Showing 15001 words to 18000 words out of 27367 words

Chapter 6 - Kasaita Book 2 Hausa Novel Complete

sabon halinsa ya bayyana.

Cikin sanyin jiki da cikowar hawaye a idanuwana na mayar da agogon na ajiye saman durowar,farar takarda mai rubutun baƙin biro mai ruwan (ink pen) idona ya gani a gefen durowar, na yi ɗan saurin miƙa hannuna na ɗauka, cikin ɗan rawar jiki na kai idanuwana a jikinta.

_Barka da Asuba_

_Mace tagari,macen da kowanne namiji na duniya yake son ya mallaki irin ta,kin zama abin alfahari a gare ni._ Na gode.

_Na je masallaci, amma komai zai biyo baya, ina neman afuwarki, saboda ni kaina bana son al'adar nan da zata biyo baya yanzun ba da daɗewa ba, ba wai naƙi tsayawa in taimaka miki ba, na kasa tsayawa ne saboda abubuwa guda uku,kunyarki,girmanki, wanda ba za su bar ni haɗa ido da ke ba,sai kuwa masallaci saboda ba a tayar da sallah sai na isa._

_Rashin ganina a masallaci zai iya haifar da ɗan ƙaramin tashin hankali, saboda za su yi zaton ko banida lafiya ne, godiyata ba zata iya samun ki ta baki ba, saboda ban san wane bakin ne ya cancanci ya yi miki godiya ba,ni dai na yanke hukuncin yi miki addu'a da Allah yasaka miki da aljanna firdausi mani'imciya._

_Husband._

Na jefar da takardar na sa tafukan hannayena na rufe fuskata, saboda kunyar da na ji,a hakan ma sai na ga kamar yana tsaye yana kallona, wannan yasa na yi sauri na lalubo makashin fitila na kashe,bargo na ja na rufe har kaina, ba wani tunani da ya faɗo mini sai na ya zanyi in haɗa ido da iyayena da shi kansa Yarima?

Tunani ya faɗo mini,na inyi sauri in shirya in ɓuya kafin Yarima ya dawo, amma kuma abu ɗaya yana neman gagara ta, shi ne tashi tsaye, amma duk da haka na samu na yi ƙarfin hali na tashi zaune, na yi shiru ina sauraran ko zan ji motsin Yarima,wai ni gudun kada in tashi ban sani ba ko yana laɓe yana kallona.

Tsayin minti biyu na ɗauka sannan na ɗan janyo jikina na kunna fitilar gefen gadona, haske ya gauraye ɗakin nawa,a nan ne na hango rigar wankan da Yarima ya ɗora a saman gefen gadona, na ja jikina zuwa inda take, nasa hannu kenan na ɗauka sai na ji motsin murɗa ƙofa, na yi sauri na janyo rigar na dawo na kashe fitila na koma na ƙwanta.

Muryar da na ji tana kirana, "Gimbiya, Allah ya taimaki Gimbiya."

Da naji na gane ta mace ce, a cikin rufar da nake na ce, "Wace ce?"

"Allah ya taimaki Gimbiya uwar kowa, jakadiya ce, mai girma Yarima ya ce in zo kina kirana,wai zan taimaka miki da wasu ayyukan."

Nan take na ji hankalina ya tashi, me Yarima yake nufi? Zuwa ya yi ya gaya mata abin da ya faru da ni? Nan take haushi ya kama ni, da nayi tunanin korar ta amma sai na yi tunani sai fa an taimaka mini, da su Mansura su taimaka mini kuwa ai gara jakadiya, tun da ko banza ta haife ni.

"Shigo mana, ba na jin daɗi ne."

Na laluba makunnin fitila na ajiye kusa da ni, sai da na zauna nasa rigar wankan sannan na kunna, da rawar jikinta ta iso gaban gadona ta zube ƙasa,tana ɗan sussunkuyar da kai, yanda na ga tana yi shi ya sa nake tambayar kaina da cewa ko Yarima ya gaya mata ne?

Kamar ta san tambayar da nayi, sai na ji tana wasu ƴan surutai, "Ai dama duk ƴa tagari shi ne ta cika ɗakinta,a yanzu ba ke ba koni na zama abin girmamawa, tunda matar ɗana ta cika ɗakinta,yau kam shagali ya same mu,ai mu yau sai yanda hali ya yi."

"Bana son magana ki tashi ki yi aikinki."

