Showing 6001 words to 9000 words out of 27367 words
ofishin da yake (Cooporate Affairs Commission).
Mahaifinshi ya tsufa, mahaifiyarshi ce mai ɗan jini a jika, wanda gidansu su huɗu ne kacal,yayyansa biyu, mace da namiji, sai kuwa ƙaninsa namiji ɗaya. Ni kaina na san ina son Anwar, Mutumin da muka shekara uku da shi muna (Friending), amma rashin auranmu da shi tun a baya, na san laifina ne, tare da ƙaddarar auran Yarima Faysal.
Iyayensa ƴan asalin Kano ne, aiki ya kawo mahaifinsa na Likitan dabbobi, suna da arziƙinsu daidai gwargwado, ga shi mutum ne mai tausayin gaske ni kaina na san Anwar na matuƙar ƙaunata.
**** **** ****
Wazirin Sarki,Galadima,Tafida, Talba da Durɓi,su ne a tebirin shawarar Sarki, wanda Sarki Jafar Sada ya tarasu ne a kan hukuncin da ya yanke a raba auran Yarima Faysal da Gimbiya Yasmin,saboda su ne mutanen da suka fi kowa kasanci da shi fiye da kowa.
An ɗauki ɗan tsayin lokacin da za'a iya ba shi sa'a ɗaya (awa ɗaya), ana mahawara a kan maganar, wanda a ƙarshe magana ta koma ta basuyi na'am da hukuncin da Sarki ya yanke ba, saboda dalilai da suka kawo irin nasu na manya, kamar dalilin waziri.
Ya Kawo dalilinsa ne a kan nan gaba idan suka nemi aure za'a iya hana su, saboda za'a ga ba sa riƙe aure da daraja, dalilinsa na biyu kuwa shi ne,a bar yaran da kansu su zo su ce basa son junansu,in sun zo da zancen haka, ina ga in an raba su ba za'ayi laifi ba wajen kowa.
Galadima kuwa cewa ya yi a kan samu haka a tsakanin ma'auratan da aka haɗa aure, ma'ana waɗanda ba su suka zaɓi junansu ba. Shi kuwa Tafida cewa ya yi abin kunya ne a garesu a ce sun yi wa ɗansu aure wanda suka tara jama'a ba iyaka daga garuruwa, jahohi, ƙasashe, amma a ce ƙwanakin da ba su wuce arba'in ba aure ya rabu, alhalin muna taƙama da cewa shi ne magajin Sarkinmu a nan gaba.
Shi kuwa Durɓi cewa ya yi anyi daidai da aka ja masu kunne aka tsorata su, amma maganar rabuwa ma bata taso ba,a kira su dai a ƙara ba su lokaci, idan har ba su sasanta kansu ba, to sai a haɗu da iyayen yarinya a ƙara tattaunawa, daga nan sai a nemi shawarar da ta fi cancanta, sannan yana mai baiwa Sarki shawarar ya je ya samu iyalinsa ya lalubi wani abu daga gare su na game da yaran, saboda su mata ne za su fi mu samun labarinsu.
*ƘASAITA BOOK 2*
*NA*
*MARYAM KABIR MASHI*
Page 4
A nan dai suka tashi saboda ganin juma'a ce za'a fita Masallaci da wuri. Sarki ya shiga ya kira iyalansa,Mama Mariya ita ce mahaifiyar Yarima, sai kuwa Hajiya Kilishi wacce take mahaifiyarsu Ahmad ga ta amarya.
Ya gaya masu shawarar da ya yanke a kansu Yarima, amma yana mai tambayarsu shawarar ya suka gani.
Hajiya Kilishi ita ta fara magana,haba Shugaba ya za'a yi a ji irin wannan maganar daga bakinka, alhalin ku ne manyan da ku ke yankewa ƙanana hukunci,haba mai girma,ai ka san auran haɗi dama ya gaji haka kafin ma'auratan su saba. Ka tuna kanka mana,watana nawa a gidan nan ban saba ba, yanzu fa ka ga a sai mutuwa kawai ta rage mini a cikin gidanka.
