Showing 24001 words to 27000 words out of 45207 words

Chapter 9 - Kufan Wuta Book 1 Hausa Novel Complete

Kana duban fuskarta zaka karanci ranta a bace yake,saidai hakan wani kyau ya qara mata na musamman,sandin bacin ran nata makara datayi,aka kuma shanyasu a bakin gate har na wajen awa daya cikin rana,wanda wannan shine irin punishment din makarantar tasu.

Kamar ance ta daga kanta saman varander dinsu,ta daga kyawawan blue eyes dinta,idanunta sauka ga malamin,sir arabi,malamin daya takurata tun zuwanta makarantar,da shegen kallo naci da kuma shishshigin shiga harkarta,shike daukarsu darasin turanci wato English,yammatan makarantar da yawa suna yinsa,saboda motar da yake hawa,kana kallonsa kasan ba talauci ko babu suka sanyashi koyarwar ba,saidai ita sam imani hakan bai dameta ko ya dadata da qasa ba,don sam jininsu ita bai hadu dashi ba,ya fiya jin kansa saboda yaga yana tashen samartaka,yana sanya shaddodi da hawa mota,ita sam a rayuwarta batason mutum me jin kansa ma,izza da fadin rai,shi yasa tako ina ya al'ameen yake burgeta.

Yana da wani irin kwarjini gami da aji,uwa uba miskiline naqin qarawa idan baiso ba,hakan yasa baya daukar raini ko izgili,amma sam baida girman kai ko dagawa.

Ta sauke nata idanun tana jan tsaki qasa qasa,gami da qare hade ranta gab da zata shiga cikin ajin nasu,sabida yadda yawanci lokaci irin wannan sanda tazo a makare mazan ajin ke binta da kallo,abinda ta tsana ita kuma kenan,don haka a dake ta shiga ajin.


"keda mutumin naki ne?,na hangeshi tsaye upstair" munira ta fada tana danne dariyarta sanda iman ke zama kusa da ita,tana duba littafin subject din da akeyi

"Shine mana,me shegen kallon tsiya,banason mutum me kallo"

"Tsaurin idanu dai,kwata kwata baki dace irinsa bama,shi bai gani ba kedin kalar matar manya ce" waiwayowa iman tayi sanda take dora littafin saman table dinta

"Kamar yaya?" Murmushi munira tayi tana ci gaba da copying note dinta

"Kamar har yanzu bakisan baiwar kyan da Allah yayi miki ba,ai kyan kyau irin naki ki morewa babban gida,inda zaa jiqaki da kudi da mota,fita qasashen waje babu kama hannun yaro,shine kika mori kyanki,amma ba kowanne irin kalar namijine zaizo ya tsaya gabanki da sunan yana sonki ba" tsaki iman taja,saboda ta dauki maganar munira a matsayin shirme,ta bude littafinta ta fara kwafar note din da sauri da sauri don ta fuskanci ya kusa dawowa ya goge wanda ya fara.

"Am telling you fa,kina ganin kamar wasa ce maganata?,to Allah koni da ban kama rabin qafarki a kyau ba,zakiga kalar mijin da zan zaba"

"Don Allah ki shiru ki barni da bacin ran da yake damuna" dariya muniran ta saki tana ci gaba da rubutun,har zuwa sanda malamin ya kammala yayi musu explanation ya sallamesu.

"Me ya hanaki zuwa makaranta Friday ne?" Iman ta tambayi munira tana maida littafinta jaka,sai data juya manya idanunta,da alama amsar da zata bayar amsa ce da take mata dadi cikin ranta sosai sannan tace

"Kinsan biki muke na wata cousin dita,so ran Friday muka tafi garinmu acan zaa daura aure,kuma ina cikin wanda aka siyawa ticket zasubi flight,kinga ko bazan bari nayi missing ko damata ta wuceni ba,nayita neman number dinki na gaya maka,sai dana fara checking wayana naga ashe bamu taba exchanging numbers ba......ki bani number dinki saboda irin hakan,kinga nama canza sabuwar waya,ranar aka bani gift dinta" munira ta fada tana saka hannunta a aljuhun rigarta.

