Showing 27001 words to 30000 words out of 45207 words

Chapter 10 - Kufan Wuta Book 1 Hausa Novel Complete

tana amsa kiran,munira ta tsammata,kuma ita dince,saita aje wayar tana jan babban hijabinta ta dora saman atamfar dake jikinta,wadda al'ameen ya zauna ya bata lokaci sosai ya tsara mata dinki na gani na fada

"Inna zan leqa waje na shigo da ita"
"Saikin dawo" inna dake zaune tana qoqarin gyara saitin radio dinta ta fada,tana son ta kamo freedom radio don jin shirin mu qyaqyata kafin biyar na yamma tayi. Slippers dinta ta zura ta tako zuwa soron gidansu.

Gab da zata fita shi kuma yana qoqarin shigowa,saura kadan suyi gware,taja da baya tana yarfe hannu tare da yamutsa fuska,abinda ya taimaka qwarai wajen fitowar dimple dinta duk sanda ta motsa fuskarta,yayin da shi kuma yaja da baya yana qare mata kallo.

Yana iya hangen yadda tayi wani kyau duk da cikin hijabi take,yana jin shi daya ne a duniya yake iya ganin kyanta koda cikin lullubi take,kuma a kanta kadai yake da wannan baiwar

"Ina zakije?"
"Qawata din nan da zata kawo maka dinki zan shigo da ita"

"Koma ciki" saiya koma da baya ya qwalawa daya daga cikin almajiran gidan kira,yace ya duba layin,idan yaga wata baquwa tana neman gidan nan ya shigo da ita,ya dawo ya zarce dakinsu sannan tuni iman ta kona ciki,duk da taso ya barta taje da kanta ta shigo da ita,saidai ba zata iya yi masa musu ba.

Ba jimawa saiga sallamar munira,iman ta fito da sauri,suka rungume juna cikin murna,kamar wadanda suka jima basuga junansu ba,kai tsaye suka fada dakin inna.

Cikin girmamawa ta gaida inna,innan ta amsa mata,sannan ta miqe ta fice zuwa dakin malam da tun daxu dama takeson shiga ta gyara masa kayan sawarsa ta barsu su biyu cikin rumfarta.

"Hajar ibrahim khalil" munira ta fadawa iman wadda keta qoqarin zuba mata lemo da abinci bayan ta qarewa falon nasu kallo

"Munira sulaiman"
"Yaudai gani a gidanku,naga randa zakizo nima namu gidan" hararta tayi cikin wasa

"Aiba zuwana kikayi ba,kawo dinki ne ya kawoki ko?"

"Eh duk da haka,inda hakanne ma ai da shagon zan tambaya nakai musu direct,da qyar mafa yaron da kika aika ya ganoni" ta fada tana daukan lemon takai bakinta

"Nazo fita mukaci karo da ya al'ameen,shi yace na koma ya tura sa'idu" ajjiye lemon tayi

"Yaudai zanga ya alameen da zancansa ya cika mana kunnuwa aka hanamu sakat,ya al'ameen din nan me shegen tsauri da takura,hala ku biyu inna ta haifa kawai" kai ta girgiza mata tana murmushi

"Mu uku ne,kawai yaya sadiq"

"Amma ban taba ji daga bakinki ba" zamanta fa gyara saman kujera

"Barshi wannan,bamu cika shiri dashi ba" dan dariya muniran tayi suka ci gaba da casa hirarsu,har ta soma bata labarin bikin wata cousin dinta da zasu fara,wanda tsiran kwana ukune dana qawarsu amina,wadda ta kawo dinkin ankonta yanzun.


Yadda taketa bawa iman labarin bikin da yadda aka tsara komai ya tabbatar mata tana matuqar ji da bikin,har ta zolayeta da haka

"Keee,ba dole ba,kinsan manyan mutanen da zasu halacci bikin?,inda naji dadi ana ya gobe dinner din amina zaayi kamu,ran dinner din amina ranar event din gidansu ango za'ayi ba namu bane,so babu lallai naje,washegari ne zaa tashi bikin gadan gadan"

"Wai ita aminan dinner zatayi?"

