Showing 27001 words to 30000 words out of 45946 words
kamota ahankali take takawa harsuka isa mota.
Tana shiga motar ta fashe da wani sabon kuka ahankali ya shafo kanta yana kallon fuskarta dan har lokacin baya iya magana.
Da shaqaqqiyar murya tace,
Nidai ka kaini gida gurin ummana.
Girgixa mata kai yayi dan ganin yake idan ya bu'de baki yayi magana wuta zata iya fitowa sbd wutar bala'in dake cin zuciyarsa.
Ummi ma da ranta ke 6ace dannewa tayi a fuske tace,
Muje akaita gidan idan hankalinta ya 'dan kwanta daga baya sai a dawo da ita.
Har cikin gida ummi takaita gurin ummanta dasai alokacin tasan meke faruwa hankalinta ya tashi matuqa.
Harsuka iso gida bamai iya magana acikinsu.
Tsit palon ba kowa dukaninsu suna 'dakunansu bawai dan basu tashiba saidan babu mai kwanciyar hankali da nutsuwa acikinsu.
A palo ya zauna ya rufe idanuwansa dasuke masa wani yaji yaji tsabar Jan 6acin rai.
Ummi kuwa 'dakin neesah ta nufa tana shiga ta tarar da ita zaune tsakiyar gado ta cusa kanta cikin cinyoyinta ba kuka takeba amma idanuwanta sunyi jajir hakama fuskarta sbd kukan data kwana tanayi.
Kallonta ummin tayi tabbas tanason neesah fiyeda 'yayanta saidai hakan bazai hana tayi mata fa'dan abinda tayiba.
Aneesah"" ummi takira sunanta da fuska a 'daure.
'Dagowa tayi zuciyarta na harbawa sbd ummin bata ta6a kiran sunanta ba.
Juyawa tayi fuska ba walwala tace,
Kizo Palo yanxu kisameni.
Jiki a sanyaye ta sauko gadon ta fito palon.
Tana fitowa ya rintse ido yanajin zafin zuciyarsa na qaruwa.
Jamaal "" ummi takira sunansa bai amsaba ya miqe tsaye tareda rintse ido yace,
Ummi bana buqatar sauraron komai dangane da wannan maganar sbd bana buqatar cigaba da zama da ita and pls ummi karku tirsasani sbd komai zai iya faruwa....
Da sauri Ahmed ya qaraso gabansa zaiyi magana Jamaal ya wanka masa Marika guda biyu a Jere.
Tasowa ummi tayi ta riqe Jamaal 'din
Cikin wani mugun 6acin rai yace,
Kaida ita wlh badan ummi ba saina nuna muku matsayinku.
Idonsa jajir shima ya 'dago murya a karye yace,
Ko yanxu ka nunamin tsayina zan 'dauka koyayane amma dan Allah ka yarda dani karka hukunta neesah ba laifinta bane zan dauki kowane irin hukunci nawa da nata.
Takaici da baqin cikin Ahmed 'din ne suka qara rufesa ya fixgo neesar ya jefawa Ahmed din harsaidata bugu a goshi jini yafara fitowa a hasale cikin karsashi yace,
Kuje can Ku qarata bana bugqatarta bare kai da har abada na cireka cikin jinina.
Kallon Ahmed ummi tayi cikin 6acin rai idonta taf da hawayen baqin cikin dake shirin afko musu tace,
Gskia ne dasa hannunka dumu dumu a 6arewar cikin?
Ido jajir yana kallon neesah dake kukan dake cin ransa yace,
Sharrin she'dan ne ummi amma dan Allah karkuga laifin neesah...wani wawan Marin takaici ummi tasakar masa tana huci kafin tayi baya inna Rabi tai saurin riqeta tana hawaye itama sbd ganin masifar data afkowa gidan.
