Showing 33001 words to 36000 words out of 45207 words
shiga taitayinta,munira ta qaraso ta rusuna gaban inna
"Don Allah inna kiyi haquri,wallahi gidan qanwar umma ta rakani,ummance kuma ta tsaidani zamu amshi saqo mu taho mata dashi,don Allah inna kiyi haquri,laifina ne"
"Allah ya tsare gaba,amma ku kiyaye,kada ku bari ku dinga yin dare a waje,'ya'ya mata ne ku"
"In sha Allahu inna,ayi haquri,na gode" munira ta fada tana miqewa,suka qarasa dakin iman din
"Don Allah qawa na roqeki,nasan zai kiraki,koda baki sonshi ki tsaya ki saureshi a rabu lafiya" munira tace da iman cikin lallabawa sannan ya fito bayan sunyi sallama.
Kayan jikinta ta fara cirewa ta sanya na zaman gida,sannan ta daura alwalar sallar isha'i,ta dawo dakinta ta tayar,data idar tayi zaune saman abun sallar,tana jin gajiya na nuqurqusarta,ta daga kai ta dubi agogo,bataji duriyar alameen ba,da alama bai dawo bane,da tuni ya nemeta.
Idanunta suka sauka kan ledar da munira ta ajjiye mata me kayan takeaway na bikin data hadota dasu,ta janyo ta bude ta gani,su souvenir's ne kala kala harda na banza da rashin sanin ciwon kudi,sai kuma kayan ciye ciye.
Jakarta ta zaro cikin kayan ta bude don ciro wayarta,hannunta ya sauka kan wasu abubuwa,ta zazzagesu da hanzarinta. Sabbin kudade ne fil a miqe,yan 200 bandir guda,idanu ta fiddo waje cikin tsoro da mamakin yadda akai kudin suka samu,sai kuma tayi tunanin na munira ne,tunda jakar na hannunta,don haka ta dauki wayarta ta cire lock din ta fara qaqarin nemanta,saita ga alamun tex,ta buda don duba daga ina yake.
Ta zaci daga kamfanin mtn ne,don su kadai ke tura mata saqo,saidai a yau din akasin hakanne,don kuwa wata tsararriyar number ce dauke da wani zazzafan saqo,wanda ke cike da wasu shiryayyu kuma tsararrun kalamai dake nuna zallar shauqin soyayya da ma'abocin saqon ya tsinci kansa a ciki.
Sau uku tana karanta saqon tana komawa farko,sai daga qarshe idanunta suka kai kan sunan bassam,ta maimaita sunan sannan ta goge saqon da sauri,zuciyarta na bugawa,ta fita ta kira munira
"Kinyi mantuwar kudinki cikin jakata fa"
"Ba nawa bane,naki ne,bassam yace a baki" kicin kicin tayi da ranta
"Amma me yasa zayimin haka?,kinsan dai bana karbar kudin kowa ko?ko sadam da yake dan uwanki ban karbi kudinsa ba kin sani,bare wannan da bansan kowa nasa ba"
"iman.....wai me yasa kike haka ne?,kinsan dai babu kyau maida hannun kyauta baya ko?,ya zaa dinga miki alkhairi kina qin karba?"
"Na karba idan an gani a gida nace me?"
"Dama ni bance ki nuna ba,idan kinsan za'ayimiki fada ki ajjiye abinki ki dinga zara kina amfani dashi"
"Banaso munira,kizo kawai ki karba abinda ki maida masa" dariya taji ta qyalqyale dashi
"Toni ina zan ganshi yanzu?,bayan kin fita daga motar naji yana waya,a taqaice dai a abuja zai kwana ba'a kano ba,sannan na riga da nayi masa alqawarin zame masa jagora wajen samunki,kinga idan kina tsoro ma kina iya bashi dama yazo gida yaga malam......hakan zaisa kuyi tarayyarku babu tsoro ko shakku,kiyi amfani da kudinki kawai malama,sai da safe" munira ta katse wayarta abunta ta barta da waya a hannu.
Karar shigowar kira ya sanyata zabura,saura kadan wayar ta subuce a hannunta,tayi qoqarin saka wayar a silent sannan ta nutsu ta duba me kiran,idan har idanunta dai dai suke nuna mata number dazu ce data tura mata saqo,saita samu kanta da latsa ok,ta kara wayar a kunneta.