"Eh mana,wannan atamfar ai ita zaa saka ranar" tabe baki iman tayi,saboda ita duk wata harkar dinner ba zuwa take ba,bata damu da ita ba,koda ta damu dinma tasan ba dabi'ar gidan bace,babu me barinta

"To inajin babu ni a zuwan"
"Saboda me?,ya al'ameen zai hanaki ko?" Dariya ta kubcewa iman

"Au,sharri zaki masa?har kinyi tafsiri ma?" Itama tana dariyar ta amsa mata

"Eh to ai nasan qarshen zancan kenan,nidai badon yayanki bane Allah cewa zanyi da wata a qasa,wannan tsanani da boyo haka?,barima dai ya shigo inga ya yake ya alamin din" maganarta saita dan shigi iman,duk da haka tana dariya ta miqe

"Yama fa shigo gidan amma kin jishi shuru,bari na duba koya gama na masa magana" ta fada tana ficewa,ta manta bata dauki hijab din nata ba.

*LITTAFIN NAN NA KUDI NE,KI TUNTUBI WADAN NAN NUMBERS DIN DON BIYAN KUDIN NAKI*


09032345899
KO KUMA
09166221261
[04/06, 4:54 pm] +234 903 165 5683: 12

_YERWA INCENSE AND MORE: MASARAUTAR KAMSHI:_

_THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME_

_DO YOU WANT THAT MAIDUGURI AND SUDANIAN SCENTS THAT LASTS LONGER AND LINGERS? YERWA INCENSE AND MORE GOT YOU AND YOUR BELOVED ONES COVERED WITH LUXURIOUS SCENTS. KAMSHIN YAN YERWA DA SUDAN💘🙏 20% OFF ORDERS. MUN CIRE KASO 20 NA KUDIN KAYAYYAKIN MU_

_KHUMRAHS_
_KULACCAMS_
_TURARUKAN WUTA_
_NA TSUGUNNO_
_NA KAYA_
_NA GIDAH_
_NA GASHI_

_NA WANKA_
_NA WANKI_
_NA MOPPING_

_AIR FRESHENER_
_CURTAIN AND CHAIRS SPRAY_
_WARDROBE BALLS_
_SCENTED PEBBLES_

_ARABIAN OIL PERFUMES_
_HAIR SPRAY AND CREAM_
_DILKE AND HALWA SET_

_KABBASA_
_BURNERS_
_KASKO_
_TONGS_
_COAL IGNITERS_

_SKIN CARE PRODUCTs_
_OUR TURARE SAMPLE SETS_
_BRIDAL SET (SAITIN AMARE)_
_KUJERAR TSUGUNNO_

_SABULAI NA GYARAN JIKI DA SAURAN KAYAYYAKIN GIDAH NA KAMSHI . KOMAI DA KOMAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA_

_MUNA TURA KAYAYYAKIN MU A KO’iINA A FADIN NIJERIYA DA KETARE_

_SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDAH, 100% TESTED AND TRUSTED_

_instagram:yerwaincense_and_more_*

_WhatsApp: 08095215215_
____________________________________


Tun daga bakin qofar dakin nasu qamshin turarensa ke karakaina,ya cika soron gaba daya,taja numfashi sosai ta sheqi qamshin,tana matuqar son qamshin turarensa,har yau kuma bata taba jin kowa da irinsa ba,babu abinda yake kashewa kudi sosai wajen siyansa irin turare.

Knocking tayi yace a shigo,ta tura qofar a hankali,idanunta suka sauka a kanshi,yana tsaye gaban mudubi yana ajjiye kwalbar turaren da ya gama fesawar yana qoqarin dora hula saman kanshi,yayi kyau cikin shadda ruwan makuba,dinkin zamani daya fidda samartaka sa zallar kyan da Allah ya bashi.

Ta cikin madubin ya kafeta da idanu,abunda bataso,sai ta kauda da kanta tana cewa

"Yaaya,ta iso tun dazu tana jiranka"

"Ganinan fitowa,wani waje zani na tsaya ne na shirya gaba daya kar na saba alqawari" ya fada yana daura agogon hannunsa,saita gaza tafiya yaci gaba da satar kallonsa har ya fuskanci haka,ta basar da sauri,sabida wani iri takeji da ganin kwalliyar da yayi din

"Yaa ina zaka da yammar nan" sai daya gama daura agogonsa tsaf sannan ya amsa

"Akwai wani da muka hadu da yace nakai takarduna,wala'alla idan da rabo zan samu scholarship,tunda suna da hanya"
"Allah yasa a dace" tayi masa addu'ar da har cikin ranta haka yake
"Ameen qanwata,na gode" tadanyi murmushi sannan ta miqe ta nufi hanyar waje.

