Showing 24001 words to 27000 words out of 27367 words

Chapter 9 - Kasaita Book 2 Hausa Novel Complete

ce." Haka na ji ya faɗa da harshen Turanci.

Sai ya ɗauki wuƙa ya baiwa Yarima, sannan na ji ya ce, "Prince Faysal Jafar from Nigeria,zai yanka cake ya baiwa matarsa."

Ya faɗa da harshen turanci, sai ya fara ƴar ƙirga, bayan Faysal ya saita wuƙar a jikin cake ɗin sai ya ce, "One, two, three." Yana faɗar muka fara hure wutar (Candle) ɗin da suke cin wuta a saman cake ɗin har izuwa biyu,yana cewa uku Yarima na Kamo hannuna muka datsa cake ɗin waje ya ɗauki tafi.

Sannan Yarima ya yanko yasa mini a baki, a kunya ce na gutsura ni ma na yanko na sa masa shi ma ya gutsura sai ɗan tafi ihu ya tashi, shi kuwa Yarima har da saurin rungume ni.

Kai rayuwar Turawa na bani sha'awa, amma iyakacinta kenan sha'awar, tunda ba Addini a tare da su,daga nan sai na ji kiɗa ya canja, cikin ƙanƙanin lokaci na ga suna kama junansu namiji da mace suna rawa suna bin kiɗan a hankali.

Yarima ya miƙo min hannu ni dai na san ban iya ba, na girgiza kaina, "No,taho." Na ɗan maƙale ya janyo ni jikinsa.

"Kalli ƙafafunsu." Ya raɗa mini a kunne na tsaya na kalla.

"Ke ma haka za ki dinga yi."

Ni dai na san kunya zan ba shi sai na ce kunya nake ji, ya dinga sani dole ni kuwa na ƙiya, ƙarshe wata Baturiya ta miƙo masa hannu sai ya sake ni ya kamata ya ci gaba da rawarsu.

Ni kuwa ina tsaye ina kallonsu ganin ta ƙwanta a kafaɗarsa yasa na ji wani ɗan abu ya dakar mini zuciya,wai a take sai na ji nayi tunanin ko dai irin ƴan matan da yake tare da su ne a nan,nan take na ji raina ya ɓaci, idona kuwa ya kasa ɗaukewa daga wajensu.

Can na ga ya ɗago yana ɗan waigen nema na, ya ɗago mini hannu sai kawai na ji na harare shi na juya, sai na ji na rasa inda zan nufa ina tunanin in tafi ɗaki sai na ji ya ruƙo hannuna ta baya ya rungume ni, tare da turo haɓarsa a jikin kafaɗata, sai na ji ya cigaba da rawa da ni tamkar muna rawar tare.

"Sorry my darling,kin san su al'adarsu ce."

"Kai kuma Addininka ne.?"

"Kai, to fa,ki yi haƙuri na yi kuskure babba,ƙato." Sai kawai muka ji kiɗa ya tsaya wajen ya ɗan ɗauki tafi.

Daga nan sai na ga wannan dai Baturan ya ɗauki bututun magana (Macrophone) yana cewa duk su tsaya inda suke za'a gabatar da kowa, ɗaya bayan ɗaya ya dinga gaya mini sunayensu,su al'adarsu shi ne a gaisa ko a ɗan rungumi juna, amma mai jawabi ya gaya musu mu haramun ne tun farko ma saboda haka sai dai a ɗaga hannu in wuce.

Sannan suka ƙara gabatar da ni,nima da bada ɗan guntun tarihina ga shi duk wanda na zo kanshi sai ya ba ni ƙyauta dama wata mace na biye a bayana da irin kayan ma'aikatan hotel ɗin in aka ba ni in miƙa mata.

Wasu har da ƴar guntuwar fulawa wasu doguwar fulawa, wasu mai yawa, wacce take naɗe a cikin leda, wasu ƙwalaye nannaɗe da ledar naɗe ƙyauta (Wrapping sheet), daga nan kuma aka bayar da umarnin a tafi ɗakin cin abinci, gaba ɗaya muka nufi can.

Waje ne shi ma ƙaton gaske, amma gaba ɗayansa wani tebiri ne zagaye da shi mai kamar an ajiye doguwar gwanda, wato ba zagaye yake ba kamar ƙarfen kuɗi zagaye yake amma kamar Oval shape.

