Showing 36001 words to 39000 words out of 45207 words
qawayenta,abinda ta lura dashi ya fara faruwa tun sanda munira ta shaida musu bassam shine masoyinta
"Komai yaji,wanka iya wanka,amma wallahi kika fito da wayar hannunki sai naji kamar zan nutse" munira ta fada dai dai yadda iman dince kadai zata iya ji.
Sauke wayar tayi tana duban munira,wanda dama ta dauko wayarne saboda jin qarar shigowar saqo,wanda kuma take da yaqinin ba daga kowa yake ba illa bassam
_"Kinyi kyau iya kyau baby.......,yanzu na shigo gida daga tafiya,amman bazan iya daurewa ba.....sai nazo naga wannan kwalliyar beautyna"_ wannan shine saqon da taci karo dashi,wanda mamaki ya kamata kan ta ina ya hangi adonta.
Maimakon ta bawa munira amsar maganarta saita buge da tambayarta
"Ya akayi bassam yaga kwalliyata?" Idanu munira ta wara
"Wallahi ban sani ba,shida baya nan yana abuja?"
"Ya dawo gida yanzu,kuma yana zancan zuwa ya ganni ba tare daya nemi address ba,bari naga gudun ruwansa,ta ina zai lalubo ni?" Ta fada tana gyara zamanta gami da gyara rufin lafayarta.
Murmushi munira ta saki
"Har yanzu bakisan waye bassam ba,mai kudin da idan yaso zai iya sanin duk wani motsi naki,amma bari mu gani,da rabon muje gidan amarya a lafiyayyar mota" munira ta fada cikin murna,batabi ta murnar munira ba,don tasan babu lallai yazo din,tunda baisan ina suke ba,saita dan goce kadan ta jingina da kujerar dake daura da ita.
A hankali zuciyarta da qwaqwalwarta suka shiga tunani,suka shiga hasko mata fuskokinsa data gani cikin hotunansa na ista cikin mabanbantan yanayi da shiga kala daban daban,tarin tulin 'yammata daketa commenting akai,da kuma qoqarin jan hankalinsa zuwa private chat,a hankali taji shauqin son ganin fuskar tasa na saukar mata,saita lumshe idanunta tana bitar lausasan kalamansa da suka zame mata abokai cikin kwanakin nan,dasu take kwana dasu take tashi,ta kuma hadasu da fuskarsa iya shiga da tsari na jikinsa,take taji komai yayi mata dari bisa dari,sai ta lumshe idanu tana sauraren hirarrakinsu,tare da kasa kunne taji xai kirata ko zai turo saqo ya nema address?.*_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*
16
Taji mamaki sosai sanda yake shaida mata yana qofar gidan,ta dubi munira duban tuhuma,ta daga hannayenta sama alamun ba ruwana.
A matuqar darare fa shiga motar sanda ya bude mata da kansa ya mata izinin shigar,shima saboda idanuwan yammata dake qofar gidan ana shirye shiryen daukar amarya da sukayi musu caa kamar zasu cinyesu.
Nannauyar ajiyar zuciya ya saki yana shafar qirjinsa
"Thank God,sai yau dana ganki sannan naji kamar an ciremin qaya, beauty,i really missed you" kunya ce tadan saukar mata,taja lafayanta ta sake boye fuskarta ta murmushi
"I liked it baby,inason kunyar nan taki,amma dai ya kamata adan fara rageta,a nunamin soyayya ko?".
Hira yake janta da ita sosai cikin wani salo da yasan yana tafi da zukatan 'yammata,ya hada mata abubuwan sha da ci duka cikin motar saman dan wani abu da ake janyowa me kama a table,saidai taqi taba komai saboda bata saba ba,ba zata iya cin komai a gabansa ba,uwa uba kuma a takure take jinta,ga kalamansa daya cikata dasu wadanda suka yiwa kanta nauyi,taketa jin kunyar yadda yake marairaice mata kamar zai kwanta aka ta soshi don Allah,yayi alqawarin zai mallaka mata komai.
