Showing 39001 words to 42000 words out of 45207 words

Chapter 14 - Kufan Wuta Book 1 Hausa Novel Complete

ce take sanyata hakan bai kamata ya barta da ita ba,don ko a jiya da daddare yana jin bambamin sadiqu kamar zai bugeta kan yace fa.kiqo masa abinci ta shantake,dama kuma can sadiqun zafi gareshi,bai cika haquri ba,don haka sai ya qarasa rumfar inna da kansa.

Sallamarsa da shigowarsa gaba daya yayita,tana zaune a qas tana saka farar safarta,ta daga kai tana murmushi gami da amsa sallamar tasa,gabanta yadan fadi da fari,saboda ganin da tayi ya danyi mata zubi da bassam saboda adon da yayi

"Ina kwana yaya?" Maimakon ya amsa mata sai ya maida mata da tambaya yana dan tsuke fuska

"Me kike har yanzu baki tafi makaranta ba?"

"Yaya makara nayi wajwn tashi"
"Kin fara wasa da karatunki ko?" Saita girgiza kai

"Aah yaya,bacci ne......"
"Is ok,idan na dawo zan karbi wayata,ki sakamin a charge idan sun kawo wuta tayi full" a sanyaye ta gyada kanta,sam batason ya karba wayar,saidai......wayarce ta shiga ranta ko kuma alaqarta da bassam ce bataso ta yanke?.

Tare suka fita shi da ita,sai daya sanyata a abun hawa ta tafi sannan ya tari nasa yahau,kasancewar ba hanya daya zasuyi ba.

Tun a makaranta ta turawa bassam saqon maida wayar,ta kuma goge duk wani account da wani abu daya shafeshi,kama daga hotunansa daga tuttura mata,da kuma saqonnin sms,sai data tabbatar bata bar komai akai ba sannan ta maida wayar tata jaka,saidai rabi da rabi na karatun ranar ba shigarta yake ba,tana can ga tunanin yadda zasuyi kewar juna ita da bassam din,ta saba chart dashi,kuma yafi.mata dadi akan kiran ways,a chart dinne take sakewa sosai ta gaya masa sirrikan zuciyarta.


*********Goma da rabi na daren ranar,wanda tayi dai dai da kwanaki biyu da amsar wayar daga hannun iman din,har ya gama shirin kwanciya saboda sammakon da yakeson yi gobe zuwa shagon dinki don kammala dikunan wasu amare,sai kuma ya miqe ya jawo locker dinsa sake jikin katifarsa,ya dauko wayar ya sanyata a charge,saboda tunaqa da yayi zai turawa wani mutum photon wasu takardu nasa.

Gefan katifar ya koma ya zauna yana jiran charge din yadan hau,saboda bashi da tabbacin akwai charge akai,ya bata mintina goma sannan ya koma gaban socket din ya zauna yakunna wayar,bayan ta daidaita ya shiga gallery dinsa ya fada laluben hotunan takardun,tunda already yana dasu,saidai sama ko qasa ya rasasu,ya dinga kaikawo bai gansu ba,har zai haqura ya sake sabbin dauka,duk da yasan ba zasuyi kyan wadancan ba,saboda wadancan din anyi scanning dinsu a computer,sai kuma ya tuna,ya wuce zuwa recycle bin na wayar.


Tun daga farko ya fara cin karo da hotunan da baisansu ba,bai kuma waye mai su ba,sa'an nan baisan mutumin dake jikin hoton ba rututu masu yawan gaske.

Sosai kansa ya daure,ya dinga bin hotunan da kallo daya bayan daya,mamaki na sake cikashi ta yadda hotunan suka shiga cikun wayarsa.

Sannu a hankali ya gangaro kan hotunan iman,iman dinsu dai,cikin salo na gaye da kwalliya,hotunan da sukayi masifar kyau suka kuma fidda duk wani kyau da Allah ya bata,duk da cewa shigarta bata bayyanar da tsiraicinta ba,amma kyan da tayi cikun hoton,kyau ne da bai taba ganin tayi irinsa ba a zahiri.