Zazzaqar muryarsa ce ta fara dukan kunnenta,a hankali ta amsa masa sallamarsa
"Kin tafi kin barni da kewarki,inajin kamar ba awannin da suka shude bane muka rabu,kamar wasu shekaru ne suka raba tsakaninmu....." Yayi maganar cikin salon iya jan hankalin diya mace,da kuma zallar qwarewa wajen sace zuciyar diya mace
"Don Alla kice wani abu kafin zuciyata ta fashe imani......zuciyata ta kamu da mahaukacin sonki,wanda har ta fara hasashen yadda rayuwa zata kasance mata babu ke". Wata ajiyar zuciya cw ta subuce mata saboda nauyi da kalamansa suka fara yiwa zuciyarta
"Me zance maka to?" Ta samu kanta da furtawa
"Koda bakice komai ba ki saki jiki ki bani dama,don koda baki fada ba na samu labarin nine mutum na farko da zan fara bude zuciyarki,so inason ayimin alfarma a kuma bani dama,nayi dashe me kyau,wanda zai bada kyakkyawar yabanya......don Allah beauty" ya qarashe maganar cikin marairaicewa.
Murmushi mara sauti ya subucewa fuskarta,ashe itama watace,ashe takai a gaya mata kalamai har haka anema soyayyarta,itama ashe takai,kalaman baqine ga kunnenta,saboda haka nan da nan ta sake ta bashi kunnuwanta,yayi amfani da wannan damar ya dinga mata hira me matuqar dadi,yana kodata gami da yabata takowanne fanni,tare da kuranta matsayin data samu cikin 'yan daqiqu,da kuma yadda zuciyarsa ta mato mata.
Kiran sunanta da taji inna nayi daga tsakar gida ya dawo da ita daga nisan kiwon da tayi,cikin hanzari ta katse wayar,ta kuma kasheta gaba daya ta tura qasan filo,cikin yanayi rashin gaskiya ta kwasa ta yiwo waje da sauri ta tsaya kan inna
"Gani inna" kallo ta bita dashi a nutse kafin daga bisani tace
"Me kika shiga daki tun dazu kika zauna kinayi ko abincinki baki dauka ba?"
"Sallah nake inna?"
"Qara'insu kikeyi?" Da sauri ta girgiza kai
"A'ah inna,isha'i ce kawai,gajiya tasa dana gama nadan kwanta,kinsan munsha zaman lalle"
"Yayanki ya shigo,bakiji shigowarsa ba?" Tayi mamaki,don har ga Allah bataji shigowar tasa ba da gaske,karo na farko da irin hakan ta faru,don babu wani abu dake shagaltar da ita ta kasa jin shigowar al'ameen din
"Banji ba inna,gyangyadi ya saceni" ta fada tana istigfarin qaryar data sharara
"Dauki abincinsu kikai musu,daga nan ki cewa sadiqu yazo ina kiransa"
"To inna" ta fada tana daukar babban farantin kayan abincinsu tayi dakin.
Kamar ko yaushe sai data tsaya tayi sallama aka bata izini sannan ta cusa kai,dashi idanunta suka fara karo,hannunsa riqe da wayarsa yana kallon wasu styles na dogayen riguna daya dora a account dinsa na Instagram,wanda bai jima da budeshi ba bisa shawarar sadiqu.
Sexy eyes dinsa da suka sake lumshewa saboda gajiya da yunwa ya buda a hankali ya sauke a kanta,ta qaraso a nutse ta ajjiye farantin
"Sannu da zuwa yaya"
"Yauwa queen.....ya gida?"
"Lafiya lau yaya,ya aiki"
"Alhmdlh,zubamin abincin" ya fada yana zamowa daga saman kujerar zuwa qasa,hankalinsa akan lallenta baqi da ja wanda yayi masifar zanuwa saman farar fatarta me haske sosai
"qunshin yayi kyau sosai queen" ya samu kansa da fadi sanda take qoqarin zuba masa abincin,saita daga kai suka hada idanu,cikin jin nauyinsa tace
"Na gode yaya"
"Amma garin yaya kikayi dare haka?" Dan raurau tayi da fuskarta
"Allah yaya munira na raka wajen event din cousin dinta,kuma ta yiwa inna bayani"
"Ki kiyaye please,kinga ke Queen ce,bai kamata sarauniya guda a dinga ganinta a araha a waje ba har dare" murmushi ya sake subuce mata,ta gyada kai tana murza yatsun hannunta,daidai sannan sadiqu ya fito daga bandaki
"Zubamin nima ina zuwa,abu me sanyi yau nake sha'awar sha" ya fadi yana nufar qofa
"Inna tana kiranka ma"
"Tom" ya qarashe amsa matan yana ficewa.
