Showing 15001 words to 18000 words out of 215794 words

Chapter 6 - Ajiya A Duhu Book 2 Complete Hausa Novel

30 Sep 2025

4565

kam ranta fes akan hakan. Burinta Waya yanzu shine Maanal ta dawo sashenta da zama kamar yanda ta zunguri Abah da zancen. Sai dai kamar ya yarda da farko sai kuma taji bai sake maganar ba. Ta Wan bashi kwana biyu ne ta sake zuwa masa da zancen, dan idan ta cika matsawa zai harbo jirgin ta ne kasancewarsa mutum mai tsarta. Ajwaad kuwa data fahimci kauce-kaucen sa zata tattarashi ne ta watsar, akwai gaSar data tanada masa ne. Sun gama tsara Nuratu zatazo nan gidan tai azumi. Acewarsu mamanta zata shirya ta tafi umrah sai ace Nuratun tazo nan ta zauna kafin ta dawo. Gefe kuma cike suke da alwashin bayan salla da sati biyu koda tsiya-tsiya sai an Waura auren Nuratu da Ajwaad idan ba haka ba kuma suyi maganin Oum...
? ? ? Oho ita bama tasan sunai ba. Duk da bata son haWin auren Nuratu da Autan nata bata taSa ji a ranta zatai wani yun?urin hanawa ba. Fatanta ma ALLAH ya daidaita komai ya canja rayuwar Nuratu Win su zauna lafiya da Maanal da shi kansa Ajwaad data san baya son haWin auren nan. Kai ko Mamy gani take bata so dan haka take nuna mata a zahiri. Da yake zuciyar Oum Win a tsarkake take kuma sai bata taSa bin ?wa?w?wafin Mamy akan komai ba sam...

? ? Yau ta kasance lahadi, dan haka Oum ta samu Abah da batun komawar Maanal aiki gobe idan ALLAH ya kaimu. A cewarta da zaman nan gara ta koma aikin sai ta samu nutsuwa sosai. Da farko Abah shiru yayi, dan sai ya dinga hango ai zuwa office Win zai saka Ajwaad yaga ya samu wata dama akan Maanal Win ne. Shiru ya Wanyi na wasu sakanni, sai kuma cikin jinjina kai ya ce,  Okay zan yi tunani akan hakan .
? ? ? Mi?ewa Oum tayi tana masa sallama, dan har yanzu basu koma dai-dai da Abah Win ba. Ta dai daina fushin da take yi da shi. Da kallo kawai ya bita yana murmushi da girgiza kansa. A ransa yace (Fatete na rigima kenan) da murmushin Oum Win Mamy dake da shi yau ta shigo ta samesa. Koda yake tun ma bikin su AA Win Oum tace ta bar mata Abah Win har sai Maanal ta tare. Hakan ba sabon abu bane ga Oum. Dan haka kawai idan ta bushi iska sai tace ta barma Mamy Abahn na sati biyu koma na sama da hakan. Wani lokacin Abahn ne ma ke gajiya ya balbaleta da masifa yace shi bai yarda ba kamar dai yanda ya sakata kwana a gunsa dole randa yayar Mamy ta kwana a gidan.
? ? ? Sosai ran Mamy ya sosu da murmushin nasa, wanda tasan akan Oum Win ne tunda sun haWu a waje. Tarasa ya zata raba wannan sha?uwa da soyayyar, duk da haihuwar da tayi, da kwantar da kai tana musu bauta su duka biyun har yanzu Oum ta fita matsayi da girman iko a wajen Aliyu. Sam baya iya Soye ?aunar da yake mata koda a gabanta ne ita Kamila. Baya shakkar yabon Oum ko sanya mata albarka ko yin kwatance da ayyukan alkairinta. Hira goma zaka zauna da shi zai ambata maka sunan Fateema so takwas ne kansa tsaye. Cikin takaici ta haWiye Sacin ranta ganin ya juyo gareta, a hankali ta maye fuskarta da sassanyan murmushi cike da makirci take tambayar fitar Oum Win wai taga ranta a Sace. Ikon ALLAH sai Abah Win yay nauyin baki yau, dan murmushi kawai ya mata baice komai ba. A ?asan ransa kuwa hankalinsa na'a kan Oum Win ne, bu?atarta yake a jikinsa ?warai da gaske, yana kewar sassanyan ?amshinta da kulawarta a garesa. Badan wai Mamyn bata masa ba ita, kawai dai yana jin na Fateema a garesa special ne. ALLAH shine kaWai yasan irin son da yake ma Fateema da ?auna a rayuwarsa, shiyyasa yake kallon al'amarin Ajwaad da Maanal tamkar nashi da Fateema ne. Dan soyayyar yaran gaba Wayanta tamkar gado ne daga tasu soyayyar, abinda kawai ya banbanta shine shi da Fateema jini Waya ne...
? ?? Haushin ganin ya tafi zurfin tunanin nasa wanda Mamy tai imanin akan Oum ne yasa ta mi?e ta wuce bedroom Winsa. Dan tana fara ganin irin wannan signing Win a garesa a duk lokacin da Oum ta bar mata shi take fahimtar ya gundura da ita hankalinsa nakan matarsa. Tasha zargin kodai Oum tana musu hakan ne dama dan wani tarko nata ko shiri, amma idan ta nutsa a bincike sai ta gano sam ba hakan bane ba..
? ?? Abah ya jima kafin ya dawo daga duniyar tunanin nashi, sai sannan kuma ya farga babu Mamy. Ajiyar zuciya kawai ya sauke ya Wauka wayarsa ya tashi ya fita domin kiran Wan uwansa suyi shawara akan batun Oum Win na komawar Maanal aiki. Wato Uncle Mahmud.....

