Showing 15001 words to 18000 words out of 45207 words

Chapter 6 - Kufan Wuta Book 1 Hausa Novel Complete

kai da bazaka iya kai kwanuka ba?,ni idan na gama zan gyara wajen,daga yau ma banason ta sake kawo abinci indai akwai baqi a ciki,saidai idan kaine a ciki" waiwayowa yayi ya zubawa lamin din ido,ya karanci tsabar gaskiyarsa yake fada saman fuskarsa,sai ya saki murmushi ya dawo ya zauna gefan lamin din

"Duk da cewa bani na kar zomon ba....amma zan baka shawara,kada ka tsaya kallon ruwa kwado yayi maka qafa,diya mace duk yadda kake raina girmanta tasha kan tunaninka,kana mata kallon kamar tayi qanqanta da soyayya,ka gwada mata bayani kaga idan bata dauke karatun ba gaba daya,ni na rasa abinda ma kake jira,an maka kyauta an kuma baka dama amma ka tsaya wani tsari naka?,ka saka kai kawai,Allah ya bada sa'a" sadiq ya qarashe yana dukan kafadar lamin.

Yana cin abincin yana tattauna zancan shi da zuciyarsa,akwai kunya soyayya da yarinya tsakanin mahaifinta da mahaifiyarta,mutanen da yake musu kallon mahaifansa,abu daya ya yankewa ransa,zai fara bata kulawar data banbanta da irin wadda yake bata a baya,zai fara dafa zuciyarta da soyayya ba tare da ya furtata gareta ba,ta yadda da kanta zatayi dako ta kuma zaqu da ranar da zaya furta mata din,saiya saki wani murmushi wanda ya qawata fuskarsa data dan qara haske kadan sabida zazzabin da yasha.


*********Kamar kowacce rana da bata da makaranta asabar ko lahadi,yauma haka ta tashi tayi dukkan wasu aiki na gidan,kama daga shara wanke wanke da kuma dora karin safe.

Ta gama komai tas inna na daga rumfarta tana sallar walha,ta debo kayan data bata din zuwa bakin famfo nan tsakar gida,sannan ta koma kitchen tana goge duk inda ta bata din.

A nutse yake takowa zuwa cikin gidan,sanye da jallabiyyarsa da yake amfani da ita yawancin lokuta idan ba fita zaiyi ba,hannunsa riqe da ledar da mlam ya bashi ya kawo cikin gidan bayan sun gama karatun da sukeyi duk safiya da wurwuri bayan an tashi almajirai.

Kai tsaye ya isa rumfar inna da sallama,ya cire slipper dake qafarsa ya shiga.

Tana zaune saman abun sallah tana jan carbi,fuskarta ta wadata da murmushi sanda ya tsuguna a gabanta yana gaisheta,cike da kulawa ta amsa masa tana sake tambayarsa qwarin jikinsa,duk da cewa ya warware

"Alhamdulillah na warware ai inna,yau ma zan fita aiki in sha Allah"

"Ma sha Allahu,Allah ya qara lafiya"

"Ameen inna...ga wannan ledar,malam ne yace na kawo a dafa masa"

"Tana kitchen ai,saika miqa mata,kace kada ta cika masa yaji da yawa" innar ta fada bayan ta bude taga meye a ciki,ya amsa da to ya miqe tsam da ledar ya nufi kitchen din.

Ta bada hankalinta ga aikin da take sosai taga kamar inuwar mutum cikin kitchen din,abinda ya sanyata zabura kenan,ta waiwayo da sauri,har tsummar hannunta tana faduwa a qasa.

Idanu suka hada dashi,yana tsaye jingine da jikin qofar,ya zuba mata idanu yana binta da kallo,gabanta yayi wani mugun faduwa,kamar karo na farko kenan data taba ganinsa,cikin sanyin jiki ta duqa don ta dauke tsummanta tare da cewa

"Ya lamin.....ka bani tsoro" kusan a tare suka duqa din,shine ya samu nasarar dauke mata tsumman,suka dago a tare,idanunsu ya fada cikin na juna,yadan ja baya kadan saboda sunyi kusanci da yawa,ya miqa mata yana ci gaba da kallonta tare da cewa

"Dama can matsoraciyar ce" idanunta ta janye daga nasa,saboda nauyin da taji zuciyarta nayi,qamshin turaren jikinsa yana busowa zuwa cikin kitchen din,kai bakace baiyi wanka ba,tsabar abotarsa da turare ne kawai,yayi wani fresh 'yar cutar da yayi kwana biyu,sai sumar kansa dake adan hautsine saboda bai gyara ta ba,daga sallah makaranta suka zauna kawai,hakan kuma sai ya qara masa kyau.