Kallo daya zaka yiwa wayar kasan cewa bata qananun kudade bace,hakanan sabuwa ce fil sai sheqin sabunta take,munira tabi wayar da kallo sannan ta amsa mata

"Nikam ai bani da waya,ta ya al'ameen nake ara duk weekends nayi game ko browsing" kallon mamaki qarara munira ta jefi iman dashi,harda dan ja baya

"Kina ss 01 amma ace baki da phone iman, jokes apart please,wasa kikemin ko number dince ba zaki bani ba?"

"Tunda baki yarda ba ai babu amfani na dage saina gamsar dake,duk yadda kika dauka hakane"

"Am sorry my friend,Allah na dauka wasa kikemin....amma kuma,ba sani ba wallahi,da dana canza na baki dayar,sai qanina na bawa wanda yake bin me bina" idanu iman ta fidda

"Ni shegiya kaza,ya al'ameen bazai bari ba,amma ina saka ran muna gama wannan term din zai siya min keypad sabuwa in sha Allah,yayi alqawarin idan nayi abun kai zai siyamin" dariya sosai munira ta saki tana kallon iman

"See you don Allah,wani irin keypad?,to ko 'yan aikin gidanmu banjin akwai me keypad,don Allah karma ki fada wani yaji,sai ajinki ya zuba,mazancan da kike jawa aji saisu rainaki,su dauka qaramar yarinya ce ke".

Rai sosai iman ta bata tana dubanta
"To sai me?,ni ina farinciki da duk abinda nake dashi,kuma iya abinda yake ganin ya dace dani kenan,kuma ina farinciki da hakan"

"Wait mana iman" munira tayi saurin dakatar da ita ganin kamar taji haushi

"Nifa ba abinda nake nufi kenan ba,ki fahimceni.....ina nufin yanzu budurwa kamarki,ai ya kamata a sakar miki mara a siya miki waya me kyau saboda gudun raini daga wajen tsararrakinki.....na tabbatar yana da kudin da zai iya siya miki babbar waya,ko yaya ne kaima kayi dan abun xamanin nan da kowa yakeyi" duban munira kawai take,tabbas ya al'ameen idan tace tana so zai siya matan,amma a hakan ma babu lallai su malam su yarda ba,sai tayi shuru bata sake cewa komai ba,saboda isowar wata 'yar ajinsu da tata wayar,tazo munira ta tuttura mata pics da wasu videos,da kadan kadan sai ga masu wayar suna zuwa,sunata sending ma junansu abunda kowa keson sawa a wayarsa.

Tana daga gefe tana kallonsu,kowacce wayar hannunta babbace,wata daga gidansu wata kuma saurayine ya siya mata,ba shakka tana bala'in son waya da maitarta,amma ba zata takura ya al'ameen din ya siya mata sama da wadda yace zai siya matan ba.
[04/06, 4:54 pm] +234 903 165 5683: 11________________

*_Huuuuuum! Idan kaji hanci a sama yayin gittawar mata ƴan ƙwalisa ko shiga gidajensu kasan maganar ta ƙamshi ce_*

*_Ina magana ne aka kayan ƙamshi ƴan gaske ba saka iska ta hure maka ba_*

*_Ina mata ƴan ƙwalisa ma'abota so da ƙaunar ingantattun haɗin turaruka ƴan gaske? To kuzo maza ga dama a tafin hanunku cikin sauƙi da sauƙaƙawa._*

*_Ana siyarda Turarukan Wuta na yan Maiduguri Set na amare. Ana bada sari kuma._*

*_Sannan akwai kayan gyaran jiki. Akwai zumar qiba result cikin 1 week. Turaren daki, jiki, kaya, tsuguno, humra, colacca, turaren wanka, mopping scents, air freshener._*

_Address Kano, Mariri Maiduguri Road. WhatsApp number 07068145252_.

