Showing 21001 words to 24000 words out of 27367 words
kamar kaina ya fara juyawa, na waiga ban hango wani wanda ya yi kama da ɗan Afrika ba, ballantana in kirawo shi, abin ka ga ƙasar Turawa, kowa da tashi hidimar ba ma wanda hankalinsa yake a kaina.
Juyowar da zan yi sai na hango Yarima ƙwance saman ruwa, amma ta bayansa kenan kanshi da cikinsa duk a ruwan suke, na miƙe tsaye na yi kamar in yi ihu, to wa zan yi wa,ni kuwa dalilina na ƙara ruɗewa a irin ƴan fina-finan da nake kallo na san in an ga mutum a saman ruwa to ya mutu kenan.
Ganin ba zan iya zuwa cikin hotel ɗin ba in kira ma'aikatan yasa na ji wani ƙarfi ya zo mini ban san lokacin da na shiga cikin ruwan nan ba sai dai gani na nayi ina kokawa da gangar jikin Yarima,manufata in juyo fuskarshi ta kalleni ta hakan zan gane ko yana da rai.
Duk cikin mintin da bai wuce ɗaya ba na yi haka,babu wani alamar rai a jikin Yarima a lokacin da na juyo shi nan take na ji zazzafan gumi na tsiyayo mini ta saman gashina, ban da mugayen hawayen da ke shatata ba tare da an rera masu waƙar kuka ba.
Ƙarfi na ji ya ƙara zo mini cikin rawar jiki na ji na janyo shi zuwa bakin ruwan, sannan na yi ta maza na ɗora shi saman gefen ruwan, da rawar jikina na zagaya na fita daga ruwan. Sannan na janyo shi.
*ƘASAITA BOOK 2*
*NA*
*MARYAM KABIR MASHI*
Page 11
Amma ina namiji ba mace ba sai ma ya ƙara komawa cikin ruwan nan, take na sa ƙara mai tsanani, na ruga a guje ina cewa a taimaka mini da harshen Turanci, ma'ana.
"Please help me! Help me!!”
Nan da nan aka zagaye shi ni kuwa gani nake duk ba su isa ba, tunda ba ma'aikatan hotel ɗin, da gudu na isa falon da ake fara karɓar baƙi (Reception) da harshen Turanci na yi masu bayani, kafin minti biyu har sun riga ni isa inda yake, ina isa na cakume shi, cewa nake, "Yarima ka tashi! Tashi!!...” har sai da suka ɗan riƙe ni, sannan aka danna ƙirjinsa da cikinsa sai ruwa ya ɗan fito ta bakinsa.
Na fizge na zo na ƙara kama shi,a taƙaice dai ban ƙara sanin abubuwan da na dinga faɗa ba har aka kawo ɗan wani gado aka ɗora shi, sannan aka tambaye ni lambar ɗakinmu da ƙyar na iya faɗa,saman gado aka ƙwantar da shi na warware bargo na rufa masa, sannan na ga an yi masa wata allura a jijiya, cikin sakan biyu na ji ya yi wani tari, na ƙara riƙe hannunsa gam, cewa nake.
"Tashi! Tashi!! Tashi!!! Yarima kada ka mutu."
Sun gaya mini da harshen Turanci, zai tashi amma in dinga murza tafin hannunsa, da ƙyar na amsa da to. Sannan duk suka fita na kuwa dage goga hannuwansa duk biyun in na yi wa ɗaya in saki in kama ɗaya,kai sai gani har da busa bakinsa,ni sam na ma manta da wani haɗa baki muke yi da shi, wani ihu bayan hari zan ce, saboda wai sai a yanzun na ji ina mugun son Yarima, amma kuma ga shi a saman gado ya zame min ƙila wa ƙala.
Na samu wajen minti talatin a haka, wanda hakan yasa na ji na karaya, sai kawai na ƙwanta saman ƙirjinsa na dinga kuka. Kuka mai tsananin gaske, amma ba wanda ake ihu ba, wanda gangar jikinka duka ke motsawa.
