Showing 12001 words to 15000 words out of 27367 words
take na ji jikina na neman kama rawa,me ye wannan? Ni dai na san har yanzun ba na son Yarima, sai dai na san ina jin kunyarsa.
Na mayar da kaina ga karatuna, amma ni kaina sai na ji muryata ta canja,lumfashina kuwa ma nema yake ya tsaya,a zuciyata nake rayawa cewa in ajiye littafin in tafi gidana, madadin in ji ƙwarin gwiwa sai na ji tamkar an sare mini gwaiwoyina,cikin hakan da nake kawai sai na ji Yarima na kiran sunana a hankali.
Jin kiran sunana ma sai na ji ya ƙara sani na dake, na dawo dai-dai saboda tunanin ko Yarima ya fahimci na shiga wata matsala da na san ba zan iya faɗarta ba,kiran sunana ya kamata a ce ɗaya ne ko biyu, amma tun da Yarima ya fara shi ban ji ya tsaya ba, tun ina ci gaba da karatun har ya zama ina saukar littafin hannuna a hankali izuwa ƙirjina.
Kallona sai ya koma ga yarima da yake kirana, wanda idona ya hango ƙirjinsa na fitar da numfashi da sauri da sauri, wani mashi ne na ji ya dirar mini ta tsakiyar kaina, jikina na ji har ya ɗauki rawa cikin sakan ɗaya, saboda kiran da Yarima yake mini ya fi ƙarfin a tsaya ƙirgawa.
Littafin saman ƙirjina wanda hannuwana suka taimaka masa ya zauna a ƙirjin nawa, sai na ji ya faɗo saman cinyata saboda hannuwan nawa sun kasa ɗaukarsa,jiri ne ya ɗauke ni ko kuwa suman sakan biyu na yi? Ni dai ji na nayi na sulale na ƙwanta saman gado sosai a riginginan da nake da ƙyar na ja filo ɗaya ya tallaɓe mini kaina.
Amma duk wannan bai hana Yarima kiran sunana ba, idanuwana, kaina,jikina sun yi mini nauyin da ba za su iya motsawa ba, balle har ƙwayar idona ta samu ganin halin da Yarima yake ciki,ko ni kaina,shin me ye wannan? Ni na san ƙwaƙwalwata ta daina aiki balle in tunano amsar abubuwan da suka tarar mini a cikin mintunan da ba su wuce uku ba.
Mai nake ji a jikina? Kamar numfashin mutum a hancina, ƙwaƙwalwata na ji na karanto mini Yarima na bin jikina, hannayena da ke ware ya bi da hannayensa a hankali har izuwa tafukan hannayena ya haɗa da nashi ya runtse gam, sumbatar wuyana na ji ya yi, ya dawo hancina,bakina,buɗaɗɗan gaban ƙirjina da riga ba ta ƙarasa rufe shi ba.
Ni na san ina ji, amma ba zan iya motsa ɗan yatsana ba, balle har ya kai ni ga iya magana,ko ƙwatar jikina ba, sai dai na san numfashina yana fita sama-sama, ina jin shi kanshi ya ruɗe ya rasa ina zai kai sumbatar nasa,ko ina ya yi ina jin sa yasa haƙoransa ya zuge zib ɗin da ke gaban riga ta, wai nan na yi ƙarfin hali zan yi magana, amma madadin bakin da na samu da ƙyar na buɗe in yi magana sai gani na tsaya da wani irin numfashin da ya kasa wucewa cikina, ya tsaya mini cak a maƙoshina,saboda jin harshen Yarima na lasar fatar cikina, sai a lokacin na ji kamar na tunano ban sa shimi ba,rigar mama ce kawai na saka da zan taho.
Jin ya nutsa hannayensa a gashin kaina yasa na samu da ƙyar lumfashina ya isa cikin cikina tare da faɗar "Hasbunallahu wani'imal wakil" sai na ji kamar ɗan jinin jikina ya dawo, na samu na yi ɗan ƙoƙarin miƙewa zaune, amma ina sam na kasa, saboda Yarima da ya samu ƙaramin taɓin hankali a jikina.