Yana cin abincin yana satar kallonta,sake kyau da zama cikakkiyar budurwa take,hatta da fuskarta ta nuna hakan balle gangar jikinta,kamar ma so take ta haura shekarunta,tana dagowa suka hada ido,sa ya mata nuni da wata leda
"Ga mayafinki can" cikin murna ta tashi ta dauko tana dubawa
"An gode yaya,Allah ya qada budi,amma yaya kala biyu ne fa"
"Wannan zai hau kowanne kaya cikin ankon,kiyi amfani dashi,daga baya saina sama miki dayan" kai ta gyada kawai,amma bataso hakan ba,saboda anyi duka qawayensu kala daya zasu saka.
Tana maidashi cikin ledar sadiqu ya shigo da lemukan a hannunsa,ya miqa mata wasu
"Ki dauki daya ki kaiwa inna sauran" ta karba tayi godiya sannan ta fice.
A wajen inna abincinta ta karba tace zataci a daki,hankalinta da tunaninta duka ya koma kan wayarta,koda ta shiga dakin,kunna wayar shine abu na farko data fara yi,tana gama kunnuwa saqonni suka fara rigen rigen shigowa a jere kusan guda biyar,saita koma ta zauna,murmushi na subuce mata tana qoqarin budawa ta karanta.
[04/06, 4:54 pm] +234 903 165 5683: 15
_YERWA INCENSE AND MORE: MASARAUTAR KAMSHI:_
_THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME_
_DO YOU WANT THAT MAIDUGURI AND SUDANIAN SCENTS THAT LASTS LONGER AND LINGERS? YERWA INCENSE AND MORE GOT YOU AND YOUR BELOVED ONES COVERED WITH LUXURIOUS SCENTS. KAMSHIN YAN YERWA DA SUDAN💘🙏 20% OFF ORDERS. MUN CIRE KASO 20 NA KUDIN KAYAYYAKIN MU_
_KHUMRAHS_
_KULACCAMS_
_TURARUKAN WUTA_
_NA TSUGUNNO_
_NA KAYA_
_NA GIDAH_
_NA GASHI_
_NA WANKA_
_NA WANKI_
_NA MOPPING_
_AIR FRESHENER_
_CURTAIN AND CHAIRS SPRAY_
_WARDROBE BALLS_
_SCENTED PEBBLES_
_ARABIAN OIL PERFUMES_
_HAIR SPRAY AND CREAM_
_DILKE AND HALWA SET_
_KABBASA_
_BURNERS_
_KASKO_
_TONGS_
_COAL IGNITERS_
_SKIN CARE PRODUCTs_
_OUR TURARE SAMPLE SETS_
_BRIDAL SET (SAITIN AMARE)_
_KUJERAR TSUGUNNO_
_SABULAI NA GYARAN JIKI DA SAURAN KAYAYYAKIN GIDAH NA KAMSHI . KOMAI DA KOMAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA_
_MUNA TURA KAYAYYAKIN MU A KO’iINA A FADIN NIJERIYA DA KETARE_
_SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDAH, 100% TESTED AND TRUSTED_
_instagram:yerwaincense_and_more_*
_WhatsApp: 08095215215_
_________________________________
Dukkan saqonnin nasa suna tafe da kalaman dake nuna rudun da ya shiga kan katsewar wayar da kuma jinta a kashe da yayi bayan ya sake kira,magiya yake mata kan ta taimakeshi ta buda wayar tata,ta daure tayi kiransa,murmushi ta kuma saki,yanzu kashe wayarta kawai ya sanyashi a damuwa?,wanne irin so ne wannan?,har ta dannan kiransa ta fasa ta katse,ta ajjiye wayar ta jawo abincinta tahau ci,saidai tana ci gefe guda kuma zuciya da qwaqwalwarta suna dawo mata da abubuwan da suka faru wunin yau,tun daga haduwarsu kawo yanzu,duk kyanta da yake fadi gani take ya fita,saita miqe ta isa gaban mudubi tana qarewa fuskarta kallo,kalamansa a kanta na dawowa kanta turyan turya,sai ta kuma sakin murmushi,ta juya ta dauki kwanon abincinta da kayan ciye ciyen bikin da muniran ta hadota dashi don ta kaiwa inna ko zata iya cin wani abun a ciki.
***********Washegari*******. Da saqonsa tayi karin kumallo,wasu irin shiryayyun kalamai dake dauke da dandasa dandasan kalaman zallar soyayya,dolenta murmushi ya subuce mata bayan ta kammala karantawa,yakansa ta shiga mamakin wai ita din me muhimmanci ce har haka?,itama ashe watace data cancanci samun qauna maqura?,tana wannan tunanin saiga kiransa,ta sake yin sauri wajen saka wayar a silent.
