Showing 9001 words to 12000 words out of 45207 words

Chapter 4 - Kufan Wuta Book 1 Hausa Novel Complete

nashi ne,saboda shi fanken bai dameshi ba,qosai ne koda ya huce zai cishi a haka yana jin dadinsa,koshi ko alala,sau tari sadiq na tsokanarsa da cewa

"Wai lallai saika nuna kai cikakken bafullaci ne,qauna ce shadidiya tsakaninku dama da qosai" wani lokaci yayi dariya ya barshi,wani lokaci kuma ya rama.

       "Yauwa,daga kan plocker dinka akwai saqo gashinan an bani,ka duba" sadiq ya fada yana qoqarin kai cup din kunun bakinsa,ajjiye towel din da yake goge kansa dashi yayi ya qarasa gaban locker din,wadda take dauke da tarkacen kayan shafa na maza,kai kace wani zabgegen saurayi ne,tarin turaruka ne kala daban daban,kama daga roll-on, sure,body spray,body mist masu sanyi,da turaruka na kaya  shaving cream,da body cream masu sauqin kudi,man wanki baki da mayukan gashi na maza,sai kuma man saka takalmi yin qyalli.

         Hannu yakai ya dauki farar takardar da aka nannadeta four corners,ya ware a hankali,sannan ya zuba mata sleepy eyes dinsa da suke a lumshe,yana bin yadda aka zane takardar da zanen furanni da kuma tsuntsaye,sannan ya sauka ga saqonnin soyayyar dake rubuce a tsakiyar wani lafcecen heart (zaku iya tunawa da wasiqar soyayya da ake rubutawa zamanin quruciya?,ya kai zunzurutun zinaren mazirarin zuciyata?😂).

        Maida wasiqar yayi sama a qasa yana lalubo sunan marubuciyar,sunan ubaida ya bayyana,saiya linke takardar,sannan ya waiwaya ya dubi sadiqu

"Yaushe ka mayar dani dan iska ka fara karbo wadan nan abubuwa kana kawomin?,bari to na ajjiye na kaiwa malam,kada wataran ya kamaka ya zaci bakinmu daya,ko kuma ni nake aikenka" da hanzari sadiq ya tashi yana danne dariyarsa yasha gaban lamin dake zura jallabiyarsa ta barci

"Kaga.....ni kada ka yimin sharri,ni ina ruwana?,ina zaune ta aiko qanwarta ta kawomin,kaga kenan bani na janyota ba ko bare kace" tsayawa yayi yana duban sadiq din,ya sanshi qwarai da rawar kai,saboda yawancin lokuta idan yaga ana tashi daga aiki lamin din ya biyo masa ya sakashi a gaba sunyo gida,suna isowa anyi magariba sunyi masallaci,saga can sun zauna karatu da malam,ana tashi hira cikin abokansu lamin din baya bari su zarce awa daya zai takura sadiq din kan su shiga gida,ko su zauna a dakinsu suyi wata hirar,ko suyi karatu,ko su kalli ball idan nepa sun agajesu da wuta,ko kuma su zauna tare da inna kafin malam ya shigo,yakan yi qorafin

"Waikai.....sai kace wasu mata da Allah,kai ko dan 'yammatan nan da akeyi na layi bamu da,kana gani su buhari fa,yarinyar nan ta bayan layinmu har dan wasiqa suke aikawa junansu" kallonsa kawai lamin yakanyi

"Shekararmu nawa ne?"
"Sha bakwai mana,ni harda watanni ma"

"Tabdijan,a shekara sha bakwan har mukai wannan matakin?,meka ajjiye?,me kake dashi?,wanne mataki ka taka a karatu?"

"Mtseeww,ka gane mana,bafa wai aure zamuyi bafa,kawai irin dai soyayyar nan da kowa ke tabawa ce,ai abun kunya ne a yadda mukafi dukka samarin unguwar nan kyau amma ace mune bamu da budurwa"

"Nidai a wajena ba abun kunya bane,amma tunda kai a wajenka haka yake,kaje Allah ya bada sa'a" daga haka ya maida hankalinsa ga qaramar tvn dake gabansa,wanda suke hasko wasan da ake bugawa ta gasar nahiyar turai,tsakanin Manchester da Barcelona.

       Yana jin sadiqun yana mitar yanzu kallon qwallon ma sudanje gidan kallo suyi cikin mutane amma abu ya gagara,kowa yana can ma su suna cikin gida kamar mayu.