"Yaaa banfa zata ba" ta fada da salon shagwabar data saba masa magana a baya,sautin muryarta yaji ya tabashi,ya kuma saukar masa da kasala,ya sauke boyayyar ajiyar zuciya,tare da dora ledar hannun nasa kan kantar da take gogewar

"Barka da safiya yaya,ya jikin naka?" Ta furta tana kaucewa kallonsa,saboda wani yanayi da takeji duk sa'ar data kalleshin

"Alhamdulillah,na warware.....gashi nan,malam yace adafa masa,inna tace karki cika yaji da yawa" a marairaice ta waiwayo

"Yaaya,na gama komi fa,Allah saura wanke wanke,kwanciya nakeso nayi" yadda tayi masa maganar ya sake tafiya dashi,sai ya harde hannayensa a qirji ya zuba mata idanu harta gama,duk da bashi take kallo ba,amma tanajin idanunsa a kanta

"Yanzu idan mijinki yace yanason ki dafa masa abu kamar haka hakan zaki ce?" Banbarakwai taji maganar tasa,fa waiwayo da sauri sai taga ita yake kallo,fuskarsa ta wadata da murmshi

"Inna na miki haka ne saboda tanason ki gina gidanki da kulawa,ki shagwaba mijinki da soyayyar da zatasa ki tsaya masa a zuciya" wata irin kunya ce ta rarrafo ta rufeta,saboda yanayin yadda yake mata maganar kawai ta sanya taji kamar qasa ta tsage ta shige,wannan kuwa ya lamin dinta ne?,magana yake mata da wani irin sound da bata sanshi dashi b,wani irin kallo na daban da sexy eyes dinsa,gaba daya taji kaman ya zare mata laka,sai ta juya tana ci gaba da aikin a hankali,kunya na nuqurqusarta.

Bata ankara ba har ya dauki kwanon dake kusa a ita ya juye kifin a ciki yana cewa

"Tunda raguwa ce ke bari na tayaki" tare suka dawo tsakar gidan,tana wanke wanke,shi kuma yana gyara mata kifin,gaba daya sai ta jita cikin wata takura da bata taba jin irinta ba tsakaninta da lamin din,saboda duk wani motsi ko daga kai da zatayi saita samu tagomashin wani kallo da ta kasa farrasa na meye?,saidai yana sanya zuciyarta karyewa da kuma yin laushi.

Ya sakankance sosai abinsa,yanata aikata mata da kallon da yake da tabbacin zai wuce kai tsaye zuwa cikin zuciyarta ne yayi masauki me kyau,koda bai furta komai a gareta ba,baya da fargaba saboda inna tace zata shiga tadan kwanta,malam kuwa yayi baqi a waje,wanda yasan yawanci idan sukazo sukan dauki awa biyu tare kafin su tafi,sadiq kuwa baida matsala dashi,shi ba baqonsa bane bare yaji kunyarsa.

Kusan tare suka gama komai da ita,sannan ya wuce dakinsu bayan ya sanyata ta saka masa ruwan wanka.


*HILTI UNISEX CHOCOLATE*

*_chocolate ce ta musamman daga qasar TURKEY_*

*_Maganin matsalarki hajiya keda mai gida cikin tsari babu yane yamen magunguna_*

*Ki tuntubi wannan number don k'arin bayani*

0818401745207

*_ZAFAFA 5 NA MIKA GAISUWAR TA'AZIYYA ZUWA GA MARUBUCIYA UMMY AISHA, TA KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION, BISA GA RASHI NA MAHAIFIYAR TA DA TAYI. MUNA FATAN ALLAH YA JIKANTA DA RAHAMA, YA GAFARTA MATA, YA KUMA BASU HAKURIN WANNAN BABBAN RASHI AMIN._*
__________________________________

_SAKINA VENDIBLES_
_SAKINA VENDIBLES_
_SAKINA VENDIBLES_

_(INDE HARKAR TURARUKA NE MASU KAMA JIKI DA GIDAH KAI HARDA TSUGUNNO. SAKINA VENDIBLES ITACE KAN GABA)_

_SUNA DA KAYA INGANTATTU MASU MATUKAR KYAU AKAN FARASHI MAI RAHUSA.)_

_KINASON ASAN KIN ISA MACE? WADDA ZAKUYI GOGAYYA DA MASU SAKA DESIGNER TURARE AMMA KI FUSU KAMSHI? DUK INDA KIKA GIFTA ASAN EH. KEDIN TABANCE , KIN ZARCE SAURAN MATA)_