Abinda bai sani ba tuni ya fara barin burbushin wani abu a cikin zuciyarta,ya sanya zuciyarta ta fara narkewa da kadan da kadan,hakanan tanajin wani abu na tabata duk sanda ta kalleshi,ta kuma tabbata kowacce mace ma dole taji irin wannan,saboda dan gayu ne iya gayu,wanda gayun ga hade da kyau da kuma ilimi quruciya da kuma wadatar arziqi.
Kafewa yayi kan shi zai kaita gidan amarya,bazai barta tahau motar kowa ba,nan kuwa ta samu qawayenta 'yan tayi,kowacce tace a motar itama zata,a haka suka dibi mutum hudu daga cikinsu suka wuce.
Ko a hanya ma bai barta ba,hira yake mata qasa qasa cikin kalaman da zasu iya wafce ko sace zuciyar kwacce irin mace,idam yaji tayi shuru cikin murya me kama da rada zaice
"Uhmmm baby......baby kice wani abu mana,don Allah karki haukatani" wani abun ko bataso saita amsa masa.
Da suka isa ma hanata fita yayi yaci gaba da dasa mata dashe me wuyar cirewa,su sauran suka shige ciki,sai da yaga an ragu sannan ya mata tattaki har qofar gidan ta shiga,sannan ya daw jikin motarsa ya jingina yana jiranta.
Tana shiga kamar dama jiranta sukeyi kowacce ta shiga ihu da kuma zolayarta
"Ku keshan soyayyarku,amma nice nake sumewa" inji zee qawarsu
"Gaskiya gaskiya kika bar wannan guy din kin tafka asara,keee.....me tsada be wallahi wannan,samun namijin da komai yaji a tare dashi kamarsa ai abune me wahalar gaske,tabdi,gaskiya kin shiga sahun mata masu sa'a a duniya" daga daga cikinsu ta sake fada
"Banda zaman amana ake ai ni zanyi wufff dashi" batasan ta jefa mata harara ba sai da suka kwashe mata da dariya
"Almura,ashe ya fara sace zuciyar da akaqi bawa kowa dama". Haka suka hadu sukayita yi mata cari.
Duk yadda taso ya barta ta samu abun hawa na haya ta koma gida yaqi ji bare gani,duk ta gama tsurewa,yayi parking qofar wani babban store ya fita bayan yace tazo su shiga tare amma taqiya.
A qalla kusa minti talatin ya barsu cikin motar ita da qawayen nata kafin ya dawo,siyayya yayi mata mai ubansun yawa data sanya iman din tsurewa,ya dubi su munira yace su shiga ciki su karbo sauran kayan duka nasu ne.
Sai da suka fita ya fidda wasu qananun leda guda biyu,daya daya bude wani dan qaramin akwati ne me azabae kyau,zobe ne a ciki me bala'in kyau da daukar idanu ya miqa mata
"Saka,so nake naga yadda zaiwa kyawawan hannuwanki kyau" ya fada yana murmshi,yadda ya tsareta da kallo ya sanya dole ta saka zoben,ko don ta tsira daga kallon da yake jifanta dashi
"Ma sha Allah,da dama da nayi kissing wannan kyawawan yatsu,Allah ya mallakamin su" tsananin kunya ya hanata magana,sai kawai ta janye hannun nata ta boye cikin mayafi.
Leda ta biyu still shima wani kwalin ne,wanda ke dauke da wata santaleliyar wayar hannu,wanda ko ba'a gaya maka ba kasan cewa ba qaramar wayar bace,bawai a girma na jiki ba,a'ah,kudaden da aka zuba kafin a mallaketa.
Miqa mata wayar yayi,ta janye hannunta taqi karba tana dubansa
"Na siyeta ne saboda ke,an saita komai da komai nata,akwai layi a ciki,na siyeshi ne saboda ni kadai,nafison duk sanda na kiraki na sameki available" babu jan dogon bayani tace mishi ba zata karba ba,yaji babu dadi har saman fuskarsa,saidai a nata ganin haka shine daidai,don batasan inda zata sanya wayar ba.