        Shi sam irin wadan na shirmen na tashen girma Allah ya tsameshi,baya bashi sha'awa ko kadan,yadda yake gudanar da rayuwarsa yafi masa dadi,shi mamaki ma yake idan yaga sa'anninsu suna soyayya,tome zasuce a wadannan shekarun nasu?,dariya suke masa idan ya fadi hakan,sau tari sukance

"Dama mune muke da kyau irin naka?,kai don bakasan yadda 'yar mata matan nan ke sonka ba,miskilancinka kawai yasa suke shakkar yi maka magana".

        Hannu lamin ya sanya kan locker din tasa bayan ya gama wannan tunanin,ya ciro wani man fito da saje da qasumba da sadiq din ya siyo tun rannan,wurgi lamin yayi dashi saman kujera

"Shi yasa dama ka siyo wannan saboda kayi sauri ka hada gemu kai dole gaka babba ko?" Yadda lamin yayi maganar cikin jin haushi ya sanya sadiq qyalqyalewa da dariya dole

"To wai kai din da kaketa haka waliyyi ne kai?,girman nan fa yana tahowa na gaya maka gaskiya,don ko a yanzu haka habarka ta fara gemu,toni kuma saina zauna a haka a rainani?,ko kai rannan ina ganinka kanata matse matse?,waye yayi wankan asuba shekaran jiya?" Ya qarasa fada qasa qasa saboda kar a jiyosu.

        Kafin sadiq ya ankara lamin ya kwada masa wani comb da yake taje sumarshi,a baki yaso ya sameshi Allah ya taqaita masa ya goce ya samu kafadarsa,sai yayi qofa yana sheqa dariya

"Kaga kenan gwara ni,kiran girman kawai nake,kai kuwa ya fara samunka,idan ka gama shiryawa ina jiranka a wajen inna" saboda wajen sana'arsu zasu wuce,don suna hutu ne saboda sun kammala rubuta jarabawar qualifying,suna jiran wucewarsu S S3,bugu da qari ma kuma weekend ne.

        Yana shiryawa maganar sadiq na dawo masa,a ranar ya faki idanun sadiq yayi wankansa ne baisan yana ganinsa ba,bayason sadiq din ya sani,saboda yana kunyar abinda zaice masa,duk da cewa daga shi har sadiq din ba jahilai bane,tun kafin zuwan wannan lokacin malam ya musu bayanin xuwan nasa,saidai shi abun naso yazo masa da wani yanayi na daban,yana jin cewa halittarsa ta dabance,don kusan bai taba ganin ko ji daga sadiq din ya shiga yanayi irin nasa ba.

       A nutse ya shirya,kamar ko yaushe tsaf dashi,cikin wani yadi mai sanda sanda me sauqin kudi,yayi kyau,dai dai da matashi mai qananun shekaru.

        A tsakar gida ya samu inna da sadiq din,ya miqe suna yiwa inna sallama,ta rakasu da kyakkyawar addu'a da kuma fatan alkhairi,ta bisu da kallo tana jin alfahari da 'ya'yan nata,wanda tsakanin sadiq din da lamin bata banbace wanda tafiso a cikinsu,tun bayan shigowar lamin din rayuwar gidan.

      Tun qarfe uku ya katse dukkan ayyukansa bayan ya dauki uzuri waje ogansu ya koma daukar iman din.

       Baifi jiran minti talatin yayi ba daliban daga makarantu daban daban suka fara fitowa,yana tsaye harde da hannayensa ya hangota,ya zuba mata idanu yana murmushi ganin yadda take waige waige,ya tabbatar da cewa shi take nema,yadan sake sakayewa kadan don ya gani ko zata iya ganoshi,saidai batayi wani nisan zango ba golden eyes dinta ya hango mata shi,saita taho da dan gudunta ma gauraye da quruciya tana dariya,tana zuwa ta daneshi.

        A hankali yasa hannunsa yana zareta daga jikinsa,ita kuma tana sake maqaleshi tare da fadin

"Ya lamin mun gama...."
"Imaannn" ya ambaci sunanta yana dan dagewa kadan

"Sakeni mana" turus tayi bayan ta sakeshi tana kallonsa,baki a tabe alamun shagwaba

"Yaya me nayi maka?"ganin yadda fuskarta ta nuna rashin jin dadinta saiya duqa a gabanta yana duban golden eyes dinta

"Iman.....daga yau kin girma fa,kin zama babba,ko baki gani bane?,kin zana jarabawar fita daga primary,zaki tafi secondary,duk wanda yaje secondry kuwa ya girma.....wadda ta girma kuma ba'ason tana taba maza kinji?" Saita tura baki gaba