____________&

? ? ? Kuka bana wasa ba Nurry tasha da jin batun Waga bikinta dana AA har sai zuwa bayan salla. Wani irin tsanar Oum da Maanal ta ?ara faWi da kauri a zuciyarta. Nanfa ta shiga Waukarma kanta alwashi kala-kala na gasama Oum da Maanal aya a tafin hannunsu. Dan ta tabbatar kamar yanda taji iyayenta na faWa makircin Oum ne kawai. Bata sami nutsuwa ba har sai da sukai waya da Mamy da Saheeba da suka kwantar mata da hankali da tabbatar mata aure na nan babu fashi. ALLAH dai ya kaimu bayan sallar da sati guda za'ai ma ba biyu ba.. Sannan a gidan zatai azumi kuma...
? ? ? ? Hakan ya Wan sakata jin sanyi da sassauci a cikin ranta. Harta Wan saki jiki ta cigaba da harkokinta musamman a media. Harda su tsara write-up ta turama ?awayenta da abokan arzi?inta cewar biki sai bayan sallah saboda har yanzu ango babu lafiya.....

___________&

? ? ?? WASHE GARI.

? Safiyar yau Litinin har Oum ta fidda ran Abah zai bar Maanal Win ganin tun jiyan baice mata komai ba. Haka shima AA Win baima saka ran komawar Maanal Win yau ba. Kawai dai ya tashi da nasa shirin ne. Bayan sallar asuba daga massallaci Abah sashen Oum ya nufa. Kasancewar yasan yanzu ita da Maanal ne a Wakin ba kai tsaye yake shiga ba. Dan haka yay sallama bayan yin knocking a ?ofar bedroom Win sannan ya koma falo ya zauna. Babu jimawa kuwa sai ga Oum ta fito daga Wakin sanye cikin dogon hijjabin sallarta. Tunda ta doso shi ya zuba mata idanunsa da suke a narke. Itako sarai data san halin kayanta da gejin da yake kawai na ha?uri da rashinta a kusa da shi sai ta basar kamar bata fahimci magiyar da yake mata da idanun nasa ba. ?an nesa da shi ta zauna, sai kuma ta Wan zamo a kujerar kaWan cike da neman magana ta ce,  Yaya Aliy ina kwana (haka take kiransa lokacin ?uruciya). Hararta yay da faWin,  A'a baba Aliy ba yaya ba. Saboda kina son a faranta ran Wanki zaki ce dani wani yayan gulma .
? ?? ?aramar dariya Oum tayi, amma batace komai ba. Shima fuskarsa da murmushi ya ce,  Kun tashi lafiya? .
? ??  Alhamdullahi .
Ta bashi amsa. Kansa ya jinjina cike da gamsuwa. Kafin ya cigaba da faWin,  Akan maganar ki ce ta jiya. Na bada dama Maanal ta koma aiki, amma da sharaWin driver zai dinga kaita ba Wanki ba. Dan bana son wata ala?a ta haWasu. Ki kuma gargaWesa babu ruwansa da yarinyata a office balle ya takurata, na saka securityn da zan san duk motsinsa akan hakan, idan ya karya min doka kuma zan ?ara yawan kwanakin suspension Win .
? ? Murmushi Oum tayi a karo na farko. Hakama AA da yazo sashen sai dai yana hawowa stairs Win yaji muryar Abah dan haka ya dakata. Idanunsa ya lumshe, tare da motsa lips Winsa a hankali ya furta,  Ayya Abah koba security ba. Badai ka yarda taje ba, ai sai abinda ka gani kawai Aban Maanal . Daga haka ya juya ya koma abinsa domin yin shirin office Win....