Da ƙyar na buɗe idanuwana sannan na ɗaga kan Yarima na tallabo kumatunsa na girgiza kaina, wanda fuskata ke fitar da hawaye da ban fahimci ta ina suke fitowa ba, yasa hannuwansa duk biyun ya ɗago kaina ya girgiza kanshi shi ma, sai a nan na lura da hawayen da suka wanke fuskarshi shi ma, da ƙyar na ji ya ce, "Yasmin!"
Yana mayar da numfashi ɗaya bayan ɗaya. Na girgiza kaina da ƙarfi, sannan na samu na miƙe na zauna, ya koma gefe ya ƙwanta rigingine yana wani irin numfashi. Na miƙe tsaye, tafiya na fara nayi luuu zan faɗi, na yi saurin zaunawa, na nutsa hannuwana a gashin kaina, jin ya rarrafo ya zo ya rungume ni yasa na ɗan samu ƙarfin cire hannuwansa daga jikina na miƙe.
*ƘASAITA BOOK 2*
*NA*
*MARYAM KABIR MASHI*
Page 7
Na mayar da zib ɗin rigata na zuge, na samu na ja mayafina da ke saman gado ba zancen tsayawa yafawa, sai da na je ƙofa, sannan na tsugunna na ɗauki takalmana a lokacin idanuwana suka sauya kallo izuwa saman gadon da Yarima ke durƙushe yana kallona ya ware hannayensa yana ɗan girgiza kansa kada in tafi.
Ganin ina kallon shi yasa na ji yana kiran, "Please Yasmin come to me." Wannan ma yasa na juya na tafi, sai kuwa da na je ƙofar fita, sannan na samu na yafa mayafina, amma takalma sai da na je ƙofar gida, sannan na iya sa su, ina buɗe ƙofa kuwa taku uku na yi na tuɓe su na riƙe a hannuna ina isa ɗakina na wurgar da su.
Fitilu kawai na kashe na faɗa saman gadona ban tsaya neman wata rigar bacci ba,fulalluka na haɗa na rungume a ƙirjina,ni kaina ban san me zan tunano ba saboda ƙwaƙwalwata ma ta daina aiki, sai dai numfashina kam ya dawo, amma da ɗan sauri nake fitar da shi tamkar na yi gudu na gaji.
Ban fi mintuna biyar ba na ji an murɗa ƙofata an shigo, da ƙyar na samu na lalubo wayar makunnan fitilar ɗakina ina kunnawa sai na ga Yarima a tsaye, yanda rigarsa take haka take ma yanzu, na lumshe idanuwana na mayar da kaina na ƙwantar alamar mamaki,jin an mayar da ƙofa an rufe yasa na ɗaga na kalleshi, ban yi wani ƙoƙarin tashi ba.
Ganin ya nufo gadona yasa na fara tunanin me zan yi yanzu ban tunano komai ba na ji ƙarar faɗuwa, kallon da zan yi sai na ga yarima a ƙasa na yi wata doguwar wuntsulawar da ban san ma ina da ƙarfin yin ta ba,ni dai gani na nayi kawai a gabansa na ɗago shi na girgiza shi, cikin wani yanayin muryar tashin hankali na kira sunansa.
Cikin sakan uku na ga ya buɗe idanuwansa yana murmushi,ni kuwa har na fara fita daga hayyacina a cikin ƴan sakannin nan, sai na ji kawai na yi ƴar dariya, shi ma sai ya ƙara yin murmushi, sannan ya tashi ya zauna ya kishingiɗa a cinyata da take durƙushe, sai a lokacin ne ma hankalinmu ya kai ga abin da ya kada shi. Takalmana ne da na yi jifa da su muka gani a gefe ɗaya, yasa hannu ya ɗaga takalman ya kalleni sai kuwa muka yi dariya gaba ɗaya, amma irin mai kama da murmushin dariya,yana cikin haka ne ya juyo ya haɗa goshina da nasa, sannan ya rataye hannayensa bayan wuyana. Cikin yanayin dariya ne ƴan hawayen da suka fito a lokacin da nake faman son in ga ya tashi suka gangaro, sai na ji ya saki takalmin ya ɗago fuskata yasa hannayensa duk biyun ya lalubo kumatuna, sannan yasa manyan ƴan yatsunsa yana goge mini hawayena tare da girgiza kansa alamar a'a.