Ni a shawarata mai girma a sa masu ido, tun da an ɗan tsorata su, balle ma yanda naga shi Yarima na yawan zuwa gidan nan,a lokacin da aka dawo da Yasmin nan gidan,kai a taƙaice sai na kore shi gida yake tafiya in dare ya yi. In kuwa suka shige ƙuryar Mama sai su ƙwashi awanni, sallah kawai ke fito da shi,don ma yarinyar na da kunya,waya kuwa in dai har ba ya cikin gidan nan har gajiya muke yi da ɗauka, sai na cewa yarinyar ta taimaka ta ɗauka, sannan zai bar mana kunnuwa su huta. A fahimtata dai Yarima ya sauko, ita ce dai ke da saura, kuma ka san dan tana mace, akwai kunya irin ta mata,ko Mama kin yi shiru?"
"Me zan ce ai kin gama faɗa, ƴaƴanki ne fa, shawarata ɗaya in har da ragowar zamansu tare,to ki kira ɗanki ki ja masa kunne, saboda laifin na wajensa,ai ya ba ni labarin duk abin da ya haɗa su tun farko."
"Allah ya huci zuciyar Sarki,a ƙara dai duba wannan magana." Inji Hajiya Kilishi.
Ya miƙe, "Zan je in huta kafin tafiya masallaci, zan duba maganar insha Allahu."
"Godiya muke,a huta lafiya, sai ka fito." Inji su gaba ɗaya.
**** **** ****
Sarki Jafar Sada ne zaune a doguwar kujerar mulkinsa, amma ta fadar cikin gida, kenan ɗakin shaƙatawar da yake ganawa da iyalinsa. Ni da Yarima kuma muna zaune a tsakiyar fadar,kowannan mu kanshi a sunkuye a ƙasa,ko ban faɗa ba kuwa na san daga ni har Yarima gabanmu faɗuwa yake yi, saboda na kalle shi ta wutsiyar ido ko motsi ma baya iya yi, saboda sanyi da jikinsa ya yi.
Cikin ɗan satar kallo ta wutsiyar ido na kallo fuskar Sarki, gumi ne ya fara tsiyayo mini a fuskata,tun kafin in dawo da kallon gabana, saboda ganin fuskarsa da na yi ba wani annuri cikinta, ballantana alamar wasa. Na ƙara mayar da satar wutsiyar idon nawa ga yarima, na gan shi yana mayar da ajiyar zuciya, duk bayan sakan biyu, ban da gumin da na hango yana yi wa kansa magangara a jikinsa.
Take kawai sai na ji tamkar in sa haɓar mayafina in dinga goge masa, wannan ne ma yasa na ji kamar zuciyata na ɗan kiɗan da ba sauti, balle ta samu ƴan rawa, hakan kuwa shi ya tunano mini daran jiya yanda muka ƙwana.
A daran jiya ni na yi imanin babu wanda ya samu runtsawa ni da Yarima, dalilin da yasa na gane hakan kuwa shi ne,ganin saman ɗakinsa da fitila duk da ba mai haske ba ce ba,a tunanina ta gefen gado ce ma ya bari a kunne. Na gane hakan ne a sakamakon leƙen da na kusan ƙwana ina yi ta labulayen taga ta,wai ko na ga Yarima a ƴar barandarsa, yanda ya saba. Amma har na gaji na haye gadona ban ga ko da ƙyallin kayansa ba, wannan ya ba ni tabbacin bai samu yin bacci ba,ƙila gara ma ni tunda na samu na shiga bargona na yi lamo. Inji Malam bahaushe ya ce, "wacce ta fi barci daɗi." To ni dai jiya, wacce ta fi barci ciwo na yi.
Saboda har yatsun hannuna sai da suka yi mini ciwo, saboda jan carbi,wai ko ya suɓuce daga hannuna in samu bacci ya ɗan ɗauke ni, amma sai dai na gaji na ajiye na cigaba da lazimin cikin zuciya, sai dai wani abin al'ajabi zan ce ko abin haushi? Wai har a wannan lokacin sai na ji zuciyata har gangar jikina sun ƙi amincewa da suna iya zama da Yarima Faysal, mutumin da yake taƙama da mulkin ƘASAITA,shin ko dai ni ce ban san son ba, ban kuma san makarai da makangan so ba? Tambayar tawa babu mai amsa mini ita.
