Showing 24001 words to 27000 words out of 45946 words
tareda harde hannuwa yana kallonta ta cikin mirror.
Aje turaren tayi ta miqe zata bar gurin ya towel 'dinta
Tai saurin dafewa tareda 'dagowa rai a6ace zatai magana saijin tayi bakinta ya sauka kan nasa sbd fuskarsa dake daf da tata.
Zaro idanuwa tayi tareda matsawa baya da sauri tareda tamke fuska sbd wani lazy smiling dayake sakar mata yana kallon tsakiyar idanuwanta zuwa pink lips dinta.
Qara tamke fuska tayi ganin kallon nasa na neman sauyawa.
Wardrobe ta bude ta jawo doguwar riga tana juyowa still sai a jikinsa sbd ya kuma matsota sosai.
Ahankali ya shigar da ita jikinsa ya rungumeta tsam tareda sakin ajiyar zuciya a ciki.
Qoqarin qwacewa takeyi amma ta kasa saita lafe itama tanajin faduwar gaba da tsoro na shigarta Wanda ta rasa gane na meyene.,
Hawayen datake 6oyewa suka gangaro mata batasan sanda tasa hannu ta qanqamesa ba.
Rintse idanuwa yayi tareda shafa kanta haka kawai shima yakejin fa'duwar gaba da damuwa mai tsanani na shigarsa.
Murya can qasan maqoshi yace,
Am going back neee,
Do you need or want sumthing?
Batace komaiba saima hawayenta dasuka 6alle.
Shafa kanta ya qara tareda 'dago fuskarta yana kallo ta rintse idanuwanta hawaye na cigaba da gangaro mata.
Saukar light kiss taji a lips 'dinta tareda sakinta ya fice 'dakin da hanzari.
Koda ya fito ayeesha na motar Ahmed na jiransa ya fa'da suka wuce xuwa airport.
Zubewa tayi bakin gado tareda toshe baki kukanta na fita ahankali sbd haka kurin tsoro da fargaba ke shigarta.
**********
Tunda suka tafi ta qara zama wata iri sbd ta rage zaman gida sosai kullum a school suke yini ita zeey sbd yanxu su zeey babu wani tuggu tunda kusan sun samu yadda suke so sbd ayeesha na can tareda Jamaal 'din.
Plan 'daya suka tsayar shine suna dawowa zasu ha'da mata wannan tarkon da dole Jamaal zai tsaneta had abada bazai kuma ko kallon mai sunantaba.
A 6angare 'daya tsananin tausayi da qaunar Ahmed ke shigarta sbd gaba 'daya ya susuce baida wata damuwa saitata,
Baya iya koda cin abinci duk ranar dayaga damuwa ko hawaye a fuskarta,
Duk wani farin cikinta shine nasa hakama kullum cikin kyautata mata yake duk ya rame sbd a 'yan kwanakin wata irin wuta da ciwo dayakeji suna cin zuciyarsa akan neesah amma yaqi yake sosai da zuciyarsa ganin bai furta mataba ko nuna mata alama sbd Sam bazai juri ganin damuwa a fuskarta ba dan yasan tabbas zata shiga wani yanayin matuqar ta gane.
Ummi ma sosai take tausawa 'danta sbd tana lure da komai kuma tana hango tsananin damuwa daciwo a idanuwansa
Duk lokacin data zaunar dashi ta tambayesa meyene damuwarsa saidai ya kwantar da kansa kan cinyarta yafara hawaye yace ummi kiyimin addua qila mutuwa zanyi sbd nikaina banajin da'din komai a duniyar yanxu.
Khadija ma dai ciwo ya tsanantar mata kuma Dr ya tabbatar mata da ciwon zuciyane yai mata mugun kamu dan haka yanxu a 6oye take siyan magani tanasha a 6oye amma Sam baya aiki sbd kullum da sabuwar qiyayyar matar jamaal ayeesha da hassadar neesah take kwana take tashi.
****
Tunda suka iso qasar ta rasa gane komai sbd Sam bayada time 'din zama gida kullum yana gurin aiki ga wani irin sabon miskilanci dake cinsa yanxu,
Abin na damunta amma daga baya data gane kukane bayason kuka tausaya mata yake idan ta fara saita koma kullum saitayi kuka
Tunda ga time 'din ya rage komai yana zama ya 'danyi wasan soyayya da ita har shopping da sauran guraren shaqatawa suna zuwa tare dan haka tuni yayi wani fresh sbd amarci da angwancewa da yayi duk da dai ba wani dacewa yayi ta hanyar making love da ita sbd Sam bata cikin jerin mata masu ni'ima duk da takawo budurcinta.
