Showing 18001 words to 19273 words out of 19273 words

Chapter 7 - Tawa Kaddarar Book 1 Complete Hausa Novel

GASKE SAIDAI ABUNDA ZAN K'ARA DAGA CIKIN BAIWATA, DALILIN KAWO MUKU WANNAN LABARIN DOMIN YAZAMA DARASI GA Y'AN BAYA, TAWA K'ADDARAR 😒_

*NA SADAUKAR GADIK WATA MACCE ADUNIYA WADDA K'ADDARAR 😒 TAZO IRIN WANNNAN, ALLAH KABAMU MAZA NAGARI MASU TSORON ALLAH.. INA FATAN YAZAMA DARASI GADIK WADDA YAKARANTASHI, KUNSANI DAI KODA YAUSHE INA LITTAFFAINA DOMIN FAD'AKARWA ILIMANTARWA WA'AZANTAR ZUWA NISHAD'ANTARWA ALLAH YASA MUGANE GASKIYA KUMA MUZAMO MASU AIKI DA ITA ALLAH YASA MUGANE*

*PAGE 91 TO 100*

FINAL FINAL FINAL FINAL PAGE.......

*INA ROK'ON ALLAH INDA NAYI DAIDAI ALLAH YABANI LADA INDA NAYI KUSKURE KUMA ALLAH YA YAFEMIN, INDA KUMA NAYI MUKU MISTAKE READER'S KIYAFEMUN, ALLAH YASA DARASINDA NA KOYAR CIKIN WANNAN LITTAFIN YA ANFANARDA AL'UMMA BAKI D'AYA, INDA AIKI MAIKYAU YAKE ALLAH YABAMU IKON D'AUKA INDA AKASINSA YAKE ALLAH YAKAREMU DAGA AIKATASHI,.. INA K'ARA BAMU SHAWARA MUJI TSORON ALLAH, KODA YAUSHE KUKA A KO INA, SANNAN MU AURE MAZA MASU ADDINI FIN MASU KUD'I, MUMA MUNEMI NAKANMU MUYI SANA'A MUDAINA ZAMAN ROK'O KODA GA MIJINE ALLAH YA HOREWA KOWA NASA YASAMU ABUN DOGARA DA KANSA AMEEN.... INASONKU MASOYANAAAAAAAA DUK INDA KUKE MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🀱 QUEEN OF WRITER πŸ“ TAKUCE KODA YAUSHE IN SHA ALLAH. KADA KUMANTA KUTAMUN ADDU'A MUSAMMAN TA LAFIYAR IDANUWANA NAGODE......*

.... Innalillahi wa'inna ilaihin Rajuun, shine kalmominda mutanen gurin keta fad'a duk Wandake gurin Yashiga tashin Hankali Mara misaltuwa, dagudu Nas yak'arasa inda yake Cikin tashin Hankali yakamashi tareda taimakonku mutanen gurin suka Wuce Asibiti, direct Emergency Akashiga da, har lokacin bakinsa baidaina fidda jiniba, oxygen Aka mak'alamasa Domin dawoda numfashinsa dake neman guduwa jini kuwa saifaman K'ara masa suke, duk likitocin Asibitin Hankalinsu yatashi ganin irin Yanayinda yake ciki,

Cikin damuwa nas yakirasu Abba da ziyat Ikon Allah ne kawai yakawosu lafiya, Ganin yanayinda yakeciki yasa take Mom tafad'i tasuma gurin, dak'yar Akasamu tadaidaita duk Jarumta irinta Daddy Saida yayi hawaye,..

Lallashinta yayi dak'yar yasamu tayi shuru amma duka Hankalinta yanakan Yanayinda tabar Aiman ciki, tabbas tasan soyayya Gaskiyace kuma Wanda kafara so tunfarko tofa ko yaushe shine zakacigaba da k'auna, duk Abunda take dauriya kawai take dankar yagane yadamu, Harda mafalkinsa tayi,.