Gaba daya qwaqwalwarsa so tayi ta tsaya da aikin yin kowanne tunani bare ta bashi hint na abinda ke faruwa,saboda yadda ta dode gaba daya kamar bata taba wani tunani ba,sai ya koma ya zauna dirshan sanda kwanyarsa ta taimakeshi ta tuna masa cewa iman itace mutum ta qarshe da wayarsa ta jima a hannunta.

Wani mummunan faduwa gaban al'ameen yayi,har yaji kamar an samu wani abu an buga masa akai,gudun zuciyarsa ya dadu sosai,sai ya sauka da sauri,ya koma binciken wayar,bakinsa cike da addu'o'i cikin rudewa.

Duk inda ya shiga babu komai an share,manhajar WhatsApp itace abu na qarshe daya duba,ba tare da yana da wani yaqini na samun wani abu ko hujja ba.

Ga mamakinsa yana shiga WhatsApp din ya bude sarai,da alamun account din da akayi amfani dashi shine har yanzu kan wayar ba'a shareshi ba.

Suna da hoton dake kan number farko kuma qwaya daya dake kan account din gaba daya ya sanyashu furta

"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" dukkan wata dakiya da jarumta tasa ta fara zagwanyewa lokacin da ya fara bin chart history din,yana karanta hirarrakin da akayi cikin inbox din,wani irin gudu zuciyarsa taci gaba dayi kamar zata faso qirjinsa ta fado waje,kunnuwansa sukayi dummm wanda ya dauka har tsakiyar kansa,a hankali cikin wani salon sanda feeling na daina gane abinda ke kewaye dashi ya fara kutsawa cikin jikinsa,yana aikawa kowanne sashe na jikinsa,a hankali ya daina gane komai da kowa sai zallar tashin hankalin daya tsinci kansa a ciki,tashin hankalin da yayi masa ba zata,tamkar zuwan ajali ga dan adam.


A hankali sai wayar ta gagara riquwa a hannunsa,ya zameta a hankali ya saketa gefansa,ya koma ya zauna sosai yana son fahimtar da kansa abinda ke faruwa,kamar bashi da idanunsa ya gani ba,saidai kuma wani sashe na kwanyarsa na gaya masa,ba iman dinsa ba,ba iman dinsa bace,hala ta bada aron wayar itama ga wani,idan ma ita dince ko dai wasa take?.

A sannan ji yayi babu abinda yake da buqata banda yaga iman a gabansa ya tambayeta abinda ke faruwa,yana da burin idan ta tashi amsa masa ta amsa da cewa wasa take,ba da gaske take ba. Ba tare da la'akari ko kuma duba da cewa dare ya fara yi ba ya miqe da hanzar ya nufi qofar fita,yana so ya sadu da ainihin cikin gidan.

Garam sukayi karo da sadiq dake shirin shigowa da ledar balangun da ya tafi siyo musu,saboda dukkanins mutane ne masu son cin dadi a bakunansu,hakan bai basu matsala ba,saboda kowannensu neman kudi yake tuquru

"Haba mana master......saurin me kake?,gani na dawo,wajen ne akwai layi,kasan ya iya gashi" ja baya yayi yana duban sadiqun da yake mulmula goshinsa,wanda shi sam bai ma damu da nasa goshin da ya buge ba,saboda rudanin da yake ciki,gaba daya ma ya manta wai sadiq din ya tafi siyo musu nama.

Idanu sosai sadiqu ya zuba masa yana masa wani baqon kallo

"Amin.....lafiya kuwa?,wani abu ya faru ne bayan na fita?" Qafafunsa dake a mace kamar lawashin da yasha rana ya fara janyewa da baya da baya,bayan hankalinsa a sannan yakai kan agogo,ya kuma tabbatar bazai iya shiga cikin gidan a yanzu ba,sabosa bai taba shiga din ba idan ba wani abu bane ya taso

"Babu komai" ya amsa ma sadiqu yana zubewa gefan katifarsa,tare da yin hobbasa na ganin ya saisaita mood na fuskarshi

"Koda naji" sadiqun ya fada yana cire takalmansa ya dorasu saman abinda suke dora takalma dake bakin qofar dakin sannan ya shigo,ya bude musu naman yana bawa amin din labarai kamar yadda suka saba duk dare kafin su kwanta.