"To, to ai komai ki ka ce shi za'ayi."

Ta miƙe da rawar jiki, sai na ga ta ajiye wasu ƙwalabe, sun kai huɗu ban dai tsaya tambayar ta ba ta shige banɗaki.

"Ai ya tara mana ruwan ɗumin,a gaishe da ɗana,ai fa na raine shi tun ranar da aka haife shi,dama ai in ka raini yaro a gidan sarauta, to kai za kayi masa jakadiya a al'adance, saboda kun shaƙu da junanku, yanzu ne dai ake son rai, sai wasu su dinga ɗaukar wata,kin ga ai ta nan za'a iya haɗa kai da ita a cutar da shi, ke kuwa da kika raine shi tamkar ɗa yake a gareki, ba ke ba cutarwa a tsakaninku.

Bari dai ki gani in yi sauri, kada a fara taruwa,ai ni murna ce ma ta hana ni yin komai,kin ga yanzun wallahi duk abin da ki ka faɗa ta zauna, komai ki ke so kuwa shi za'ayi miki,ai daga yau kin zama shalelen Sarki.

Duk maganganun da take kuwa cikin rawar jikin ɗaukar ƙwalaban da ta ajiye ne, da rawar jiki ta nufi banɗakin.

Kafin ta fito na yi ƙoƙari na miƙe, wanda cikin sauri na na mayar da bargo na rufe zanin gadon da na tashi a kai,dama abu ga zanin gado fari ƙal, cikin dabara na dinga jan zanin gadon, amma ya ƙi fita, ina haka sai ga jakadiya ta fito.

"Dama na tanadi kayayyakina,ai ina sai kin juya Yarima kamar waina,na dinga gyara ki kenan, yanzun haka waɗannan sai da na je ƙasar Sanigal na siyo su wajen jika ashirin da biyar,dama burina ɗana ya samu mace tagari."

Ni kuwa kamar an kulle bakina, ita kaɗai ke surutanta tana rawar jiki, can sai ta lura da ɗan jan zanin gadon da nake yi.

"Ina,ai sai wanda ya zaunu gidan sarauta ya san yanda ake shimfiɗa zanin gadon nan ranki ya daɗe."

Tun ta ɓangaranta na ga tana ɓalle wasu abubuwa, ɗora su da tayi a gado sai na ga dogayen abu tamkar ƴar fill ɗin ɓalle kaya (fila) ta ɓalle har ta zo inda nake, tana gamawa na janye zanin gadon na ƙudundune shi.

"Don Allah jakadiya kada ki bar kowa ya gani,ki ɓoye mini shi, zan tambaye ki anjima,ko da yake ba ni shi nan ma in shiga da shi in wanke."

"A'a Gimbiya me ye amfanina."

"A'a bai dace ba, ba ni."

"To,ai..ai...ai.....dashi ake... ake...imm...im ki dai shiga wankan in ɓoye miki,ai...ai...ɗana ya kamata dai ya wanke ke dai shiga Gimbiya."

Ban dai fahimci abin da take nufi ba, haka nan dai na shige banɗakin na ƙyale ta a tsaye tana ƴan soshe-soshe, ina shiga na ji wani irin mugun ƙamshi, wanda dole idan ya shiga hancin mutum sai ya lumshe idanuwa, daga nan ma zai iya tafiya mafarkin tsaye.

Na buɗe idanuwana, na ce lallai jakadiya tana son Yarima zan ce,ko kuwa ni take so? Har na ɗaga ƙafa zan shiga cikin ruwan da ke cike da bahon wankan wanda kalarshi ta koma ja-ja ja-ja, sai na tuno cikin surutan jakadiya na ji tana cewa lallai sai an fara yin wankan sabulu sai ayi wanka, kuma na tsarkake jiki, daga baya sai a shiga ruwan bahon, ana ɗaukar minti talatin har fi a ciki, saboda komai na sinadarin ƙamshin ya ratsa jiki.

Na girgiza kaina,lallai harka da irin su jakadiya akwai ilimantarwa, zan kuwa ja ta a jikina ta dinga koya mini sirrikan zama da miji da jama'a,lallai sarauta sai ɗanta,sai kuwa wanda ya gaje ta, wannan turare kullum kana wanka da shi,ai sai ka hana mijinka fita ƙofar gida.