Ganin har ƙarfe uku na dare ta yi yasa na miƙe na yi alwala domin in ragewa kaina da zuciyata zafin da suka ɗauka, sannan in roƙi Allah da ya zaɓa mini abokin zama wanda yake mafi alheri a gareni, Anwar ko Yarima, saboda ni na kasa gane wa nake so a cikinsu.
Ƙarfe goma na safiyar yau juma'a sai ga ɗan aike daga fadar Sarki,magatakarda ya kawo mini saƙon zungureriyar takardar da ta ƙara tayar mini da hankalina,dama daga wanka na fito, cikin nauyin jiki don ma na samu na ɗan gyara fuskata, da ɗan mutstsuka mai ina shirin saka kayana saƙo ya iso mini.
Tun da na zauna a gefen kujerar tsakiyar ɗakina ban iya ma buɗe takardar ba, saboda ji nayi kamar kaina ba a wuyana yake ba,ni kaina ban san iya mintunan da na ɗauka ba a nan zaune, sai da Mansura ta shigo sannan na ji tana tambaya ta wai lafiya? Duk maganar da take mini a farko na ɗauka mafarki nake, sai da na ji an dafa mini yatsun ƙafafuna, sannan na ɗaga na gan ta a durƙushe gabana.
Ban san hawaye nake fitarwa ba sai da na dawo hankalina ga shi duk tafiyar nan da na yi ban ji na je kowacce duniyar tunani ba,ni dai cewa na yi ko kuwa don haukan minti biyar ɗin da aka ce duk ɗan adam na yin shi duk rana kenan dai shi na yi a zaune.
Miƙawa Mansura takardar na yi na ce karanta mini da ƙarfi. Da ta karanta sai na ji ba wata takardar tafiya gida ba ce,ko ince takardar rabuwa da Yarima ba, ashe ta saƙon in je Sarki na kirana ce,in an sauko daga masallaci,tana gamawa na ce mata je ki waje ga ni nan zuwa, to ina za ni? Wa zan gayawa? Tunanin da na cigaba da yi kenan.
Cikin mintuna baƙwai sai na ji Aunty Salwa ta faɗo mini a raina, na yi sauri na miƙe na ɗauko wayata na daddana nambobin, minti ɗaya aka ɗauka, ina fara gaya mata abin da ke faruwa. Ya isa haka ta ce mini,in je tana son ganina,ba zancen waya ba ne ba, saboda haka in tambayi Yarima in fito da wuri,in biya ta gidanta.
Wannan fa ya bani ƙwarin gwiwar in shirya in isa gidan Yarima,a yanzun ɗin nan. Baƙar shadda ce Galila, wacce aka yi wa aikin hannu, duk ta sha ɗigon farin aiki, ƙasan zanin kuwa aiki ne mai yanka-yanka, iya kusurwar cinya yake, sai hannu iya rariyar hannuna, duk ya sha tsagun irin na jikin zanan.
Turare na ɗauka hannuna ina shirin fesa shi a jikina, sai na ji murɗawar ƙofar ɗakina a hankali, ban yi tunanin juyawa in ga kowa ke shigowa ba, saboda ganin ina tsaye a jikin madubi kenan ko wa ye zan gan shi ta cikin madubina. Gabana na ji ya yi wani abu wanda ya ratsa mini naman jikina ya bi ta cikin jinina har ya fito ga saman fatata. In da gashin da ke saman fatar duk ya miƙe tsaye, wannan ne na ji ana cewa tsigar jiki.
"Me ya kawo mini? Ganin Yarima da na yi ta cikin madubina ya shigo da doguwar rigar bacci jikinsa mai wani irin aikin sarauta, amma iyakacinsa bakin ƙofa, ya jingina da ƙofar ya mayar da hannayensa ya goya a saman ƙirjinsa ya harɗe ƙafafunsa da juna, tare da mayar da kai ya jingina shi a jikin bakin ƙofa sannan ya ɗan ɗaga kansa sama da turaran a hannuna na ɗan wayance na iso wajen da yake a tsaye.
"Yarima barka da asuba."
Ya juyo da kanshi ya kalleni, sannan ya amsa da laɓɓansa ne kawai na ga sun motsa, har da lumshe idanuwa da buɗewa.
"Lafiya?"