Saida yakwana Uku sannan yadawo hayyacinsa Hawaye kezuba daga idanuwansa suna rufe"Mom Dan Allah kudawomin da Sauda itanakeso,"

"Kayi hak'uri soon yaudai naji kunya nakasa baka Abunda kakeso, baka tab'a tanbayata Abuba karasa Amma wannnan karon bazan iyaba Aiman, naji Labarin komai daga ziyat Aiman Kayi hak'uri taka k'addarace haka,"

"Daddy kune kuka cutardani domin Bakubani tarbiya maikyauba bakununamin Mahimmancin d'an Adam ba Kud'i kawai nasani da shalhiya nakasa gane Rayuwa na k'ararda Rayuwata Abanza yanzu Daddy Ina soyayyarda Kukemun kunkasa dawomin da Sauda kunkasa dawomin lafiyata kaicona Inama mutuwa nayi Nidai *TAWA K'ADDARAR 😒* Bata kasance maikyau ba, nas tinda Sauda bazata dawo gareniba tayafemin Aminu Yabani dama nahad'u da ita narok'eta yafiya Kafin namutu," yak'ara maganar Yana kuka

Dakansa Shida ziyat Suka nufe gidansu Dr Amin Saidai Koda suka isa sunfita, maigadin kesanar dasu suntafi gidansu kakarsuce ba lafiya, direct cansuka wuce, cikin Rashin sa'a Kuma dukansu sund'unguma zuwa Asibitin amma sunji Asibitinda Aiman yake Akakaita, suna Isa cikin Sauri sukafito d'akin suka nufa Saidaima bakin k'ofasuka had'u, Cikin sauri nas yak'arasa Inda suke yace"Dan Allah dr Aminu kadube girman Allah kabari Sauda tazo taduba Aiman wllh yanacikin mawuyacin hali kuma sunanta Kawai yake fad'a itakawai yakeson Gani Dan Allah,"

"Wani Abu yasameshi ne,"? Cewar Aminu cikin tausayawa domin ganinsu firgice yasan ba lafiya ba,

"Eh wllah tinsanda kuka had'u yana fita yayi hatsari Shine kukaga annuna alabarai Wanda Motar ta k'one wllahi motarsa,"

"Subhanallah yana Ina Yanzu,"?

"Yanacikin Asibitin Nan Emergency Anason fiddashi waje dank'ara duba lafiyarsa,"

"My dear muje muganshi ko,"

Tindasuka fara maganar Zuciyarta ke halbawa da K'arfin jin yayi hatsari kuwa datina yarda motar tayi saiduk Suka k'ara d'agamata Hankali amma tadaure d'auke Kanta tayi Kafin tace"Allah yabashi lafiya nidai ba indazani,"

"Haba Sauda Ubangijima idanmuka Masa laifi muka rok'eshi yafiya zaimana Afuwa Amma Meyasa mu Y'an Adam bazamu kasance masu yafiya ga Y'an uwanmuba, Dan Allah Abba kusaka baki wllahi Aiman yanacikin wani hali Kuma yayi laushi,"

"Nasani mu masu laifine gareku amma yau gani inamai k'ask'antarda kaina gareku Dan Allah kuyafemuna sannan Sauda kizo kiga d'ana dan Allah," duk'urshe k'asa daddy yayi gabansu yana kuka,

Sosai dukansu sukaji tausayinsa lalle kowa da tashi k'addara, binsa Sukayi ganin halinda Aiman yake ciki kuwa ko wannensu Saida ya koka bama kamar Sauda domin takasa furta kalma d'aya, Hak'ik'a so Shu'umine kuma duk Wanda kafaraso tunfarko Lalle Soyayyarsa bazata gushe cikin rankaba Koda kuwa bakwa tare domin soyayyar farko tadabance musamman ta tsakani da Allah,.

