Showing 27001 words to 27367 words out of 27367 words

Chapter 10 - Kasaita Book 2 Hausa Novel Complete

sannan ya riƙe kunnuwa ya gwale idanuwa,dama abu (Tubarakallah) inji Malam bahaushe. Sannan ya ce, "Sorry." Dole ne ma na yi dariya, na yi murmushi kuwa sai ya yi saurin rungume ni.

Ya ɗago kaina ya goge hawayen fuskata. "Kin yi haƙuri?" Na ɗaga kaina.

"Ban yarda ba, sai kin ce eheee."

Yanda ya tale baki ya ce eh, dole ta sa ka dariya, na sa dariya na daki ƙirjinsa da dukkan hannayena, ya girgiza kansa alamar jin daɗi sai ya rungume ni tare da faɗar "I love You too." Nima na amsa masa da "I love You too much." Amma a zuciyata,na koma na ƙara lafewa a ƙirjinsa.

**** **** ****

Satinmu huɗu a Greece,amma wurare ɗai-ɗai ne ban sani ba, balle ma da muka shirya sosai da shi. Ƙasar London,Rum(Italy) da kuma Turkey,duk su ma satinmu bibbiyu, wanda idan na haɗa su waje ɗaya mun ƙwashe watanmu biyu da sati biyu.

Yau kuwa ranar Asabar ce, wacce ta yi daidai da ita ce ranar da muka iso Nijeriya, sai da ma Yarima ya tashe ni daga bacci ya sanar da ni an zo Nijeriya, wanda tun da muka shiga jirgi ya janyo ni ya ƙwantar a ƙirjinsa, ɗan wasannin shafa mini baya ya kama yi, wannan ne ma yasa har bacci ya ɗauke ni ba tare da na sani ba.

Maƙale nake a kafaɗar Yarima har muka iso bakin ƙofar fitowa daga jirgi cikin ɗan ƙaramin lokaci na yi saurin janye jikina daga gare shi, saboda hango mutanenmu da na yi sun zo taryarmu. Dogarawa kenan. Ya janyo ni jikinsa.

"Me ye haka,mun iso Nijeriya za ki fara gasa ni, wallahi sai mu koma."

"Kalli gabanka." Na faɗa a lokacin da muke sauka matattakalar benen jirgin.

Waziri ne da sauran manyan fada a tsaye suna jiran saukowarmu, ban da dogarawa waɗanda sun kai ashirin, motoci kuwa sun cika filin jirgin Jos International Airport,da gani ka san na taryar mu ne. Cikin sakan ɗaya na ga Yarima har ya rikiɗe ya koma Yarima na da dana sani, da na juyo na kalleshi ta wutsiyar idanuwana ni kaina sai na ji tsoronsa ya sauko min.

Alhamdulillah!

Mu haɗu a littafi na uku. Daga Mai ƙaunarku.

Aunty Maryam Kabir Mashi.















Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login