Showing 9001 words to 12000 words out of 27367 words
kalaman Aunty Salwa waɗanda ta karantar da ni tsantsar so kuma me ye shi da tafiyar da wanda ake so.
Na dawo hayyacina lokacin da na ji Mai Martaba ya ce, "Ƴata ina fatan za ki gafartawa mijinkin abubuwan da ya yi miki a baya, na rashin ƙyautatawa, saboda ya yi nadama ya nuna ba zai sake ƙwatanta miki su ba, ya nuna mini yana son matarsa."
Yabo, nasiha da maganganun da Mai Martaba da iyalansa suka yi mini shi ya sanyayar mini da jikina, sannan Sarki ya yi mini alƙawarin yi wa Yarima hukunci, matsawar bai gyara halayyarsa ba, ya tabbatar mini da sati ɗaya ya bani idan har na ga ba daidai ba,in sanar da shi. Irin maganganun mutane da suka yi mini sun sa na ji alamar ɗan ɗigon wani abu a zuciyata, wanda na tuno da Aunty ta ce wai shi ne alamomin so.
Ƙarfe shida saura mintuna goma sha baƙwai motocin ayarina suka shiga get ɗin gidan Yarima,wai sai na ji na tsinci kaina cikin wani irin nishaɗin farin ciki. Mu ma muka sauka inda ake ajiye motocin gidana. Yarima na hango a tsaye ya jingina da ɗaya daga cikin ragowar motocin da ke ajiye a rumfar ajiye motocin.
Dukkan hannayensa ya saka su a aljihunsa ƙafafuwansa kuwa ya harɗe su a waje ɗaya, tabbas sai na ga ya ƙara yi mini ƙyau,ko kuwa don baƙar T.Shirt ɗin da ke jikinsa ce ta ƙara haska shi dama abu ga farar fata. Amma yanayinsa ya nuna mini da ganinsa cikin ɗan ruɗani yake, saboda yana hango motocina sai na ga ya yi saurin miƙewa tsaye sosai.
Murmushin da nake yi kuwa,ni na san ya shiga har zuciyata, motocin na tsayawa shi ma na ga ya ɗan taho alamar zai iso ga motata, ganin an buɗe mini na fito shi ya sa naga yayi tsaye cak, tare da mayar da ajiyar zuciyar da ta fito fili, wanda ya yi ta cikin lumshe idanuwansa duk biyu. A hankali na ga ya zaro hannu ɗaya daga cikin aljihunsa ya shafi gashin kansa da shi, sannan na ga ya buɗe idanuwansa ya ɗan ɗaga su kaɗan ya kallo ni.
Ni kuwa tuni har na kusa zuwa inda yake a tsaye, saboda ita ce hanyar da zan bi in shiga cikin gidana,ni kaina na san na canja tafiya, amma wani abin ban mamakin da na yi shi ne ina isa inda yake tsaye sai na ji ba zan iya yi masa magana ba balle har ta kai ni ga tsayawa wajensa. Sai dai kawai na yi murmushi na raɓa ta gefensa na wuce.
"Kin tayar mini da hankalina,kin daɗe sosai."
Maganar da na ji ya yi daidai lokacin da na zo zan wuce ta kusa da shi, na ɗan juyo da kaina na ɗan kaɗa idanuwana tare da yin murmushin da na san ya ƙara bayyanar mini da ƙyan fuskata,ƴar lotsawar gefen kumatuna ta bayyana a fili (Dimple), wacce na tabbatar ita ce sirrin fuskata.
Na juya na nufi gidana a inda ina shiga falo wayar hannuna na yin ƙara, Yarima na ga an rubuta tare da lambarsa na yi murmushi na kanga wayar a kunnena.
"Hey!" Na faɗa.
"Muryarki ta yi mini daɗi a zuciyata, ita kaɗai dama nake son ji ko hankalina ya daɗa ƙwanciya."
"Wa ke magana ne ban gane ba?"
"Yasmin mijinki ne." Na yi murmushi na kashe wayar.
Ina aje wayar ƴan matan suka yi mini sannu da dawowa na amsa masu tare da ɗan ɓata mintuna biyar a wajensu, domin in basu nasu haƙƙin, na lura kuwa hakan na yi masu daɗi matuƙa. Ina hawa ban tsaya komai ba sai hidimar wanka, saboda ganin magriba ta kawo jiki sosai.