Sai kuwa na jina lumshe idanuwana ina yin ƴar wata dariyar kuka-kuka, murna-murna, sannan na sunkuyar da kaina sosai na ci gaba da ɗan kukan murna,gashin kaina kuwa ya zubo ya rufe mana fuskokinmu. Ina jinsa ya sa hannayensa ya tattare gashina, sannan ya ɗago kaina da hannayensa, kallon da ya yi mini yasa a take na ji na nutsu, saboda haɗa ido huɗu da muka yi da shi,kafin in yi wani motsi tuni ya kai bakinsa ga nawa, kafin inyi wani tunani har ya lalubo harshena ya riƙe.
Wasu tsutsotsi na ji suna yawo a kaina na yi sauri na ƙwace bakina, amma sai na ji kuma na faɗa ƙirjinsa na ƙwanta,jin ya mayar da ni ya rungume tare da sumbatar gefen wuyana cikin nutsuwa na ji ya ɗagoni yana sumbatar ko'ina na jikina, wata zuciya ta dinga karanta mini maganar da Aunty ta yi mini amma wajen da ta ce.
"Muddin jikinku ya fara haɗuwa, to dole ne so ya shiga mai tsanani, ba zai iya rabuwa da son taɓa jikinki ba, har sai ya tabbatar da kin zama tasa, wannan kuma shi ne zaman aure mai haifar da so,ƙauna,kulawa da juna,ki yi haƙuri idan hakan ta iso gare ki, wannan shi ne auren."
Kafin in dawo daga tunanin sakan uku sai dai na ji kamar jikina ba riga, kafin in yi wani abu sai na ji har hannuwan rigar mamana sun dawo cinyar hannuwana, kafin in ƙarasa tuna me nake ciki, sai na ji laɓɓansa a saman ƙirjina.
Tabbas ajiyar zuciyar da ya fitar mai ƙarfin gaske ba ta hana ni ɗago kansa ba, na girgiza kaina, wanda idanuwana ke a rufe,jin ya ambaci sunana cikin wata ɓoyayyiyar murya yasa na yi saurin miƙewa tsaye,a tangal-tangal na isa bakin gadona na zauna,a lokacin ne na samu damar gyara rigunan jikina, na ɗago na kalli Yarima Faysal da ke durƙushe a inda na bar shi.
An ɗauki mintuna biyar kowa na haka, sannan na ji ya zo ya zauna kusa dani, ya ɗauki wata minti biyun kafin ya yi komai ko in ce yayi magana, ya ɗan ja numfashi a hankali, sannan na ji ya fara magana.
"Ya kamata a ce komai ya wuce a tsakaninmu,ya kamata a ce yanzun mun amince da junanmu ko ma samu rayuwar aure mai ƙyau,ni na san laifina ne tun farko, amma yanzu ni na san dole in zama ƙasa gare ki, na yi tunanin shi mulki ko ina ma yinsa ka ke yi ashe ba zai yiwu ba ga iyalinka ba waɗanda ka ke ƙauna, waɗanda su ne rayuwarka gaba ɗaya."
Kada ki ji haushina ko kiyi mamakina, wallahi Yasmin ban san aure ba, ban san so ba ban taɓa tsayawa na kalli ƴa mace ba balle har in ji ta a jinin jikina. Yasmin sai ke,ki ture auren haɗi a tsakaninmu,ki mayar da shi mu ne muka ga juna muna so,in ke ba haka ba ne a zuciyarki wallahi ni,ni na ganki na ji ina son ki tun ranar farko.
A lokacin da na zo gidanku ganin ke ce ki ka fito matsayin matar da aka zaɓa mini na ji daɗi,sanyi a zuciyata, amma tsananin mulkin da yake a kaina ya hana ni nuna miki. Ke wallahi na ma nuna, tunda da ba ke bace ba,ba kowacce ta isa in tako in bata haƙuri har in bi ta gidan Yayarta.
Yasmin na baki rayuwata gaba ɗaya, wallahi ba zan iya rabuwa da ke ba, har sai na ga kin zama jinina, na zama naki. Yasmin ke ce wacce ta taɓa sace zuciyata gaba ɗaya. Ki tausaya ki so ni,ko ƙya dawo mini da zuciyata ta cigaba da tunanin rayuwa da ke.