Sama da mintuna ashirin ina haka wanda tuni har tunanina ya bani in bugawa Aunty waya in ce a zo a tafi da mu. Hannu na ji an sa an shafi gashin kaina ɗan motsi da numfashi su suka sa na yi saurin ɗaga kaina saboda in ga mai taɓa mini gashina. Yarima ne ke kallona yana murmushi, na yi wata sassanyar ajiyar zuciya na dinga murmushin daɗi don ma ina jin kunyarsa da tuni na yi tsalle.
Na tashi da sauri na dawo saman gadon na faɗa jikinsa ya mayar da hannuwansa ya rungume ni ina jin shi yana ta shafa gashin kaina, alamar lallashi ina jinsa yana ƙoƙarin ya ɗago ni amma na rungume shi tamau, ina jinsa ya faɗi kalmomin nan da harshen Turanci.
"Yasmin do you love me now? Zaki iya sakin jiki da ni?"
Na ɗaga kaina wanda ke ƙwance a tsokar naman kafaɗarsa.
Tabbas murnar Yarima ta fito fili,dana amsa masa ina son shi, ya ɗauke ni baki ɗaya ya ɗora ni a gadon da yake ƙwance, ya mayar da ni ya ƙwantar a ƙirjinsa ya janyo bargo ya lulluɓe mu a ciki, fuskokinmu kawai ke waje, na ɗago na ce masa.
"Ka samu sauƙi?"
Ya yi murmushin da yasa na ji sabuwar kunyarsa ta dirar mini sannan ya ɗaga kai alamar eh, wanda jin ɗaga kan kawai nayi saboda ni tuni na mayar da kaina a ƙirjinsa na ƙwantar.
Lallai yanzu zuciyata da gangar jikina sun amince mini da ina son Yarima,su ma kansu son Yarima ya cika su dama. Na yi sauri na ɗan yi alamar zan tashi ya ruƙo gashina ta bayana, na juyo da sauri har da ƴar ƙara da ido da kai ya tambaye ni ina zani? Na sunkuyar da kaina ina murmushin da yake fita tare da ƴan ragowar hawayen idanuwana.
"Magani zan ɗauko maka, likita ne ya ce da ka tashi na baka."
Da kai ya nuna mini cewa inje na ɗauko, ina murmushin mamaki na cikin zuciya kenan bai fito fili ba, saboda mamakin yanda Yarima ya ƙware da maganar kai ko da yake ba mamaki idan na yi la'akari da farkon haɗuwata da shi yanda ya yi wa dogarawansa magana da gilashin hannunsa.
Bayan na kama shi ya tashi zaune na taimaka masa na jingina shi jikin kan gado wanda nasa filo a bayansa sannan na zauna kusa da shi na miƙa masa maganin da ruwa a kofi, maganin ƙwaya ɗaya ne ɗan ƙarami, sannan na ƙara janyo kujerar da na ɗora ɗan farantin da kofin maganin na ajiye kofin sannan na miƙa masa kofin ruwan madara ya shanye.
Saboda magriba ta kawo jiki,in na yi la'akari kamar a ce ƙarfe shida na Nigeriya kenan, wannan yasa na ce ya yi ƙoƙari ya je ya shiga ruwan ɗumi a banɗaki ko ya samu ƙarfin jikinsa sosai,bai yi mini gardama ba ya miƙe abinka ga namiji sai na ga baya ko irin ɗan tangaɗin nan na marasa lafiya.
Ina zaune ni kuwa na rabka uban tagumi a gefen gado ina jiran ya fito, wanda tuni na tafi duniyar tunanina, na da Yarima ya mutu da ya zan yi? Ba don komai ba sai don yanda zuciyata ta fara nutsuwa wajen son zama da shi a matsayin mijin aurena,wai don shirme sai na ji hawaye sun taho na samu na lumshe idanuwana su kuwa suka ci gaba da gangarowa.
Ban ji fitowarsa ba, saboda idanuwana a lumshe suke, kuma linzamin tunanina ya canja salo ya koma tunanin abubuwan son da Yarima ya nuna min a fili, na tuna ranar da ya mallake ni a matsayin matarsa irin nuna so da ƙaunar da ya yi mini a wannan daren ƙwaya ɗaya cal.
Jin an sumbaci laɓɓan bakina shi yasa na dawo daga duniyar tunanin da na tafi, na buɗe lumsassun idanuwana sai na ga Yarima tsaye a kaina, na yi saurin ƙwantar da kaina a cinyata na ce, "Kai Yarima."