_AKWAI KHUMRAH WHITE AND BLACK_

_KULACCAM BLACK (FOR HAIR( AND WHITE FOR BODY_

_WASU DAGA CIKIN KAYAYYAKIN MU SUN KUNSHI👇_

Turaren wuta list*
Queens special
Kajiji mix
Kajiji whole
Gabgab
Brown Hawiii
Special Halut
Sandal balls
Sandal strips
Sandal flakes
Dubai oud
White Hawii
Classy Dufr
Black bange
Black bange
Musky Dorrot(Na tsuguno)
Cous cous

*_DA SAURAN SU DA YAWA_*

*_Handles_*
*Instagram* @sakina_vendibles *Facebook*
@Sakina vendible *Tiktok*
@Sakina vendibles_


Tsaye take gaban mudubin nata tana karanto addu'o'i,bayan ta gama shirinta tsaf na tafiya makaranta don zana jarabawar placement,kamar kullum,tayi kyau cikin uniform din da a kullum idan ta saka zaka dauka ta sanyashi ne da nufin gayu ko ado,saidai sam ba haka bane,qirarta ce,haka Allah ya yita,fatarta na daukar kowanne irin nau'in dressing.

Lokaci daya gabanta ya dan fadi,ta kuma lumshe idanunta sanda ta jiyo muryar ya al'amin yana tambayar inna bata fito ba,wannan wani baqon yanayine da bata jima da tsintar kanta a ciki ba,a duk sanda zataji murya ko motsin ya al'amin din.

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tana wara idanunta da suka dauki mintuna a kulle sanda ta tsinci muryar inna tana kiranta,cikin yanayi na me kama da me alhini ko tsoron haduwa da ya al'amin din ta zura takalmanta half cover masu kyau,wanda al'ameen dinne ya siya mata,kamar yadda fiye da rabin komai nata da take amfani dashi na rayuwarta.

Dashi suka fara hada idanu sanda ta fito tsakar gidan,saita sauke idanunta daga kanshi da hanzari saboda yanayin kallon da ya jefeta dashi,wanda shi kansa baisan yayi ba,tayi masa kyau sosai yau din,duk da ya saba ganinta amma yau din kamar an qara mata girma da shekaru,itama cikin ranta take tadinshi,yayi wani kyau cikin shadda light blue daketa qyalli,bisa alamu sabuwa ce kar,yau ya fara sanyata,hakan kuma baya rasa nasaba da daurin auren dan abokin malam din da zashi,wanda malam dinne ya wakiltashi yaje,saboda a jiya shi ya wuce Niger,can dangin inna da akayi mata rasuwa zai musu gaisuwa.

Ko kadan bata zargi kanta kan yadda takejin sauyi da baqunta tattare da ya al'amin din ba,saboda ita kanta tana ganin kamar shima ya sauya,kallo da yanayin firarsu gaba daya ya canzata,bata saba jin nauyinsa ba idan suna hira a baya,tana hira dashi kamar yadda takeyi da ya sadiq,amma a yanzu tanajin akwai wani banbamci a tsakaninsa da ya sadiq din.

Tana qoqarin gaidashi inna ta fara mata fada

"Kinsan yana jiranki zaki shiga ki zauna....."
"Innaaa.....bansan lokaci yayi bafa....girkin nan shi ya cinyemin lokaci" ta fada a shagwabe kamar yadda ta saba,boyayyen murmushi ya kubce masa,abun ya zame mata cikin jininta,ta saba maganarta a haka,abinda ke sake daukan hankalinsa dangane da ita kenan,duk da yana qoqarin boyewa da kuma dannewa
"kaima duk da kai aminu,da tafiyarka,tasan hanya ai,ta tafi da kanta"


Baice komai ba,yadan saki sassanyan murmushin nan nasa,sannan ya matsa inda ta hada komai nata ya sanya hannu ya dauka yana fadin

"Mun wuce inna,daga wajen daurin auren shago zan wuce"

"Ba zaka dawo ka karba abin karin naka ba" sumarsa irinta buzaye daketa qyalli ya shafa da hannunsa

"Ina da ayyuka da yawa ne inna.....akwai dinkin wata amarya da nake,nace mata tazo jibi ta karba,banaso tazo ban gama ba" kai inna ta gyada,ta sanshi da matuqar qoqari wajen cika alqawari,mutum ne shi kaifi daya,mai matuqar qoqarin ganin ya cika alqawari,sam bashi daga cikin jerin layin teloli

"Haka ne,to Alla ya dafa ya tsare mana ku,sai kun dawo"

"Ameen inna" suka amsa gaba dayansu,sannan ya sanya iman a gaba suka fice.