Na san za kiyi shakkun zama da ni, wallahi ki cire duk wani shakku,ki ɗauka kin samu mijin da sai abin da ki ke so za'ayi miki, matsawar bai saɓawa shari'a ba,na karanta takardar Aunty na ji matsalolinki,ki yi haƙuri, zan ɗauki mataki mai ƙarfi a kan abubuwan da ba ƙya so a cikin gidana.
Ki yi tunanin yanzun kunnuwa da idanuwan Sarki da jama'a da dama yana kanmu ya kamata mu kuma mu basu mamaki." Ya sauko ya zo saitina ya durƙusa a gabana.
"Yasmin ki rufa mini asiri kada ki sa a raba ni da ke, wallahi mutuwa zan yi idan..."
Na yi sauri na sauko na rufe bakinsa da tafin hannuna,ni na kasa gane kaina, ina son Yarima ko kuwa tausaya masa nake yi? Ya kamo hannuna ya sumbaci bayan hannun, sannan ya juyo da tafin hannunsa ya miƙo mini.
"Na fi son ki amince da kanki,ki ɗora mini amanarki a tafin hannunki ki saka mini ita a nawa tafin hannun,in kuma har yanzu ba ƙya sona ki bani amanar ni zan yi miki abubuwan da zasu sa ki so ni."
Na kalli tafin hannun sannan na juyar da kaina.
"Please, Yasmin,kada ki guje ni don Allah." Na tashi na koma na zauna a gadona, ya ƙara matsowa ya ɗora hannunsa a cinyata.
Na tunano yanda Sarki ya ce mini da irin ƙaunar da ya nuna mini,na tuno Mamee tare da Dadyna, na tunano Aunty Salwa,na ga ita ma kamar yanda aka kawo ni haka aka kai ta, amma yanzu ƴaƴanta uku,shin ko shi ne son? Ko shi ne auran? Na juya na kalli Yarima da ya ƙura mini idanuwa,na tuno irin mulkin da ke gare shi, ban da dukiya da barori,ƙarti da ƴanmata, da tsofaffi, amma yau ga shi yana yi mini magiya da in so shi.
Zuciyata a take ta amince da in so shi, na juyo tafin farin hannuna na kalla, wanda na ga tsagu guda uku manya, amma na tsakiyar ya shiga cikin babban ɗaya, ke nan ni da Yarima, sai son da Yarima ke mini ne ya shiga cikin jikina, na matsa, hannuna na ɗora a saman hannunsa sai na ji ya yi ajiyar zuciya ya riƙe hannun nawa sosai.
Na samu na karɓe hannuna sannan na koma gadona na ƙwanta a gicciye, ina jin Yarima ya taso ya zauna a gadona, wanda ya lalubi makunnin fitila ya kashe, sai dai na ga duhu a cikin runtsatstsan idanuwana, ina ji ya juyar da ni nayi rigingine ya zuge zib ɗin da na lura ya tsone masa ido, idanuwana na ƙara runtsewa da ƙarfin gaske a lokacin da na ji ya juyar da ni yana saɓule rigar jikina.
Na yi saurin ƙanƙame jikina da na ji hannayensa na ƙoƙarin ɓalle ɗan masankallin da yake riƙe da rigar mamata, na runtse hannuwan gam da na ji ya kai wa tsakiyar bayana sumbata, ban dawo daga tafiyar balaguron da na yi ba sai naji ya haɗani ya rungume a ƙirjinsa ta bayana, gashin da ke ƙwance a ƙirjinsa ya tsirar mini fatar bayana, tabbas na fitar da numfashi wajen kala goma a lokaci ɗaya, amma har a yanzun na kasa gane me ye so da ƙauna.
**** **** ****
Motsin da na dinga ji yana tashi sama-sama cikin hankalin, shi ya farkar da ni daga baccin da nake yi, na buɗe idanuwana da ƙyar sai na ga hasken fitilar gefen gadona, amma ta ɓangare ɗaya, na ɗan juyar da kaina a hankali gudun kada inyi motsi da ƙarfi. Yarima na gani tsaye gaban durowata ɗaure da tawul a jikinsa. Kunya ta saukar mini tare da wani ɗan saurayin murmushi, duk da na san hankalinsa ba kaina yake ba, ina kallo har na ga ya janyo wasu kayan daba zan iya shaidasu ba, saboda ɗakin babu haske sosai, ina kallonsa ya iso wajen gado ya ajiye su a inda na yi saurin runtse idanuwana ganin yana shirin cire tawul ɗin jikinsa.