Ya juyo ya kalleni,a take na ga idanuwansa sun yi jajir.
"Da ki kaga me?"
Ya faɗa cikin maganar raɗa-raɗa.
"Idanuwanka na ga sun yi ja.”
Sai na ga ya yi murmushin da ya dinga fitar da sauti, sai na ga ya wuce ni ya shiga cikin ɗakin ya samu kujerar da ke tsakar ɗakin ya zauna, sannan ya ɗago hannu ya yafito ni, ya nuna kusa da shi, ma'ana in zo in Zauna. Ban wani nuna damuwa ta ba na iso amma sai na ji na kasa zama saman kujerar na koma gefe ɗaya na zauna a ƙasa, madadin ya yi magana shi ma sai na ga ya zamo ƙasa ya zauna kusa da ni, na yi alamar zan matsa, gaba ɗayan shi ma ya juyo gare ni tare da kaikansa wuyana. Cikin maganar raɗa na ji ya yi magana.
"You hate me.”
Ya ƙara yin sama da kan shi zuwa daidai kumatuna.
"Sarki ya aiko in je."
Na yi saurin faɗa ina mai alamar tashi, yasa hannuwansa duk biyu ya rungumo ni jikinsa ta gefena.
"Yarima."
"Yasmin, Yasmin, Yasmin,jiya na ƙwana ina roƙon Allah ya cire mini ke daga zuciyata but still... Na lura ke har yanzu zuciyarki ba ta son zama da ni." Ya yi murmushi.
"Nayi tunanin in zo in yi sallama da ke, Idan har na fahimci ke har yanzu you don't want to stay with me,saboda ni na san halin Sarki, ba ya sauraran komai idan ya riga ya faɗi magana.”
Duk wannan maganar da yake yi a cikin raɗa yake yin ta, irin ta marar lafiya, sannan ga shi ya matse ni a jikinsa, sai shinshinar min wuya yake,yana ƙara tura kansa cikin wuyana,ni kuwa idanuwana a lumshe suke ban da numfashina da ke neman ɗaukewa.
"Ba zan iya tsallake duk hukuncin da Sarki ya yanke min ba, amma zan ɗan yi iya ƙoƙarina in ga ko na samu nasara.”
Ya yi shiru a daidai lokacin da ya juyo da fuskata a tasa.
"Amma na yanke hukuncin barin ƙasar.”
"Saboda me?" Na faɗa a sanyaye nima.
"Saboda ke.”
"Kai da baka so...” yasa yatsunsa biyu a laɓɓana yana zagaya su, wannan yasa ban iya ƙarasa magana ta ba.
Na yi ɗan hanzari kaɗan na miƙe, saboda jikina da na ji ya fara rawa.
"Wai me ye haka Yarima?”
Na yi irin maganar nan wacce da ji na da ƙyar na ƙwato ta daga bakina, ya mayar da numfashi ya kai sau baƙwai, sannan ya miƙe tsaye.
"Sorry.” ya juya ya tafi, har ya kai ƙofa na tuno da maganar zuwa gidan Aunty Salwa,na yi masa magana.
"Yarima,ni zan je gidan Aunty Salwa yanzu, bayan masallaci nima zan wuce Sarki ya aiko in je."
"Ki gaishe ta.” Kawai ya ce ya juya ya fita,a inda nake tsaye a nan na durƙushe na yi wajen minti talatin sannan na samu da ƙyar na miƙe na ƙarasa shiryawa.
Ban ƙara ganin Yarima ba sai da na shiga ɗakin Hajiya a nan ne take ce min Yarima na cikin ƙuryar ɗakinta a ƙwance, ban iya tambayarta ba ko lafiya sai na ji zuciyata tana son ta ganshi, na san kuwa ba zan taɓa iya wuce Hajiya in nufi ƙofar dakinta ba, har na zauna na ji ta ce, "Shiga ciki mana ki zauna man baƙi sun yi yawa, balle ma yau juma'a." Na ce to, tare da saurin tashina.
Amma ina shiga sai na ga Yarima ya juyo da kansa ya kalleni ya mayar gefe ɗaya, na isa bakin gadon a daidai lokacin da nake zaro takardar da Aunty Salwa ta bayar in kawo masa.