Haka suka cigaba da zama kwatsam saiga ciki ya bayyana.
Tashin farko da Dr ya sanar da ita tanada ciki yanka masa mari ne kawai batayiba sbs baqin ciki dan idan da akwai abinda ta tsana bayan neesah da Ahmed to yara ne bare ace wai ita da kanta zata haifesu.
Baro asibitin tayi bayan ta biya wani babban pharmacy ta siyo *****pills 3 sachet sbd batajin zata iya qara koda kwana 'dayane da cikin bare har Jamaal yasan tanada wani banxan ciki.
Tana isa gida kiran zeey nashigo wayarta saidata 'zauna ta 'daga wayar murya a cunkushe.
Lafiya dai Mrs cpt?
Saidata qaramin tsaki tace,
Inafa wata lafiya yanxun nan daga asibiti nake, can you imagine wai nice da ciki?
Wlh yau baqar ranace agareni dan Allah ji nake kamar na zaroshi na watsar a zinc.,
Cikin yanayin takaici itama zeey tace,
Gskia kam yanxu wayaketa wani ciki alhalin ko 'duwawuka baki gama bajewa a gidanba tunda haryanxu tsinanniyar na nan.,
To yanxu me kika yanke akan hakan?
Na riga na siyo magani zubar da sh***ge kawai zanyi yau 'din nan basai gobeba.
Kafin zeey tayi mgn taji qarar doorbell ta miqe ta bude masa tareda 'dan hugging 'dinsa kafin ta juya ta shiga bedroom suka cigaba da waya.
Zama yayi a palon yana qoqarin zame takalminsa ya hango envelope da sunan asibiti ajiki cikin hanbag 'dinta data bari palon.
Wat ya fada da qarfi cikin wani mugun farin cikinda baita6a yi ba arayuwarsa lokacin daya gama karanta result na cikin datake 'daukedashi.
'Dakin yashiga ba zato taji ya rungumeta tareda bata wani lafiyayyen kiss sbd nan take wata irin muguwar soyayyarta da abinda ke cikinta sukai masa muguwar shiga.
Zamewa tayi tana masa kallon mamakin farin cikin dake fuskarsa dan rayuwarta bata ta6a ganinsa cikin farin ciki hakaba.
Result 'din ya nuna mata yana qara kai mata kiss a wuya yace,
Thank you my eshaa.
Qaqalo murmushi tayi tareda zamewa baqin ciki cikin ranta kamar ta rufesa da duka.
Miqewa yayi yakoma palo yana cewa,
Lemmi share this happiness wit my ummi sbd nasan abinda take farin cikin samu tuntuni kenan.
Yana fita ta 'dago wayarta ta mayar kan kunne sbd har lokacin zeey bata kasheba.
Wani shu'umun murmushi mai sauti zeey tasaki tareda cewa,
Qawata lakacin dawowarku yayi sbd wannan damace dazamu jefi tsuntsu biyu da dutse 'daya.
Tunani ayeeshan tayi tareda sakin wata muguwar qaramar dariya tace,
Tabbas ciki zai zube neesah zata kar6i igiyoyin aurenta uku a hannunta.
Dariya zeey tasaki tace,
Hahhhhh lokacin damuka da'de muna jira gashi yazo a cikin sauqi domin matuqar cikin nan ya zube ba Jamaal ba ka'dai har ummi saita tsaneta hmmmnn wat a great and best plan.
Mamuh💋
🌲 *R H F W F*🐄
_Don't forget to vote, follow and comments_
[11:53AM, 4/10/2018] �?+234 703 593 2228�?: *_DACEWA_*
_(when east meets west)_
_By_
_Mamuh geee_
*_Viawattpad@mamuhgee_*
*44-45*
Zaune suke a palo ummi na kallon wata drama a tashar cwtv
Itakuma neesah kwance take jikin ummin tana chatting da amirah,
Khadija ma tana palon zaune tana chatting sama sama sai inna dake kicin tana aikin abincin dare.
Wayar ummin ce tayi ringin tana dubawa taga Jamaal ne tai answering idonta nakan tv.
Wani farin cikine ya mamaye zuciyarta da fuskarta lokaci 'daya jin abinda ya fada mata bayan sun gaisa.
Cikin hamdala tace,
Yanxu dai ina fatar dai batajin matsala ko damuwar kowa komai ko?
