢_
*NA SADAUKAR GADIK WATA MACCE ADUNIYA WADDA K'ADDARAR 😢 TAZO IRIN WANNNAN, ALLAH KABAMU MAZA NAGARI MASU TSORON ALLAH.. INA FATAN YAZAMA DARASI GADIK WADDA YAKARANTASHI, KUNSANI DAI KODA YAUSHE INA LITTAFFAINA DOMIN FAD'AKARWA ILIMANTARWA WA'AZANTAR ZUWA NISHAD'ANTARWA ALLAH YASA MUGANE GASKIYA KUMA MUZAMO MASU AIKI DA ITA ALLAH YASA MUGANE*
_BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM_
*Page 1 to 5*
............. Ahankali take tafiya sanye Cikin uniform d'in Islamiyyarsu tadawo, Zaune Yake cikin motarsa tareda Abokinsa daya kawowa ziyara Unguwar kallonta yake har Saida tab'acewa ganinsa ya d'auke idansa Ajiyar Zuciya ya sauke Mai k'arfi,
"Abokina Wai ya'akayi ne Naga kazubamata Ido kodai kanaon Shiga daga ciki ne,"?
"Kamar kasan Abunda ke cikin Raina Aminu Wallahi Kawai inasonta, Kuma Inason na Aureta,"
"To ai wannan badamuwa bane nasanta Sosai muna mutunci tanada kirki Sosai Kuma tanada Ilimin Addini zanmata Magana kaga duk yarda mukayi da ita saina fad'ama"
"Dan Allah Aminu kashawomin kanta ta Yarda Dan wallahi inasonta tinda nafara ganinta nake sonta saboda naganta Kawai yasa nake sintirin zuwa wannnan Unguwar"
"Kada kadamu Komai zaiyu kayi Addu'a Kawai"
............ dawowarta daga Islamiyya ta had'amu da Aminu ya tsaidata, "Malam Sauda Andawo ne,"?
Cikin kulawa ta Ansa"Eh Wllh Aminu yakake,?
"Lafiya k'alau dama Inason Wata Magana dakene in badamuwa Dan Allah"
"Okay bakomai inajinka"
"Maganar Gaskiya Abokina Aiman yaganki kuma yanuna yanasonki Aure Shine Yasani gaba Kafin yabayyana gareki, mutumin kirki ne inkebamu dama Anjima muzo gida tare dashi kiganshi,"
"Shikenan badamuwa saikunzo kaga Kafin Nan nayi magana da kaka,"
"To mungode Sosai saimunzo"
Wucewa tayi, shikuwa Yakira Aiman yamasa Albishir,
Da Sallama tashiga Gidan Kaka A'i ta Ansa
"A'a kindawo sauda"
"Eh kaka"
"Tojeki kicire kayan kizo ga Abincinki nan,"
"To kaka,"
Saida tagama Komai sannan tazo inda take ta zauna tace "Kaka Wai Aminu ne yacemin Abokinsa yana sona Kuma da Aure harma yace Anjima zasuzo tare"
"Masha Allah ai Abun farinciki ne kinsan Aminu ba mutumin banza bane tinda har zai iya baki Abokinsa kinsan shima Yanada kirki Allah yasa Alheri,"
"Ameen kaka"...
Anagama magarib kuwa saigasu, Yaro Yashigo yasanarwa Kaka Anakiranta waje inji Aminu,
Hijabinta tasaka tafita, cikin motarsa yazo saisai duk sunfito waje da Sallama ta K'arasa gurinsu gaisawa Sukayi, sake gabatarmasa dashi Aminu yayi sannan Yawuce,.. Nidai kallon Aminu nayi domin nakasa fassara yanayinsa da Alama Dai Akwai Abunda yab'oye,
"Kamar yarda Abokina Yafad'a miki Ni sunana Aiman Sadiq Kuma bantab'a Auren ba Inason kibani damar Shiga Cikin masu neman auranki Dan Allah"
Kanta Ak'asa tace"Allah yazab'amuna Abunda yafi zama Alheri,"
"Ameen Amma idan bakisona kada ki takura Zuciyaeki,"
"Bakomai Allah Yamuna zab'i Kawai"
"Kina Sona yanzu"
Murmushi kawai tayi tawuce Gida Abunta,
Dariya yayi shikanshi yasan ba kalar Matarda zaiso tak'ishi domin Yanada Kud'i Kyau ga Ilimin Boko,
Kud'i yacire yabawa wani yaro yasa Akaimata gida,
Ahankali shak'uwa maitsanani da soyayya Mai k'arfi tashiga tsakaninsu, Cikin wata 5 duk wasu Samari nata takorasu saboda Aiman Domin tana tsananin sonshi duk Wanda yake tare da ita zaisan hakan,