Cikin tattausar muryarsa yayi sallama cikin falon,munira ta daga kanta daga danna wayarta da takeyi tana amsa sallamar

"Wow"bakinta ya motsa ta furta kalmar qasan zuciyarta,ta gyara zamanta sanda suke magana da iman

"Karbomin fura wajen inna" ta amsa da to sannan ta miqe ta fita zuwa wajen innar,dakin ya danyo shuru,saiya qarasa kujerar dake daga bakin qofa ya zauna a hannun kujerar.

Cikin fara'a gami da mutuntawa munira ta gaidashi,ya amsa kadaran kadaham,sanda iman din ta dawo da furar a cup ta miqa masa itama ta koma ta zauna.

Sai daya fara kurbar furar a hankali cike da nutsuwa sannan yace

"Muga kayan" saita dauka ledar ta aje masa a gabansa ta fidda kayan tana masa bayani,baice komai ba harta gama yana shan furarshi,sai data kammala dai dai sanda ya gama sha ya miqe da cup din a hannunsa

"Imani....ki dauka ki aje wajenki,idan zan fita jibi ki tunamin"
"To yaya" ta amsa masa sanda yake fita.

"Wow....wow,wannan shine ya al'ameen?,badan wani abu ba da na saka kai wallahi" harara iman ta balla mata

"Ba zaki yaudararmin yayana ba,saboda nasan baida kudin da zaki tsaidashi takara" dariya ta saki,tabbas abinda ke cikin zuciyarta kenan,saidai ba zata iya fitowa kai tsaye ta gayawa iman din ba,tako ina al'ameen yakai namiji,abu daya ya rageshi rashin 'ya'yan banki masu yawan gaske da zasu maisheshi wani,amma banda haka tabbas gawurtacce kuma isashen namiji ne.

"Yanzu haka maganar ci gaba da karatunsa ce ta futar dashi" iman tadan bata labari

"Allah sarki yayanmu,Allah ya bada sa'a"
"Ameen" iman ta amsa mata,daga haka suka fada wata hirar.


********. *******Tana daga zaune gefan katifar dake shimfide dakin iman,bayan ta karbi dinkunanta da sukayi kyau sosai wanda al'ameen din yayi mata,wayarta na hannunta tana ta danne danne,da yake gwana ce qwarai ita din wajen danna waya,shi yasa babu inda ke mata wahalar shiga loko da saqo na kowacce irin waya

"Kiyi sauri don Allah muje kada mu samu layi" munira tace da iman wadda ke shiryawa zasu wuce gidan qunshi,saboda gobe zaa fara bikin qawartasu

"Na gama ai,hijabi kawai xan saka" ta fada tana ware gogaggen hijabinta me kyau

"Kiwa Allah ki aje hijabin nan,wallahi wajen 'yan gayu ne sai kisa a dinga mana kallon tara saura kwata,ko kamar nawa mayafinne ki saka,tunda kinga dai babba ne,kuma bashi da shara shara" inan din ta buda baki zatayi magana munira ta dakatar da ita

"Nasan yanzu zaki kawo karatun ya Alameen,goben ma kenan haka zakiyi?" Murmushi kawai iman tayi,don kamar ta shiga zuciyartata,maganar al'ameen din ya hanata saka mayafai zatayi mata,saita aje hijabin,ta bude ma'ajiyar kayanta,ta ciro daga cikin sabbin lafayar da yagana ta bata,wata 'yar uwar mahaifinta har guda biyar masu azabar kyau da tsada.

"Kai kai kai,ke kinga kyan datayi miki kuwa,ma sha Alla,da ana musayar kyau Allah da tuni na karba naki na hadaki da nawa" munira ta fada cikin nuna santi da yabawa da kyan iman din tayi,wanda zahirin gaskiya gaskiya ta fada,wani kyau lafayan tayi mata,idan ka kalleta kamar ba zaka dauke ido ba,ita kanta dai data juya ta sake kallon kanta a madubi ta gasgata hakan.


Tana tsaka da sanya halfshoe dinta da ya alameen ya siya mata 6k wanda ya dace da lafayar jikinta wayarta da ya alameen din ya bata tecno ta dauki tsuwwa,munira ta kalli sashen da wayar take,ta tuntsire da dariya tana cewa

"Ana kiranki a rakani kashinki?' sai data manna mata harara sannan ta isa inda wayar take
"A haka nakeson kayata"

"Amma dai wallahi ba girmanki bane,dressing dinki sam bai kamaci wannan wayar ba" ta saba da jin wannan lafuzzan daga bakin muniran,don haka tayi banza da ita ta isa inda wayar take ta daga abunta.