Kowa ya ja kujera ya zauna,mu kuwa muka zauna ƙarshen tsinin tebirin kenan kowa mu yake kallo, duk yawan mutanen nan kuwa kamar an ƙirga su kowa ya samu wajan zama,dama kafin mu isa an gama shirya komai kowa an ɗiga masa lemun ruwan nan nasu,rabin kofi,mukaɗai aka ajiyewa wata doguwar ƙwalba an rubuta concentrated sof drinks.

Ana ci ana yiwa juna tsiya, daga wannan ya ce mini shi ya koyawa Yarima magana a ƙwashe da dariya, sai wancan ya ce shi ya koya masa cin abincinsu, suka dinga hirar makaranta, tsiya dai kala-kala sun yi wa juna,anan kuma suke yaba masa da iya zaɓen mata,wai har cewa suke aƙwai mata masu ƙyau a Nijeriya?.

Nan na ga ashe idan aka yi Birthday yanka cake ɗin ake ashe a baiwa kowa, saboda na gan shi a ɗan faranti gaban kowa, da gani kuma yanka shi aka yi, tabbas na ga yanda turawa ke rayuwa, dole Yarima ya zama ɗan rayuwa,ni har kunya na dinga ji idan na hango wasu na tsotsar bakin juna,ko ƴar soyayyarsu, ga shi a gaban kowa ma yi suke ba wanda ya damu da wani, wani lokacin ma Yarima ke taɓo ni in gani sai in sha masa kunu.

Ba mu tashi ba sai wajen ƙarfe uku na darensu wanda sai da muka zo ɗaki ma na ga dare ya yi, kafin a gama shigowa da kayan da aka ba ni ƙyaututtuka na cewa Yarima zan ɗan shiga ruwan ɗumi saboda na gaji da yawa, shi kuwa har da yi mini kashedin in na fito shi zai zaɓa mini kayan baccin da zan saka, na bishi da to. Ya koma falo saboda tsayawa ya ga masu aikin hotel ɗin sun gama shigo da kayan duka.

Ban wani daɗe ba ganin dare ya yi, ga shi idanuwana cike suke da bacci, saboda haka ban fi mintuna biyar ba, ina fitowa tun daga ɗaki na ɗan ji tashin muryar Yarima kaɗan kaɗan, duk da dama shi ba mai sakin murya ba ne ba,ko waya yake yi za kaga kamar ba a jin abin da yake cewa, amma yau nayi mamakin jiyo muryarsa.

Na buɗe durowa na ƙwaso rigunan bacci uku, na taho da su domin nuna masa ya zaɓa mini,me zan jiyo.

"Mama wallahi lafiya lau muke,tana wanka."

Har na washe baki na taho in karɓi waya mu gaisa da Mama, sai na ji maganarsa ta canja salo, na yi tsaye cak saboda jikina da na ji ya yi nauyi,gudun kada in yi taku da ƙarfi ya jiyo ni.

"Mama ai dabara na yi mata, to gajiya na yi,yau nayi mata ciwon ƙarya a ruwan wankan nunawa na yi na mutu na taso sama,kin ga ɗiyarki na ihu a zo a taimake ta,miji zai mutu. A'a Mama, wallahi dama don in gane tana so na ko har yanzu zaman dole take yi da ni.

Eh, na gane,kin ga yanda ta ruɗe dama na haɗa baki da ƴan hotel ɗin. Mama ai hotel ɗin da Mai Martaba Sarki ke sauka ne,mun saba da su sosai,su na haɗa baki da su na ce su yi mini allurar (B. Complex), kin ga ai na ɗan ci in ƙoshi na ƙwana biyu." Sai na ji ya sa dariya.

A'a Mama, ina zan yarda ta yi kukan da za ta haɗu da wani ciwon, ai ni ma da na kama ciwon gaskiya wallahi Mama lafiya ƙalau,ni yanzu ma na ji ta ƙara shiga raina, saboda hankalinta, wallahi ina son ta,so sosai, Mama ki daina koƙwanto, yanzu mu duka muna son juna.

Mama kenan, na so insa a ɗauki hotan ɗiyarki in aiko miki ki ga yanda take kuka. To na daina za ta ji, ta shiga wanka daga ma ƙasa muke yanzu, abokaina na nan suka haɗa mata fatin murnar auranmu, amma kin san Turawa suna kiran shi da Birthday,amma fa duk sun ruɗe wai na iya zaɓen mata, zan daina, sai anjima. Ki gaishe da Baba Sarki da Hajiya, kowa ma. Ita ma a aika a ce tana gaishe su, to to,bye Mama I love you,I miss you great Mama."