*Sai kunzo🤳🏻*
___________________________________



Tare suka jero da muniran bayan an tashi kamar yadda suka saba,suna tafe suna dan hira munira na tsokanarta

"Nikam kullum aka tashi daga makaranta dalibai basa gajiya da kallonki iman?" Tsaki taja,itama abun yana damunta,don har ta yanke shawarar fara sanya niqabi

"Sai suyita ai,kamar kai dayane mutum,su ba bil'adama bane 'yan uwanka"

"Kin fita daban seriously,shi yasa kike shan kallo" munira ta fadi sanda take nufan wata mota ash jaye da hannun iman,dakatawa iman din tayi tana qoqarin kuma zame hanunta daga na munira

"Ina kuma zaki kaini ga hanyar titi?" Waiwayowa tayi tana dubanta,fuskarta dauke da murnushin nan

"Oops,sorry,na manta in gaya miki,me daukana ya dawo da daukata,dama shike maidani gida indai naje gidan uncle jibril,yawanci ina bin motar haya ne idan ina gidanmu" kai iman ta jinjina tana saita hanyarta zuwa titi

"To sai gobe,Allah yabamu alkhairi" da sauri tasha gabanta

"Ban gane ba,bayan ta hanyar unguwarku xamu wuce,ki shigo don Allah,yana da kirki,zai ajjiyeki unguwarku,cousin dina ne sadam,lokacin tashinmu lokacin ne shi kuma yake komawa gida cin abinci,shi yasa yaje biyowa ta nan ya daukeni mu wuce tare" kai iman ta jinjina

"A'ah fa,zanbi adaidaita kamar yadda na saba" dambu taliya ta kada iman amma taqi,har sau da na cikin motar ya fara mata horn,dole ta haqura tace da ita

"Shikenan,bani number wayar to"

"Idan kin kira amma kice ni kike nema,don ya al'amin ko inna cikinsu wani zai daga,saboda numbers dinsu ne" dariya munira ta saki

"Allah ya sawwaqe,yanzu inda saurayi kikayi haka zaki gaya masa kenan?"

"Ke kika sani,ni bani da wani saurayi ma" da wani mamakin take duban iman din,saidai ta share ta soma karanto mata digit's din tana lodawa a wayar tare sa serving,sukayi sallama tana jajata mata Allah yasa ta samu mota da wuri,saboda sadam ya gaya mata ana wuyar abun hawa yau din,sakamakon taadar da man fetur yayi,da yawa wasu masu ababen hawan sun haqura sun ajjiye abun hawan nasu a gida.

Ta samu tulin dalibai kuwa masu jiran abun hawa,haka nan tabi sahunsu itama,tana fatan su samu da wuri kodon ranar da ake dasawa.


Kusan duk motar da zatazo ta wuce a cike take,wata kuma kafin ta qarasa inda ta tsaya wasu sun shige sun cikata,tana nan a tsaye tsayin wasu mintuna ta hangi kamar gilmawar motarsu munira,sai kuma taga ta tsaya taja da baya ta dawo dab da ita

"Why not ki qyaleta....ba'a dole wajen taimako fa" sadam daya dan hada rai ya fadawa munira

"Qawatace,banason ganinta tana sha ranar nan,kayi haquri minti daya"

"Ok" ya amsa qasa qasa yana jona wayarsa a chargy,munira ta bude murfin motar ta fito ta nufi inda iman take.

Da farko musu taso ta sake mata,sai da taga muniran taji haushi,sannan kuma me motar ya fara buga musu horn sannan ta bita,sanyin ac ya ratsata sanda jikinta ya shige motar,ta maida murfin ta rufe sanda munira ke mita

"Haka kawai ki tsayar da kanki a wannan ranar babu gaira babu dalili,bayan ga abun hawa,ai tsaiwa a ranar nan sai dole"

"Ina yini" tayi qoqarin gaida matuqin motar ba tare data amsa mitar da munira ke mata ba

"Laf....lafiya qalau.... 'yammata" harshensa yadan sarqe,bayan idanunsa sun sauka a fuskar iman dake ciro jakar bayanta zuwa saman cinyarta ta glass din gaban motar,gabansa yadan fadi,ya zuba mata idanu na wasu sakanni ba tare daya iya dauke idonsa daga kanta ba,tunda yake bai taba ganin halittar mace da komai yaji.....ta kuma tafi da imaninsa irin wannan ba,wani irin kyau mai cika idanun me kallo,abinda yasa yadan daburce har ya qara mata da kalmar 'yammata kenan ba tare da ya sani ba,kalmar kuma data dan ja hankalin munira tabi sadam din da kallo,don tasan ba dabi'arsa bace hakan.