Cikin dabara na mayar da kaina inda yake da farko,bai fi minti ɗaya ba na ga ya nufi gaban madubina ya ɗauki turarena ya fesa, wata wauta irin ta Yarima har da sumbatar ƙwalbar turaran nawa sannan ya ajiye kai tsaye ya nufo inda nake ya zauna kusa da ni sosai.
Na yi saurin lumshe idanuwana tamkar bacci nake, ina ji ya dinga shafa kumatuna, ya shafi gashin kaina, ya sunkuyo ya sumbaci kumatuna, yasa hannu ya dinga zagaya laɓɓana.
"Beautiful,Ina roƙon Allah ya taimakawa rayuwarki, yasa ke ce matata har in mutu, ya sa ki haifa mini ƴaƴa masu tarbiyya kamar ki. I love You."
Ya ɗaga hannuwana da suke waje ya janyo bargo a hankali ya lulluɓe ni, sannan ya sumbaci kafaɗa ta.
Ina jin motsin janyo durowa a hankali, bayan ƴan mintuna kuma sai na ji an rufe ta, ina jin tashinsa can kuma na ji ya dawo ya sumbaci bakina.
"I miss You." Ya zaro hannuna ya tura a ƙirjinsa.
"Kin ji yanda ƙirjina ke bugawa don zai rabu da ke." Ya miƙe ya tafi.
A hankali na buɗe idanuwana sosai amma zuciyata ta cika da tunanin ina Yarima za shi a cikin daran nan? Na ɗauki wajen minti uku ina tunani tare da al'ajabin fitar Yarima da dare kamar haka,ban kai ga tunani ko baiwa kaina amsa ba, sai kawai na ji ƙarar tashin mota, hankalina na ji ya tashi matuƙa, wannan ne yasa na yi saurin ƙwaye bargon da ke lulluɓe da ni cikin sauri na miƙe saboda kawai in ga inda motar za ta tafi a tsohon daran nan.
Cikin lokaci ɗaya abubuwa uku suka saukar mini shi ne mayar da ni baya da aka yi aka ƙwantar da ƙarfi, al'ajabi alamar tambaya. Al'ajabi shi ne ganin jikina ba kaya. Tambaya kuwa,me ya sameni naji jikina ba ƙarfi? Mayar da ni baya kuwa shi ne jikina na ji ya riƙe gam, ga mugun ciwo da na ji yana yi.
To me ye kuma? Kafin in karanto amsa kuwa, sai gani ina kokawar jan bargo da lulluɓe kaina saboda firgita da nayi jin wata ƙara na tashi kusa da ni, cikin rawar jiki na samu na lalubo makunnan da ke ƙarƙashin filona tare da karanta Ayatul kursiyu na daure na kunna fitilar ɗakina.
Hasken da ya gauraye ɗakina ya yi sakan uku kenan da kamawa amma sai ta cikin bargo na iya leƙo idona ɗaya, da ido ɗayan nan na dinga bin ɗakina da kallo,in ga ta inda ƙarar nan ke fitowa,saman ƙaramar ƴar durowar da ke kusa da gadona (side bed) na ga ɗan ƙaramin agogon tsugunno, sai a lokacin na ji ɗan kuzarin miƙa hannu in ɗauko shi domin kashewa.
*ƘASAITA BOOK 2*
*NA*
*MARYAM KABIR MASHI*
Page 8
Lokacin da agogon ya nuna kuwa biyar saura ƙwata na asuba. Me ya fitar da Yarima ƙarfe biyar saura? Ko dai suna da wani abu ne na sarauta wanda suke yi daidai wannan lokacin? Ni kaɗai ke tunanina, da agogo a hannuna, na ɗan ɓata raina, na girgiza kaina, shi kenan rayuwata ta ƙare, sai da na amince da Yarima, sannan wani