Showing 18001 words to 21000 words out of 27367 words

Chapter 7 - Kasaita Book 2 Hausa Novel Complete

ba zan ƙara zaman dabbanci ba a gidanka,ƙiri-ƙiri ku mayar da al'ada addini."

Yasmin ni kaina ba na so, ya zan yi dama na san sai kin zarge ni."

"Zargi ne ma?"

Ya zauna jikin gadon zai kama ni.

"Kada ka taɓa ni,wa ya sani ko yanzun ma ka fita ka faɗawa jama'a cewa ka rungume ni."

"Oh! My Darling....."

Dagewa na yi nasa kuka mai ƙarfi, sai na ji ya tashi ina jin takun fitarsa,bai fi minti biyar ba sai na ji an shigo. Aunty Salwa ce ta shigo da saurin ta.

"Aunty kin ga Yarima ko, ya cuceni, ya wulaƙanta ni a gaban jama'a." Na ƙara sa da kuka.

Ta iso ta zauna kusa da ni tare da dafa kafaɗata.

"Haba Yasmin bai dace ba a ce kin zargi mijinki ba a kan abin da ya faru,in har za kiyi la'akari da taron da aka yi a yanzu, wannan zai nuna miki cewa tun kafin a san za'a haifi shi kanshi Sarkin haka akeyi, na fahimci al'ada ce su wacce take muhimmiya a wajensu. Saboda muhimmancinta fa Sarki da kansa yau tun da baƙwai na safe ya je ya gayawa Daddy,kin ga irin murnar da Sarki ke yi kuwa,ni a ɗan tunanina da na yi, wannan shi ne mataki na ƙarshe da za'a gane wa ye Sarki na gaba,in ka dace da mace tagari, to daga lokacin ma za'a iya kiranka Sarki mai jiran gado,in kuwa da sauƙi, to ko mutuwa sarki ya yi an san ɗansa wanda ya cancanci a baiwa sarauta.

Ki yi tunani ki gani,ni tunanin abin da za ki yi ƙoƙarin ki hana a nan gaba, shi ne yin taron,ko nunawa jama'a zanin gadon yanzun ki tashi ki canja kayan jikinki, kamata ya yi ma ki ɗan shiga ruwan ɗumi."

Aunty ce ta taimaka mini na shirya jikina na ƙara narka wasu kayan, duk da cikin waɗanda Mama ta aiko mini da su ne, shi ma wani irin yadi ne na alfarma mai ruwan jinin kare mai duhuwa (Coffee colour), Ina niyyar in koma in da ake taron, amma ina sai na ji zazzaɓi ya rufe ni. Aunty ta ɗauko magani ta bani na sha, amma duk da haka, sai na ji ƙwanciya kawai nake so.

Ƙarfe ɗaya da ƙwata limamin masallacin gidan Yarima ya ƙwallah kiran sallar azahar,jin mata na ta ƴar hayaniya yasa na gane an tashi, amma sai na ƙara yin lamo saboda kunya da ta hanani haɗa ido da kowa, ina jin su Hajiya Kilishi da sauran mutane aka shiga ana yi wa Aunty ya mai jiki.

Yanda na ji Aunty nata hira da mutane yasa na gane lallai da ƴan'uwanmu suke hira,shin wa ya gaya musu? Haushi da takaici suka ƙara dirar mini a zuciyata.

Yanda na ji ana yi masa sannu da zuwa da tambayarsa ya mai jiki shi ya tabbatar mini da Yarima ne ya shigo, ƙara lamo na yi tamkar ma yanzun na fara barcin, ina jin shi yana tambayar na yi sallah? Aka bashi amsa a'a, sai na ji ya ce lallai a tashe ni inyi sallah.

Bayan sallar isha'i ne ya shigo ɗakina ni kuwa a wannan lokacin na samu sauƙi sosai kamar ma ban yi wani zazzaɓi ba, asali ma ina zaune a kan abin sallah ta da alƙur'ani mai tsarki a hannuna ina karantawa, ba don komai ba saboda godiya ga Allah da ya taimakeni na riƙe mutuncina, sannan na yi godiya ta musamman ga iyayena da suka yi mini tarbiyya tagari.