Yau kam addu'ata ta sha bamban da ta kullum, tunda yau na yi ta ne a kan Allah yasa Yarima ya ci gaba da sona har abada,ni kuma Allah yasa inji ina son shi,in gane son in aikata shi nima, Allah yasa in dinga yi wa Yarima biyayya a kan duk abin da ya umurce ni da shi.
Ƙarar wayata ita ta ɗan sa na waiga na kallo ta saman gadona, har na kawar da kaina manufata ba zan ɗauka ba, sai na yi tunanin ko Aunty ce, wannan tunanin ne yasa na miƙe cikin ɗan hanzarina na isa ga wayar tawa. Yarima na ga an ƙara rubutawa. Na yi murmushi na kanga a kunnena.
"Don't say hello to me. Saboda muryarki na rikita ni, ina gayyatarki cin abinci ƙarfe taƙwas na daren yau."
Kafin in yi magana har ya kashe. Na koma da baya na ƙwanta saman gadona na lumshe idanuwana haɗe da murmushin daɗi,nan take na tambayi kaina shin ko dai ina son Yarima ne? A take na ji ƙwayar idanuwana na karanto mini fuskarshi,shin ko wannan shi ne son? Na yi saurin tashi ina girgiza kaina,kai a'a,ni na san ba na son Yarima. Na yi tsaki na miƙe na nufi ƙasa wajen ƴan matan gidana.
A hankali suka dinga ba ni labari,a nan har na dinga zolayarsu da cewa ko wacce sai ta gaya mini sunan saurayinta. Muna cikin haka wayar da ke falo ta ɗauki ƙara, tana nuna mana alamun an bugo waya kenan. Mansura ce ta yi saurin zuwa ta ɗauka, cikin sakan ɗaya da kanga kan wayar a kunnenta na ga ta yi saurin durƙushewa ƙasa, sannan na ji tana gaishe da mai maganar. Yanda take yi tamkar tsaye take a gabansa, sai dai na ji ta ce, "To." Da sauri da sauri na ga ta iso gabana bayan ta ajiye kan wayar ta tsugunna tamkar tana neman in gafarta mata daga wani laifin da ta yi mini sannan ta yi magana.
"Allah ya taimaki Gimbiya, Yarima ne ya ce ki ɗauki wayar hannunki." A take na ji gabana ya faɗi, wanda ya yi daidai da kallon agogon da ke manne a kusurwar falon. Ƙarfe tara saura mintuna sha takwas,nan na tunano gayyatar da aka yi mini ta zuwa cin abinci ƙarfe taƙwas na daren yau.
Cikin ɗan gaggawa na nufi sama tun kafin na isa falon sama na ji wayar tana ta kukan kirana, na yi saurin gudu na isa, tare da saurin kanga wayar a kunnena.
"Hey." Na faɗa cikin muryar da tafi kama da ta marar lafiya.
"Na san kin gane na samu kaina cikin son ganin ki,shi yasa ki ke wahalar da ni." Shi ma tamkar ba shi da lafiya yake mayar mini da amsa.
"Sorry."
"Ina jiran ki."
Bai jira na mayar da amsa ba na ji ya kashe. Na ƙurawa kan wayar ido, tamkar zan ga hoton Yarima a ciki, na yi murmushin da ya ratsa jijiyoyin jikina, sannan na miƙe.
Ƙarfe tara daidai ina gaban madubina ina kallon jikina, riga da siket ne na atamfar Super Holland, ɗinkin wanda ya bi jikina ne, shi ne mai (shape) babu wani ƙwalliya a gaban ɗinkin sai dai buɗaɗɗan wuya ne mai zagaye. Sai kawai dogon zib tun daga saman wuya har izuwa bakin ƙugu, wanda makamin zuge shi,zamu iya cewa ya yi kama da ɗan ƙaramin zobe, shi kuwa siket ɗin irin ɗinkin nan wanda ƙarshensa buɗaɗɗe ne sosai.
Takalman dana saka, basu da wani tsini sosai, mayafin jikina kuwa kalar takalman ne, wanda suka yi shige da ɗaya daga cikin ƙwalliyar atamfar wato ja, turaren (Glorious Lonkoom) shi na feshe jikina da shi, wanda wayar G.S.M ce mai kalar ja a hannuna. Na yi murmushi sannan na tambayi kaina, shin me yasa nake jin farin ciki a zuciyata? Na lumshe idanuwana haɗe da tunanin wai ga Yarima nan zai rungume ni ta bayana.