? ? ? Oum ma bayan tafiyar Abah Waki ta koma tace Maanal tai shirin office Abah ya bari. Duk da zama waje Wayan dama ya isheta sai taji gabanta ya faWi. Na farko dai tana jin kunya da tunanin yanda zata kalla ?an company a yanzu. Dan tasan dai sun gama sanin ita Win matar ogansu ce a yanzu. Na biyu yaya rayuwarta a companyn zata kasance a yanzu kuma tsakaninta da mai kamfanin. Tunda a gida ya rasa kowace dama a kanta acan da babu idanun Abah kuma fa?.....
? ? ??  Ko baki son komawa ne Baby? .
Oum ya katse mata tunani. ?asa tai da kan nata tana ?a?aro murmushi. Sai kuma ?asa-?asa ta ce,  A'a Oum. Kawai dai ina jin nauyin ?an kamfani ne .
? ? ? Dariya sosai Oum ta sanya da faWin,  Oh oh! Har yanzu dai Babyna na nan da wautarta. Ina ruwanki da su bayan yanzu ke oga ce. Matar oga ai oga ce ko. Tsakaninki da su sai girmamawa ai. Dan haka ki kwantar da hankalinki ki ri?e girmanki, ki ?ara ?wazo da himma akan aikinki. Kiyi abinda ya dace na rike martaba da girmanki domin kare mutincinki dana mijinki. ALLAH yay miki albarka .
? ?? Cikin jinjina kai Maanal ta ce,  Amin ...
? ?? Wanka ta shiga, Oum kuma ta fita zuwa kitchen haWa musu breakfast dan tasan Auta baya wasa da fita akan lokaci, duk da Abah ya kafa dokar ba tare zasu tafi ba tana son Maanal Win ta koyi yanayin fitar tashi tunda na Wan lokaci ne zasu koma fita a taren..