"Ni bana kula kowa Allah ya lamin,ko mazan ajimu ma Allah,kaine kawai,kuma kai ba yaya na bane?" Kansa ya gyada yana sake fidda murmushi

"Yayanki ne,amma ko nidinma daga yau na hana kinji?saboda kin zama big girl" Kanta ta gyada,saidai da alama har cikin ranta bata gamsu ba,yana ankare da ita yadda tayi kicin kicin da rai,duk yadda yake janta da hira kan yadda taji jarabawar taqi sake masa ta bashi labari,bai gaji ba yaci gaba da janta da hirar har suka iso bakin titi don su tari abun hawa.

        Dalibai ne birjik da masu daukarsu,daga gefansa wata 'yar matashiya ce riqe da hannun wata daliba,da alama qanwarta ce,tunda ya shiga wajen dauko iman ya lura da yadda taketa satar kalloshi,dauke kai yayi yanzun ma kamar dazu,ya sanya hannunsa cikin aljihunsa ya fito da baqin glass dinsa da yakan sanya lokaci lokaci.

      Sanyawar da yayi saita sake haska kyanshi cikin farar fatarsa,ya miqa hannu yana tsayar musu da adaidaita sahu,gaba kadan dasu ta tsaya,ya taka ya tsaya yana masa bayani inda zai kaisu.

       Yana shirin shiga yarinyar ta qaraso tana fadin inda zata itama

"Shiga muje" mai adaidaitan ya fada mata jin hanya daya ce,abinda yasa fasa sanya qafafunsa,ya kuma dauke kwandon iman da ya zura a motar yaja baya yana cewa

"Kuje kawai" binsa ta danyi da kallo

"Dukkanmu qannenmu muka dauko,kowa gida kuma yakeson zuwa,kuma tunda yace muje ai hanya dayace ko?" Ta fada tana dan fara'a,kai ya gyada

"Ga wasu 'yan uwanki can daga gaba,idan hanya daya zaku shikena sai ya cike dasu" yanayin fuskarta ya nuna bataso ba,amma haka ta saka qanwartata itama ta shiga.

       "Yaya sun tafi fa,dama shiga kawai mukayi" sosai ya kalleta sannan ya amsa mata

"Babu kyau hada maza da mata guri daya,nima bazanji dadi ba idan kika shiga keda wani" tadai jishi ne,amma bata fahimta abinda yake nufi ba.

      Basu dade ba suka sake samun wani abun hawan,a hanya ya siya mata tarkacen alawoyi,abinda ya sanyata sakewa kenan,ta dinga bashi labarin jarrabawar,da kuma yadda ta amsa kowacce tambaya,don kusan duk abinda ya karanta mata shi taga ya fito.


*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥
_Safiyya Huguma_

*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥
_Billyn Abdul_

*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅
_Hafsat Rano_

*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_

*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥
_Mamuhgee_



Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k


*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*


*KATIN MTN*👇👇

09166221261


*_TEAM ZAFAFABIYAR_*🔥🔥 *KUFAN WUTA*🔥🔥🔥

NA

*HUGUMA*
*ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥


*LAST FREE PAGE*

*_GA WADDA KE BUQATAN BIYAN KUDINTA,ZATA IYA TUNTUBARMU TA WANNAN NUMBERS DIN_*

09032345899
KO
09166221261




Tun bayan zana jarabawarta ya soma mata tanadin tafiya zuwa makarantar gaba ba tare da kowa ya sani ba,ya siya duk abubuwan da yasan zata iya buqata da kadan da kadan,zuwa lokacin ya fara canza yanayin kusancinsu,sabida girma daya fara zuwan mata,a sannan ta shiga shekara ta goma sha uku,duk wasu abubuwa daya kamata ace ta sani yana koyar da ita cikin dabara da kuma hirarsu,abubuwan da ya kamata diya ta sani a shekarun fara girmanta,bugu da qari innarta itama ba baya bace,sau da dama idan ya gaya mata wani abun takan ce inna ta gaya mata,saidai bata fiya daukarsa serious ba kamar idan shine ya gaya matan,tafi maida hankali idan shine ya fada mata da kansa.

Cikin sa'a jarabawarsun ta fito,taci wata government school da basu da nisa da ita,ba bata lokaci malam ya fara mata shiryen shiryen komai,saidai ya tadda amin yaci rabin aikin,shuru malam yayi cikin mamaki tare da qara qaunar amin din har cikin jininsa,irin kulawa da iman ke samu a wajensa ko dan uwanta da suke ciki daya sadiq bata sameta ba.