Cikin jikinta take jin kunya nauyi da kuma wani irin yanayi,yayin da shi kuma tunaninsa yayi nisa game da yadda zai tafiyar da koma a tsakaninsu bisa tsari da tsafta,tafiyar sai tazo da sabon salo,saboda ba haka ya saba rakata zana jarrabawa ba,sau biyu tana satar kallonsa,ya ganta sarai,amma sai yayi kamar bai ganta din ba,har zuwa sanda sukayi tsaye a bakin titi suna jiran abun hawa,daga layin cikin layin da yake facing dinsu,wata mata dake sanye da uniform fari da ash,wanda hakan ke alamta ma'akaciyar jinya ce wato (nurse) take tunkaro bakin titin,dukkaninsu sun ganta,har zuwa sanda ta iso titin daga daya tsallaken ta tsaya

"Kamar haka nakeson ganinki.....ina miki sha'awar karatun jinya,ina miki sha'awar ilimi me zurfi"muryar al'ameen wadda ta fara cika da amo na mazantaka a 'yan watannin nan ta ratsa kunnen iman din.

A hankali ta daga kanta ta sanya dubanta ga matar,tun ba yau ba dama ta sani wannan shine burin al'amin din a kanta,ta dade da haddace hakan,kusan kowa a gidan ya sani,don haka sau tari idan suna irin wannan hirar ma babu me ce musu uffan,tsakaninsu ne

"Kiyimin alqawarin zaki cikan wannan burin" cikin mamamki kalamansa ta daga idanu kamar zata klalleshi amma kuma ta kasa,saboda tuna yadda take ji,da kuma yadda idanuwansa ke mata nauyi yanzun a jiki da zuciya

"Bake da kula kowanne irin saurayi,bake ba soyayya" lafazin nasa ya ratsa ta tsakiyar tunaninta ya katse mata shi shi wani sauti mai taushi kuma qasa qasa.

Wata irin kunya ce ta dirarta mata,ire iren maganganunsa kenan da suke caza mata kai,da kuma sake sanyata jin kunya da nauyinsa,maganganun da a baya baya mata su,tadan sadda kanta qasa,qaramin murmushi yana qwace mata

"Eh,wannan ce hanya daya da zaki taimaki cikar wannan buri nawa,ki bari,idan lokaci yayi,ni zan zaba miki É—anÉ—asheshen miji da zai dace dake" qarasa rufeta kunyar tayi,sai ta kare fuskarta da hannunta tana cewa

"Ni ban kula kowa ya al'ameen,kuma ma waye zai kulani nima?,dubeni fa?" Murmushi ne ya qwace masa sanda ya saka hannu yana tsayar musu da wata adaidaita sahu sannan ya bata amsa

"Kina da kyau imani....ke kyakkyawa cw ta ajin qarshe ko farko zance,irin kyan dake jan hankalin kowannw namiji....wanda ke ba zaki gane hakan ba,amma a taqaice,ke sarauniya ce" wanda tun daga ranar ta samu sunan queen daga wajen al'amin,sunan da ya koma kirata dashi lokaci lokaci,musamman idan ya zamana babu malam ko inna a wajen,don ta sadiq dama ya maidashi kamar wani kakansa,ba wai kunya ko nauyinsa yakeji ba,yayin da sunan ya tsayewa iman,yake kuma matuqar yi mata dadi,zuciyarta nata mata saqe saqe akan al'amin din,me yasa ya canza?,me yasa yanzu yake tsaye mata a rai?.

Cikin guntar karatun litattafan hausa data fara a boye ya samu amsoshi da dama,saidai kuma har yau bai furta mata ina sonki iman ba,to hakan meyake nufi?.

*******. ******. ********

Tun dazun data zauna a wajen hankalinta yake rabi da rabi,daya a wajen,daya kuma ya karkata kan jinkirin shigowar al'amin gidan yau,sau biyu tana tura almajiran gidansu suna gano mata rumfar karatu ko yana wajen malam sai ace mata baya nan,tunda ta gama ayyukanta tayi alwalar magariba ta shimfida musu tabarma ita da inna a nan wajen sukayi sallah take saka ran shigowarsa,amma shuru kakeji,gashi har qarfe tara na dare na haramar yi,har sadiq ya shigo yaci abincinsa ya sake fita.