Wannan dalili yasa ta kasa musanta masa sanda ya bata gift na ledar daya loda mata siyayya,suna tafe munira na mata rakiya kamar kowanne lokaci,saidai jikinta asabule yake
"Munira,nufar gidanmu fa kike da wadan nan kayan"
"Na sani,ki tsaya ki gani mana" ta bata amsa babu alamun damuwa a tattare da ita.
A bakin famfo suka samu inna tana tarar ruwa a buta,da alama bandaki zata zagaya,ta daga kai tana amsa sallamarsu,cike da ladabi kamar kullum munira ta gaida innar,ta amsa mata tana tambayarta mutanen gidan,ta soma gajiya da ganin yarinyar tare da iman,bata fiyason mu'amalar iman din da baqin fuskar qawaye ba,duk da dama silar bikin sakina ne ya kawota gidan.
"Inna wai kaya ne da sakina ta bayar a rabawa tsakaninmu qawayenta da muka yi mata hidiman biki,shine nace ta ajjiye mana a wajenta,idan yaso in an tashi sai a raba,sai iman din ke tsoron kada ki fada,shine nace bari na roqeki don Allah"
Idanu innar ta sauke kan ledar da muniran ke nuna mata,kowaccensu tayi shuru tana jiran jin amsar da innan zata bayar,kamar ba zatae komai ba sannan ta amsa
"Ba damuwa,amma karsu jima,banason ajiyar abinda ba naka ba"
"In sha Allahu inna" daga haka ta miqawa iman ledar,sukayi sallama ita ta juya ta fice.
Cikin kwanakin gaba daya bassam ya sanya wuta wajen nema soyayyar iman din,ya kuma ci galaba da gagarumar nasarar da bai taba kawowa kansa zai samu ba,ita kanta iman din ta fada wani muguwar soyayya da bata taba tunanin zata fada ta ba,sannu a hankali ta dinga ganin kyan da bassam da kuma sauran jama'a ke kururutawa tata,ta kuma hango dacewar da sukayi da bassam din. Da kuma dacewarsa da zamantowarsa miji a gareta.
Ta samu sakewa da dukka kaya da siyayyar bassam sanda taje maiduguri ta dawo,saita sanya dukka kayan cikin tsarabar da yagana tayi mata,a zuwan ita ta bata su,ta fidda fella fellan laces din ciki ta bawa al'ameen ya dinka mata.
Haka kawai yaji jikinsa yayi sanyi sanda ya bude laces din xai dinka,tailor ne shi da yasan aikinsa,ya kuma san kudin kaya masu tarin yawa,a idanu kawai akace ka yiwa lace din kudi kasan ba qarami bane bare aje ga ainihin kudinsa,kusan guda uku ne kuma dukka haka suke.
Yagana 'yar kasuwa ce,tana kuma samu sosai da kasuwancinta,to amma kuma laces din sunyi tsada da yawa,saidai daga bisani ya gargadi kansa,yakuma share maganar cikin ransa,tunda ya riga ya aminta da wace iman din,rainonsa ce,ta kuma tsotsi tarbiyya daga inda suka tsotsa,wato wajen inna da malam,ya budesu yayi mata dinkuna masu kyau,da suka sanya ta dinga murna sanda ya kawo mata su,ta kuma ajjiyesu,batayi amfani dasu ba sai da bikin murjana,daya 'yar ajintasu.
Ta fita sosai cikin qawayen nata,ta kuma fita daban,ta haska yadda ya kamata,ta dinga jin kanta yana fasuwa cikin qawayenta,saidai tayi qoqari matuqa wajen hana kanta jin izza ko girman kai.
Kasancewar bassam ma'abocin tafiye tafiye ne,baya nan akayo bikin murjana,yaji babu dadi sosai,saboda yaso su kasance tare a lokacin,don har yanzu abu na gaba da yake buri da buqata shine ta gabatar dashi a gidansu,ya samu 'yancin zuwa ganinta kai tsaye a duk sanda yaso.