Idan yace yana gane abu daya da sadiqun ke fada to tabbas ya zabga qarya

"Ya baka cine?,wai anya lafiya kake kuwa?" Kalmar da sadiqun yace dashi kenan yana rutsashi da ido,abinda yayi silar daya ringa miqa hannu ya a zaqular naman yana hadiyewa ba tare da ya tsaya cikakkiyar taunawa ba bare ya gane wanne irin taste gareshi,haka ya dinga tsaya masa a maqoshi kamar wanda ke cusa dan wake,abinda yayi sanadiyyar qwarewarsa kenan yahau tari,wanda ya sarqafeshi sosai,sai da yasha ruwan sanyin da sadiqu ya bashi sannan ya lafa,da wannan ya fake yaje ya kwanta,saboda qirjinsa da ya dauki zafi,sadiq yace may be ko ulcer dinsa ce ta motsa kuma.

Tunda ya kwanta idanuwansa a rufe suke gam,ko qwaqwaran motsi baya qaunar yaji a kusa dashi bare magana ko surutu,lokaci bayan lokaci yana bude idanunsa ya sauke ga agogo,yana qididdigar mintunan da suke gabansu kafin wayewar gari.

Zuciya da tunaninsa sunkai sun komo,ya kuma rasa a wanne bigire zai ajjiye tunani da zuciyarsa,karafkiya qaryata juna da sa'insa babu kalar wadda ba'a samu ba tsakanin sashe biyu na zuciyar dake qirjinsa,wata zuciyar na rinjayar da qaryar cewa ba iman bace,haka ba zata faru ba,yayin da wara zuciyar ke tabbatar masa da iman dince,saidai ta aikata komai ne bisa rashin sani,koma meye ya riga ya yankewa kansa hukunci kawo qarshen komai,koma meye zai faru ya faru,qirjinsa bashi da qarfin daukar zuciyar da zata rasa iman haka cikin sauqi,saima ya korewa kansa wannan tunanin da yake kallonsa a baqi kuma mummunar fata cikin rayuwarsa.


Dai dai lokacin da iman din take can kwance saman tata katifar a zahiri,a badini kuma tayi matuqar yin nutso kuma me zurfi cikin kogin qaunar bassam,wanda ta ara masa daqiqa masu dama yana sake karanta mata yadda qaunarta ta tashi zuciyarsa a aiki,irin girma da kuma matsayin da take dashi,abinda ya sake sawa taji kanta ya fasu,alfahari da samun bassam da kuma soyayyarsa ta shigeta,ta bude masa tata soyayar sosai wadda ta narkar da ilahirin zuciyar bassam,ya kuma dauka mata alqawura masu matuqar nauyi a mizani,girma kima da kuma martaba cikin duniyar soyayya,wanda daga qarshe sukayi tarayya kan alqawari guda,duk rintsi.....duk wuya.....suna tare,babu gudu kuma babu ja da baya,dukkan wanda ya sauka daga kai ko kuma ya sauya,la'ana da kuma hukuncin cin amana yahau kansa.

Wannan kusan itace hira mafi dadi da sukayi da bassam a wajenta tsahon tarayyarsu,domin kuwa ko bayan ya sauke wayar sun rabu kasa runtsawa tayi,murmushin dake kan fuskarta cikun duhun dakin yaqi barin fuskarta,hirarraki muryarsa da gwala gwalan kalamansa sukaqi barin qirji da zuciyarta,ta dinga tariyarsu tana jin wani dadi qauna da shauqi yana sake kamata,zuciyarta jaririyar zuciya ce,wadda ta fara soyayya ta zahiri a karon farko,don haka komai baqo ya kasance mata,sai daga bisani fa samu baccin yayi awon gaba da ita,cike da mafarkan bassam,wanda a ciki har ya zama miji a gareta.


Kwata kwata baccin da yayi tsahon daren dukansa bai wuce na awanni uku ba,suma din a tsitstsinke,a kunnuwansa akayi kiran asubahi,yayi alwala suka fice masallaci tare da sadiqu,wanda hakan al'adarsu ce,kuma acan suke tadda malam.