"Kintabbata kinasonshi Sauda,? Dan bazanso yimiki dole ba Tinda banwa kowa dole Cikin y'an uwankiba,"
Cikinjin kunyar mahaifinta tace"Eh"
"Sauda kinsan halina bana magana biyu wallhi tinda kace kinasonshi komai yafaru daga baya Saidai Kiyi hak'uri,"
"Bama Abunda zai faru in Sha Allah" Cewar kaka
"Ni Kam Abba naso Ace Aminu Sauda ta aura wallahi domin Yanada kirki Kuma Yana...,"
"Haba aunty Rashida ga Wanda kesona Kuma Ina sinahi Zaki kawo maganar wani kuma? Nifa mutunci Kawai ke tsakanina da Aminu,"
"Amma Sauda Aminu....,"
"Ya Isa Rashida rabu da ita, nagane tini idanta yagama rufewa saboda Yaronnan tinda taji tagani Kuma shikenan wllahi duk Abunda zai biyo baruwana tashi kije kice yaturo d'in,"
Mik'ewa Tayi takoma ciki tafad'a masa murna Kawai take domin tana daf da mallakar zab'in ranta,
Rashida kuwa Takoma gidanta Amma Allah Yasani batason Auran Sauda da Aiman gani d'aya tamasa taji baikwanta A Ranta ba,
Shagalin bikin Akafara murna kuwa ba'a Magana gunsu musamman Sauda, kulawa soyayya k'auna duk gani take gun Aiman hakan Yasa take Ganin tafi kowa Sa'ar samun Miji,.. Saidai duk shagalin bikin Aminu bayanan yabar garin Duka cikeda damuwa Wanda bansan meye dalilinta ba,
A yaune jama'a Suka shaida d'aurin Auran Aiman da Sauda Kan sadaki dubu 50,000...........•••••••••••••••
_BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_
WhatsApp number 07064904617
*TAWA K'ADDARAR 😢*
```TRUE LIFE STORY```
_FREE BOOK_
_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._
```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK...(24) RUHIN JINN PAID BOOK.. (25) JAMI'IN SIRRI C~I~D PAID BOOK 300 ONLY.. (26). SANADIN PARTY HORRO STORY..(27) ASHRAF_LOVE 💞STORY....(28) TAWA K'ADDARAR 😢 FREE BOOK...
loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝```
_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *TAWA K'ADDARAR 😢 FREE BOOK*
_Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._
*Arayuwa zaka burge wasu Kuma zaka bawa wasu haushi, wasu zasu soka Wasu Kuma zasu k'ika wasu zasu yabeka wasu kuma su kusheka, Haka rayuwa take tafiya idan Kama wani wani bazaka masa ba, dukanin Sak'onninku suna zuwa gareni na Yabo da Akasin hakan, ban Damu da zagin wasu ba Domin kuwa nasan cikakkiyar ni'ima tana Aljanna Amma duk da hakan Ni Mujaheedah Matar mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 nakakce Alhmdllh Domin Alk'alamina A tsalkake Yake bana Batsa ko shashanci ko cin zarafin wani ko Aibatawa, Ina Rubutu Kan tsarin tafarkin Ilimi domin bada Shawara nasiha Fad'akarwa Wa'azantar ilimantarwa, kuma Alhmdllh Sak'ona Yana zuwa daidai inda Allah ya nufa Kuma Yana ban Lada daidai da Aikina, kuma Ina Samun Masoya daidai nufin Ubangiji ✨ Inaaa Alfahari daku Masoyana Kuma Ina sonku Tabbas _BASEERARA ITACE ARZIKINA😍_ Allah ya k'ara wadatamu yamuna K'arshe nainyau yasa mucika da imani yabamu Masoya Nagari ya karemu daga Mak'iyanmu, Allah kabama k'asarmu NIGERIA zaman lafiya da Arziki Mai Amfani..... AmeenAmeen......... Mujaheedah Matar mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 HAUSA NOVELS 📚 TAKUCE🥰🥰*
//////////////////////////////
*JINJINATA GADIK ILAHIRIN K'UNGIYAR KING AND QUEEN WRITING CHAMBER 💪*
//////////////////////////
........................................