Saidai ita a nata bangaren cike take da tsoro da kuma fargaba,tsoron yadda zatayi bayani wa malam inda ta sanshi,a inda suka hadu,da kuma yadda akai har suka saba babu wanda ya sani,ina zatace ta samu lasisi ko kuma umarnin sauraronsa,uwa uba kuma ta sani,burin ya ami tayi karatu,basuyi cewa zata gabatar da mijin aure a dai dai wannan gabar da take aji biyar a makarantar secondary ba.
Duk da baizo ba amma tuni wayarsa ta samu baquncin hotunanta tsala tsala ta hannun jakadiyarsa munira,wanda suka sake haukatashi tare da susutashi,suka kuma sanyashi qara daura damara da cin burin kasancewa da iman din,da kuma maidata ta zama matarsa kuma mallakinsa,ko me zaya kashe kuwa.
Tafiyar al'ameen zuwa jigawa garinsu ya sake qulla wani sabon kusanci da kuma shafin soyayya tsakanin iman da bassam,saboda wayarsa daya bar mata aro kafin ya dawo,ita kuma tayi amfani da wannan damar,ta bude account na Instagram WhatsApp da Twitter,yadda zata samu damar ganin bassam din yadda ranta yakeso.
Ta kuwa kalleshin,babu wani hoto nasa data tsallake ba tare data masa kyakkyawan kallo uku ko sama da haka ba,gayu iya gayu,kudi iya kudi ta gansu,gefe guda kuma ga ilimi kamar yadda take da sha'awa,daya qyalla idanu ya sameta ta WhatsApp kuwa kamar zaiyi me saboda murna,hakan ya sanya ta sake zama mayyar waya,kullum tana manne da ita a daka,Allah Allah take ta gama abinda take ta dauki wayarta su kasance tare.
Tuni inna ta fara lura da canje canjen dabi'u da kuma halaye tattare da iman din,abinda yasa ranar da amin ya dawo daga qauye,suna tsakar gida,inna na saman babbar tabarma,shi kuma yana kan kujera 'yar tsuguno yana bawa inna labarin ci gaban da qauyensu keta samu,iman din na saman tabarma daban,ta tattara hankalinta gaba daya saman wayar,abinda yaso jan hankalinsa kenan,duk da suna hira da inna,amma kusan bayan kowanne minti sai ya daga kai ya kalleta,yasan cewa ba haka suka saba da ita ba a lokaci irin wannan daya dawo daga tafiya,tana nuna kewarta sosai a kanshi,abinci na musamman take masa,ta hada da ruwan zafi na wanka takai masa,yana cin abincin tana damunsa da hirar abubuwan da suka faru bayan baya nan,shima kuma tana tambayarsa abubuwan daya gani da sauye sauye da aka samu.
Miqewar da tayi yasa inna tace
"Ina zuwa?" Fuska tadan ya mutsa kadan
"Kwanciya zanyi inna,na gaji" idanu ta kafeta dashi
"Me yake damunki ne kwana biyu da kika koyi kwanciyar wuri?"
"Kawai inna,saboda makaranta ma,da shirye shiryen qualifying da mukeso mu fara" sam maganar bata shigeta ba bare al'amin,wanda ya maida kansa ga qaramar keypad din daya tafi da ita,yana serving station din da yake yawan sauraran labarai a cikinsu
"Wannan wayar ke daukan hankalinki iman......" Maganar da taso tadan tsoratata,amma saita dake,saboda tasan halin innar da matuqar bin qwaqwaqwafi
"Games ne da yawa na dauko inna,kuma inajin dadin yi"
"Dole ki maida masa wayarsa,tunda tana neman canzaki" saita marairaice cikin tsoro da faduwar gaban kada a yanzu yanzu innar tace ta miqa masa abarsa tunda ya dawo,kafin kuwa ta gama tunanin nata abinda ta zata din ya afku,innar tace da ita
"Bashi wayarsa maza,tunda Allah ya dawo dashi lpy alhmdlh,aikin mori abinda kika mora,dama kullum malam cikin fadan me yasa ya barta a hannunki yake"
"Don Allah inna........"