Na buɗe ido da ɗan saurina har da ƴar ƙara haɗe da ɗan tsallena, tamkar da gaske, na yi dariyar da na ji tamkar yau ne ranar da aka yi mini wahayi da farin ciki, sannan na nufi gidan Yarima.
Falon ƙasa na yi sallama na shiga, kafin in rufe baki mutane sun kai baƙwai suka zube a gabana suna kirari da gaisuwa a gare ni, na amsa masu cikin nuna nima fa ƴar mulki ce, kafin in ƙarasa wajensa,tuni an malala mini wata lallausar darduma a wata kujerar da ke kusa da shi da alama ta mulkinsa ce.
Yarima kuwa yana ƙwance a gadon mulkinsa mai kama da katifa,ko in ce kujera mai hannuwa, amma mai faɗin gaske, ban da fitilu da ke zagaye da ita, ita kanta katifar mulkin sai ka tattaka hawa biyu sannan ka same shi ana uku ƙwance,ke nan kamar kana hawan matattakalar bene.
Yanda yake a ƙwanciyar rigingine nan wayoyin hannu da na gida sun zagaye shi sun kai baƙwai, amma kai da ganinsa ka san hankalinsa ba ya a wajen mutanen da ke zagaye da shi, suna ta fadancinsu,su ma za su kai taƙwas, daga ƙwancen da yake kawai ya waigo da kansa ya kalleni.
Hararar lumshe idanuwa ya yi mini,wacce zan iya cewa ta bayar da ma'anoni da dama, gaisuwa,kin mini laifi,ƙauna,son ganin ki nake,na ji daɗin zuwan ki.
Cikin nuna ban fahimci mai yake ciki ba na ɗan ɓata fuska alamar na ji haushi,nan take na ga yana girgiza kansa, sannan ya juyo ya kalli mutanen da suka kasu gida biyu. Wasu a wajensa suna yi masa firfita da gyara shi, ban da kirari da suke yi masa. Wasu kuwa suna a kaina ni ma ana yi mini nawa,kallonsu kawai ya yi sai na ji suna cewa.
"Mun bar ku lafiya, ƴaƴan mulki, waɗanda suka gaje shi, godiya muke."
Kafin su ce sun yi gaisuwar nan da suke,ko in ce sallama,tuni wani dogari ya iso gabana da faranti a hannunsa lulluɓe da farin yanki,a take na fahimci komai wai in ina so inyi musu ƙyauta.
Na ɗan sunkuyo kaɗan na ɗauki bandir uku na miƙawa na kusa da ni da hannu na yi masu inkiya da su raba. Ai kuwa na sha godiya da kirari irin na ƙwararrun dogarawa. Cikin mintuna uku falon ya koma shiru, daga ni sai Yarima da ke ƙwance, kamar mai jiran motar asibiti (Ambulance),ta zo ɗaukar shi.
Mun samu mintuna biyu a haka, sannan na yi murmushi na ce a zuciyata, mulki sai mai shi, sai kuwa ɗan da ya gaje shi. ƘASAITA, sai Sarki, sai kuwa jinin da ya fito ta sarauta. Na girgiza kaina sannan na yi murmushi na miƙe tsaye na nufi inda yake ƙwance.
*ƘASAITA BOOK 2*
*NA*
*MARYAM KABIR MASHI*
Page 6
Dole,in zamo ƙasanshi, ta wani ɓangaren kamar yanda Aunty ta faɗa, matattakala biyu na hau, sannan na zauna gefe ɗaya.
"Sorry." Na faɗa cikin sanyin murya. Ya juyo da fuska ya kalleni,kunyarsa tasa na sunkuyar da kaina, ina jin motsawarsa ashe matsowa ya yi ya kama yatsun hannuna ɗaya.
"Yasmin kin firgita ni sosai,kin tayar mini da hankali,kin saka mini rashin walwala a jikina."
Ya sumbaci tafin hannuna na ɗan yi saurin janyewa nuna alamar kunya, na ɗan juya kansa jin a daidai nan yana magana.
"Yunwa nake ji, ki taimaka mini da abinci."
Na sa tafin hannuna na ɗan ture shi.
"Ba ƙya so?"
"Tashi mu je ka ci abincin." Na faɗa cikin muryar sassarƙewa.