Rarrafowa yayi yana hawaye murya na rawa kamar zararre yace,
Ure angry ummi and you have every right to be amma
Ummi kuyimin hukuncin komai amma dan Allah kice kar Yaya ya rabu da neesah ummi sonda nake yiwa neesah yakusa zuwa qarshe dan nasan kasheni sonta zaiyi amma bazan ta6a bari tarabu da Jamaal ba, ummi inason neesah,ummi sondanake mata bazai bari nabarta ta cutuba um...
Dukan baqin ciki Jamaal ya rufesa dashi tako ina shikuwa ko motsi yaqi yi sai kallon neesah dake kallonsa cikin wani irin yanayi na shiga zuciya tana kuka ahankali.
Ummi ma kukan take ahankali takasa koda motsi ga jini dake fita ta baki da hancin Ahmed amma har lokacin Jamaal yakasa daina dukansa.
Har lokacin idonsa nakan neesah batasan sands ta matso da gudu ta rungumo kansaba dayayi sharkaf da jiniba ta fashe da kukan sonsa da tausayinsa.
Zuciyarsa ce taqara tunxura da baqin ciki tareda zafin rai ya fixgo qatuwar electric flower verse ya 'daga a hasale zai qarasasu kowama ya huta da azabar zuciya khadija dake tsaye tuni tana kuka kamar ranta zai fita ta qarasoda gudu ta gifta inna rabi ma tuni ta riqesa nan ya dafe zuciyarsa dake shirin bugawa yabar palon yana rangaji dan har lokacin tana rungume da Ahmed 'din da tuni ya fice hayyacinsa hannunsa gam cikin nata.
Jiri takeji da zazza6in tashin hankali amma haka ta miqe da gudu ta nufi 'daki ta 'dauko key zeey dake 'dakin tana leqen komai ta taso da sauri ta kar6i key sbd neesan kanta bazata iya driving ba.
Harsuka fice gidan ummi bata motsaba saima sabon kukan dayazo mata inna Rabi na rarrashinta jiki asanyaye da tashin hankali.
Baya take taredashi hannunta na riqe da nasa duk da itama tuni tafara ganin dishi dishi kafin idanuwanta suka rufe ruf.
Wani shu'umin murmushi zeey tasaki tareda qarawa mortar gudu ta nufi hanyar barin gari.
Tafiyar 5 kilomita tayi daga cikin garin kafin ta gangara daji ka'dan shige gate 'din 'dan babban gidan leloh da yaransa.
Yaran liloh biyu suka shigar mata dasu ciki tabar motar nan takar6i mukullin motar liloh 'daya ta koma cikin gari a guje.
Qofar gidansu ayeesha ta parker batareda tafitoba takirata awaya ta fada mata tana qofar gida.
Ayeesha da tuni dama ta girgije tun bayan barinsu jamaal ta fito cikin Riga da wando black tareda blue facingcap da black speck ta fito riqeda handbag ta fada motar dama zeey bata kashe ba ta Figa da gudu suka bar qofar gidan.
Suna parking motar Habib nashigawo harabar gidan.
Wani kallo yake watsawa ayeesha yana cewa,
Finally dai today is our day of victory.
Cikin farin ciki mara misaltuwa tasaki dariya tareda kar6ar kwalbar hannunta leloh ta kur6a tace,
Yes and all tnx goes to our dearest zeey.
Dariya suka sheqe da ita gaba 'daya suka 'dunguma zuwa palon.
Mamuh💋
🌲 *R H F W F*🐄
_Don't forget to vote, follow and comments_
[8:31AM, 4/9/2018] �?+234 703 593 2228�?: *_DACEWA_*
_(when east meets west)_
_By_
_Mamuh geee_
*_Viawattpad@mamuhgee_*
*48-49*
Ahankali tafara bude idanuwanta dasukai mata nauyi dakuma qirjinta dake mata matuqar ciwo.
'Dakin tabi da kallo taga lafiyayyen 'dakine ta lumshe ido tana jin azabar ciwon kai da qirjinta yana qaruwa.
Dafa bango tafarayi ahankali ta tashi zaune saita hango Ahmed gefenta a yashe bayako numfashi gabanta ya buga nan take komai yadawo mata ta rarrafa kansa ta girgizashi jikinta na rawa hawaye na gangaro mata.