Zuwa bakwai ta kammala komai daya kamata. Ta fito fes da ita cikin Abaya maroon color datai mata matu?ar ?yau da haska chocolate color skin Winta data sha gyaran aure ta sake kwanciya luff-luff. Ga wani ni'imtaccen sassanyan ?amshi dake tashi a jikinta. Sam batayi wani kwalliya ba a fuskar, iya hoda ce sama-sama sai kwalli da Wan lips-gloss kaWan. Dan ko taje girarta ma batai ba. A dining ta zauna kamar yanda Oum ta bata umarni, ta ajiye ?aramar handbag Winta saman table Win dining Win itama. Dai-dai nan shima AA ya shigo, tun kafin su ganshi mayataccen ?amshinsa daya gama manne jikinsa da komai nasa ya iso hancinansu. Yayi matu?ar ?yau cikin Maroon suit shima sai long sleeve shirt fara tas. Harga ALLAH sai da zuciyar Maanal ta Wan motsa. Amma sai ta dake abinta tama fara ?o?arin zuba abincin a ranta tana ?un?unin (wayace ya sake airin kayanta)
? ? ??  Auta har an fito? .
?? Oum ta faWa dai-dai isowar AA dining Win. Kansa ya jinjina mata, tare da kamo hannunta ya sumbata yana mai Wan bata side hug. Sai kuma a ?asa-?asa ya furta,  Barka da safiya my everything .
? ? ? Murmushi Oum ta sake masa, tana mai amsawa da,  Ka tashi lafiya ya ?arfin jikin? .
? ? ? ?  Alhamdullahi Oumna, ai Wanki ya warke sarai in sha ALLAHU  .
? ?  Masha ALLAH haka muke fata ai Auta .
? ? ?? A hankali Maanal data ?i sake kallon inda yake duk da zuciyarta na cike da zumuWi da maradin hakan ta ce,  Ina kwana .
? ? Batare daya kalleta ba shima ya ce,  Lafiya . Daga haka ya kalla Oum a Wan shagwaSe ya ce,  Oum yunwa zata cinye hanji na .
? ? ? ?aramar dariya tayi tana kallon Maanal, itama Maanal Win dai-dai ta Wago ta hararesa. Dan itace ke faWar haka idan tana jin yunwa. Gira Waya ya Wage mata irin (Ni Win kike harara?) sai ta sake murguWa masa baki sannan ta Wauke kanta. Ita dai Oum wurin tai ?o?arin bar musu tana faWin,  Bestynka ta zuba maka abincin zanje nayi wanka ne .
? ? ? ? ? Kamar Maanal zatai kuka tabi Oum da kallo. Sai dai batace komai ba. Sai da ta shige sannan ta Wauke idanun nata. Tsohon minti Waya kafin tace,  Me zaka ci? .
? ? ?? Shiru kamar bazai amsata ba hankalinsa akan waya. Kamar wadda taji haushi ta Wago manyan idannunta ta zuba masa. Kaifin idanun nata da tasirinsu a garesa ya sashi kasa jurewa shima ya Wago lumsassun nasa? ya zubasu cikin natan. Bata iya ta janye nata ba suka shiga ma juna kallo mai taushi da kassarasa kuzarin jiki. Lips Winta ta sake motsawa a hankali batare data raba idanun nasu ba ta ce,  Nace mi kake so? .
? ? ?? Cikin kasala da tausasawa kamar baya so shima ya motsa lips Win nasa ?asa-?asa ya furta,
 Ke! ...........
'?


_Ehemm-eheem nace ba, 1+1 nawa kenan? An bamu assignment ne a makarantar islamiyyar mu ne ni kuma ban gane lussahin ba=? ?=?#?, shine nace bara na tambayeku>???



*_AJIYA A DUHU na kuWi ne, 500 ne kacal, ?ar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. =?O?_*

*09032345899*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=؞?AJIYA A DUHU....=؞?_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??
*_BOOK 2_*


