Showing 12001 words to 15000 words out of 45207 words
sauqi.
Tana dab da bakin qofar dakin nasu sadiq ya daga labulen ya fito
"Ki zubamin a plate ya dan sha iska,yanzu zan dawo" ya fada yana sanya takalminsa,ta amsa da to kana tayi sallama ta saka kanta zuwa cikin dakin.
Babu kowa a dakin,sai motsin ruwa daga toilet din nasu,ko ina fes yake,sai qamshin tsintsiyar turare da kuma turarukan da suke amfani dasu daya gauraye dakin,tanason dakin tun ainihi,saboda yafi kowanne daki dake gidan sanyi da kuma dadin zama,a zamanin quruciya,tasha shiga dakin ayita nemanta,har bacci yayi awon gaba da ita.
Table din da tasan suna ajjiye karikicen kayan abincinsu ta qarasa kai ta dora a nutse,sannan ta bude fa fara zuba lafiyayyen tuwon farar shinkada,da miyar taushe wadda aka sakawa tantaqwashi,cikin mintuna qalilan qamshi ya bade dakin.
Plate biyu ta zuba harda lamin din,saita koma saman doguwar kujerar dake dakin ta zauna,tana dakon ya fito tayi masa sannu,duk ranta babu dadi sosai,dama kusan sati guda suna sabani dashi,basa haduwa sam,inna ta gaya masa yana wasu dinkunan biki ne,shi yasa yake fita da wuri ya kuma dade bai dawo ba,ga kuma makaranta.
Tana tausayin yadda yake nema tuquru,ya dauki sana'arsa da muhimmanci,fiye da yayanta sadiq,don shi wasu lokutan yakan zauna a gida yace bazai fita ba,musamman idan lectures suka hade masa ranar yasha wuya,amma bata taba ganin lamin din yana hutu ba,idan tayi magana sai ya saki murmushin dake qarawa idanunsa lumshewa yace
"Babu wani hutu a nan duniya,namiji kuma da struggling aka sanshi".
Yana da dabi'ar jimawa yana wanka,don haka sai ta tura hannunta cikin gashin kanta tana dan warashi saboda ya sake samun iska,a hankali har dankwalinta ya zame daga kanta,saita kamo gashin ta rabashi biyu ta fara kitsa kalba wai ko zaifi saurin shan iskan.
Sai da ya sanya hannu ya sake sharce gashinsa da kyau,sannan ya kama murfin qofar bandakin ya murdata ya bude a hankali cikin rashin qwarin jiki.
A hankali idanunsa suka fara sauka a kanta,tayi nisa da kitsa jelar kalbar,kayan jikinta sun haskata ainun,har suna canza mata yanayi zuwa ainihin bafulatanar niger kuma shuwa zam.
Bin jelar da take kitsawar yayi da kallo,zuciyarsa ta wani buga,sai ya lumshe idanunsa kana ya budesu duka lokaci daya,maimakon dauke idanunsa da yayi niyyar yi daga kanta,haka sai ya gagara,ya maida idanun nasa yana ci gaba da kallonta
"Anya ko zaka iya ci gaba?,zaka iya daurewa?,zaka iya cika alqawarin daka daukarwa kanka?" Jerin gwanon tambayoyin da ya jefawa kansa kenan,sai ya sake lumshe lumsassun idanuwansa da zazzabi ya sake sanyawa suka rusuna suka kuma janye,ya budesu lokaci guda yana qoqarin hadiye wani abu,kana yayi qoqarin jan qofar bandakin ya rufe,lokaci guda kuma yana takowa zuwa cikin dakin,yana qoqarin daure fuskarsa.
Motsin nasa yaja hankalin iman,bata damu da rashin walwalar dake fuskarsa ba,saboda tasan cewa bashi da lafiya,qila shine abinda ya kawo qarancin walwalar.
"Sannu ya amin" ta fada cikin nuna tsantsar kulawa
"Yauwa" ya amsa mata a dan dake,saita sake zubawa fuskarsa idanu,yau kadai sai take ga ya canza mata,wani girma da kwarjini da tsahon rayuwarsu tare bata taba gani saman fuskarsa ba a yau take gani,kodon yaune ta fara yi masa kallon qurilla?,ko don yaune kadai ranar da zata iya tunawa ya hade mata rai haka?