Miqewa sadiqu yayi ya dubeshi bayan an idar da sallar,wasuma har syn fara watsewa

"Nikam yauma idan zaman azkar dinkan nan zakayi saidai mu hadu a gida,don wallahi jiya kwata kwata bacci bai isheni ba" ya fada yana miqa

"Shikenan,saina taho" ya amsa masa yana sake maida kansa qasa,don bayason sadiq din ya fahimci bai samu bacci ba.

Yana kallon sadiq ta qasan idanunsa har ya fice,hakanan yaji bazai iya komawa cikin gidan ba,ya kintata wani lokaci ne da zai cimma iman,duk da cewa yau tana da makaranta alhamis ce.

Cikin wani nishadi da walwala take zuba kunu da awarar data soya cikin cup da plate don taci ya wuce makaranta,ta gama shirinta tsaf,kana duban fuakarta zakasan wani nishadi takeji,bassam ya raya darenta ya kuma qawata mata safiyarta da kyakkyawan saqon barka da safiya.

Ta juyo zata fito kenan yayi sallama bakin qofar kitchen din,idanunsu suka shiga cikin na juna,sai ta hangi baqon yanayi tattare dashi,saidai bata kawo komai ba cikin ranta ta zarce da gaisheshi,ya amsa mata yana nazarinta

"Akwai ruwan dumi?" Ya tambayeta yana jingina da qofar kitchen kamar yadda ya saba,tsaiwarsa kwnan duk sanda zai karba ruwan,duk da yawanci a gajiye yake shigowa dama saboda exercise da yakeyi,sabanin yau,da babu execise din da ya iya fita,saidai zuciyarsa a jigace take qwarai,wanda hakan yayi tasiri har zuwa gangar jikinsa,ya matsu ya kuma damu ya fidda abinda yake zuciyarsa da ransa komai da komai ma ya huta

"Yaaya...gashi" ya tsinci muryarta tana masa magana,da alama tun daxu ta zuba ta miqa masa,sai ya karba ya fara kurba a hankali,bayan ya matsa mata hanya

"Idan kin gama ki dauko litattafanki ina jiranki" har tadan dakata sai kuma ta amsa da to tayi gaba,kasancewar ta saba lokaci lokaci yakan rakata,koda ba har makaranta ba to xai kaita bakin titi,saidai a kwanakin nan abun yaja baya.


*_LITATTAFAN ZAFAFA BIYAR_*

_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_
_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_

_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE  MU TA: _

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*👇👇

09166221261

YAN NIJAR 👇

+227 95 16 61 77

Ga 'yan nijer zasu tura katin moov ko Airtel zuwa wannan number
______________________

ZAFAFA BIYAR

VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)

VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.

TWO PAGES DAILY
INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.


*_TEAM ZAFAFABIYAR_*18

Jerawa yayi da ita kafada da kafada sanda suke takawa a hankali,idanunsa qur saman hanya,zuciyarsa na taraddadi da fargabar abubuwan da zayaji.

Satar kallonsa ta sakeyi a karo na barkatai,ganin sun nufi hanyar makarantar tasu kai tsaye ba tare da ya tsaidan mata da abun hawa ba

"Yaya,a qafa zumuje?,ka manta?,kawai dan nisa fa?,naga munbi ta layin nan" lokaci ya kalla a hankali kafin ya sauke hannunsa ya kuma sake rage speed na tafiyar,ya zaro wayar dake aljihun hagunsa ya miqawa iman idanunsa cikin nata

"Karbi ki dubamin" cikin rashin fahimta ta miqa hannu ta karba wayar,ta kuma bude kamar yadda ya umarceta.

Abinda ta gani din shi ya birkita kwanyarta cikin sakanni,duk da tasan da wanzuwarsa,amma bata tsammaci yaci gaba da wanzuwa cikin wayar ba,take rudewa suka bayyanar mata,saidai tayi qoqarin bawa kanta dakiya da qwarin gwiwa,tunda babu wani na sabo ko rashin tarbiyya kaf cikin charts dinsu,bugu da qari ma tana jin lokaci yayi da zata bayyanawa duniya bassam dinta

"Waye wannan?" Amin ya fada yana kallon wayar kafin ya maida dubansa ga fuskar iman. Har cikin ranta taji tambayar kamar tazo mata a dai dai,don saboda dama ya amin dinne kawai take tunanin zatayi maganar dashi,ya kuma fuskanceta har ya kai zancan gaban malam,to saidai shima duk sanda ta yunqura zata yi masa maganar sai taji ya mata wani mugun kwarjini,amma yanzun komai zaizo da sauqi.