______________


.......Daburcewa taso yi, ta kuma rasa yanda zata fassara amsar ta shi. Cikin suSutar baki ta ce,  Ban gane ni ba! .
? ? ? Wani Wan iskan gajiyayyen murmushi ya saki a iya lips Winsa. Kafin ya sake narke idanunsa dake sar?afe da nata har yanzu.  Kince mezan ci? Me nake so? Nace KE! . Ya faWi (ke) Win da wani kalar sanyin murya yana Wan waro fararen oily idanunsa da ?yau cikin natan. Ai babu shiri ta janye nata zuciyarta na bugawa da sauri-sauri. Sai taji gaba Waya ma jikinta na neman fara rawa. Shi ko tsaf ya fahimci halin data shiga, dan haka ya saki murmushi cike da ?eta. A ransa kuwa rayawa yake (Ba Abanki yace bazai bani ba sai na horu. Kafin na gama horuwar kema sai kin horu yarinya) a fili kam harWe hannayensa yay a ?irji kawai ya zuba mata ido. Ita dai ta miskile tana haWa masa abincin a gabansa. Can ?asan ranta luguden daka kawai zuciyarta keyi, jitake kamar ta zura da gudu, amma bazata yarda ta zubar da kanta a garesa ba...
? ? ? ?  Ehheem! Ehemm!! .
? ? Gyaran muryar Fawzan ta maido AA daya zubama Maanal idanu a hayyacinsa. Janye idanun yay luuu ya maida kansa, Fawzan ya Wage gira yana murmushi. Shima sai AA Win ya Wage masa tasa girar irin (Miye?) Win nan. Dariya Fawzan ya sanya, tare da jan kujera kusa da AA ya zauna. Maanal data Wan rage Waure fuskar da tayi ta ce,  Good morning Yaya F .
? ? ? ?  Morning ?anwar Yaya F, Baby Oum, Autar Abah, sannan kuma Bastyn Besty .?
? ? Duk yanda taso dannewa bai yiwu gareta ba sai da ta saki murmushi tana turama AA duk abinda ta zuba masa, sai dai bata yarda ta kallesa ba. Sai ma hankalinta data maida kan Fawzan ta ce,  Yaya miza'a zuba maka? .
? ? ?  Ai duk abinda kika san yayi daWi zuba min kawai Lilly.
?? Murmushi Maanal Win tai tana jinjina kai. Sai da ta kammala zuba masa sannan ta koma cin nata. Suna gab da kammalawa Oum ta fito, duk da Maanal dama ba wani tana ci sosai bane ba. Oum na fitowa ma ta mi?e kamar wadda ke akan ?aya. Cike da tsokana Fawzan ya hau yima Oum kirari, kafin ya gaidata. Itako tana dariya abinta cike da farin ciki. Sai ga babban yaya da su Naufal dake cikin shirin makaranta. Saheeba biye da su. Suma Oum Win suka shiga gaidawa cike da girmamawa, yaran kuma sukaje suka rungumeta. Itama Nibras ta shigo cikin shirin aiki, da alama ta makara ne. Idonta akan AA ta gaida Oum cike da ladabi, hakama babban Yaya sannan ta juya tana gaida AA Win daya juya yana magana da Naufal. A ta?aice ya amsa mata batare daya juyo ba. Maanal dake karantar yanayin kowa musamman Saheeba da tunda suka shigo taga ta mata wani irin kallo ta Wauke kai a ta?aice ta ce,  Auntys barkanku da safiya .
? ? ?? Babu yanda suka iya daga Saheebar har Nibras Win dole suka amsa. Sai dai kowanne da kalar zafin da yake jin Maanal Win a ransa. Yayinda shigar tata ta saka zuciyarsu sosuwa. Duk da bawani kwalliya tayi ba, babu kuma wani ?yale-?yale a tare da ita kamar nasu. Amma tayi matu?ar yin ?yau mai sanyi. Ga ?amshinta na fita a nutse babu wata hayaniya. Tunda kuma tai musu kallo Waya ta watsar da su a tasu fahimtar. Yanzu kuma ta jefesu da gaisuwar raini. Oho ita bama tasan sunayi ba. Tama maida hankalinta ga babban yaya suna magana...
? ?? Shigowar Abah ta saka kowa maida hankalinsa kansa. Sai Mamy dake biye da shi ri?e da briefcase Winsa. So??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????sai Abah dake kallon zuria'ar tasa farin cikin ya mamaye ransa. A ransa rayawa yake (Nanfa duk mallakina ne, zuri'ata ce. Idan kuma ALLAH yaba Fawzan haihuwa da Ajwaad shima Fadeel aka ?aro masa sai mu sake yawa). Mamy kam zuciyarta ce ta sosu da ganin wahalarta zagaye da kishiyarta. Tayi-tayi ta hana wannan zaman safen a sashen Oum tarasa yanda zatayi. Dan ita inma sun shiga gaisheta sama-sama ne, amma Oum kuwa anan ma suke breakfast wasu ranakun koda matansu sun girka sai su ?i cin nasu sai sun zo nan musamman Fawzan da matarsa ke malalaciya..... Tunaninta ne ya katse saboda gaisuwar da Maanal ke mata. Amsawa tai fiskarta da murmushi, sai kuma ta tsargu da yanayin shigar Maanal Win. Ta Wan saci kallon AA dake tsaye kusa da Maanal gab batare da suma sun farga da yanda suke ba. Dan ya mi?e ne zai amshi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login