Ina jinsa ya koma da baya ya ƙwanta da ƙarfi tare da ajiyar zuciya, na juya na kalleshi yana mayar da numfashi a hankali, ya juyo muka haɗa ido na yi saurin miƙewa, sai na ga ya yi murmushin kunya ta kama shi, shi ma sai ya miƙe.
Alkyabbar da ke jikinsa ya ƙara gyarawa, sannan muka nufi wajen cin abinci, sai da muka isa sannan ya cire alkyabbar ya miƙo mini,na karɓa sannan na tafi ga ɗan ƙarfen da ake ajiyewa na rataye ta, ina juyowa na gan shi tsaye sai kallona yake,muna haɗa ido muka yi murmushi gaba ɗayanmu.
"Zan tafi idan kana yawan kallona."
"Dole ne in kalle ki Yasmin,saboda kin canja mini rayuwata gaba ɗaya,kin mayar da ni tamkar ba ni da jini a jikina."
"Ka gani...."
"Ki yi haƙuri ba zan daina ba fa."
Na juya alamar zan tafi.
"Zo, na daina." Ya ɗauke fuska ya zauna sosai na iso na tsugunna a gabansa domin in zuba masa abinci.
Tuwon niƙaƙƙiyar shinkafa ne,miyar dagwargwajajjan naman kaza, wacce aka yi ta da agushi, ya yi kalar kore-kore da gani ya sha kori (curry),shi kuwa tuwon ya sha naɗi a leda tamkar a hotel, na zuba masa, sannan na buɗe ɗaya ƙwanon, farfesun dagwargwajajjiyar hanta ne, shi kuwa ɗayan farfesun kifi ne, wanda hausawa kan ce masa ragon ruwa, ga shi ya sha albasa mai lawashi a cikinsa, da gani an saka shi a injin ɗin zare ƙayar kifi,ko kuwa in ce injin ɗin sa ƙaya ta yi laushi.
"Ke fa?"
"Ni naci a gidana."
Ya yi murmushi.
"Sam ban amince ba,ni dai na san kunyata ki ke ji, amma tsaya ki ga yanda za'ayi."
Ya miƙe tsaye a inda ni kuma dama a tsayen nake ya isa makunnan fitila ya kashe ta, dawowar da zai yi sai ya rungume ni a jikinsa, ya yi ajiyar zuciya.
"Sorry, ban lura da ke ba." Ya faɗa cikin raɗa, sannan ni kuma na zame na zauna.
Zaunawar da na yi tayi daidai da kamawar wata ƴar fitila mai duhuwa wacce haskenta kawai za ka gani, amma ba zakaga mutum ba sosai, yanda nake zaune nan haka ya zo ya zauna kusa da ni a hankali ya dinga lalubo bakina yana saka mini tuwon nan, shi ma a haka ya ci nasa.
Idan na girgiza kaina, shi ma sai ya ce ya ƙoshi,ni kuwa na san Yarima yana tare da yunwa sosai, saboda tashin hankalin da ya saka kansa, na ganin zai rasa ni. Cin abincin da ya kamata ayi shi cikin mintuna sha biyar, sai ga mu mun ƙwashi awa ɗaya. Na gane haka ne a lokacin da na iso kicin domin ajiye ƙwanukan abincin da muka ci,ni kuwa na yi tsaye a kicin ɗin na rasa me ke damun jikina, saboda wasu abubuwa da nake jin suna yi mini yawo tamkar kiyashi na bi mini jiki,shin ko son kenan? Shin ko na kamu da ciwon son Yarima ne nima? Kamar yanda na ga duk ya yi laushi a kan ciwon da ya kama zuciyarsa da gangar jikinsa,wai shi ciwon so na.
Motsin da naji yasa na yi saurin ci gaba da harhaɗa ƙwanuka tamkar dama aiki nake tun da na shigo.
"Sannu da aiki."
Na juyo na kalle shi ya jingina da gefen ƙofa, ya rungume hannayensa a ƙirjinsa, murmushi kawai na yi masa,a zuciyata na ce lallai Yarima yana son ƙananan kaya, saboda riga mai dogon hannu da take jikinsa wacce ya ɓallewa maɓallan gaba na rigar.
"Ki bar shi, da akwai masu gyarawa."