"Ina dankwalinki?,me yasa zaki bude kanki gaban abincinmu?,ko so kike ki haramta mana ci?" Yayi maganar still a dake,hannunta ta sanya ta baya ta janyo dankwalinta ta lulluba saman kanta,tun daga sanda ya horar da ita zama da dankwali,mawuyacine ka sameta babu shi,maimakon ya zauna sai ya nufi inda kayan shafarsa suke,ya janyo turaren da yake mulke singalalin hannayensa dasu ya fara shafawar,wannan dalilin yasa komai nashi qamshi yake,komai nasa kana iya ganeshi saboda qamshinsa na daban da yake yawan amfani dashi,abu guda daya cikin rayuwarsa da bai daukeshi da sauqi ba,yana kuma iya sanya ko nawa ne ya siyeshi wato TURARE.
Bayan ya gama ya dauki na jikin ya fara fesawa,cikin lokaci qanqani sassanyan qamshinsa ya budade dakin,iman dake zaune ta lumshe idanunta tana zuqar qamshin har cikin zuciyarta,tana mutuwa da mayatar son wannan qamshin tun ba yau ba,tayi tayi ya siya mata ko ya san mata nashi amma ya gaya mata turaren maza ne,mata kuma basa sanya turare maza,dole ta haqura,take amfani da wanda ya zaba mata,har kawo yau.
Bata ankara ba taga ya iso gaban flask din,ya bude flask din data zuba dan farfesun busashen kifi datayi musu da sauran kifin da malam ya siyo musu tun shekaran jiya waccar,basu iya cinyeshi ba saboda basu da yawa a gidan
"Ka kawo na zuba maka ya amin" ta fada tana kai hannunta da sauri kan kwanukan,saidai cikin rashin sa'a sai hannayensu suka hadu waje guda,saboda ya kawo nasa hannun ne shima don ya zuba,itama takai nata.
Da sauri ya janye nashi hannun,zuciyarsa na wani irin lugude cikin qirjinsa,karon farko itama a rayuwarta data ji wani shock har cikin jijiyoyinta,shuru ya ratsa na second guda,kafin ta rigashi sake maida hannunta tana yunqurin zuba masa,tare dayi masa sannu da jiki,ranta da zuciyarta yana bata cewa yau miskilanci ne ya hadu da ciwo hala,abinda ta jima bata gani ba tattare dashi.
Idanunya ya sauka kan jelar kalbar datayi guda daya,wadda keya reto gefan kunnenta saboda tsahonta
"Da sauqi alhmdlh" ya amsa yana janye idanunsa,tare da lalubar kansa,wai yau din me yake damunsa ne?,kamar yau ne ya fara ganin iman din.
Sosai yayi qoqarin hana idanunsa sake maida idanunsa kanta,saboda ya tabbatar a yau din akwai wani sabon al'amari dake shigarsa wanda baisan dashi ba
"Shikenan yaya?" Ta fada tana sake nannade jelar kalbar cikin yatsanta guda daya tana kuma kallonshi
"Eh" ya amsa mata a taqaice
"Allah ya qara lpy" ta fada tana juyawa zuwa hanyar fita,don ta karanci da gaske yau 'yan miskilancin ne a kusa,ta kuma fi kowa sanin halinsa idan suka motsa masa,idan ya sauko da kansa zai nemi inda take,ita kuma tayita qorafi kenan a sannan,saidai yayi murmushi kawai yace baisan sanda shi hakan ta faru ba.
Baisan ita yabi da kallo ba sai da ta fita a dakin,idanunsa suka sauka kan labulen dake lilawa,saiya dauke idanunsa da sauri,ya zamo daga gefan katifarsu ya sauka qasa sosai yaja abincin gabansa,yanata qoqarin ganin yaci,saidai duk da hakan tunani ne fal ransa.
Yana tuna maganar da sukayi da malam tun yana ajin farko a collage,malam din ya masa kyautar da har duniya ta nade bazai taba mantawa dashi ba,ya shaida masa ya bashi iman din halak malak,ya bashi ita a matsayin matar aure.