"Karki min magiya"
"Zan karba gobe inna,ki qyaleta" al'ameen ya shiga maganar,saboda ko waye mutum komai qanqantarsa bazaiso irin wannan titsiyen ba,zuciyarsa kuma fes take kan iman din,baya shakka ko zargin zata aikata wani abu ba dai dai ba,ko kuma ya saba da tarbiyyan gidan,yadai bata uzuri kan cewa rashin sabo ne,da kuma daukin wayar tunda ta jima tana sonta.
_________________________________
*mg's skincare*
Shin Ina matan suke🗣️🗣️🗣️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi😃🤩
Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaran jiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum👌hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️
Shin kinafama da
Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?
Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki😫
Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 🤗ga amare uk wnd yy using bridal set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind
Bridal kit:18k
Beauty kit:11k
Student package:7k
Herbal whitening soap:3k
Chat
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Facebook: mg's skincare
Instagram:glow_with_mgs
Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg's babushi akasuwa🤝
Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go🤩
Then @mgs skincare gat you covered 💯
Now is time to glow😍
Pamper ur skin🦵
Shine like bride👰🏻♀
Glow🧖♀️
💯 tested nd trusted🤝
Guarantee
Sannan muna da hadaddun frames masu kyau gamai bukata yayi mgn 0704688116617
_YERWA INCENSE AND MORE: MASARAUTAR KAMSHI:_
_THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME_
_DO YOU WANT THAT MAIDUGURI AND SUDANIAN SCENTS THAT LASTS LONGER AND LINGERS? YERWA INCENSE AND MORE GOT YOU AND YOUR BELOVED ONES COVERED WITH LUXURIOUS SCENTS. KAMSHIN YAN YERWA DA SUDAN💘🙏 20% OFF ORDERS. MUN CIRE KASO 20 NA KUDIN KAYAYYAKIN MU_
_KHUMRAHS_
_KULACCAMS_
_TURARUKAN WUTA_
_NA TSUGUNNO_
_NA KAYA_
_NA GIDAH_
_NA GASHI_
_NA WANKA_
_NA WANKI_
_NA MOPPING_
_AIR FRESHENER_
_CURTAIN AND CHAIRS SPRAY_
_WARDROBE BALLS_
_SCENTED PEBBLES_
_ARABIAN OIL PERFUMES_
_HAIR SPRAY AND CREAM_
_DILKE AND HALWA SET_
_KABBASA_
_BURNERS_
_KASKO_
_TONGS_
_COAL IGNITERS_
_SKIN CARE PRODUCTs_
_OUR TURARE SAMPLE SETS_
_BRIDAL SET (SAITIN AMARE)_
_KUJERAR TSUGUNNO_
_SABULAI NA GYARAN JIKI DA SAURAN KAYAYYAKIN GIDAH NA KAMSHI . KOMAI DA KOMAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA_
_MUNA TURA KAYAYYAKIN MU A KO’iINA A FADIN NIJERIYA DA KETARE_
_SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDAH, 100% TESTED AND TRUSTED_
_instagram:yerwaincense_and_more_*
_WhatsApp: 08095215215_
__________________________________
Washegari bai karba wayar ba kamar yadda yace din,saboda sabgoginsa na dinki da kuma neman samun damar ci gaba da karatunsa da yaketa fafutuka,saidai a ranar yanajin yadda inna ke mitar yadda iman din fa tashi a makare ta fara ayyukan gida,wanda saboda quracewar lokaci bata samu gama aikin ba,inda daga qarshe ta shirya ta wuce makarantar a makare,innan kuma ita ta qarasa sauran aikin da ya rage din.
Washegari qarfe takwas saura minti biyar na safe ya fito a shirye zashi su hadu da mutumin daketa masa fafutukar ganin ya samu tallafin karatu,ya gaida inna dake dauraye flask din malam na kunu sannan ya tambayeta malam,tace yana qofar gida,ganin takalman iman na makaranta yasa ya tambayi inna iman dun bata wuce makarantar ba?
"Ina zata wuce,ta zama abunda ta zama,babu abinda ta iya sai kasala da sakalcin banza" sai yaji a ransa indai waya