Maimakon ya yi mini magana sai na ga ya zauna gefen gadona, ina jin gani ya yi ba ni da niyyar dainawa, saboda ya yi kusan mintuna ashirin da biyu, amma sai in buɗe wani fejin in cigaba, ganin haka na san yasa shi ya taso ya zo ya zauna bayana, madadin inji ya yi magana sai na ji ya ɗaga hijabin da ke jikina ya shiga ciki, daga nan kuwa sai dai na ji ya sa hannayensa ya rungume ni ta bayana, kenan hannayensa suna saman ruwan cikina, sai a lokacin na ji ya yi magana.

"Ya isa haka nan Yasayyada, ya kamata a zo a kula da baƙo ko shima ya zo ya yi wa matarsa sannu.

Madadin in tashi ko in mayar masa sai dai na ajiye Alƙur'anin na mayar da kaina na matse a tsakanin gwaiwoyina saboda dalilin abu biyu. Na farko na san ni ba zan iya haɗa ido da shi ba, saboda kunya. Na biyu kuma saboda ɗan haushinsa da yake a zuciyata.

Ganin ya samu sama da mintuna sha biyar yana fama da ni in ma yi masa magana na ƙiya, ya sa naga ya sake ni ya miƙe tsaye,dama tuni ya cire hijabin jikina ya mayar da ni ya ƙwantar a cinyarsa,yana ta ɗan kokawar cire tafukan hannayena waɗanda ke rufe da fuskata, wanda ko ya cire zan runtse idanuwana da ƙarfi.

Sai dai na ji yana cewa, "Mama ta ƙi yi mini magana, Mama ki zo,wai haushina take ji,ni ma na gaya mata ba laifina ba ne ba,kona ba ta ba zata karɓa ba."

"Kai! Ni na ce." Na faɗa cikin sauri. Ya juyo muka haɗa ido na harare shi.

"Dama na ce miki cewa ta yi ni ɗin me."

Na taso zan karɓi wayar ya juya na bi shi ya juya na riƙe hannunsa,wai ni in karɓe wayar, amma saboda ƙarfi irin na namiji ya riƙe hannun gam.

"Mama ban yi mata ƙarya ba, cewa ta yi ban isa in sa ta karɓa ba."

Na yi tsalle na fige wayar.

"Mama wallahi ba da gaske ba ne ba sai na kashe wayar nasa kuka. Bacin ka gama wulaƙanta ni a gaban jama'a yanzun kuma so ka ke mahaifayarka ta tsane Ni?" Na tafi na faɗa gado.

Kusan mintuna arba'in kenan da zuwan Mama,ni kuwa tsugunne a falo jikina ya sha naɗi da hijabi, hankalina ya nutsu da abin da Mama ke faɗi, kamar yanda ta fara da farko.

"Ba wata kalmar da zan yi amfani da ita inyi miki godiya, sai dai inyi amfani da ƙarfina in yi miki addu'ar Allah ya saka miki da ƴaƴa nagari, kamar yanda iyayenki suka yi dace da ke ƴa tagari.

Ki yi haƙuri ki zauna da mijinki lafiya, duk abubuwan da suka faru a baya ya kamata a ce kun haƙura kun ajiye su gefe,kun mayar da su yarinta, wannan abu kuma da ya faru abu ne na al'adar sarautar gidan nan tun iyaye da kakanni.

Hikimar yin shi kuwa shi ne hana rigima idan Allah ya ɗauki ran Sarki,a wancan zamanin,kin san kowacce masarauta a wancan zamanin da irin hikimar da ake amfani domin fitar da Magaji,wato wanda zai gaji sarauta. A zamanin da zaki ga wata masarautar su kan sa yaransu su yi tafiya mai nisa domin ɗauko wani abu ko samo wani abu. To su kuwa wannan masarautar ta haka suke ganewa. Ina son ki yi murna kuma ki godewa Allah da yasa ki ka samu kanki a wannan matsayi.

*ƘASAITA BOOK 2*


*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*


Page 10


Tsaya in baki wani labarin da ba wanda ya san shi daga ni sai Mai Martaba, sai kuwa ita wacce abin ya sama sai kuwa Allah.

Kin ga wannan abin da ya faru da ke a yau, to shi ne ya haddasa tsana mai tsanani tsakanin Sarki da matarsa ta farko, Hajiya uwarsu Abdulrahman, da na taɓa ba ki labarinta. Mai martaba ya bani labari cewa, lokacin da aka kawo ta tana amarya ita ce ta dinga nuna masa ya zo gareta,kin san yanda auran sarauta yake da wuya a bar ka ka auri wacce ka ke so, sai dai a zaɓa maka.