Bashi da abinda zaice masa banda godiya,godiyar da take saka amin din jin nauyi da kunya,saboda shikam har yanzu a nasa ganin bai sakawa su malam din da komai ba,don har kwanan gobe arziqinsu yakeci,sun sanyashi cikin iyalinsu,yana kwana ya tashi muhalli daya dasu,kuma har kwanan gobe malam din bai daina ciyar dashi da dauke masa wasu buqatu irin na uba da dansa ba.

Duk da haka malam din ya kwakkwafeshi kan ya dinga adani da tanadi,ya daina qarar da duka nemansa akan iman din kadai,ya shaida masa yana taru,bai nutsu ba sai daya samu tabbacin hakan daga bakin sadiqu.

Bangaren inna ma saidai addu'a da fatan Allah ya jiqan mahaifansa,amin din hannun kyauta gareshi,abun duniya bai rufe masa idanu ba sam,kulli yaumin baya taba shigowa hannunsa rabbana cikin gidan,wannan dabi'a tasa har sadiqu ya koyeta,hakan kuma bai sanya ya manta da yayarsa dake garinsu ba wadda tasha dawainiya dashi ba,duk sanda zaije ganinta yakan riqe wani abu me kauri yakai mata.

Cikin nasara iman ta fara zuwa makarantar,yarinya ce mai hazaqa da kaifin basira,gefe daya kuma ga alamin,ya soke hirar dare saidai karatu,idan sun gama karatun ayi hirar kafin inna ta korata ta kwanta,cikin qanqanin lokaci tayi suna cikin makarantar.

Sannu a hankali rayuwa keci gaba da tafiya musu cikin nasara,iman ta gama js 1 ta tafi js 2,har ta tafi zuwa js 3,a sannan tuni yammatanci ya fara zuwar mata,duk wani baiwa da surar kyau na 'ya mace ya fara bayyana a jikinta,wani irin sassanyan kyau wanda hatta da inna ya sanya take sake saka hankalinta da kulawarta akan diyartata,don ko ita duk da tashen kyau da tayi zamanin quruciya bata kai iman din ba,inda Allah ya taimaketa iman din nada wani irin nutsuwa da kuma kamun kai,bata da hargagi ko hayaniya,ko rawar kan yaran da suke tashen girma.

Ta bangaren alamin ma ya sanya kulawarsa sosai akan iman din,bama shi ba harda sadiqun da suke ganin kamar bai damu da al'amuranta a baya ba,saboda lokacine na sabbabin qawaye,kuma lokacine da qananun samari da suma suke tashen girma suke iya shiga rayuwar yarinya,su sauya ta tare da koya mata dabi'u kala daban daban.

A sannan Allah ya fara sanyawa nemansa albarka,don cikin shagon nasu da suke dinki a yanzu haka shima ya mallaki keke nasa ma qashin kansa,idan bashi da makaranta zama yake ya wuni yana dinkinsa,idan kuma yana da lectures sai ya bada haya wani ya hau,da kudin dinkinsa yake sponsoring karatunsa da komai na rayuwarsa,ya taimaki yayarsa da a yanxu babu abinda zatace dashi sai hamdala,hakanan daga inna har malam gajiyar alamin din sukeci sai godiya.

Yana da tsari da kuma bin komai a sannu,bai dauki rayuwarsa da zafi ba,bai kuma dauki kansa a wani ba,komai nashi moderate yake yinsa tsaka tsaki,babu qarya a ciki,baya kallon wai collage yake,dole sai yayi abinda wane da wane sukeyi,idan ka ganshi baka isa ka aibatashi ba ko kai waye,yana da tsafta da sutura ta zamani bakin gwargwado,saidai duk abinda yasan zai zame masa wahala baya kawoshi cikin rayuwarsa,hatta da wayar hannunsa mai matsakaicin kudi ce,bai damu da sai ya riqe babba ba,tunda wannan din zatayi masa komai da babbar zatayi masa,yakanyi tunanin gwara ya sanya kudin cikin sana'ar dinkinsa,don a yanzu wani keken yakeso ya sake siya banda wanda yake dashi.

Dukkan wani rufin asiri da kuma kyautatuwar rayuwa ya sameshi,iya shi da sadiqu a qananun shekarunsu sun tsayawa gidan,sun saukewa malam abubuwa da yawa su sukeyi,don hatta da harkar karatunsu,kama daga kudin registration da sauransu su sukewa kansu da kansu.