Sai na ga ya kashe yana ƴar dariya har da sumbatar wayar, sannan ya tashi tsaye ina jin da niyyar ya zo ɗaki sai kawai ya juyo ya ganni a tsaye juyowarshi nima tasa na saki kayan da ke hannuwana wannan kuwa na lura da ta firgita shi,dan kuwa ya gane na ji duk abin da yake faɗa.

Ya yi saurin nufo inda nake tsaye, kafin ya iso na shige ɗaki da saurina na faɗa gado, ya iso ya yi saurin ɗago ni.

"Yasa..."kafin ya ƙarasa kiran har na ji wasu zafafan hawaye sun zubo mini,wannan ne ya hana shi ƙarasa kiran.

"Me za kace mini yanzun kuma?" Na faɗa cikin sanyin murya.

"Yasmin sorry,wallahi har a zuciyata na yi haka ne domin na gane kina sona kamar yanda ni ma na daɗe da sonki,in za ki tuna ma haka na cewa Mama."

"Ni dai ba zan iya auran ku ba,komai muke ciki kowa sai ya sani."

"Haba My love, ya zaki ce mini haka, alhalin kin san yanda zuciyata take ƙaunarki."

Na sauka ƙasan gado ya durƙusa, "Yasmin ki yi haƙuri ki so ni nima."


*ƘASAITA BOOK 2*


*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*


Page 13


Kansa a sunkuye yana ɗagowa muna haɗa ido na yi saurin sunkuyar da kaina.

"Ka daina yi mini haka,bai dace ba,ka durƙusa mini ina matsayin matarka."

"Kin amince ke matata ce?"

Na koma da sauri na kife kaina jikin katifa, sannan na ɗaga kaina. Ya hawo a hankali ya tura kai a cikin wuyana ya sumbace ni.

"Na gode, to tashi in zaɓa miki rigar baccin."

Ya ɗago ni na tashi zaune ya yi saurin tafiya ya ƙwaso kayan ya iso ya zube su a gado har ya zaɓa mini ɗaya daga ciki ya miƙe tsaye.

"Kafin in fito daga wanka kin saka mini ita, kada ki lulluɓe ta na san ki da kunya."

Yana yi yana cire coat ɗin da ke jikinsa da shet (suit) shigar nasa kayan (wedding Anniversary) ɗin kenan. Ina jin motsin fitowarsa na yi saurin miƙewa tsaye tare da sunkuyar da kaina ina faman murza ƴan yatsun hannuna,ni kaina na san rigar baccin ta yi mini ƙyau. Doguwa ce iya wucewar gwiwata amma matsatstsan ƙugu gare ta,siririn hannu gare ta kamar ɗan mariƙin hular sanyin yara, kuma a murɗan yake tamkar ɗan abin ɗaurin hular yara.

Amma tafe take da ƙoƙunan rigar Mama daga cikinta wanda za su iya tallabo maka ƙirjinka ya ɗan bayyana a waje, ya kuma fitar da tsakiyarsu, sai dai sakata ake yi kamar ana saka wando, saboda haɗe take da ɗan diras ɗinta, jikinta gashi-gashi ne kamar gashin jikin jaririyar mage, kenan laushi, amma ba ya tsirar mutum.

Ƙasanta kuwa kamar ƙarshen jelar mage an daddasa sannan kuma sai ka maƙala ɗan siririn maƙallamin rigar mama sannan za ka zuge wani zib da ke cikin bayan rigar, wanda ba a gane shi, sai an laluba saboda gashin jikin rigar ya ɓoyeshi. Ɗan wani guntun mayafi gare ta,ko na ce ɗan abin da zaka rataya a wuyanka, shi kuwa kamar ƙatuwar jelar mage, saboda duk ta rufe mini wuyana.

Kunya ce ta hanani ɗaga idanuwana daga tsayuwar murza ƴan yatsun da na yi, jin shigowarsa ɗakin ta sa na ɗan ɗaga idanuwana na kalleshi, cikin sauri na sunkuyar da kaina saboda ganinsa nayi ɗaure da tawul mamadin ya sako rigar wankan shi, ɗan tsayin mintuna biyu ya yi ban ji motsin shi ba, gyaran muryar da ya yi ita ta kawar da tsit ɗin da ɗakin ya yi.