Bayan kamar mintuna hamsin da uku na fito daga banɗaki, wani al'ajabi ya dirar mini a take, tawul ɗin da ke hannuna ina tsane kaina na saki ƙasa,shin me ye haka kuma?

Ɗakina na ga ya canja gaba ɗaya, wajen zaman gadon da zanin gadon sababbin wasu zagayayyun filalluka sun kai goma sha biyu aka zuba a saman gadon, kowanne an yi masa mazauninsa, shi kansa labulan gadon ya koma kalar zannuwan gadon, haka labulayen da ke zagaye a ɗakin nawa, na ƙara zagayawa sai na ga wata irin lafiyayyiyar kujera zan ce ko gado ƙarama daga gefe, ta sha dardumai, daidai da kafet ɗin gaban gadon an canja mini shi, da komai ruwan fari ne a ɗakin, yanzu kuwa ruwan bulu ne mai haske, ma'ana tamkar fararan kayan da suka sha bula.

Mata ne su uku zaune a ƙasa, ban da jakadiya ta huɗu, wani ƙamshi ɗakin ke yi wanda kuma ya sha bambam da na banɗakin da ya ruɗani, saboda mamaki har ma na kasa tunawa da komai,maganar da suka ɗauki yi gaba ɗayansu ita ta dawo mini da hankalina a jikina.

Irin kirarin nan da ake wa ƴaƴan sarauta shi na ji suna yi mini,wanda ba zan iya riƙe komai daga cikin abinda suke faɗa ba, na isa wajen abin sallata tare da saka rigar sallata, na sa hijabin sallah, waɗanda na tarar duk an canja mini su, hatta da mazauninsu ma sai da aka canja.

Sai a lokacin na ɗago kai na kalli jakadiya cikin ɗan jan kai irin na masu mulki na yi masu magana.

Jakadiya ku ɗan bani waje in shirya ko?"

"Ki dai kimtsa Gimbiya, amma ai masu shirya ki sun iso suna ƙasa."

Wannan maganar ta jakadiya tana yi tana tafiya, wacce a lokacin da ta kai ƙofa ta gama yin ta, wannan ne ni kuma bai bani damar mayar mata da amsa ba,ko kuwa in ce tambayarta ba, da cewa su wa zasu shirya ni, wanda ya wuce ni kaina?.

Kafin in gama sallah da lazimin da na kan taɓa bayan kowacce sallar farillah tawa, jakadiya ta leƙo ya kai sau taƙwas a inda daga ƙarshe ta ga na kammala na miƙe tsaye ina ninke hijabin sallah ta. Wannan kuwa ya yi daidai da shidda da ƙwata na safiyar asabar.

Ko mai ban ƙarasa shafawa ba na ga jakadiya ta shigo tana cewa, "Ku shigo ku shigo mana."

"Me zasu yi miki in sun shigo?"

"Dama masu shirin ne."

"Shirin me?"

"Jikinki,daga gidan Mai Martaba aka turo su."

"Ba na so kina jina,ku fita."

"Allah ya huce ran Gimbiya ai.."

Wayar da ke kan ƴar durowar gefen gadona ta ɗauki ƙara.

Cikin gaggawa jakadiya ta isa ta yi saurin ɗauka ta kanga a kunnanta,ganin cikin saurin da bai wuce na sakan ba ta durƙusa ƙasa yasa na gane, Yarima ne ko kuwa shi kansa Mai Martaba Sarki ne.

"Eh,to,to." Ta ce kawai,ta cakumo kan wayar ta nufe ni.

"Allah ya ja da rai gata." Sannan ta miƙa mini.

Kafin inyi magana tuni na gane muryarsa, duk da ji ta ƙara zame mini baƙuwa,saboda ta koma ƴar ƙarama mai zaƙin gaske.

"Good morning, I hope you are recovering?"

"Darling what happening?"

"Oh, darling sorry, honey say hello to me please,ko na samu nutsuwa."

Ni na san dama ba zan iya amsa masa duk maganar da zai yi ba saboda abu biyu kunya da haushin tonan asirin da ya yi mini,saboda haka na kife kan wayar ba tare da nayi magana ba,bai fi minti ɗaya da ajiye wayar ba na ga Hajiya Kilishi ta yi sallama ta shigo. Subhanahi! Shi kenan ƙaryata ta ƙare, wannan tonan asirin na san ya je kunnan Sarki.