To wannan ne yasa ba so a tsakaninsu, lokacin wata ƴar barga yake so, wato irin ƴaƴan masu aikin gidansu, aka hana shi auranta aka aura masa Hajiya Asabe. Ranar da Allah yasa za su haɗu da ita a matsayin miji da mata, sai ga shi ya sameta ba yanda ake so ba, wato ta taɓa sanin wani bayan shi.

Tun a daren ya kira jakadiya ya sanar da ita, jakadiya ita ta kawo shawarar a samo kaza a yanka ta,jininta a zuba shi a shinfiɗarsu, wannan dabara ita aka yi, balle a wancan lokacin jakadiyarsa mai himma ce da wayo, ita ta yi masa wannan dabarar har ya samu ya haye a matsayin zai gaji sarauta.

Tun daga wannan lokacin ya tsani Hajiya Asabe, har ya zama yana zarginta da fita waje in ta fita unguwa. Ke a ƙarshe dai sai da suka rabu hankalinsa ya ƙwanta. Ke ki godewa Allah ko in ce mu godewa Allah, wallahi ni ma nan da ki ka gani sai da aka yi mini wannan taron,ki yi haƙuri ki zauna da mijinki lafiya. Mu dama tuni abin da muke son ji kenan, saboda duk wani masoyin Yarima zai so a ce ya ji wannan ranar, ta zo kuma yanda ake son ta.

To ni zan koma sai kun zo mana sallama ko, Allah ya yi muku albarka, kira shi ki ce ni zan koma."

Abin ka da falon sama muke dama sai kawai na shiga ɗaki, ina shiga ya ɗago kai ya kalleni daga inda yake ƙwance,bai tashi ba har na iso gabansa.

"Mama na kira." Na samu na faɗa,a inda na juya na koma wajenta.

Sallama kawai ta yi da mu ta yi tafiyarta,iyakata bakin ƙofar falo, Yarima kuwa shi ne ɗan doguwar rakiya. Kafin Yarima ya dawo ni kuwa har na saka rigar baccina na haye gadona, saboda ba zan iya cigaba da haɗa ido da Yarima ba. Ina kallon shigowarsa, ta ƙyallin idona ɗaya, ya zo ya tsaya a gabana kallona kawai ya dinga yi yana murmushi.

Ya yi tsayin mintuna biyu a haka, sannan ya shige ciki, kenan ya koma ta bayana,ni ga shi babu damar in juya in kalli me zai yi ba. Ina jin shi ya shigo cikin bargon da nake ƙudundune sannan ya hayo ta saman jikina ya ɗauki makunnin kashe fitilar ɗakin.

Me ya manta? Na faɗa a zuciyata, saboda jin ya sauka daga saman gadona,ƙyallin idona ɗaya na ƙara buɗewa a nan ne na ga ya isa ga ƙofa yasa makullintaa ya kulle, cikin bargon ya koma tare da kashe fitilar ɗakin gaba ɗayanta, ina jin shi ya zare ɗan abun ɗane gashin da na sa na ɗaure gashina (band) cikin ruwan sanyi na saukar da ajiyar zuciya jin ya sumbaci bayana, tare da rungume ni jikinsa ta bayana.

"Na san kina ji na ki kayi shiru, because you hate me Yasmin,har abada ba zan taɓa yaudarar ki ba,sona,ƙaunata, mulkina,ƘASAITA, duk naki ne,in har babu ke a tare da ni na san zan iya zama ba ko ɗaya a cikin abubuwan da na lissafa,ni na san ƘASAITa ta biya ni, tunda ta hana mata da yawa yi wa rayuwata katsalandan.

Ki yi tunani, da ni mutum ne mai sakin fuska da mata nawa ne zasu dinga neman cin fuskarki, saboda suna kishi da ke. Ke kaɗai na fara sakarwa fuskata, da jikina baki ɗaya, kuma na yi imanin ke ce ƙarshe. Please Yasmin ki saki jiki da ni saboda ke special ce a gare ni, kamar yanda sunanki ya ke special a wajen jama'a.