Sai data gama wayar ta dubi muniran

"Su hamra ne,already wai suna wajen,har an fara yiwa wasu,mu kadane bama nan"

"Nasan zaa rina dama,munyi delay da yawa" munira ta fada tana daukar ledar kayanta.

Saida suka biya wajen inna,munira ta yiwa innan sallama da kuma godiya,ita kuma iman ta karbi kudin qunshin sannan suka fito suka wuce.

AMARYAR KB BEAUTY PARLOR,katafaren wajen gyaran amare da uwayen gidaje,yammata harma da zawara,waje ne na alfarma wanda ya kasance iya kudinka iya shagalinka,wajene daya amsa sunansa,duk sanda kaje haka zakaga manyan hajiyoyi suna karakaina,suna dukkan wani nau'in gyaran jiki da kuma kayan magunguna na gyaran jiki da aka warewa waje na musamman a ciki.

Amarya sakina itama iyayenta da danshinsu,hakanan wanda zata aura din shima ba baya bane,tun asali gidansu basu damu da karatun boko ba,kasuwanci sukafi bawa qarfi,don haka sanda miji ya fito mata ya kuma tabbatar musu zai siya mata dukkan wani certificate,basu wani jinkirta ba aka cireta daga karatun aka fara shirin auren nata.

Tun daga shigarsu wajen iman tasan waje ne na matan da suka isa,dukkaninsu qawaye ne,saidai bata wani saba can dasu kamar yadda suka shaqu da munira ba,don haka bayan 'yan caftarsu ta qawaye da murnar shigowarsu,sai ta samu waje saman kujerun da aka tanada a wajen tayi zamanta,tana sauraren hirarrakin dake tashi a wajen,da kuma shige da ficen 'yan gayu mazansu da matansu.


Hira suke irin ta matasan yammatan dakeji da tashen quruciya,dukkansu babu wadda ba daga babban gida ta fito ba,kusan ita daya ce ma kawai zaa ce iyayenta ba wasu masu kudi bane,saidai ita din ma shigarta fes take,kai bakace hakan ba.

Abu daya ne idan ka lura dashi zaka gane banbamcinsu,manya manyan wayoyin dake hannun kowaccensu,da kuma irin kudaden dake jakarsu,kowacce ta fito da tata tana harkar gabanta.

Mutum uku cikinsu saida samarinsu sukazo har qofar wajen suka basu kudin lallaen da gyaran gashi,kowanne cikin babbar mota,hakan kudin da suka basu sababbin ne a rafarsu.

Kafin zuwan nasu suka saka gasa,duk wadda kudin da aka bata yafi na sauran yawa ita zaa fara yiwa,daga qarshe fahima ita ta cinye,dole ita aka saka za'a bari a fara yiwa.

Ita dai nata idanu,sai wata matashiya dake kusa da ita wadda batafi sa'arsu ba da aka sawa lalle,tun dazu ake kiranta babu me daga mata,don haka iman din ta matsa kusa da ita

"Bari na daga miki"
"Yauwa na gode" ta fada a yagance tana murmushin jin dadin hakan da iman din tayi mata,ta riqe wayar da kafadarta ta fara amsa kiran,murya can qasa,wanda da alamu saurayinta ne ya kira,don sunyi doguwar waya sosai,har aka gama yiwa amarya sakina qunshinta da qawarta da sukazo tare,ango yazo daukarta,dukka suka tashi mata takiya,munira na cewa sai sunje sun gaisa.

Ko alamar motsawa iman batayi ba,amma munira ta finciki hannunta,dole ta bisu.

Yana jingine jikin fara qal din motarsu,wadda da alama sabuwa ce,su biyune shida wani matashin saurayin kamarsa,cikin fara'a da barkwanci irin na angwaye da qawayen amarya,tana tsaye daga gefe tana kallonsu,don ita komai ma sabo ne a wajenta,saboda wannan shine karonta na farko na bikin qawa a waje,ko cikin dangi ma ba kasafai take zuwa ba saboda nisa da suka dan mata,daga na uwa har na uban,sai dai daiku dake nan garin da suke.