Ta gwada kiransa ta wayar inna kuma sau uku ana ce mata a kashe wayar take,har inna dake jin radio ta rage sautinta tana jajjabin rashin shigowar tasa,wanda bata sauke ba sai ga sallamarsa.

Wani boyayyar ajiyar zuciya da batasan daga inda ta taho ba iman din ta sauke,shi dinma koda ya shigo idanuwansa suna kanta,ta miqe a kunyace a kuma nutse tana gyara daurin dankwalinta tare da qoqarin yi masa sannu da zuwa tana yunqurin karbar ledojin hannunsa

"Yauwa Queen" ya furta qasa qasa yadda innar ba zata jiyo ba,saita saki murmushi tana dora kayan saman daddumar data tashi a kai,inda shi kuma ya qarasa yana zama a kai tare da yiwa inna barka da gida,ta miqe daga kwanciyar da take tana amsa masa tare da tambayarsa dadewar da yau yayi,har tana shirin tura sadiq ya dubosa.

Murmushi yayi yana jin dadin yadda har kullum inna ke nuna masa qauna da soyayya irinbya da da uwa

"Aiki ne yau ya riqeni inna,ban gama musu ba,kuma gobe zasu shigo da safe su karba,na katse ne na shiga kasuwa,shi yasa dinkin ya kaini har dare" jinjina kai inna tayi,tana sake jin qaunar al'ameen din cikin rai da zuciyarta,har kullum shi mutum ne dake sanya cika alqawari gaba da komai a rayuwarsa,ya tsani saba alqawari

"Sannu da qoqari,Allah yayi jagora"
"Ameen inna" .

Iman na daga kitchen tana qoqarin hado masa abincinsa tare da dora masa ruwan wanka take jiyo hirar tasu,ta hada komai a nutse a kuma tsaftace kamar yadda inna ta horar da ita ta fito dashi zuwa inda yake zaunen.

"Sannu da aiki autar inna" ya furta cikin kulawa,ta saki murmushi bayan ta duqa ta aje a gabansa

"Kinga bar abincin nan,zo kiga.....siyayyarki ta tafiya nasreen memorial academy" sosai maganar tayi mata ba zata,makarantar da inna ta kusa dukanta a kanta,saboda yadda ta nace ta kafe tanason makarantar,ita kuma inna ta haneta da zancanta,saboda private school ce da duk term ake biyan kusan dubu goma sha biyar,innan kuma tasan matsawar alamin din yaji tofa sai ya kaita,shi yasa ta sanyata a daki ta ja mata kunne,koda ta sanarwa malam murmushi yayi

"Bansan ko tabarar auta ke damu hajar ba,banda haka.....yaci ace wasu abubuwan zuwa yanzu tafara ragewa,yaron nan hidima da kuma bautar da yake mata ko ciki daya suka fito iyaka kenan,kinyi dai dai,taci gaba da zuwa ta gwamnatinta yadda ta saba,tunda ita takeyi tun tasowarta,kuma tana da basirar gane abubuwa,gashi lafiya lau komai ke tafiya"

Laqwas jikinta yayi sanyi sanda yake fiddo siyayyar da yayi mata yake kuma shaida mata sati me zuwa zata fara zuwa,an gama koma,idanunta suka ciko rau rau da qwalla tana satar kallon inna,tana tsoron kada tace itace ta tusashi gaba ka dole sai ya kaita,ko kuma ita ta gaya masa zabinta.

Ta bangaren innar ma jikinta sanyin yayi,wane irin yaro ne al'ameen din?,ta tabbatar yinin da yayi har dare a shago kudin wannan siyayyar ya hada ya kashewa iman din gaba daya,tabi kayan da ya zazzage din da kallo,litattafai ne tari guda, school bag,takalmi me kyau da 'yan makaranta,biruka da pencils,hatta da uniform din makarantar gashinan a dinke a goge sai sanyawa kawai.

Fada sosai inna ta rufe iman dashi,wannan karon harda al'amin din,kan me yasa zai dinga biyewa iman din da duk abinda tace tana so,ita din 'yar wace da bazata ci gaba da zuwa makarantar gwamnati ba,kamar yadda saura suke zuwa?.

Sosai yaji babu dadi saboda kukan da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login