Sosai alamin yaji girma da nauyin kyautar malam din,bazaice baya son iman ba,kamar yadda bazaice yanajin soyayyarta a ransa ba,soyayya irin ta aure ba,yana mata soyayya irin ta 'yan uwantaka,saidai shi kansa yasan cewa matsayi ya bata a zuciyarsa bana wasa ba,matsayin da take dashi a wajensa ba na nan kusa bane,saidai koma mene a sannan yana ganin tayi matuqar qanqanta ya tunkareta da maganar soyayya,tunda yaci mata buri da kuma tanadi nayin zuzzurfan karatu,ya karba hannu bibbiyu kuma ya samu zuciyarsa tayi na'am da hakan,saidai ya barma ransa akwai ajiyayyen lokaci da zai fara tunkarar iman din da dasa mata soyayyarsa ta hanyar data dace,ta hanyar da bata kaucewa shari'a tsari da kuma al'ada ba,saboda haka ya nemi alfarmar malam din bayan ya gabatar masa da qudurinsa,ya shaida masa babu komai,shidai fatansa Allah ya sake hada kansu,sai gashi a yau rana tsaka ya soma jin wani baqon lamari game da iman din,tun lokaci bai kai masa Target din da yayi ba.
*1*~ *_KUFAN WUTA_*π₯
_Safiyya Huguma_
*1*~ *_BAQAR INUWA_*π₯
_Billyn Abdul_
*1*~ *_RAYUWAR MACE_*π
_Hafsat Rano_
*1*~ *_MASARAUTA_*πͺ
_Miss Xoxo_
*1*~ *_NOOR ALBI_*β€βπ₯
_Mamuhgee_
Guda 1π300
Guda 2π400
Guda 3π500
Guda 4π700
Guda 5π1k
*_ZAKU BIYA KUDINKU ANANππ_*
Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank
Number shaidar biyaππΌ
*_09032345899_*
*KATIN MTN*ππ
09166221261
*_TEAM ZAFAFABIYAR_**_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*
*_DUK WADDA TASA HANNUNTA TAYI MAN SHARING LITTAFI NA ZUWA WANI WAJE ALLAH YA BIMIN HAKKINA DON ISARSA DA BUWAYARSA_*π€²π½π€²π½π€²π½π€²π½
*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,ZAKI IYA TUNTUBARMU TA WANNAN NUMBERS DIN*
09032345899
Ko kuma
09166221261
06
Daki ta wuce kai tsaye don cire kayan,tana tafe tana hangen fuskarsa cikin idanuwanta,bata taba ganin wanda miskilanci yakewa kyau ba irinsa ba,ba tun yau ba,tun shekarunta basu kai haka ba tasan da wannan.
Sake shanshana hannunta tayi karo na barkatai tana sheqar qamshinsa data dauko wajen saurin bude masa Flask din abincin,saita saki ajiyar zuciya,haka kawai yau din take jin zuwan nata dakinsu wani iri,cikin kasala ta qarasa cire kayan,sai ta zumbula doguwar rigarta kawai,ta dauki littafanta ta tafi dakin inna,saboda yau ta tabbatar babu zancan karatu,tunda amin din baya jin dadi.
Sanda ta shiga dakin innar ta fita dubo amin din nata,babu jimawa ta dawo,tana ta mitar yadda ya dawo ya shiga daki ya kwanta da ciwo a jikinsa bai gayawa kowa ba,motsi kadan sai tambayo sadiqu jikin nasa,bata samu sukuni ba sai data tabbatar da sauqin.
Wani abu daya tsayawa iman din a rai,yadda ta dinga juyi wajen bacci tana hango fuskar ya amin din,sai zuciyarta ta dinga raya mata kodai laifi tayi masa,qamshinsa daya nacewa hannunta ya dinga shiga hancinta,a ranar ta jima tana juyi kafin ta samu bacci yayi awon gaba da ita.
Washegari abokansu na unguwa da wajen aiki daidaiku suka dinga zuwa dubashi,abinda zai baka tabbacin yana da kyakkyawar mu'amala da jama'a,dole inna tasa bayan ya dawo daga makaranta,da zata dora sanwar dare ta qara mudu,ta kammale komai kafin magariba kamar yadda ta saba,ta shiga bandaki tayi wanka saboda zafin da ake dan tabawa,sannan ta shirya ta dawo falo wajen inna sukayi sallar magariba.