Ki so ni,zaki sameni mai sauƙin kai, komai ki kaga na yi na mulki a baya, saboda tsare mutuncin kaina ne."

Ya kama ni ya juyo ni a jikinsa sosai kumatuna ne ya ƙwanta a ƙirjinsa ya yi ɗan saurin ɗago kaina na san dalilin ɗaga ni haka.

"What? What? Yasmin, still you hate me." Na koma na ƙwanta a ƙirjinsa mai ni'imtaccen gashi, ina jinsa ya yi ajiyar zuciya ya ƙara rungume ni gam a jikinsa.

Gashin kaina yasa hannu yana ɗan shafa shi a fuskata, ban iya buɗe idanuwana ba, amma nasa hannuna na riƙo gashin tare da yin murmushina.

"Zan je sallah ne masallaci ki tashi ki yi taki sallar, saboda yau zamu ɗan fita zuwa wani ɗan lokaci, amma ƙasar Greece za mu fara zuwa,a can nayi karatuna, sai in nuna miki wuraren dana sani, ragowar ƙasashe uku ke ce za ki zaɓa."

"Ni ba zan je ba."

Ya sa haƙoranshi ya cije laɓɓana duk biyun, har sai da na ɗan yi ƙara kaɗan, na samu na ƙwace na cusa fuskata a ƙirjinsa.

"Zane ki zan yi da tsintsiyar ƙwaƙwa na ga alama."

Nasa yatsuna na ɗan ja gashin da ke ƙwance a ƙirjinsa, yasa ƙara kaɗan tare da ƴar kokawar ƙwace jikinsa ya mirgina ya tashi yana dariya ya sunkuyo ya sumbaci kumatuna.

"Zan rama ne, gudu nake kada na makara da kin faɗa."

Ni kuwa na ƙudundune kaina a filo, ina ƴar dariyar murmushi ina jin shi har ya kammala alwalla ya fito daga banɗaki, saboda jan faɗa har da buɗe ƙafata ya yayyafa mini ruwa.

"Tashi."

Na yi saurin jan ƙafata shi kuwa ina jin dariyarsa a hankali har ya fice daga ɗakin. Fitarsa zan iya cewa jinkirin minti ɗaya na yi na miƙe da tsallen murna, na sauka daga gadona, jin ƙuguna ya ɗan amsa, shi ya tuna mini ashe fa ba na jin daɗin jikina, na yi murmushi na shige banɗaki tare da tunanin na zama ta Yarima Faisal.

**** **** *****

Ƙasar Greece,nan muka sauka FIVE STAR HOTEL,shi ne masaukinmu, wanda ɗakinmu shi ne ɗaki na ɗari da goma sha biyu (112) , ya kama kuma hawa na uku kenan. Bai fi mintuna biyar ba da shigowar mu ɗakin ba wata ƴar ƙararrawa ta kaɗa cikin sauri na ga Yarima ya fita falon da muka baro,mu kuwa muna ɗaki Yarima na ɗan shirya mana kayanmu.

Jin an ɗauki ƴan mintuna yasa na fito falon da ɗan saurina, fararan mutane ne biyu Turawa, sanye da farar rigar shirt da bulu ɗin wando, sai baƙaƙen takalma a ƙafarsu, wannan ne ya nuna mini alamun su ne ma'aikatan hotel ɗin da muka sauka.

Baki ɗayan hankalinsu ya dawo gare ni,ni kaina sai na ji kunya ta kama ni kallon da na ga suna yi mini, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci Yarima ya nufo inda nake.

"Shiga ciki." Ya faɗa a daidai lokacin da ya iso gareni. Na shiga ciki ina ɗan murmushina na mamakin yanda Yarima ya nuna kishinsa a fili.

Wajen yammarsu, wacce a tamu yamman za mu iya kiranta ƙarfe biyar da wasu mintuna na yamma. A lokacin ne muka gama komai muna zaune a falonmu mu dai ga mu nan, ba ka cewa ƙiyayya ba kuma za ka kira mu masoya ba, tunda kowa a kujerarsa yake a zaune,ni zan iya cewa kishingiɗe nake a tawa kujerar duk maganar da ya yi idan ta amsa ce in bashi amsarta,in naji zan iya.

Ana cikin haka hankalina ya kai ga talabijin ɗin da ke ta aiki ita kaɗai, na yi saurin tashi zaune har da ɗan salatina.