Jin sautin maganarsa na yi yana yi mini magana cikin sarƙaƙƙiyar murya. "Miƙo mini rigar wanka ga ta nan a kan gado."

"Tawa ce wannan taka na ciki."

"Na sani taki nake son sakawa a yau,ko ba za'a ba ni aro ba?"

"Za'a baka." Na faɗa a daidai lokacin da na juya domin ɗauko masa.

Kaina kuwa a sunkuye nake tafiya har na iso inda yake tsaye, cikin ɗan yanayi na kunyar gaske na miƙa masa rigar ba tare da na ɗaga kaina ba, juyawar da zan yi na koma ta yi daidai da ruƙo hannuna da ya yi ta bayana ba zan iya ƙwatanta yanda jikina ya amsa girgizar da ya yi ba, juyo ni ya yi ya haɗa ni da ƙirjinsa rigar da ke hannunsa kuwa ina ji ta sulale a tsakaninmu ta faɗi ƙasa.

Bai yi magana ba, amma sai na ji ya sa ɗan yatsansa yana zana mini cinyar hannuwana,wanda har ya dire a yatsun hannuna,ɗago tafin hannuna ya yi ya ɗora a saman ƙirjinsa,gashin ƙirjinsa wanda yake cike da lemar ruwa ya haɗu da ɗan sanyin ruwa ya tsirar mini tafin hannuna,na yi saurin lumshe idanuwana tare da kiran sunansa "Yarima."

Cikin kunnena na ji ya yi magana, "Faysal dai, ke ya kamata na kira da Gimbiya, Sarauniya,Yarimiya,kin san kuwa kin cancanci sunayan nan, saboda kin riga kin siye zuciyar Yarima, wanda yake taƙama da mulki.

Wanda bai taɓa tunanin da macen da za tasa zuciyarsa ta koma tamkar ba tashi ba, Yasmin ke zuciyata kawai take tunani,ni a yanzu ma ji na nake ƙarya ne ni ba nine Yariman da kike faɗa ba."

Sai na ji ya yi murmushi mai fitar da sauti tare da ɗago fuskata,"Open your eyes, kalleni."

Da ƙyar na iya kallonsa na sakan ɗaya.

"Yanzun ni naki ne Yasmin,ki daina jin shakkun komai,ki daina jin kunyata,ki fitar da tsorona daga zuciyarki, kin canja mini rayuwata gaba ɗaya."

Ina jin shi yasa hannu ya janye ɗan dogon gashin da na rufe jikina da shi.

Ya sunkuyo ya sumbaci ƙirjina na yi saurin ƙwantawa ƙirjinsa ya tallabe kumatuna.

"Yasmin you love me sure?"

Na ɗaga kaina alamar eh, ya ɗauke ni cak ni kuwa na koma na ƙwanta a ƙirjinsa ya hau gadon sosai, sannan ya ƙwantar da ni ya janyo filo ya ɗaga ni ya gyara mini ƙwanciyata sosai, ya juya ya janyo bargon da ke maƙale jikin gado ya lulluɓa mini har izuwa ƙirjina,sannan ya sunkuyo ya sumbaci goshina da laɓɓana yasa hannu ya gyara mini gashin da ya sauko mini a saman fuska.

Ni kuwa cikin lumsashshen ido nake kallonsa sannan ya ce, "ina zuwa." A cikin raɗa sai na ga ya sauka na buɗe idanuwana sosai na bishi da kallo a take sai na ji na tsorata saboda ganin shi ɗaure da tawul haka ya nuna min ashe Yarima na da tsokar jiki,ganin wasu cinyoyin tsoka a cinyar hannunsa duk sun yi kusurwoyi kamar ta ƴan kokawa (Wrestling).

Ga wata tsoka ta ƙwanta a gefunan wuyansa, ban da tsokar da na hango a cinyar ƙafarshi, ya buɗe durowa ina kallonsa sai na ganshi ya juyo yana fesa wani abu a hannunsa, ganin dogon gwangwani ne yasa na gane abun sa ƙamshin ɗaki ne (Room Freshner) duk da ban ga sunansa ba, cikin sakan uku ɗaki ya kaure da ƙamshi mai sanyin gaske, ban da laushin shaƙa da hancina ya yi.