*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
(Sarki da sarauniya Write's)
*"We Rule The world of Writing"*
https://www.facebook.com/profile.php?id=100063945240173
••••••••••••••••••••••••••••••••••
*INAAA KUKE MATA IYAYEN KWALLIYA DA GYARAN JIKI?? INAA MASU BUK'ATAR GYARA FUSKARSU DAMA JIKINSU? SHIN KINASON RAGE GIRMAN CIKINKI TO KU HANZARTO DOMIN SAMUN NAKU KODA KUD'INKA SAIDA RABONKA MAMAN TEEMA AND MORE 08100100821......... INAAA MASU FAMA DA MATSALAR RASHIN HAIHUWA? INA MASU FAMADA ULCER? INA MASU FAMADA K'IBA ANA NEMAN ARAGE? INAMASU JIKI SIRANTAKA ANANEMAN YIN K'IBAR? INAAA MASU FAMADA SIKILA? INAMASU FAMADA CIWON JIKI?? KAI DUK WANI WANI CIWO DA ALLAH YA HALARTA ADUNIYA TO YAYI MAGANINSA DAN HAKA KU HANZARTO AGUJE DOMIN SAMUN NAKU MAGANINMU BASHIDA MATSALA YASAMU KARRAMAWA DOMIN TINDAGA CHANA YAFITO GHT KENAN KABADA KUD'I MUBAKA MAGANIN MATSALARKA IN SHA ALLAH... HAKA MASU NEMAN MAGANIN MATA KO WANNE IRI AKWAI WANDA HARSAIKIN BADA LABARI HUNNNMMM RIGIJI GABJI WASU KAYA SAI AMALA KAWAI KUYI MAZA KIYI MAZA KAYI MAZA HAD'UWA DA MAMAN TEEMA DOMIN SAMUN MAGANIN MATSALARKI KO WACCE IRI 08100100821 ITACE NUMBER TA DOMIN HAD'UWA DANI KUWA NI MARUBUCIYAR LITTAFAI HAUSA KATUNTUB'I WANNNAN 07064904617 MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 HAUSA NOVELS 📚 CE*
_LABARI MAI TSUMA ZUCIYAR MAIKARATU, YANA KUNSHE DA DARASIN RAYUWA IRI IRI, KUMA LABARIN YAFARU DA GASKE SAIDAI ABUNDA ZAN K'ARA DAGA CIKIN BAIWATA, DALILIN KAWO MUKU WANNAN LABARIN DOMIN YAZAMA DARASI GA Y'AN BAYA, TAWA K'ADDARAR 😢_
*NA SADAUKAR GADIK WATA MACCE ADUNIYA WADDA K'ADDARAR 😢 TAZO IRIN WANNNAN, ALLAH KABAMU MAZA NAGARI MASU TSORON ALLAH.. INA FATAN YAZAMA DARASI GADIK WADDA YAKARANTASHI, KUNSANI DAI KODA YAUSHE INA LITTAFFAINA DOMIN FAD'AKARWA ILIMANTARWA WA'AZANTAR ZUWA NISHAD'ANTARWA ALLAH YASA MUGANE GASKIYA KUMA MUZAMO MASU AIKI DA ITA ALLAH YASA MUGANE*
_14/10/2023_
*Page 6 To 10*
.........Bayan Kai Amaryar kowa ya watse, can saigashi da Abokansa sai raha suke Shidai Yanayinsa ba yabo ba fallasa Wanda Ni nakasa fahimta, Addu'o'i Suka musu da nasiha Sannan duk suka watse, kallonta yayi ya d'auke Kansa d'akinsa Yakoma Saida yagama komai yadawo, Ganin haryanzu kuka take sai Abun yabashi haushi Amma yadake "kizo kici Abinci,"
Girgiza Kai tayi Alamar a'a
Baisake tankataba, ga mamakinta saitaga yaci Abinsa kad'an Yarage yatashi Yashiga toilet wanko bakinsa yayi, "Wai still Baki tashiba? Kije kirage wad'annan kayan ko iska kiji, kinzo saiwani kuka kike kamar wadda Akama Auren dole,"
Jinfurucinsa gatsal bako wani lallashi yasa tad'ago takalleshi, Shikuwa ko Ajikinsa Dan harya kwanta gefen gadonma yanata latsa waya yana murmushi,
Tsoro fargaba yasoma kamata kodai musanya Akamata na mijinta wannan ba Aiman d'inta bane,?
Tinaninta ya tsaya cak dataji yajanyota jikinsa yanama wasu Abubuwa,
Cikin tsoro tace"bamuyi sallah bafa,"?
"Banyi kesan kewaice musulma Kuma Mai Ilimi Ni kafirine Kuma jahila, banji zanyiba Kuma bawanda ya Isa Yasani nayi Abunda nayi niya shi Zanyi," had'e bakinsu guri d'aya yayi,
Nidai Matar mlm Sainayi waje inatinanin meke Shirin faruwa gameda wannan Auran??