Cikin kunnena ya ce, "Ke Yasmin me ye.?"
Na ɗaga ɗanyatsa na nuna shi, "Me ye,tawul, Yasmin sai in ƙi ɗauro tawul ni da matata ni ne fa kawai a ɗakin"
Da jin yanda sautin maganar ke fita ka san Yarima bai saba da yawan magana ba, saboda cikin nutsuwa yake yin ta.
"Ki ɗago Yasmin na zama naki fa."
Na girgiza kaina.
"Sai kasa riga."
Ina jin sa ya zauna dab da ni tabbas na ji sunkuyowarsa daidai da kunnena, saboda jin hucin numfashinsa, madadin ya yi magana sai dai kawai na ji ya hura kunnena,tsigar naman jikina na ji ta yamutsa, na rasa ya zan yi sai dai kawai na koma gado na ƙwanta a ƙudundune.
Haɗani ya yi ya rungume a ƙirjinsa, amma ta bayana, kalaman da suke fita daga bakinsa su suka sakani na ji ɗakin na juyawa da gadon da nake ƙwance, jin ya ƙara hura mini saitin ƙofar kunnena yasa na mirgina ɗaya kusa da shi na samu na miƙe na gudu, na shiga banɗaki, saboda na san nan kaɗai ne in na shiga na tsira, shi ma idan na kulle saboda ƙaton falo ne da ɗaki ɗaya kawai su ne ɗakunan hotel ɗin.
Na kulle ƙofar, amma sai na ji na jingina da ita tare da sulalewa ƙasa na zauna, kai sai na ji ina jin kunya ni kaɗai a banɗaki, na ƙudundune kaina jikin cinyata, na dinga murmushin da zan iya kiranshi na daɗi,wai don tsananin shirme irin nawa da na ɗaga fuskata sai in mayar wai kunya nake ji.
Sai da na ƙwashi wajen mintuna sha uku a haka, sannan na yi sauri na miƙe tsaye saboda tunanin da na ji ya faɗo mini a take,shi ne sallah na san bai fi sauran mintuna a kira sallah ba,ko kuwa in ce lokacin sallah ya yi tun da garin arnaku muke balle mu samu kunnuwanmu da jin kiran Sallah.
Na saɓule kayan dukkansu a gaban ƙaton madubinsu na banɗaki na kalli kaina tas na yi murmushi ganin ba ni da ko ƙwantalan ƙurji a dukkan jikina ballantana tabo, sannan ko'ina na jikina farinsu ɗaya,in an ɗauke saman tsokar ƙirjina.
Na shige ƙwami na zauna dirshen sannan na saki famfunan dukkan biyun ɗaya na zubo da ruwan zafi ɗayan kuwa na sanyi yake ƙwararo min, cikin ɗan gaggawa na gama wankana,gudun kada Yarima ya jira ni da yawa, saboda na san shi mutum ne mai son jam'i. Ina fita sanye da rigar wanka,shi kuma yana sallame sallah.
A zuciyata na ce har ya ƙagara. Na ɗauki kayana riga da wando,wandon ruwan baƙi ne rigar kuwa mai dogon hannu ce ruwan madara, sannan rigar ba ta wuce ƙugu ba, na fito na zauna gaban madubi na yi gaggawar shafa ɗan Wetlips kawai nasa a laɓɓana, na taje gashin kaina na ɗaure shi na sakeshi a baya, sai kuwa turaran da na feshe jikina da shi.
Alkyabbata na zura domin gabatar da sallah, ina isa wajen da na keɓe mana domin sallah na ga Yarima ya miƙe, sannan ya ce mini "Bismillah." Sai wannan lokacin tunani ya faɗo mini cewa nafila ce Yarima ya yi irin waɗannan halayyar ta son Addininsa yana ba ni mamaki, saboda ban taɓa tunanin yana ma sallah ba, ballantana ya iya riƙe Addininsa da hannu bibbiyu, balle da na je gidan yari na ga irin yanda yake baiwa jama'a wahala, ga mulki har na fitar hankali.