Cikin matsanancin kuka tace"kadaina magana Aiman bakada Lafiya, bazaka mutuba zakatashi kadaina Fad'in zaka mutu ba Yanzuba saikagama tuba ga Ubangijinka, kayi imani da k'addara wannnan itace taka k'addarace ka ansheta hannu biyu daga Allah ne kamar Yarda na Anshe *TAWA K'ADDARAR 😒* nayafemaka Aiman," kukane yaci k'arfinta hartana durk'ushewa k'asa

Murmushi maizafi yayi"nagode Sauda Allah yasaukeki lafiya Dan Allah Amin idan kuka haife Namiji kusaka Masa sunana, wannnan itace *TAWA K'ADDARAR 😒* nak'arba Kuma nagode Allah"

"In Sha Allah Aiman kuma zaka tashi kacigaba da rayuwa Had'id'a neman tafiyar Ubangiji,"

"kubarshi Haka yahuta surutun ya isa kowa yayi waje Dan Allah," Cewar d'ayan likitan

Addu'a da karatun Qur'ani sune suka ragemata Abunda takeji gameda Aiman,

Shikuwa Aiman k'asar waje Akafita dashi Aiki Akamasa ga K'afarsa kuma Cikin Ikon Allah Anyi nasara bayan yaji Sauk'i dagacan Sukawuce Ummara Sosai yarok'e Allah Kuma Cikin Ikon Allah Yasamu dama har yacire Sauda cikin Ransa Saidai yakan tina da ita kuma yana mata fatan Alkhairy,

Koda yadawo Nan Yasami labarin matarsa shila garin bin mazan nata tabi wani matsafi yayi tsafi da ita Yabada Rayuwarta Abbanta kuwa Bak'inciki yazama silar had'iye Zuciyarsa yamutu,

Sauda tahaihu Kuma Yara 2 Macce d'aya Namiji d'aya kamar Yarda yayi masa Alk'awari hakan takasance yasa Sunan Aiman, sosai Aiman yayi murna Kuma yana k'aunar Yaron Sosai, da k'yar Akasamu yayi Aure Zaman lafiya yakeda matarsa inda yagama rungumar k'addara Kullum Cikin istigfari yake Kuma Alhamdulillah Yasami sauk'i..............

BAYAN SHEKARA BIYAR Zaune suke dukansu sai raha suke ko wanne fuska d'auke da murmushi domin sungama d'aukar k'addararsu, yanzu Aiman yara 2 Mace da Namiji maccen taci Sunan Sauda Sosai yakeji da Yarinyar,..

"wannnan ai itace *TAWA K'ADDARAR 😒* nagama Imani"Cewar Aiman

"Haka nima Naga *TAWA K'ADDARAR 😒* Kuma na K'arb'a," Cewar Sauda

"Hahaha Tina baya Kawai kuke ai Nima Naga *TAWA K'ADDARAR 😒*"

Dariya sukayi dukansu, tareda had'a Baki gurin Cewa"Yanzu kuma Duka K'ADDARAR 😒 Takoma Alkhairy Alhmdllh Kawai zamuce, Allah yak'ara bamu ikon bin Gaskiya da tawakkali Cikin ko Wacce k'addara, *TAWA K'ADDARAR 😒* dama taka zuwa tasu Allah yabamu Ikon cinyewa,"............β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’

_ALHAMDULILLAH_

17/11/2023 NOVEMBER FRIDAY

*Allahumma Ameen ya Rabby 🀲 Ni Mujaheedah Matar mlm Ammyn khausar 🀱 QUEEN OF WRITER πŸ“ na Ansa Kuma Ina K'ara Rok'on Allah daya Bamu ikon cinye jarabawar k'addaramu Allah Yasa muyi K'arshe maikyau mucika da Imani 🀲, Allah Yabamu maza masu imani tsoron Allah Ilimin Addini masu k'aunar mu saboda Allah masu sonmu da Zuciya d'aya Allahumma Ameen ya Rabby 🀲 Kuma kowa ya Amsa da Amin.............*

*Kada KUMANTA da sani Cikin Addu'o'in ku Masoyana Allah Yabani lafiyar Idanuwana Kuma yakareni daga mak'iya wad'anda nasani dama wad'anda bansaniba, Allah Yasa mudace 🀲 nice dai taku harko YAUSHE MAISON GANIN FARINCIKINKU DAMA D'EBEMUKU KEWA ZUWA TUNATARDAKU DA ILIMANTARWA WA'AZANTAR NICE DUKA ✍️MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🀱 QUEEN OF WRITER πŸ“ HAUSA NOVELS πŸ“š*

_BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_

WhatsApp number 07064904617

5
6
7

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login