Hawaye ma na ji kawai sun tarar mini a cikin ƙwayoyin idanuwana,mata biyar ne biye da ita, da ganinsu ka san matan masu faɗa a ji ne, wato matan masu kuɗi, saboda biyu daga cikinsu na san su suna zuwa duba ni da na zauna zaman jinyar saran maciji a gidan Sarki.

Kaya ne lodi-lodi a hannunsu, irin farantan da jakadiya ta taɓa kawo mini kayan siyan baki,a ranar da aka bar ni ni ɗaya. Da ƙyar na samu na gaishe su saboda kunya. A nan jakadiya ta gayawa Hajiya na ƙi yarda a yi mini komai, da lallashi da ban magana ta shawo kaina, shi ma dan ina jin kunya da nauyinta, ga shi kuma tana da girma a idanuwana.

Ta tabbatar mini da cewa ita ma haka aka yi mata, sannan duk ɗan hakimi a kan haɗa masa ƴar ƙwarya-ƙwaryar irin wannan bikin idan dai har matarsa takai, to balle ni wai da nake matar ɗan Sarki gaba ɗaya. Dole dai ta sa na tsaya,nan fa naga hidima, ƙunshi mai zane, hannuwa da ƙafafuwa, wani irin naɗin kitso ƙwaya shida kacal, wanda na ga ya fi yi mini kama da kalba, amma bambancinsu shi naɗinsa kamar ana murɗa igiyar shanya.

*ƘASAITA BOOK 2*


*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*


Page 9


Ni gyaran da ake yi mini ko ina amarya Ni ban same shi ba, saboda sai da Hajiya Kilishi ta sa na tsugunna ga turarurruka kala-kala shida, dukkansu kuma na garwashin wuta, sai a lokacin da suka gama ne ma aka buɗe kayan da suka shigo da su. Wata ƙwarya ce ta sha zanan baƙi ƴar ƙarama aka miƙo mini,wai in shanye abin da ke cikinta, ban yi gardama ba na kafa bakina sai naji kamar ruwan inibi da madara, kamar kuma madara da ruwan ƙwaƙwa, ni dai na shanye.

A taƙaice dai hidima ta tashi sabuwa tamkar ana wani ƙasaitaccen biki. Ƙarfe goma na safe kuwa ai gida ba inda zaka zauna, saboda jama'a. Hajiya Kilishi ta gaya mini cewa za'a tambaye ni me nake so, saboda mutane da kunya da wuya in iya magana, amma in rubuta a takarda,in an tambaya in bai wa jakadiya,kar in yarda wai a ga fuskata sosai,in zamo mai kunya.

Da za'a fita da ni inda zan zauna, sai da aka sa nayi tsaye na ware ƙafafuwana a saman wani kaskon wuta mai fitar da hayaƙin ƙamshi, shiga ta kuwa ba zan iya faɗar ko meye a jikina ba,ni dai kiran shi da yadi mai laushin gaske,ko kuwa les ne? Oho,ni dai na san sai dai kalar sa ce ruwan hoda, takalma da alkyabbar jikina kuwa ruwan madara ne, tare da mayafin da na zizara a saman kafaɗa ta.

Wannan al'ada ina amfaninta, na faɗa a zuciyata. A lokacin da na isa kujerar zamana inda muka zauna ina amarya,yau ma anan muke,ni da Yarima, sai dai kujerun da shimfiɗun kafet ɗin sun sha bamban da na baya,sam ban sani ba, ashe kowa ya hallara ni kawai ake jira, hatta da sarki ya iso yana nashi rukunin, ango Yarima kuwa nan na sameshi a zaune.

Ba zan iya gane ko su wa da su waye ba ne a bayana, saboda gilashin da ke manne a idanuwana, ban da wani mayani da Hajiya Kilishi tasa ta ɗan lulluɓe min rabin fuskata, filin kasan ƙasan kuwa daga can gefe ɗaya raguna ne kawai ake gasawa a ƙarƙashin wuta, tamkar dai waɗanda zasu yi fati.

Aka buɗe fili da addu'a da sauran bayanan manyan mutane, wanda a ƙarshe Sarki ne da kansa ya miƙe yana bayani da godiya ga waɗanda suka zo,ni kuwa da ɗansa Yarima mun sha albarka, a lokacin ne naji Yarima ya zuro hannu ta alkyabbarsa ya kama hannuna.

