Showing 45001 words to 45207 words out of 45207 words

Chapter 16 - Kufan Wuta Book 1 Hausa Novel Complete

sa gaba?iman baki sona ne?,ko ya amin din naki bai miki ba?,idan banyi miki ba iman ki fito ki gaya min,saboda ni ba baqonki bane......"ga fada maganar cike da qwarim gwiwar samun akasin abinda zuciyarsa ke raya masa,saida amsar da iman din ta bashi tayi matuqa girgizashi,ta motsa masa zuciyarsa fiye da yadda ya zata ko kuma ya tsammata......amsar da bai taba kawowa koda cikin mafarkansa zai jita daga bakin iman din ba,bai taba zaton zata iya furtata ba


"kayi haquri ya amin........bassam nakeso" ta amsa masa,tamkar dama jira take a bata wannan damar.

Dukkan wata jijiya dake kai saqo jini da kuma iska a jikinsa zuwa muhallansu sai da ta tafi hutu na sakanni,kafin ya samu nasarar zuqo numfashinsa,bayan ya tabbatar numfashin ya koma saman qirjinsa yadda ya dace,sai ya fara kokwanton duniyar zahiri ce ko ta mafarki,saboda haka yayi qarfin halin motsawa kadan

"Iman.....sake maimatawa naji". Yayi maganar sautin muryarsa na fidda wani amo wanda zai alamtawa mai sauraron da kunnensa da kuma qirjinsa ya cika da hikima cewa lallai akwai wani abu mai tsananin nauyi da yake shirin danne zuciyar da wannan sautin ya fito daga gangar jikinta......

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login