Ko alamar rai bata gani atareda shiba a ru'de ta rarrafa gurin qaramin fridge 'din dake 'dakin ta bu'de bataga ruwa acikiba hasalima ko aiki bayayi ta miqe jiri na 'dibarta ta fa'da mataccen toilet 'din dake 'dakin daqyar ta samo ruwa da alama ma sun dade dan harsun fara canza kala amma bata damuba ta 'debo ta zuba masa a fuska.
Sam babu alamun zai motsa ta qara zuba masa amma bai motsaba.
Jikintane yasaki ta zube gabansa tareda rungumo kansa ta fashe da wani irin kuka mai ciwo da bata ta6ayiba a rayuwarta sbd har cikin tsakiyar ranta takejin sonsa ayanxu.
Kuka take kamar ranta zai fita hartana shaqewa..
Ahankali taji ya motsa kansa yana qoqarin 'dago kansa amma ya kasa.
Dariyar farin ciki da kukane suka zo mata lokaci 'daya ta 'dago ta kallesa hawayen jajayen idanuwanta na tsananta gudu murya a dashe tace,
Ahmed pls don't leave me...
Lumshe idanu yayi cikin azabar ciwon dayakeji daqyar bakinsa ahankali yace,
Anty neesah pls forgive me,
Son danake miki ne yasa idanuwana rufewa harna aikata abubuwa da dama pls forgive me.
Cikin sheshekar kuka tace,
Ahmed na yafe maka amma pls kar katafi kabarni daidai lokacin da zuciyata take tsananin buqatarka.
Lumshe idanu yayi yace,
Ina miki so mai tsani Anty neesah shiyasa ko ayanxu bana baqin cikin mutawa ahannunki saidai baqin cikina zan tafi nabarki cikin tarin maqiya marasa imani su ayee...
Numfashinsane yafara qoqarin sarqewa ga jinin daya qara 6allewa daga bakinsa.
Tashi tayi da sauri cikin tashin hankali tana waiwayensa ta nufi qofar 'dakin ta fita Neman taimako.
Zaune suke suna tattaunawa cikin farin ciki ga kayan drinks da snacks a gabansu..
Habib da ayeesha suke zaune kujera 'daya duk kusan Rabin jikinta cikin nasa
Sai zeey dake zaune ta 'Dora qafafunta kan table 'din gabansu
Leloh ma qafarsa akan table 'din take yana busa sigarinsa tareda korawa da giya.
Zeey ta 'dau remote ta rage volume tareda kallonsu tace,
Guys time na tafiya muyi abinda yakamata kowa yakama gabansa sbd ni da anbi ta tawa datun kafin nazo nan dasu zan Parker motar a daji na kunna mata wuta duk su qone kowama ya huta.
Murmushi ayeesha tasaki tareda hararar Habib tace,
Wannan kwa'dayayyen yace saiya cire kwadayinsa akanta ya muka iya.
Liloh yasaki wata yar iskar daria yace,
Kuma nima saina huta da ita bayan yagama sbd kyawu irin nata bantaba ganinsaba dan haka zan 'dandana na tabbatar idan har ciki haka abin yake.
Koma me zakuyi kuyi dan a qaje nake danaga fitar numfashinta na qarshe bayan nagama ganin kun wulaqanta rayuwarta kunyi mata kaca.....
Idonta ne ya sauka cikin na neesah kafin ta qarasa maganarta ta miqe batareda wani tsoroba ta nufeta tana wani shu'umin murmushi.
Duk iya yanda taso danne mamakin da tsoronta kasawa tayi tafara binsu da kallo 'daya bayan 'daya idanuwanta na ka'dawa da mummunan 6acin rai kafin ta tsaida kallonta kan zeey tanajin wani 6acin rai na shigarta.
Daria zeey tasaki cikin kallon raini zatai magana neesah ta 'daga hannu ta yanka mata wani gigitaccen mari saiga ha6o ya 6alle mata ta 'dago a hasale zatai magana nesaah ta kuma watsa mata wasu marika biyu atare.