Ban da dama tun da na zauna yake ta zunguran mini ƙafa da tashi ƙafar, ta ƙarƙashin kujerarmu,ni na san ba mai gani, tunda alkyabbun jikinmu sun rufe har ƙafafunmu, na ji kalma ɗaya da ya faɗa ita ce, "You Are cheerful Yasmin."

Na samu na sulale hannuna ba tare da na kalleshi ba. Ƙyaututtuka kam na sha su, shi kansa Sarki ƙyautar gidan gonarsa na ƙauyan Bukuru ya ba ni, ya kuma ce zan ziyarci ƙasa huɗu, sai wacce na zaɓa, sannan ya baiwa iyayena sababbin motoci guda biyu, ban da wani dunƙulin abu a cikin jar jaka da naga ya ce tasu ce, sai dai ban san komai ke ciki ba.

Waziri ya bani bayi huɗu da dokuna uku,doki biyu goɗiya, ɗaya namiji, da sabuwar mota ƙirar KIA (Optima). Ni wata ƙyautar ma in an faɗeta sai inji kamar ma ƙarya sukeyi, magana kuwa cikin nutsuwa yanda ba mai ji, Yarima ya dinga yi mini ita sau ɗaya na yi murmushi, na ji ya ce, "Thank God."

Kaina na ji ya sara tare da juyawa wani amai mai zafin gaske da na ji ya taso mini,wannan kuwa ya sameni a daidai lokacin da na ga wasu fadawa biyu sun miƙe tsaye da wani farin abu a hannunsu,sam da ban gane ko meye ba, sai lokacin da naji sun ce, "wannan farin zanin da kuke gani, shi ne zanin shaidar cewa ƴarmu ta kai ɗakinta, wato Gimbiya Yasmin."

A take na gane zanin gadon ɗakina ne wanda na baiwa jakadiya amanarshi, shi ne fa hankalina ya yi matuƙar tashi, a take na tallabe ƙirjina alamar amai, Yarima ya yi saurin dafa ni.

"Yasmin meye?"

Wata tambayar raini ma na faɗa a zuciyata, kafin ya ƙara yin wata magana sai dai na hango an ware zanin gadon nan kowa ya kama gefe ɗaya, kenan dai an yi masa buɗewar zanin da za'a shanya.

Cikin sakan biyu sai dai na ji amai ya wanke mini jiki dama ni gani ban iya ganin abin tashin hankali ba, sai inji ni ina ta amai, kamar wata mai yaron ciki,ko kunya ma Yarima bai ji ba naga ya miƙe da sauri ya kama ni,kafin sakan uku sai dai na ga wani koran labule ya sauka a gabanmu da bayanmu dama gefenmu ba kowa kujerunmu ne kawai.

Cikin ƙanƙanin lokaci Yarima ya ɗaga ni na miƙe tsaye,da amai ya yi tsalle sai jikin Yarima amma sai na ga ko a jikinsa shi dai buƙatarsa in taka,gyaran murya na ji ya yi sai dai na ga hannu ya zuro ta wata ƙofa ya miƙo masa wani yanki ja, mai kama da yankin bargon jariri, har ya fara goge mini,ganin ina layi yasa na ga ya ɗauke ni cak sai dai na ji ya yi gyaran murya.

A take na ga kawai yana tafiya labulan nan na binmu ba mai ganin kowa ba mai ganinmu, shi kuwa ɗan yankin nan ya shinfiɗa shi saman ƙirjina wanda amai ke ta zuba a jikinsa,ni dai dole ta sa na koma saman ƙirjin Yarima na ƙwanta, idanuwana kuwa tuni a lumshe suke.

Jin an ajiye ni wani abu mai laushi yasa na buɗe idanuwana,gani na a ɗakina saman lallausar katifar mulkin nan zan ce ko kujera? Wacce ta sha dardumai na alfarma, da rawar jiki na ga ya cire alkyabbar jikinsa da ta sha feshin amai, sannan ya duƙo wajena yana ƙoƙarin cire mini tawa,na ɗaya masa hannu alamar ya tsaya.

"Don't touch me." Na faɗa.

"Yasmin ki yi haƙuri in taimaka miki."

"Bana so,ni ka kira mini Aunty Salwa."
Na saka kuka, yayin da na ci gaba da cewa "ka cuceni,ka tona mini asiri,ka yaudare ni, Allah ya saka mini, yanzun kuma gidanmu zan tafi,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login