**********Kamar yadda al'adar gidan ranar kowacce juma'a tuwon shinkafa akeyi miyar taushe,wannan juma'ar ma hakan take,gefin magariba IMAN ta gama komai,ta kuma killace gidan kamar yadda ta koya daga mahaifiyarta,saboda a yanzun da shekarunta suke goma sha biyar,dukkan wani aiki da ada yake wuyan innar yanzu ya dawo wuyanta,ta horu da wannan tun tana da shekara goma a duniya,don haka sam komai baya bata wuya a yanzu.

Tsaye take gaban dogon madubin dake jingine,wanda ya kusa rabin qofar dakinta,gefe da gefansa sama da kuma qasansa an zagayeshi da katako mai kauri saboda ya bashi kariya,tare da samun damar tsaiwa sosai a muhallin da aka ajjiyeshi.

Daure take da zanin data fito daga wanka dashi,sai tasa hannu ta zare dan qaramin hijabin da take xurawa duk sanda zata shiga wankan,take jiqaqqe gashinta daya kwanta har gadon bayanta ya bayyana,yasha ruwa sosai,saboda wankan tsarki da tayi na al'ada data gama.

Sai data sanya qaramin towel ta sake goge gashin nata sarai,tadan fifitashi kadan yasha iska,sannan ta shafeshi da mai,ta kuma sanya cumb ta tajeshi,take ya dauki sheqi,cikarsa kuma ta bayyana,taja kujera ya qarama da takan zauna akai idan zatayi kwalliya,ta fara mulke jikinta da mayukanta da take amfani dasu.

A nutse ta gama shafa manta,ta shafe fuskarta da powder,tana yi tana duba dan qaramin agogon dake manne a saman mudubin nata,wanda lamin ya siya mata,saboda tashi tafiya makaranta.

Gaban akwatinta dake shaqe da kaya ta zauna tana duba kayan da zata sanya din,batason ta saka wadanda zasu dameta,saboda zafi da akeyi,uwa uba ma kuma ba jimawa zasuyi a jikinta ba zata cire ta saka na kwanciya barci.

Garin daga kayan idanunta suka sauka kan wasu kaya baqaqe masu adon farin zare,da sauri ta sanya hannu ta daukosu tana waresu,sai yanzu ta tuna dasu,kayan da inna rabi ta bata(yar uwar innarta),kaya ne na buzaye masu kama da saqin fulani,saidai shi plain zani ne da kuma riga mai kama da buba,wadda iyakarta cinya,kala biyu ne kayan,akwai jajayensa,dukansu ta ajjiyesu da zummar zata saka kuma bata saka din ba,sai yanzu data binkito wajen ta gansu.

Miqewa tayi ta fara gwada rigar,ta isa gaban madubi,tar kamanninta suka fito,baqaqe kayan sun kwanta saman farar fatarta sun qara mata wani irin kyau,sun kuma tafi da qirar jikinta,duk kuwa da cewa a sake suke,sai ta dan soma jujjuyawa kadan tana sin ta sake ganin yadda suka amsheta,tana qiyasta ranar da zata sakasu.

Qwalla mata kiran da inna tayi ya dakatar da ita daga abinda takeyin,tana daga dakin ta amsa tana duba agogi,tasan ba shakka ta gota lokacin da take kaiwa su ya saddiqu abinci,don haka ta rarumi zanin kawai ta daura,ta yafa dankwalin kayan saman kanta.

Innar bata tsakar gidan,tabbacin cewa daga rumfarta take mata wannan kiran,bata kai ga shiga rumfar innar ba ta jiyo muryarta tana fadin

"Ki dauki abincinsu aminu ki miqa dakinsu,ashe tun yammaci ya dawo bashi da lafiya,bai qaraso ciki ba ya shige dakinsu ya kwanta abinsa,sai yanzu da abubakar ya shigo yake gayamin" har cikin ranta taji wani rashin dadi jin cewa baijin dadi,bai kuma gayawa kowa ba,bayan ita idan bata da lafiya bai barinta tayi jinya ita kadai,tun daga zamanin quruciya har yanzu data fara sanin ciwon kanta,sai ta amsawa innar da to,ta juya da sauri zuwa kitchen,ya debi kayan abincin data riga ta shirya musu,wanda dama ba kasafai take kai musu ba,sunfi shigowa su dauka da kansu,ta nufi soron tana takawa a hankali,cikin ranta tana fatan samun jikin nasa da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login