Na sunkuya wajen famfo na wanke hannuwana, sannan na iso inda yake tsaye ni ma na tsaya saboda ba hanyar wucewa, maimakon ya gafara in wuce sai na ga ya rakuɓe gefen ƙofa sosai, ma'ana in zo in wuce, wanda ya yi mini alamar da hannunsa ɗaya, duk da dama idanuwansa tsaye suke a kaina suna yi mini kallon kamun barewar damisa a jeji, ma'ana tamkar idanuwansa za su lumshe gaba ɗaya.
A hankali na zo na raɓa zan wuce, sai da na shiga tsakiyarsa sai ya sa hannuwansa ya kare ni, wato ya saka ni tsakiya sai da ya lumshe ido ya buɗe ya ɗan girgiza kai alamar kana son faɗar wata magana, sannan ya yi magana.
"Ina za ki?"
"Kina da gidan da ya wuce nan?"
"Eh."
"Wanne kenan?"
"Wanda iyayena suka saka ni a ciki."
Ya ɗan juyar da kansa ya kai sau huɗu, sannan ya dawo da kallonsa gare ni.
"Ina son da kiyi mini wani aiki."
"Na me kuma?"
"Mu je sama ki gan shi."
"Dare fa ya yi, goma ta wuce."
"Ƙuya kenan fa."
Nayi murmushin kunya.
"Na isa,mu je in yi maka ko na tafi kada inyi dare."
"Matata na ce mini za tayi dare a wajena,Yasmin kenan." Ya faɗa a daidai lokacin da ya sauke hannuwansa na wuce.
Sama na isa, wanda shi dama yana biye a bayana, kujerar da ke kusa da gado ita na zauna shi kuwa a zagayen gadon da ke tsakiyar ɗakinsa, ina kallo ya janyo durowar kusa da gadonsa ya ɗauko wata babbar ambulan mai fulawoyi ja, wanda ita kuma bulu ce mai haske (light blue), ya ɗago ya kalleni,ni kuwa dama shi nake kallo.
"Zo ki gani."
Na yi murmushin zuci na miƙe, saboda tunanin me Yarima ya mayar da ni,yarinya ko me? Na iso na zauna gefe ɗan nesa da shi ya miƙo mini na karɓa ina mai mayar da hankali a kan ambulan ɗin.
"Buɗe mana."
Ban ce komai ba na buɗe ta, litattafai ne guda biyu wanda yanayin hotan da ke jikinsu da sunansu ya nuna mini cewa su Nobel (Novel) ne, na ɗora su a cinyata, saboda jin da sauran wani a ciki,alawoyin chakuleti na ji a ciki (Chocolate), ina zarowa na ga an rubuta Bounty a jiki.
Na ɗago na kalleshi wanda kallon yana nuna alamar tambaya.
"Taimaka mini za ki yi ki karanta mini su, amma yau mu fara da ɗayan duk da na san da wuya mu yi ƙwata a yau, amma ƙila ma yi sati muna karantashi, chakulet kuwa matata na siyawa, saboda na san zata taya ta hira."
Ya haye can ƙarshen gado ya ƙwanta irin ƙwanciyarsa da ya saba,wato rigingine, sannan ya yi filo da tafukan hannayensa, ya mayar da idanuwansa ya lumshe. Na girgiza kaina sannan nima na gyara sosai nasa fulalluka na tare bayana, sannan na soma karantawa.
Ni kaina na san muryata ta yi daɗi a wajen karatun, na san kuma duk mai sauraren karatun zai ji daɗinsa, saboda dallah-dallah nake yinsa, cikin cikakkiyar nutsuwa. A ƙalla ni na san na ɗauki mintuna talatin zuwa talatin da ƴan mintuna ina karantawa, sannan na ɗago kaina na kalli Yarima wanda na ji ya yi shiru,ni a tunanina ya yi bacci, amma sai na ga ya ɓalle maɓallin gaban rigarsa gaba ɗaya.
Ni kaina na san Yarima na da gashin da ya ƙwanta a ƙirjinsa, dalilin ganin kuwa,ɗakinsa da na taɓa shiga na same shi yana bacci, amma abin mamaki sai na ga na yau yafi na ranar yawa,baƙi,ƙwantacce tamkar sumar jariri. Na yi saurin mayar da kaina ga littafin da ke hannuna, amma kuma sai na ji na samu kaina da son kallonsa duk bayan ƴan mintuna. Ɗagowar da zan yi in kalleshi sai naga ya ware duk biyun gaba ɗayan rigar jikinsa ta sauka saman gado, cikinsa, cibiyarshi,ƙirjinsa da kafaɗunsa duk a waje suke,