Atare dukkansu suka miqe suna kallon yanda idanuwan neesah 'din sukai jajir alamun takai qarshen fusata.
Baya zeey tayi tareda rarumo qatuwar kwalbar giyar leloh ta kwa'dawa neesah a kai tuni goshinta ya fashe da jini.
Sake 'daga fasashiyar kwalbar tayi ta soka daidai cikin neesah daidai nan Ahmed daya taso yana bin bango ya kara kwalbar tayi masa kyakkyawar suka a ciki.
Ihu neesah tasaki tareda 'daga hannuwa ta riqosa lokacin dayake qoqarin zubewa amma taji an damqota ta baya.
Kuka take tana kiran sunansa tareda qoqarin qwacewa sbd ganin ya zube jini na gangarowa daga jikinsa amma har lokacin idanuwansa ita suke kallo bakinsa na motsawa ahankali tana iya gano sunanta yake fada.
Hannu take miqawa ta kamo nasa daya ke miqo mata Habib yafara janta yana cewa,
Yaudai duk wani miyau na saina maida akanki kafin ya yayyagaki mu cinna miki wuta harke har wannan sabon tauraron zuciyar taki.
Janta yake da qarfi yana qoqarin turata 'daki tana ihu tana qoqarin qwacewa.
Lumshe ido Ahmed yayi cikin azaba kafin ya tattaro 'dan qaramin kuzari ya fixgo bindigar wandon leloh daya hango ya harbi Habib saura qiris yasamu neesah sbd hannunsa dake rawar rashin qarfi.
A kafa'da Harbin yasamu Habib ya zube gurin a sume.
Miqewa yayi da qyar ya riqo hannunta yana nunasu zeey da bindigar duk da ba sosai yake ganiba sbd har lokacin jini sosai ke fita a jikinsa.
Qofa suka nufa yana nuna musu bindigar sbd ko mgn baya iyayi.
Mota neesah ta bude Allah ya taimakesu akwai key ajiki zeey bata zareba tashiga seat 'din driver Ahmed ya kalleta ahankali yace,
Neesah kitafi xan taresu harsaikin kai gida just know one thing neesah I love you,ina sonk.....
Shigar bullet 'din da wani yaron leloh ya harbo a gefen qirjinsa ya katse maganarsa
Neesah ta qwalla qara batasan sanda ta qarfi ya shigotaba ta fixgosa daga ciki ya fa'do cikin motar ta fixga da mugun speed sukabi ta cikin gate suka bar gidan.
Mamuh💋
🌲 *R H F W F*🐄
_Don't forget to vote, follow and comments_
[8:31AM, 4/9/2018] �?+234 703 593 2228�?: *_DACEWA_*
_(when east meets west)_
_By_
_Mamuh geee_
*_Viawattpad@mamuhgee_*
*50-51*
Gudu take sosai tana kallon gefensa dayake kallonta da idanuwansa dake qoqarin rufewa yana murmushi jini na zubowa daga bakinsa.
Hannuta 'daya ta miqa ahankali ta kama nasa tana hawaye murya na rawa tace,
I love too Ahmed,, ina sonka har cikin raina so mai tsanani so am begging you not to leave me pls Ahmed., ina sonka...
Saukar harbi taji cikin motar tasu ta 'dago da sauri taga motarsu zeey ce taredasu leloh ta figi motar ta qara gudu.
Harbin motarsu suke tako ina inda ayeesha ta fixge bindigar hannun leloh ta saita kan neesah tana cewa lets finish this today.
Harbowa tayi Ahmed ya yunquro da 'dan qaramin kuzarinsa ya tare bullet din ya sauka a tsakiyar bayansa.
Wani wahalallen nishi yasaki tareda zubewa jikinta.
Sakin motar tayi tareda rungumosa tana rintse ido tace,
Let's die together my Ahmed.