Haka kawai ya samu kansa cikin rashin nutsuwar da yake da tabbacin ya fada kogin soyayyar iman ne farat daya,ya dinga satar kallonta lokaci bayan lokaci,har sai da iman din ta ankara,ta kuma tsargu,tare da tuhumar kanta na meye xata shiga motar wasu,koda rana zata kasheta?,sai ya basar,ya fara soko musu hira,yana kuma jan iman din din

"Wanne layi zamu shiga?" Ya tambayi iman din kai tsaye,idanunsa na kanta ta cikin mirror

"Ya isa,anan ma zan sauka" ta fada tana sake gyara jakarta

"A'ah,ai da kin barmu mun cikasa ladanmu ko?" Ya fadi yana dan saki murmushi,munira ma ta saki nata tana gyada kai

"Aikuwa dai"

"A'ah na gode,babu nisa,zan qarasa da qafata" bai sake cewa komai ba ya fara qoqarin faka motar,sannan ya saka hannunsa a aljihun gaban motar ya budeshi,ya ciro wrapper din 'yan dari dari sababbi ya miqa munira

"Bata,tasa kati a waya"
"Ina taga waya,saidai tasha chocolate" munira ta fada cikin sigar zolayar iman tana miqa mata kudin.

Kememe iman taqi amsar kudin,saima ta soma takawa tayi gaba abinta tana cewa sai gobe

"Ni nasan ba zata karba ba,amma ka barni da ita,zan kai mata gobe" tace da sadam,saiya sauke ajiyar zuciya,cikin kasala ya tada motar

"Ban taba ganin yarinyar data yimun ba irin qawarkin nan ba,ki shigemin gaba don Allah na mallaketa" dariya munira ta saki

"Karka damu,indai zaka saki kudi duk ba zaya gagara ba"

"Mayyar kudi,bansan ina zakikai son kudi ba muni" dariya ta sake

"A'ah ya sadam,kudi fa abun sone,babu meson wahala ko talauci,ko aikin nan da kake yanzu ba kudin kake nema ba?". Murmushi yayi kawai,don yasan wajen magana badai a kada muniran ba,gaba daya shi yanzu hankalinsa ya tafi ga iman.


Koda washegari taje mata da kudin makaranta cewa tayi ba zata karba ba wallahi,harda qarin handset daya siya ya dora mata akai,kusan fada sukayi da iman din akan hakan,ita ta dage saita karba,dan uwanta ne,kuma babu dadi maida hannun kyauta baya,yayin da iman din tace sam batasan wannan zance ba,kawai daga haduwa da mutum sai ta karbi abun hannunsa?,tace waye ya bata ma a gida?. Wani kallo muniran tayi mata

"Au daman duk yammatan da samari ke musu kyauta nunawa suke a gida suce wanene ya basu?,kowacce boyewa take tayi amfani dasu abunta,ki karba kawai,don gaskiya bazan iya maida masa ba,don bansan bayanin da zanyi masa ba"

"Ki riqe na baki kyauta tunda ba zaki iya mayarwa ba"
"Bani ya bawa ba,amma zan ajjiyesu har zuwa randa zaki amsa" ta fada cikin bacin rai tana zuge handbag dinta ta jefasu ciki,zancan bikin qawayensu guda biyu dake matsowa da aka zauna yi shi ya raba gardamar,duk da haka muniran bata sauko ba.

Koda aka tashi tun daga bakin gate ta lura da motar jiya ce tazo daukan muniran saita zame ta gudu,ta canza hanya ta shiga motar haya tayi gida,washegari ta dinga mita da qorafi iman din tace da ita

"Kada ma ki soma batawa kanki rai,don Allah bazan sake shiga motar wani a gida baa sani ba" tasan da gaske take idan tayi magana,don haka bata sake cewa da ita komai ba,sai kumbure kumbure da take mata alamun tashi fushi,dariya ta saki

"Kyayi ma ki sauko" amsar da iman din ta bata kenan.


********. ******. ********

A nutse ya ajjiye almakashinsa saman keken da yake kai,sannan ya miqe ya nufo inda iman ke zaune saman wani stool tana fuskantarsa.