Kowa cikinsu ta fara gabatar masa da kanta da kuma sunanta,har aka gama,munira ta waiwayo

"Matso mana iman" abinda yaja hankalin angon da abokin nasa kenan"

Idanu abokin ya zuba mata sosai,ya furta

"Subhanallah" har zuwa sanda ta iso idanunsa yana kanta

"Itama cikin qawayenku take?" Saurayin me suna hashim ya tambaya bayan ta gama gaidasu

"Eh....iman,ba kasafai ta fiya son shiga jama'a ba ai"

"That's good" ya fada yana gyada kai,still ita yake kallo,abinda yasa ta takura kenan,taja da baya tana fadin

"Bari naje kafin ku gama,kada azo kanmu babu kowa"

"Wait iman....ki tsaya ki karba kudin liqi mana" kafada ta daga

"A'ah,na gode sosai wallahi" daga hakata qara sauri tayi ciki tana mita cikin ranta,gaba daya batasan me yasa mazan yanzu suke da shegen kallo ba.

Basu jima sosai ba suka dawo,sauran su uku kenan da suka rage ba'a yiwa ba

"Haba iman.....haba da Allah,me yasa kike abu kamar baki waye bane,ke dan samarin nan ma na yayi da akeyi ki kasa yi,guy iya haduwa amma ki yarfashi ki taho,ke kinga yadda ya rude da zancanki bayan kin taho,Allah annabi a hadaki dashi?,at last dai dole muka bashi number dinki" idanunta ta zaro

"Me yasa zaku bashi don Allah,me yasa zakuyimin haka?" Ta fada adan rude,dukkaninsu suka sanya dariya

"Seriously da gaske nake,yanzu me zance da ya al'ameen idan yaga wani ya kirani?"

"Waima.....wai.ya al'ameen,to meye a ciki?,shi kansa yasan kin isa a kirakin,waima idan bai bari an kirakin ba,jiqaki zaiyi yasha?,a yadda Allah ya halicceki iman saidai idan ba zaki dinga fita ba a gida zaki boye kanki" munira ta qarashe bayanan suka kuma goyi bayanta

"Gaskiya kam,koni da za'a bani dama yaya na zan yiwa kamu" budurwar da ta taimaka mata dazu ta sanya baki a hirarsu,kowa ya sanya dariya.

Ko a jikin munira ta qara gaba ta cire dan kwalinta don a fara yi mata gyaran gashi,yayin da iman ta dinga binta da harara tana gasa mata ita.


Daidai sanda aka gama musu wayar muniran ta dauki tsuwwa,ta daga da hanzari

"Ina zuwa.....Allah bazanyi missing ba,gani nan zuwa" shine abinda muniran ta fada tana maida wayarta jaka

"Don Allah don annabi qawalli ki rakani kamun nan,ban zaci abun haka aka shiryashi ba sai yanzu da batula ta kirani,ba zamu jima ba in sha Allah zamu taho,kinga hanya daya zamuyi,gida zan koma zan debo kayana,sai gobe zan wuce gaba daya" da farko uzuri ta bata kan yamma tayi sosai,kafin suje ma magariba tayi,kuma malam yana fada idan tayi dare a waje,haka ya al'ameen,da qyar munira tasha kanta,tace zata rakata har gida ta yiwa inna bayani,zannan ta aminta,nan cikin kayan data amso dinki ta zabi daya daga ciki ta sauya,ta kuma biya aka mata lite makeup,tayi tayi iman ta dauki wani a ciki itama ta sauya tace aa,kayan jikinta sun isheta.

Tun daga shigansu wajen iman ta tabbatar lallai bikine na manya,wadanda sukaci suka tada kai,wani mahaukacin gida ne mai dauki da tafkekiyar haraba,wanda ama qawata ta da decorations irin na biki,duk yawan jama'ar dake wajen ta daukesu tsaf,harda ragowar sararin da motocin gidan ke fake abinsu basusan anayi bama.

Tunda suka shiga din iman ta samu seat ta zauna,daga inda take din tana iya hango yadda komai ke wakana,amarya tayi kyau iya kyau tare da angonta,sai gudanar da komai ake cikin fariya boko da kuma nuna wadata.

A hankali ta daga kanta ta kalli yadda sama ta fara duhu,alamu suna nuna anyi kira sallar magariba zuwa yanzu,duk da bata iya jiyo kiran ba saboda tashin kidan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login