"Gashi in ji Aunty." Ya juyo ya kalleni ya lumshe idanuwansa kamar wanda ake ƙoƙarin ƙara masa ruwan ledar asibiti, domin ceto ransa daga ciwon amai da gudawa da ya yi masa mummunan kamu. To haka na ga Yarima na buɗe idanuwa da ƙyar.
Ya zaro hannu tamkar hannun ya yi masa nauyin ɗagawa ni kuwa na ɗora masa takardar a kai, madadin in zauna sai na dawo falo na biyun Hajiya na zauna saboda ba zan iya zama a wajensa ba......
Maganar da Sarki ya fara ita ta katse mini tunanin da na tafi, wanda a cikin mintuna biyar kacal na yi shi.
"Yau ne ranar da muka yi alƙawari da kai zaka zo mini da abin da na umarce ka, ina jiranka."
Yanda na ji cikin naman jikina na rawa haka kuwa na tabbatar Yarima na cikin halin da ya fi nawa, da jin maganar da Yarima yake yi,ka san a tsorace,a firgice,a nadamance da kuma karfin hali irin na maza yake yin ta. Bayan ya miƙe da ƙyar ya koma can kusa da Sarki.
*ƘASAITA BOOK 2*
*NA*
*MARYAM KABIR MASHI*
Page 5
"Baba ka yi mini afuwa a kan abin da na aikata maka na rashin ƙyautatawa,a baya na yi alƙawarin ba za ka ƙara kama ni da wani laifi ba na rashin ƙyautatawa ba."
Sai na ji ya rage sautin maganar ta juya izuwa sanyi da rawar murya.
"Ba..ba yan...zun ina son abin da ka ke so, zan iya zama na har abada da abin da ka ke so." Ya yi shiru.
"Yanzun me ka ke son inyi maka kuma? Bacin ka kunyata ni ka tozarta ni a idon jama'a."
Ina kallo ta wutsiyar idanuwana ya ja jikinsa ya matsa sosai kusa da ƙafafuwan Sarki.
"Baba ka yi mini hukuncin duk da ka ga ya dace da ni, wallahi zan ɗauka matsawar dai yin hakan zai huce zuciyarka zai saka ka yafe mini.
"Ka zaɓi ɗaya cikin abu biyun nan,auranka ko sarauta."
"Baba duk wanda ka zaɓar mini ina so."
"In zaɓa maka ka ƙara yi mini yanda ka ga dama."
"Baba ka yi haƙuri, wallahi kuskure ne,ba zan ƙara ba har abada."
"Koma ka zauna, zan yi tunani a kan ka, ke kuma ki gaya mini gaskiya zaki iya zama da shi ko kuwa?"
"Duk hukuncin da ka yanke ya yi mini nima."
"Tashi je ki ciki."
"Na gode." Na miƙe a sanyaye na nufi ciki.
Tsayin mintuna arba'in Yarima ya yi shi da Mai Martaba, amma ni ina ƙwance saman lanƙwasashshiyar kujerar Mama, na yi lamo alamar bacci nake yi, ina ji ya shigo suka shiga ƙuryar ɗaki da Mama sun ɗauki mintuna sun kai ashirin sannan suka fito, ina jin shi ya yi sallama ya fita.
Bayan sallar la'asar ne,Mai Martaba Sarki yasa aka kira ni zuwa fadarsa ta cikin gida, zan iya kiran lokacin da huɗu da rabi na yamma,ni da Mama muka shiga fadar wacce ita ƴar rakiya ce, wani sanyin daɗi na ji ya sauka a zuciyata,a lokacin da Mai Martaba ya ce Mama ta zauna ita ma. Ba mu fi minti biyu da zama ba sai ga Hajiya Kilishi ta shigo.
A nan Sarki ya umurce ta da ta zauna, wanda dama alamar da ta nuna Sarkin ne ya aika a kira ta. Maganganu, misalai,nasihun da suka yi mini yasa a take na ji zuciyata ta karaya a kan duk wani abu da na ƙudura a kan Yarima na game da wahalar da shi.
Lallai Yarima ya samu yabo a wajen mahaifansa, da kishiyar Mama, Hajiya Kilishi, ta faɗi irin halayyarsa da suke ji, ita ma, sai na dinga jinsa a zuciyata a take kuma na tunano