"Me ye?" Ya tambaye ni.

Har sai na ji na ɗan ji kunya, "Wa ye wannan? Ɗan uwanku ne?"

"A'a. Ya naga kina ta murnar ganinsa?" "Ɗan wasa ne na finafinan Indiya." Ya gyara zama sosai.

"Ya sunansa?"

Na ce, "Sharukhan."

"Haka nan ki ke son ganinsa?"

"Ina bala'in son shi ne, ya iya acting."

"Me kika ce?"

"Cewa na yi ina son shi."

Ya yi murmushi mai fitar da sauti.

"Ko wajensa za ki koma?"

Nan take na juyo na kalli fuskarshi,ko kallona ma bai yi ba, balle ya bani wata amsa, na miƙe na nufi cikin ɗakina na ƙwanta,bai fi mintuna sha biyar ba sai gashi ya shigo, ya iso ya zauna gefena.

"Ban fahimci abin da ki ke nufi da tasowa ki ƙwanta ba, daga na yi miki maganar mutumin da ba muharramin ki ba?" Ya juyo sosai ya sumbaci kumatuna.

"Ki yi haƙuri in kin ji ba daɗi." Na ɗan yi murmushi.

"Ban ji komai ba, na dai zo na ƙwanta ne kawai."

"To taso mu sauka ƙasa ki ga mutane kafin gobe in kai ki wurare da dama waɗanda na sani."

Na yi murmushi na tashi zaune, da niyyar in tashi mu tafi, ya riƙe hannuna.

"Kisa doguwar suit ɗinki,saboda jama'a."

Yau ƙwananmu huɗu a ƙasar Greece,a ƙwanakin ukun da muka fara fita ba inda Yarima bai kai ni ba, wuraren wasansu na yara, amma su manya ma na zuwa,a nan ma ya ga na fara sakin jiki da shi, balle da aka ɗora ni wata mota mai sa jiri ina saukowa na kasa tafiya, sai dai Yarima ne ya ƙwantar da ni saman kafaɗarsa muka samu wajen zama yana yi mini dariya.

Wani abin burgewa irin na ƙasar Turawa, shi ne ba wanda ya damu da abin da ka ke ciki, balle a tsaya kallonka, shi kansa Yarima sai yanzun na ƙara gane cewa dogarawan da ke bin shi a baya suke ƙara masa girman kai, amma yanzun ba ki gane shi ko ɗan waye.

A ƙwanakin nan huɗu kuwa ba wata alama da Yarima ya nuna mini sai ma ɗan tilasta ni in yawaita shiga ruwan ɗumi cikin hikima irin tasa. Tabbas Yarima na sona,ni kaina na amince da hakan,ni kuwa zuciyata har yanzun tana baƙunta da shi, shi ne ta kasa tsayawa ta saki jikinta da shi, har ta gano irin son da take yi masa.

Yanda nake ƙwance a gadon da ke bakin ramin wanka,in ka hango ni ba ni da maraba da Turawa, saboda kayan jikina,siket ne baƙi da farar riga a jikina, wanda gilashi ne manne a idanuwana, irin ɗaurin ɗanƙwalin Turawa nima shi na yi, shi ne ka ɗaure gefe-gefe amma tsakiya a baje saman baya.

Kaina ƙwance yake gefe, ina kallon cikin ramin wankan,babu inda idanuwana suke sai kan Yarima da ke ta wasan wanka a cikin ruwan, duk da duk ɗan lokaci ya zo bakin ruwan ya ɗan watso mini shi kaɗan,in ɗan yi ƴar ƙarar ƙissa, shi kuwa ya yi ƴar dariya ya ƙara komawa sosai cikin ruwan.

Ganin inda ya nutsa kansa ya tsaya cak ruwan baya motsi irin ana wanka da shi, shi yasa na ɗan ɗaga kaina sosai ko zan ƙara hango shi, amma ba na ganin sa ko kaɗan, cikin sakan ɗaya sai na ji kamar kaina ya sara, irin na tashin hankalin nan, ban san lokacin da na miƙe tsaye ba, isowa na yi bakin ruwan na tsugunna duk gwiwa biyu ina jira,in ga ɗagowar Yarima.

Tun ina ganin kamar wasa, har na ga ya ƙwashe mintuna,nan take na ji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login