Sai data katse ya qara kira sannan ta daga
"Beauty.....girmanki ne,amma kuma so kike na haukace na kasa aiwatar da abinda ya kaini abuja?kinsan kuwa samun hadin kanki shine kawai abinda zai bani nutsuwar aiwatar da abinda naje yi din?" Murmushi ta saki a boye
"Ni wacece da hakan zata faru da kai?"
"Kina mamakine ko kina tantama?,lallai da alama har yanzu bakisan irin matsayin da kike dashi a wajena bane,kinsan tunanin kina da wani masoyin da ranki keso kadai daga jiya zuwa yau ya sanyani nayi zuru zuru,zakiyi mamakin yadda na koma,please beauty......kicemin ni kadai ne wanda ya fara yaqin neman soyayyarki,duk nasan mafarkine kawai nakeyi,amma mace kamarki lodi lodin maza nasan ke gware a kanta" yadda yake maganar cikin laushi da sanyi ya bata dariya,har batasan tace dashi
"Kai kadai ne" ba,wani qaramin ihu ya saki,wanda yake nuna zallar farincikin da zuciyarsa ke ciki
"Yes.....kice na sanar da mommy a daidai" idanu ta zaro
"Me?" Ta tambayeshi cikin mamaki da fargaba
"Eh, already labarinki yaje wajen mommy,tun a jiyan ban iya barci ba sai dana gaya mata komai dana sani game da ke,infact ma ita harta matsu taga beautyna,na gaya mata,ta qara haquri har na shawo kanki tukunna"
"Bassam" ta kira sunanshi a karon farko
"Nifa na yiwa yayana alqawarin bazanyi soyayya da kowa ba, already ma yace shine zai zabarmin miji" wani mummunan faduwa gabansa yayi,take ya rikice mata,har abun yayi matuqar bata mamaki,da gaske yake kan duk abinda ya fada,da gaske ne yadda yake kururuwar sonta
"Please give me a chance beauty,ki bani dama....na miki alqawari indai na kasa sace zuciyarki da samun soyayyarki zan amshi sunan looser,zan kuma rabu daki,amma na tabbata yayanki baya nufin abinda ya fada" sai data ce ta bashi damar sannan taji salama da sukuni cikin muryarsa.
Da hanzari tayi masa sallama tana katse wayar,ganin ya kusa cinye mata lokacin aikinta,ta cusa wayar qasan pillow,sannan ta janyo dankwalinta ta daure sassalkan gashinta ta futo tsakar gida,qirjinta cike fal da bitar kalamai da al'amuran da suke gudana tsakaninta da bassam,tun daga haduwarsu kawo yau.
Tana tsaye a kitchen tana dama kunu,tayi nisa cikin tunaninta,a hankali ya qaraso bakin qofar kitchen din,idanunsa suka sauka a kanta
"Assalamu alaikum" yayi sallama cikin tattausar muryarsa dake cike da wata irin nutsuwa ta halitta,ta waiwayo a hankali suka hada ido,sai ta saki murmushi tana dan motsawa kadan
"Wa'alaikumussalam,ina kwana ya amin"
"Lafiya qalau queen,ki tashi lpy?"
"Lpy qalau....."
"Ma sha Allah,na godewa Allah da queen ta tashi lpy" murmushi ta sake,sai taji kalamansa na mata kama dana bassam
"Zan samu ruwan dumi?" Tunda taji haka tasan daga motsa jiki ya dawo,shi yasa suk safiya bata rabo da ruwan dumin saboda shi,matuqar tana kitchen din,tasan yana shigowa zai nema
"Eh yaya" ta fada da sauri,tana juyawa zuwa inda ta ajjiye flask din ruwan zafi,ta fara zuba masa,idanunsa na biye da ita.
Daidai yadda tasan zai iya sha ta zuba ta miqa masa,hannu biyu yasa ya karba
"Na gode" murmushin da ya sake fidda dimple dinta tayi,tana jin kunya ta masa abu ya gode mata.
Ta zaci fita zaiyi a kitchen din,amma sai taga yaci gaba jingina da qofar,yana kurban ruwan yana binta da kallo,yana monitoring duk wani motsinta,wutar qaunarta tana sake ruruwa cikin ransa,yana jin cewa lokaci kadan ya rage komai yazo qarshe,banda ma delay da ya samu naci gaban karatunsa yadda yaso,da tuni zuwa yanzu komai yayi nisa,saboda ya riga ya tsara ci gaba da karatun iman din a gidansa,hankalinsa sai yafi nutsuwa da hakan
"Akwai wani abune yaya?" Ta tambayeshi cikin jin kunya da kuma nauyinsa,miskilin murmushinsan nan mai cike da nutsuwa da wata izza izza ya sake,ya tashi daga jinginar da yayi ya tako zuwa kitchen din,ya dora mata cup din kusa da ita
"Babu komai.....kawai ina kallom queen dita yadda take qara girma kullum tana zama 'yar budurwa"
"Kai yaaya" ta fada da sauri tana sunne fuska,shi kuma ya saki 'yar qaramar dariya mai sauti kadan,ya taka ya fita a kitchen din.