Bayan mun gama ne na ji ya ɗaga hannu sama yana jero sunayen Allah gaba ɗayansu daga nan kuwa na ji ya faɗa ga addu'ar Allahumma izzal Islama wal Muslimin har ƙarshenta, sannan ya rufe da wata addu'a wacce tun ina yarinya na ji ana yi mana ita, abin da ya bani mamaki kuma sai na ji ya rufe da ɗayar ma wacce zan ce kowa tun yana yaro ma ya iya ta.
_Rabbana atina fidduniya hasanatan wafil alkhirati hasanatan waƙina azaban nari._ _Rabbana latuziƙ ƙulubana ba ada izhadaitana wahablana min ladin ka rahamatan innaka antal wahab._
A take na tuna da malamin islamiyyarmu da yake ce mana ana son duk sallah a dinga karanta ta,falalarta Allah kaɗai ya san yawansa, sai dai yawan yin ta na kawo arziƙi duniya da lahira.
Hankalina na ji ya ƙara nutsuwa a kan Yarima,ganinsa yanda yake kula da Addininsa. Muna kammalawa ya miƙe ya gabatar mana da sallar isha'i ni dai gaskiya na ji mamaki matuƙa a kan yanda na ga Yarima na tafiyar da rayuwarsa,in na yi la'akari da yanda yake a baya, mutumin da ko motsi ma baya iya yi sai dai a yi masa.
Bayan kammala addu'armu ne na ga ya tashi ya buɗe aƙwatinsa ni kuwa sai bin shi nake da kallon mamaki, wasu kaya na ga ya ɗauko da alama dai na mata ne, ya zauna saman gado sannan na ji ya kira ni na tashi na je inda yake, nima na zauna a gefensa.
"Waɗannan kayan nake son ki saka mini su yanzu,zamu fita mu ci abinci a can."
Riga ce doguwa har ƙasa take, amma sai ɗan siririn hannunta, sai kuwa ƴar samanta mai dogon hannu har izuwa wuyan hannunta, dole ta sa na tattare su na matse a tsakanin cinyata,gudun kada su ja ƙasa,a cikin banɗaki na isa gaban madubin banɗakin na tare gashin kaina na ɗaure shi da ɗan mayafin da na gani maƙale a jikin kayan, na yi murmushi ganin na yi mugun ƙyau, abin ka ga kalar jinin kare, sai kuwa dogayen hannuwan rigar, amma ragowar jikinsu kuwa duk jinin kare ne (Maroon colour).
Na fito ina murmushi, sannan na yi saurin sakin rigar sai na ga take ta saman tsakanina da ɗan leɓunta zai kai taku biyu ta cikin ce kawai ke ƙwance a daidai ƙafafuna. Na isa bakin madubi na zauna domin gyara fuskata, na gyare ta da wata irin hodar da take fitowa da ainihin kalar fatar jikinka,jan baki kuwa kalar kayana na saka, jinin kare kenan,dan in ƙarasa zama su turawan har ma gashin ido na saka, gashin ya yi tsaye abin gwanin ban sha'awa.
Girata kuwa sai na goga mata ƙarin baƙin jagira, domin ta ƙara fitowa, na ɗauki turare zan fesa, sai na ji ya riƙe hannuna har na ɗan ji tsoro saboda ban ga isowarsa ba, ɗan firgitar tsoron da na yi sai ma naga ta burge shi ya kamo hannuna ya miƙar da ni tsaye sai na ga ya sumbaci goshina, kunya ta sa na sunkuyar da kaina ya tallabo haɓata da hannunsa ɗaya.
"Your beauty make you to be the Prince's wife. Yasmin ya za'ayi in samu kamar ki in yi sakaci in rabu da ke,ai ya zama dole in ajiye mulkina in zama bawa a gare ki, saboda in samu in mallake ki da zuciyarki su zamo sun gauraya da jinina."
Idona a nashi amma sai na ji kamar idanunsa sun fi ƙarfin nawa, saboda wasu kunamun haske da suka fito daga cikinsa suka shiga nawa idon, wannan yasa na yi fari da idanuwana tare da lumshe su, wanda ɗan guntun murmushin da na yi, ya nutsar da gefunan kumatuna, abin da na san yana ƙara fito mini da ƙyauna a fili.