Washe gari nashiga d'akin kwance naganta sai kuka take gwanin tausayi domin Rashin Imani Yamata muraran ko sallah takasa tashi tayi shikuwa tinda yagama samun burinsa Yabar d'akin, d'akinsa ya koma ya Kwanta kife da ciki bacci yana bacci harda safe Around 10:00 duk bacci yake Abunsa, ko sallar Assuba yau k'intashi yayi,
Agogon d'akinsa Yasoma kukan k'arfe 10:30 Ma'ana dai yana tashinsa ne domin hakan ne k'a'idarsa tatashi daga bacci, mik'ewa yayi Yashiga band'aki yayi Alwala yayi sallah Wanka yayi Yashirya cikin k'ananan kaya kyawonsa maijan Hankalin Y'an Mata ya bayyana turarukansa yabulala jikinsa, Wayarsa yasoma nema banganiba hakan yatina masa tana d'ayan d'akin Kai tsaye yanufe d'akin
Lokacin tasamu tamik'e da k'yar harma tayi sallah tanakan sallaya tana kuka Wayarsa dake gefenta tasoma ruwa, ganin tak'i dainawa yasa takai Hannu tad'auka ga mamakinta saitaga sunan "MY SUGER BABY" yana yawo gabanta yabuga da k'arfi, tini wani sashen Zuciyarta yasoma Bata Shawarar tad'aga, jikinta na rawa tad'aga takara Wayar a kunnenta, D'ayan b'angaren akace"Haba baby danka Aure wannan k'azamar shine zaka shareni Duka jiya baka kirani ba, kanacan kana Abunda kasaba Kai wallhi Aiman bunsurune Sam Bakada aji ko Wacce Macce saikabi, kadafa kamanta da amincewata ka Aureta, yanzu idan nabuk'ace karabu da ita dole kasaketa, Nidai kazo yanzu Ina inda muka saba had'uwa Ina buk'atarka ne, kuma,...,"
Shigowa d'akin yayi mugun kallo yake jefamata ganinta tana waya da Wayarsa Kuma jikinta sai rawa yake tana Hawaye, d'aure fuskarsa yayi tareda mik'a Hannu Alamar tabashi Wayarsa,
Cikin tsoron Yanayinsa tamik'a Masa yakai dubansa ga wayar Ganin Mai Kiran yasa Yad'aga da sauri
"Waimeke damunka inata Magana tind'azu kayi shuru banason bura'ubafa Aiman kasan halina wallahi,"
"I'm so sorry my suger Baby network d'inne yake cracking, yanzu Ina zamu had'u,"?
"Hotel mana yau banajin Zama ko Ina sai hotel Ina new hotel room 121"
"Oka ganinan zuwa my suger Baby," dogon kiss yasakarwa Wayar sannan yakashe,
Kallonsa take cikeda mamaki tsoro takaici, shima mugun kallo ya watsa mata Kafin ya K'arasa inda take, hannu yasa yakama kunnenta yaja da k'arfi Saida tayi k'ara Kuma Cikin rashin Imani yasa Hannu yabuge Mata baki da k'arfi Saida yafashe Yace"will you keep quiet? Wannan shine na k'arshe dazaki sake d'agamun waya zakiga mezan miki banza bak'auya kawai,"tureta yayi yayi ficiewarsa nanta duk'urshe tana kuka tajima hakan ganin numfashinta yana barazanar d'aukewa yasa tadaina ga yunwa tana Addabar cikinta mik'ewa tayi tana d'ingishi tasoma neman kitchen, Koda tashiga bakomi ciki duka ya kwashe kayan Abinci harma wad'anda Aka kawo gidansu duk bakomai Zama tayinan tasake saka kuka,
Shikuwa yana fita Saida ya d'auke Komai na Abincin yasa Cikin boot d'insa sannan yabar gidan bayan yarufeta tabaya,
Hotel d'in yanufa can suka Soma masha'arsu da shangiyarsu, sai kusan 12:00 sannan suka rabu yadawo Gida A hanya yasai mata shinkafa da wake yahana Asamata komai hakan gaya yasiyota Kuma tinta safe yace Abashi,
Koda yashigo tana Zaune palourn tajingina da kujera duk tafita hayyacinta yunwa tagama galabaitar da ita, d'auke kansa yayi kawai yajefamata ledar yayi shigewarsa d'akinsa yakwanta Abinsa,
D'aukar ledar tayi tabude shinkafar tayi Sanyi sosai domin Cikin fridge Akacirota Batada zab'i dole tacita hakan tana kuka maiban tausayi...............................
_BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_
WhatsApp number 07064904617
*TAWA K'ADDARAR 😢*