Sunne kai tayi irin na alamun jin kunya

"Saurayina ne ya amin"ta fada tana rufe fuskarta da tafin hannu.

Hasbunallahu wa ni'imal wakil,ita yayi qoqarin zuqowa saga mafitar maganarsa zuwa saman harshensa,sannan yayi azamar dafe wata bishiya da tafiyarsu ta ratso dasu ta gefanta don neman agajin tsaiwa sa qafafunsa.

Kasancewar sautin addu'ar tashi bai samu fitowa ba illa maqalewa da yayi saman harshensa.......wannan ya sanya sam batasan me yake faruwa ba,cikin wani irin tashin hankali yaci gaba da kallon iman duk da fuskarta a rufe take da hannunta

"Iman......ina alqawarin da kika yimin ba zakiyi soyayya da kowa ba?,ina alqawarin da kika yimin na bani damar zabar miki miji na gari?" Yanayinta ya sauya kadan cikin boyayyar fuskarts,duk da bata kalli tasa fuskar ba amma ta fuskanci sauyun sauti sosai fiye dana dazu

"Yaaya.....kayi haquri,na saba maka wannan alqawarin,amma shima ina da tabbacin irin mijin da kakeson zabarmin dinne,kuma zaka yaba da zabina yaya,ya shiga rayuwarta ne katsam" qara dafe bishiyar yayi da kyau saboda jin jiri na dibansa da yayi,babu sauran kwana kwana ko boye boye

"Iman......nine mijin da na yi miki tanadi,ni ya amin dinki nine mijin dana zaba na kuma killace kaina saboda ke,iman.....ni amin nike sonki iman,zuciyata ta girma da sonki ta kuma rayu da sonki tsahon shekaru masu yawa". Kamar wadda aka jibgawa wani abu a saman kanta haka taji,ta yaye fuskarta da sauri da kuma hanzari don tana da buqatar tabbatarwa kanta ba shirin film akeyi a wajen ba,tana son ta gani da gaske ya amin ne?,kuma ba wasa yake mata ba?.

Saidai kuma.....kallon farko ta karanci zallar gaskiyar dake fitowa tun daga zuciyarsas shimfide saman fuskarsa muraran,abinda ya sake firgitata,ta danyi baya kadan tana jin tashin hankali yana rufto mata,ta yaya haka zata faru?,ta yaya zaice wai da sonta ya rayu?,me yasa bai gaya mata tun da can ba sai a yanzu data riga tayi alqawari da wani,data riga tayi nisan kiwo cikin duniyar soyayyar wani?,ta yaya zata gane yaren da yakeson koya mata bayan bashi ta iya ba?,meye yake shirin faruwa?.

"Ya ameen,da gaske kake?,nice fa iman dinka?"kai ya gyada mata yana kallon tsakiyar idanunta kai tsaye

"Na sani,iman dita ce,shi yasa nake gaya mata halin da zuciyata take ciki,ina sonki iman......burina kuma na aureki,in fact,malam ya jima da bani ke!" Maganarsa ta qarshe saura kadannta wargaza kwanyarta

"Me?!" Ta furta da wani sauti me kauri da amo

"Eh,malam ya bani ke tuntuni" ya fada yana gyada mata kai tare da tabbatar mata.

Kanta ta soma girgizawa,sam sam kwanyarta ba zata dauki wannan batun ba,wacce iriyar magana ce haka mara dadin saurare?,ta yaya zaizo mata da wannan maganar?,tsahon zamansu da rayuwar da sukayi a muhalli guda bai taba tunkararta da maganar ba sai yanzu?sai daidai wannan lokacin?.

Ci gaba tayi da gigixa kanta tana koma da baya,kafin ta juya cikin wani irin hanzari ta nufi hanyar gida,ya miqe da sauri yabi bayanta yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login