Tana saman abun salla tana dakon baqin da suka shiga dakinsu ya sadiq din su fita ta shiga ta dubashi,don da safe da zata wuce makaranta ta samu yana barci,data dawo tanata aiki ga kuma 'yan dubiya,abinda yasa wunin yau gaba daya bata ganshi ba kenan,duk sai takejin babu dadi,take kuma ji wani iri,kamar akwai nisa distance dake shirin shiga tsakaninsu kenan,ta lura tun daga sanda ta shiga js2 yayi bala'in sauyawa,ko wasa da dariya da zaman hira da suke ada yanzu babu kaso casa'in cikin dari,saidai kulawar da yake bata babu abinda ya sauya
"Naji hayaniyar ta ragu,ki leqa kikai musu abincin,nasan halin amin,indai yana ciwo bason abinci yake ba" tsam ta miqe tana gyara yafen mayafinta data yi sallah dashi,sannan ta nufi kitchen ta debi abincin tayi soro.
Da sallama ta cusa kai soron,wata baqauwar murya ce ta amsa mata,matasa ne guda biyu da zasuyi shekaru kusan daya dasu sadiq,daya na zaune saman daddumar da aka shimfida masa saman ledar dakin,dayan kuma na zaune gefan katifar sadiq.
Dan daburcewa tayi kadan saboda yadda taga sun zuba mata ido,sam bata saba cudanya da maza ba,uwa uba kuma ta zaci lamin da sadiq ne kawai a cikin dakin,saita taras da akasin haka
"Yana bandaki,yanzu zai fito" daya daga cikin samarin ya fada ganin yadda tayi turus,saita duqa a hankali ta ajjiye kwanukan,tana samun waje gefe daya ta tsugunna don jiranshi ya fito bayan ta gaidasu.
Shuru yadan ratsa a tsakani,daya daga cikin samarin da tun dazu yake satar kallonta ya fara janta da hira,da qyar take amsa masa tambayoyin da yake mata,qasan ranta haushinsa na kamata,don me zai dameta da wata hira,bayan ita ba itace ta kawota ba?.
Minti kusan takwas sannan ya bude toilet din ya fito,jikinsa da lema sosai,har jallabiyar daya sanya tana mannewa a jikinsa.
Da ita ya fara hada idanu,kowannensu ya janye idanunsa daga na dan uwansa,wani nauyi yau daya taji idanun nasa sunyi mata,rashin fara'arsa ta kwanakin nan gaba ta sauyashi,ta sanya tana jinsa kamar wani baqo a wajenta.
"Ya amin....barka da dare,ya jikin naka?" Sai daya gyada kai yana hadiye wani abu daya tsaya masa na haushi da takaicin junaid,saboda ya lura da irin kallon da yake binta dashi
"Da sauqi alhmdlh..... I hope kinje makaranta?" Yayi mata tambayar dai dai sanda sadiqu ke shigowa da lemukan fanta masu sanyi a hannunsa,sai maltina ta gwangwani guda biyu,dama abinda yaje siyo musu kenan,da zummar idan ya dawo yaje ya dauko musu abincin
"Naje yaya"
"Ma sha Allahu,qanwar saddiq ce da alama?" Junaid ya tambaya idanunsa a kanta yana washe baki,bata amsa ba saiya gyada kai,ta maida idanunta tana kallon yadin mayafin dake jikinta kamar ba bata ba
"Tubarakallah......kina aji nawa yanzu?"
"Js 3"
"Kune 'yan placement na bana ko?" Sai ta sake gyada masa kai kawai,don ta ankara da yadda ya lamin din yayi dif kamar baya dakin,hasalima man shafawarshi yake budewa zai shafa,saidai fuskarshi a dinke take tsaf
"Muje ki lalubi cokula ki bani" sadiq yayi saurin fada sanda junaid ke qoqarin jefa mata tambayar,abinda ya sanyata miqewa sadiq yabi bayanta,duk da hakan sai da junaid din yace
"Kaje ka dawo muyi magan.....ko mu fara da amin kafin ka iso" ya fada yana dariya dariya,daya dan saurayin yana tayashi,suna dan duban amin da suke zaton zai tanka,saidai baice dasu komai ba,hakanan yanayin fuskarsa na nan a dinke,abinda yasa ya musu kwarjini ya kasa maganar dashi,don dama tuni sun dade da sanin halinsu,tun suna 'yan qasa da shekara sha takwas,lamin din ba kowanne yayin magana da shirmen magana yake tankawa ba.