Ya ɗauko wata ƴar ƙwalba bayan ya ajiye wancan sai na ga yana ɗan ɗigata yana shafawa a gashin ƙirjinsa,a zuciyata na ce ashe maza ma suna ƴan gyara irin na mata. Ina kallo ya ɗauko turare ya fesawa jikinsa ya mayar da durowa ya rufe, juyowar da zai yi sai na ga idanuwansa sun ƙara fitowa sun yi ja,dama abu (Barakallah), manya da su, sai ya juye mini kamar na ƙwatanta shi da ɗan fim ɗin nan na ƙasar Indiya (Salman Khan), har da faɗin ƙirjin ga tsokar curi-curi a cinyoyin hannunsa.

Na ɗan yi saurin kawar da kaina gudun kada ya gane kallonsa nake yi,jin bai hayo gado ba yasa na ƙara waigowa sai na ga ya kunna mana hitar gasa ɗaki (Room heater), sannan ya isa ga makunnin fitila ya kashe ta sai fitila ɗaya ke ci, ta gefen gadonmu, tun da ya hayo gadon ya ƙwanta tare da kashe fitilar gefen gadonmu ban ji ya yi motsi ba, ga shi kusan mintuna ashirin kenan.

Zuciyata ba abin da bata saƙa mini ba,na ko lafiya ko kuwa ya yi bacci? Hakan ya sa na juya nima na cigaba da addu'o'in ƙwanciya baccina, na yi ƙwanciyata, jin ya ce, "Alhamdulillah." A bayyane yasa na ce ashe idonsa biyu. Madadin na ji ya yi magana sai kawai na ji ya ɗan cizar mini bayana na ɗan firgita kaɗan saboda a bazatan da cizon ya zo min tare da faɗar.

"Kai Yarima!"

Kafin in ƙarasa ya kuma cije leɓatun kunnena, daidai wajensa ɗan kunne, kafin na yi magana ya kurɗa ya ciji wuyana, kumatuna, na yi saurin juyowa na fuskance shi, sai kawai na ji ya cije laɓɓana.

"Kai...." Yasa tafin hannu ya rufe bakina.

"Don't talk." Numfashina na ji ya yi sama wanda ya ɗauki mintuna uku kenan bai dawo mini ba, ba wani abu ya janyo mini haka ba shi ne salon yanda Yarima ke tsotsar ƴan yatsun hannayena.

Shin Yarima ne kuwa? Tambayar da zuciyata ta yi mini kenan,a daidai lokacin da numfashina ya dawo dai-dai kunya ta kama ni da na ji ya amsa mini da "Yasmin ni ne."

A nan take na tabbatar wa kaina maganar da ke cikin zuciyata ce ta fito fili. Idanuwana kuwa na ƙara runtsewa,runtsewar da ta kai ni har wayewar gari ban ƙara buɗa su ba.

Ji na cikin ruwan ɗumi yasa na san mafarki nake,a cikin mafarkin na dinga cewa, "Yarima mafarki nake na shiga ruwa."

A kunnena na ji ya ce "Buɗe idanuwanki ba mafarki ba ne ba."

Na firgita sai na ji ni rungume a ƙirjin Yariman a cikin ruwa, na waiga na kalle shi ƙwance cikin ruwan kumfa sai ƙamshi kawai ke tashi, na juyo na kalli kaina nima cikin ruwan kumfa.

Na sa hannu na dinga laluba jikina, na ji zargin da nake ya tabbata na rashin kayan jikina, na juyo na ƙara kallonsa sosai sai na ga ya lumshe mini ido na juya a sanyaye na ƙwantar da kaina jikin gefen bahon wankan, sai na ji hawaye, saboda tunanin gane ni ba kaya.

"Why! Why!! Why!!! Yarima? Me yasa ba ka tashe ni ba? Me yasa ka kalle mini jiki?"

Ya ƙwanta bayana, "Yasmin,don kina matata kin manta mun amince da junanmu."

Ya sumbaci bayan wuyana, "kada ki yi da na sani ko ki ji haushin abin da na yi,me yasa ba ki da yarda Yasmin? Nifa na amince da ke ce matata, ke me yasa ki ke kokwanto ne har yanzu?"

Ya yi saurin dawowa gabana jin ina fitar da ƴar jaririyar kukan ƙissa, wanda Aunty ta ce mini ana yi, ya dago kumatuna ya tallabe da hannuwansa masu kumfa.

"Ba ki son abin da na yi miki? Na ɗaga kaina.

"To shi kenan ki yi haƙuri tsaya na baki haƙuri sosai."

Sai na ga ya ɗebo kumfa yasa a saman kansa ya ɗiga a goshi, hanci a kunnuwa,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login