Daji motar tafara gangarawa dasu Wanda hakan yafara Jan hankalin motocin dake wucewa suka fara tsayawa da sauri su leloh suka tsaya daga nesa dan kar agane su suka biyosu.
Wani qaton rami motar ke qoqarin fa'dawa bayan tafara kamawa da wuta Ahmed ya tattaro wani qarfi ya tura 6an6areta jikinsa tareda turata waje da qarfi ta window riqe hannunsa tayi tana ihu tana kiran sunansa ya kalleta a wahalce yace,
Neeees'''bai qarasaba sulbin Jinin hannuwansu yasa ta sulbuce daga hannusa ta ganngara gefe kanta ya daki wani qaton dutsi nan take ta sume motar ta fa'da tareda kamawa da wuta sosai.
Ajiyar zuciya suka sauke kusan duk atare ganin yanda wuta kecin motar sun tabbatarda bamai Rayuwa tsakanin neesah da Ahmed.
Kallon zeey ayeesha tayi cikin samun wani cikakken kwanciyar hankali tace,
Finally I got all I ever wanted.
Cikin taya aminiyarta farin ciki tace,
Well then lets all wish you a happy married life wit your captain,,you alone.
Juya kan motarsu sukayi suka bar gurin hankalinsu a kwance.
Aliyu mamman aliyu shine babban aminin Ahmed yana kawowa gurin yaga daidai lokacinda motar ke qoqarin fa'dawa rami yakuma tabbatarda motar neesah ce ya fito motarsa da sauri amma kafin ya iso motar ta fa'da tareda kamawa da wuta amma yaga lokacin da neesah ta gangaro ta daki dutsi.
Gurinta ya qarasa da sauri ya 'daukota yana kallo motar ta cinye tas da wuta ga amininsa aciki duk da kuka yake sosai kamar qaramin yaro.
Motar police ce tareda tasa suka 'dauko gawar Ahmed daya qone qurmus bayan an kashe wutar tareda neesah dake sume kamar gawa suka nufo cikin gari.
Asibiti suka fara kai neesah tareda barin 'yan sanda biyu gadinta kafin suka nufi gudansu Ahmed da gawarsa Wanda isarsu yayi daidai da isowar dady daga tafiyarsa.
Koda aka ciro gawar gaban dady aka bu'de saura qiris ya zube saida aliyu yayi saurin tarosa daidai fitowar Jamaal sbd jiniyar dayaji tashigo har cikin harabar gidan.
Gabansane yayi mummunar sarawa yayi saurin dafa motar sbd mahaukacin jirin daya 'dibesa.
Xubewa yayi gaban gawar tareda dafe kansa hawaye suka gangaro daga idanuwansa a karo na farko arayuwarsa tun tashinsa baita6a koda hawaye ba bare kuka sai yau dayaga gawar Ahmed.
Rawa jikinsa keyi sosai kamar qaramin yaro ko mgn yakasayi.
Khadija ce tashigo harabar gidan cikin motar ta tun kafin tai parking jikinta yayi masifar sanyi ganin kamar gawa gabansu dady tanayin parking ko key bata tsaya cirewaba ta fito da sauri jikinta na rawa.
Cak ta tsaya gaban gawar tareda qurawa gawar ido tagano tabbas Ahmed ne duk da ya qone sosai amma ta gane shine hannu ta 'dora akai tareda sakin kuka mai qarfi ta zube a qasa.
Inna Rabi ce ta fito da hanxari jin ihun khadija
Itama wani qaqqaran salati tasaki tareda fashewa da kuka ahankali.
Duk da tana cikin tsananin damuwarda ko motsi bata son yi sbd azabar ciwon kai dake damunta haka ta miqe jin hayaniya harabar gidan gashi inna Rabi data leqa bata dawoba.
Turus ta tsaya ganin gawa ga khadija daketa kiran sunan ahmed 'din tana kuka kamar ranta zai fita.