Ganin ya dosota saita dauke idanunta a hankali,ya saki qaramin murmushi da ya sake qawata fuskarsa,ya zauna saman wani keken dake daura da ita,ya dora qafarsa daya saman wata kujerar roba da babu kowa akai.

Shagon nasu yanzu babu kowa sai wani dan matashi guda daya daketa faman dinki,da alama masu kayan suna hanya ne,koma bayan sanda ta shigo din da yake cike da matasan,sunata shirin fita wata ball ta abokinsu,shi dinne yace ba zashi ba,don ba wani abokinsa bane na kusa,saboda dama ba mutum ne shi me tara abokai da yawa ba.

"Banfiyason zuwanki shagon nan ba,kina ganin dai yadda kullum yake cike da mutane" dan turo baki gaba tayi

"To ya alameen,idan ka dawo gida inna ba zata bari muyi magana bafa.......kuma lokaci yana qurewa,bikin gaba daya saura uku" idanu ya zubawa lips din da take turowar,kamar ya kama ya tsotse haka yakeji,saiya dauke idanun nasa yana tattara kansa waje guda

"Me yasa baki kirani a waya ba?" Saita fidda idanunta duka a kanshi

"Ka manta ne,inna ta hanani taba wayarta,tace ina qarar mata da kati"

"Haba da Allah haba,ya zaayi ace budurwa kamanki aron wayar inna kike?,ai kinfi qarfin haka,wani idan ya ganki zai zaci babbar iPhone ki manya manyan Huawei kike riqewa" ya fada da salon tsokana.

Kallon da al'ameen ya jefeshi dashi yasanya shi jan bakinsa yayi shuru,kafataninsu sunsan halinsa baya daukar wargi,hatta da ogansu me shagon wani lokaci kamar shakkar al'ameen din yake saboda kwarjinin da Allah ya zuba masa,uwa uba kuma mutum ne shi mai tsaiwa akan gaskiya,idan kaga ya dage kan abu,to idan akayi zuzzurfan bincike shine me gaskiya

"Bani mu gani" ya fada yana miqa mata hannu,sai tabi hannun nasa da kallo daya nannade hannun rigarsa zuwa gwiwar hannu saboda yaji dadin kallo,cike yake da gargasa da jijiyoyin da zasu shaidamaka cikin jikinsa a murde yake,kuma qaqqarfan namijin duniya ne.

Kunya ta kamata sanda ta miqa masa yankin atamfofin guda biyu taga ya janye hannunsa yana jan hannun rigarsa yana rufe hannayen nasa,idanunsa kuma na bisa fuskarta,da alama yaga kallon data bishi dashi kenan.

Murmushi ya saki sanda taja hijabinta ta kare fukarta,yana qoqari yaga ya gujewa duk wani abu da zai sanya taji wani abu tattare da ita,bayason ya raba mata hankali tun yanzu ko yayi cikakken wasa da hankalinta,saidai lokaci yana nan zuwa da zai mantar da ita kowa cikin duniya saishi kadai.

Tana miqa masa ta sauka daga kan kujerar don ba zata iya ci gaba da zama ba

"Qawata zata kawo dinki yaaya don Allah,kada kace aiki ya maka yawa"

"Karta damu,indai ta wajenki ta biyo"

"Saika dawo" ta fada tana masa sallama,bai amsa ba illa binta da yayi da kallo,kominta a nutse kuma a tsare Allah yayi mata shi,yana jin sara qiris ya fara tilastata sanya niqab,yana jin ciwo cikin qirjinsa da zuciyarsa duk sansa ta fita koda makaranta ne,yafi jin dadi da samun nutsuwa udan ya dawo gida ya sameta cikin gidan.

Wani irin shauqinta yakeji yana fusgarsa har ta bacewa idanunsa,ya sauke ajiyar zuciya yana sauka dubansa ga qyallen atamfofin data bashi,ya daga kai a hankali ya dubi matashin daketa aikinsa

"Yahaya......ka dubamin atamfar nan don Allah ka gaya min kudinsu gobe ko jibi"

"An gama" ya fada yana miqewa tare da miqa hannu ya karbesu.

*********. *******. ******

K'arfe hudu da minti ashirin da hudu wayar inna ta kada,iman data kai jug din data hadawa munira lemo kitchen ta dire da sauri ta dawo ta daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login