Har sadiq ya dawo da spoon din ya zuba abincin suka fara ci yanayinsa bai koma dai dai ba,yanajin sanda junaid din ke neman izini daga wajenshi ko sadiq din ya gana da iman,domin yace shikam ta gama yi masa,yadda yaketa kodata da yabata yasa wani abu yayi masa tsaiwar mashi a wuya,ya dinga jin kamar ya kai masa naushi a fuska,abinda ya sanyashi miqewa ya fice zuwa qofar gidansu ya zauna saman dakali.
Fayau yau qofar gidan yake,saboda kusan dukkan almajiran malam sun tafi ganin gida,sau biyu dama yake barinsu suje duk shekara ganin gida,su kuma dawo lokaci daya sanda ya sanya musu.
Iskar zafi na kadawa sosai ta wajen,sai ya jingina bayansa da ginin qofar gidan,ya lumshe idanunsa yana sakin ajiyar zuciya,saman harshensa yana jin wani daci daya tabbatar bayan na rashin lafiyar da yayi,harda mugun kishin iman din daya tsinci kansa a ciki.
Baisan ya akayi haka ba,daga jiya zuwa yau gaba daya iman din ta birkita zuciyarsa,sonta ya taso masa da wani irin qarfi da a baya bai taba jin makamancinsa ba,daga jiya zuwa yau kuma da abokansu wajen mutum hudu ke taya iman din sai yaji ya kasa sukuni,shigowarta na qarshe da daddare kawo musu abinci ya sanya yayi mata kallon qurillar daya tabbatar da cewa eh tabbas ta girma ta kuma fara zama budurwa.
Bai dauka cewa girma zai zowa iman din haka gadan gadan ba,duba da yanayin jikin fulani da take dashi,to ashe duk ganinta da yake cikim hijabi yasa yake wannan hasashen,girma da murjewa take ta ciki ba tare da an ankara ba,har ga Allah bazai iya fadan yadda ya dauki bashi itan da malam yayi da matuqar qima da daraja ba,saboda kima da mutuncinsu da yake gani,to amma ya sakawa ransa cewa bazai tunkari iman din da wata magana ta soyayya ba a yanzu,zaici gaba da bata kulawa ne kamar yadda suka saba a baya,har sai ta shiga ajin qarshe ko na kusa da qarshe na kammala secondary dinta.
Tun ba'ayi nisa ba ya gane akwai gyaran daya kamata yayiwa tarayyarsu,kamar yadda suke kusa da juna koda yaushe din nan ya kamata ya janye,ta dinga kallonsa a matsayin yaya da gaske,don tun farkon girmansa ya fuskanci cewa yana da wata dabi'a a halittarsa a matsayinsa na da namiji na yawan sha'awa,inda Allah ya taimakeshi me yawan kamewa ne shi,banda hakan......yadda 'yammata ke mutuwar sonsa.....iya cikin matan dake kawo musu dinki kawai,banda na 'yan ajinsu a makaranta,gefe guda kuma ga 'yan unguwa da sauransu,wannan ya sanya ya sake janyewa iman din,abinda yaketa bata mamaki kenan da taraddadin shin me tayi masa ne?,duk da cewa qasan ransa shima baijin dadin hakan,saidai hakan shine dai dai,kuma zai sanya nutsuwa a zukatan malam da inna,koda basu nuna masa hakan saman fuskarsa ba.
Tsakiyar tunaninsa yaji hayaniyarsu junaid suna fitowa,suka masa sallama ya amsa musu sama sama,ya bisu da kallo sanda sadiq ke taka musu zuwa bakin titi sunata hayaniyarsu irin ta samari,sai ya bisu da kallo har suka dan kaucewa ganinsa.
Ba jimawa yaga dawowar sadiq din,ya qaraso inda yake zaune ya dafa kafadarsa
"Tashi mu koma ciki,wajen na akwai sauro,ko gama warkewa bakayi ba kazo ka zauna ka baza masa jikinka yanata gutsira a banza" yunqurawa yayi ya miqe cikin qarfin hali yabi bayan sadiq din zuwa cikin dakin nasu.
Sunwa wajen kaca kaca kamar yadda akasan yanayin cin abincin maza samari yake,yana jin sadiq din ya buda murya ya fara kwadawa iman din kira,yasan kuma cewa zaiyi tazo ta gyara wajen ta kwashe kwanukan,sai lamin din ya dakatar dashi
"Dakata malam,kuturu ne