Jiri me qarfine ya 'dibeta tayi baya Jamaal ya dago tsalle ya tareta ta rintse idanu saiga hawaye sun 6alle masu qarfi sbd sobon son Ahmed 'dinta da wani mugun tausayinsa da kewarsa dasuka rufeta lokaci 'daya ta fashe da kuka ahankali mai shiga rai tana tunanosa.
Duk iya tashin hankali iyalan gidan sun shiga dan kowa kuka yake sosai sbd Ahmed 'din abin son kowane.
Har aka shiryasa aka rufesa aka dawo bamai iya magana sbd sosai mutuwarsa ta ta6a kowa na gidan musamman ummi data zabge lokaci 'daya ga wani irin ciwo da zuciyarta keyi.
Har washe garin rasuwarsa neesah bata farfadoba sbd likitoci sun tabbatarda sosai ta bugu akai.
Mamynta datazo ita ke jinyarta sbd inna Rabi ayyuka sun mata yawa na mutane dan gidan kusan acike yake sosai da mutane.
Sai ranar daza'ayi adduar uku ta farfado tana ihu tana kiran sunan Ahmed kamar zararra.
Daqyar aka samu ta saurara sbd allurar da akai mata ta kashe jiki.
Lamo tayi jikin mamy hawaye nabin fuskarta amma tanajin ra'da'di da zafi a zuciyarta amma ko juya idonta bazata iyayiba bare ta motsa sbd allurar da akai mata.
Duk iya yanda aka tsammata daga gareta alamarin ya wuce nan dan sosai
Zabure zabure takeyi duk lokacin da allurar tasaketa harsai ankuma yimata wata.
Cikin kwana 'daya tashin hankalinsu ya ninku bayan na rasuwar Ahmed sbd sabon alamarin dake tattareda neesah,
Kallo 'daya zakai mata tabaka matuqar tausayi sbd yanda ta yamutse ta rame kamar wadda tayi jinyar shekaru gashi kowane lokaci yanxu cikin bacci take sbd allura da ake mata koda yaushe sai hakan ya ta6ata matuqa dan wani irin haske da yellow yellow tayi kamar mai wani ciwon.
Kuka mamy keyi sosai sbd tsaf tarigada tagama hango ta6in hankali atattare da neesah ga rashin abinci da ciwo dake cin qwaqwalwarta sun sauyata sosai.
Doctors biyar ne suka taru suka duba result 'din hoton qwaqwalwarta suna jinjina alamarin.
Babban Consultant 'din cikinsu shiya 'dago ya kalli Abba da dady sai Jamaal dake gefensu tsaye shima duk ya rame yayi wani 'dan haske yace,
Well alhaji I'm really sorry to say this but a iya qwarewar bincikenmu mun gano buguwar da kanta yayi tareda mummunan firgitar rasa wani ko tsoron wani yasa qwaqwalwartata yanxu bazata iya aiki daidaiba saidai nan zuwa da 'dan wani time idan komai yafara ragewa daga firgicin datake cikin by god grace muna sakaran everything will fall to its normal place saidai yanxu kada a ringa matsa takurata sosai da tambaya ko kuma wani Abu dazai firgitata.
Ajiyar zuciya suka sauke atare Abba yayi masa godia suka miqe suka fito office 'din jiki ba qwari.
Tunda Jamaal yadawo gida ya kwanta a kujerar palonsa yakejin nauyin qirji Sam ko bu'de idanuwansa baya sonyi sbd Jan dasukai tun ranar da komai yafaru har rasuwar Ahmed dakuma ciwon neesah yakejin kamar zuciyarsa zata buga sbd komai ya qara shige masa duhu babban abinda yafi 'daure musu kai shine harbin bullet biyu dasuka gani ajikin Ahmed 'duk daya qone amma saida 'yan sanda suka gano kuma sun 'dauki hotunan guraren domin gudanar da bincike amma yanxu neesah da itace only hope 'dinsu itama tasamu ta6in qwaqwalwa.
Ayeesha ce da tun washe garin ranar rasuwar tadawo tana kukan munafurci Wanda ko kallo bata ishi ummi