*ƘASAITA BOOK 2*
*NA*
*MARYAM KABIR MASHI*
Page 12
"Sorry,ina baki kunya ko? Tashi na daina."
Ya kamo ni na miƙe tsaye, sannan ya fesa mini turaren da ke hannunsa.
"Komai ya yi sai dai abu ɗaya da ki ka manta."
Na ɗan yi ƴan dube-dubena, na ga jikina ba abin da ya rasa, na tambaye shi amma irin tambayar nan ta ido.
Ya warware ɗan mayafin da na ɗaure gashin kaina ya lulluɓa mini shi irin lulluɓin nan na ƴan gayun boko shi ne a nannaɗe kai kawai a saki leɓe ɗaya a baya, ɗaya kuwa gaba, wanda ya bazashi ya rufe ƙirjina da shi, sannan ya zagaya ya fito da gashina ya ƙwanta baya, ya zagayo.
"Tsaya ina zuwa."
Har da ɗan gudun saurinsa ya isa ga aƙwati ya buɗa sai ga ɗan aƙwati ya fito da shi ya iso ya ɗora saman madubi, sannan ya buɗe sai ga sarƙa da ƴan kunne da zobe da agogo, duk shi ya saka mini su,ni kuwa ina tsaye ina kallon ikon Allah.
"Kin san dalilin gyara miki mayafi?"
Na girgiza kaina.
"Saboda You are full house wife." Na yi murmushi.
"To an gama, sai in ce miki yau zan miki wani abin mamaki, amma sai mun sauka ƙasa, sannan zan ɗaure miki idanuwanki da wannan ɗan hankicin sai mun isa."
"Gaya min tun a nan."
"No,sai kin gani da idonki."
Riƙe yake da hannuna muna tafiya har sai da muka iso ƙafar bene,sannan ya rungume ni jikinsa wai kada in faɗi,balle wani irin takalmi mai tsini ya saka ni sawa,ni dai na san mun daɗe muna sauka ƙafar benen,don na ji ya ce in tsaya ya dawo. Na yi tsaye tare da riƙe katakon da ke kare mai tafiya.
Ɗan tsayin mintuna biyu sai ga shi ya dawo, ya kama ni ina ji muka ci gaba da tafiya,ƙafata ta gane an zo irin ɗan filin nan na tsakanin wani hawa da wani sai na ji ya tsayar da ni ya zagayo ta bayana sai na ji ya ce.
"Zan ƙwance miki, amma kada ki buɗe ido sai na ce ki buɗe."
Sai da ya samu minti ɗaya da ƙwance mini,sannan na ji ya ce, "Open your eyes."
Ina buɗewa sai na ga wasu abubuwa masu ƙyalli sun zubo da yawa, waɗanda suka hana ni kallon abin da ke gabana, can cikin mamakin da nake yi sai na ji tafi ya cika mini kunnuwana tare da kiran.
"Happy birthday to you! Happy birthday to you Yasmin, Happy birthday to you."
Can sai na ga kamar an yi sama da wani farin yanki sai kawai na ga hall (ɗakin taro), cike da mutane sun saka cake ɗin murna a gaba (Birthday cake) Na juyo na kalli Yarima irin kallon murna da mamaki, sannan na ce, "Thank you." A kunya ce.
"Kin fi ƙarfin haka a gare ni." Sannan muka jero muka sauko ana ta tafin waƙar da suke yi tun farko.
Kai tsaye wajen dogon cake mai hawa wajen shida muka tsaya a gabansa, sannan na ji waje ya yi shiru, can daga sama na ji ana cewa.
"Muslim prayers." Sai na ji an karanta Fatiha, can kuma sai na ji an ce, "Christian prayers." Sai na ji suna yin addu'arsu da harshen Turanci, duk da ita kanta fatihar da harshen Turancin aka karanta ta.
Ana shafawa ɗakin taron ya ɗauki ɗan ihun waƙar yanka cake ɗin murna, amma ta waƙar kiɗan Bature, sannan aka zo aka zagaye mu. Wani Bature ya tsaya gefenmu sai na ji ya ce, "Wannan ɗan Sarki ne a Nijeriya, wannan kuma matarsa