Wunin ranar gaba daya bassam bai barta ta huta ba,kowanne motsi nashi sai ya gaya mata ga abinda yakeyi,duk wani schedules nasa daga safiya zuwa dare tsaf sai data sani,tamkar tare suke aiwatar da komai.
Ko wajen kamun surayya haka tayita fama da saqonninsa,yayin da munira ta hanata sakat da zancansa,batasan ya akayi ba sai ji tayi qawayenta sun fara tsokanarta da MRS BASSAM,kowacce a cikinsu cewa take
"Gaskiya ba qaramar sa'a kika taka ba,yaro ne matashin saurayi da jini ke zagayawa a jikinsa,yaro ne da kudi amma hausawa sukance abokin tafiyar manya, friend dina ne a insta,kije kiga yadda 'yammata ke rushing a kansa,daya daga cikin qawayensu ta fiddo wayarta,ta shiga account dinsa na Instagram ta buda mata hotunansa ta miqa mata.
Ta jima riqe da wayar a hannunta tana bin duk wani abu nashi daya dora a can,ta yadda da duk abinda suka fada din,daga kan hotunansa dake kan shafin nasa zakasan ba qananun kudi yake riqewa ba,kowannw hoto sutturu na alfarma ne a jikinsa,rabu da matan social media da kyakkyawan namiji,tarin followers ne dashi jingim maza da mata,abun ba'a cewa komai,kowanne hoto nasa ko wata magana da zaiyi,zaka tadda tarin comments da likes rututu a qasanta,ta sake gyara zama tana bin wallafar tasa.
Ba qarya bane,komai yaji tattare da bassam din,ta sauke ajiyar zuciya tana sakin murmushi sanda wata 'yar ajinsu da ba wani magana suke da ita can can ba ta shigo tana tsokanarta itama da mrs bassam
"Ya hadu guy din,bazan boye miki ba,nayi iya qoqarin na sameshi,to amma nasan ni ba type dinsa bace,shi din sai kyawawa dama irinku,ina tayaki murna gaskiya iman" murmushi kawai iman din ta bita dashi tana sake maida idanunta kan fuskar bassam.
Kwana biyu sukayi suna casar biki,tana zaune qawayenta nata liqi wa amarya,saboda tasan ita din bata da kudin da zatayi liqin,sai daga bisani ta bude jakarta dauko wayarta don duba lokaci,batason ta sake dare kamar na rannan idanunta suka sauka kan kudin da bassam din ya bata,bata taba komai ba a ciki banda kudin transport datayi musu ita da qawayenta,saita zari masu yawa a ciki,itama ta isa saman stage t fara liqawa ango da amarya,take taji kanta daidai da sauran qawayenta dake wajen,suka dauki ihun sai mrs bassam,abinka da zuciya da kuma aikin dan adamtaka,sai taji kata yana fasuwa a hankali,sannu sannu sai datayi liqi me yawa da ya sanya mc kama sunanta sannan ta sauka ta kona gurin zamanta,cin maganinta ya sanya samari da yawa dakeson kawo mata caffa suka kasa qarasowa inda take.
********Washegari**********
Wunin sakina,ranar ne kuma za'a kaita,saidai dukkaninsu basuje ba sai yammaci,dukka qawayen suka hadu,cikin daya daga cikin lafayoyinta da bata taba sanyawa ba ta shirya kanta,duk tafisu tsada shi yasa ta zabi ta sanyata,milk color ce me haske,sai adon gold a jiki,takalmin qafarta me tsini ne kuma mai tsinin dunduniya,ta ciki wani lace ta sanya mara nauyi,wanda ya amin yayi mata dinkin straight skeet da riga me dogon hanu,ta tara gashinta tayi masa nadin alkaki ta qasan daurinta samfurin ture kaga tsiya.
Fadin kyan da tayi a lokacin bata bakine,saika rantse da Allah daga gidan wasu hamshaqan ta fito,saboda kulawa da take samu gami da sutura me kyau,kowa kaffa kaffa da dama dama da ita yake cikin