Eh yace ahankali tareda miqawa ayeesha data fito wayar danta gaisa da ummin.
Hello ummi ina wuni?
Lpia klau ayeesha ina fatan dai ba wata matsala dakikeji ko?
Ahankali tace,
Eh ummi kawai dai inason nadawo gidane sbd abubuwan danakejin inason ci babu su anan 'din.
Hankali kwance ummi tace,
Dan wannan kam dole adawo dake sbd ma samun cikakkiyar kulawa.
Murmushin jin 'dadi tayi tana cewa,
Nagode ummi.
Yana kashe wayar ya jawota jikinsa yana kallon tsakiyar idanunta yace,
Gida kikeson zuwa?
Cikin sigar shagwa6a ta 'daga kai.
Gyara mata zama ajikinsa yayi tareda lumshe udo ahankali yace,
Zan maidaki gida tunda babyna nason zuwa gida.
Tunda ummi tafara waya khadija ta 'dauke wuta sbd ta fahimci inda zancen ya dosa murya na tsananin rawa tace,
Ummi matar yaya Jamaal ce keda ciki?
Cak neesah ta tsaya daga abinda take sbd jiran amsarda ummin zata bayar.
Fuska 'daukeda murmushi tace,
Eh Allah ya kawo dawowama zatayi nan sbd kyakkyawar kulawa.
Cak kowaccensu kuzarinta ya tsaya neesah miqewa tayi ahankali ta nufi bedroom 'dinta ta rufo qofar
Khadija kuwa duk iya yanda taso danne hawayenta kasawa tayi saida suka sauko tai saurin miqewa gudun kar ummi tagani ta nufi 'dakinta itama ta rufo suka bar ummin nabin qofofin 'dakunansu da kallon mamaki na zallar kishi data hango daga yanayin kowaccensu..tirqashi ta fa'da aranta tana jinjina kai.
Sati biyu da maganar saiko gashi sun dawo batareda zato ko tsammanin zuwansu ba dan lokacin ummi ce kawai sai dady daya dawo yana gari.
Khadija taje asibiti sbd ciwonta da yayi tsanani dan har wani kakin jini take wani lokacin,
Neesah kuwa tana school tun safe.
Cikeda farin cikin ganinsu ummi da inna Rabi suka hau hidimarsu dan tuni ayeesha tafara qirqirar tanason wannan batason wancan
Dan hakama ko yanxu bayan sun huta dawowa tayi gurin ummi tace inna Rabi tayi mata wainar filawa me kwai da cabbage aciki.
Jiki ko na rawa akayo mata ta zauna bawai dan tanasoba sai dan kawai ta qara saka soyayyar cikin acikin zukatansu yanda zasufi jin zafi idan wani abu yafaru.
Khadija ce tafara dawowa tana ganin ayeeshar zaune a palo tana cin wainar ta 'dauke kai gabanta na faduwa ta gaida ummi a sanyaye harzata shige 'daki ummi tace,
Khadija bakiga ayeesha bane ko sannu da jiki bazakiyi mata ba?
Ha'diye wani yawun kuka tayi batareda ta juyoba tace,
Ina wuni?
Ya jiki?ban lura bane ummi.
Tana fadin haka ta fa'da dakinta ta rufo qofa.
Sai da maraice tadawo agajiye take ta matsu taje ta cire hills 'din qafarta.
Kamar ance ta duba gefen part 'dinsa saita hangosa a tafe yayo wanka cikin qananun kaya black trouser da dark blue shirt,
Ya qara fari sosai sai 'yar qasumbarsa dake kwance luf tayi duhu ga wani qyallin fresh da fatarsa keyi.
'Dauke kai tayi tareda tamke fuska tashige palon.
Kallo 'daya tayiwa ayeesha ta 'dauke kai zuciyarta na mata nauyi Sam ko gefen bata sake kalloba bare tasan da ummi a palon ta fa'da bedroom 'dinta da sauri.
Koda yashigo palon direct bedroom 'dinta ya nufa
Koda yashiga tana toilet kawai saiya zauna kan dressing chair din gaban mirror ya lalubo wayarsa a aljihu yaji yabarota part 'dinsa sai kawai ya 'dauki novel 'din dake kan mirron mai suna _the prince of chikago gambler_ yafara dubawa.
'Daure da towel ta fito batada wani kuzari dan tunda taga ayeesha ta rasa kuzarinta saima zazza6i dake qaqarin kamata.
Sam bata lura dashiba saidata kawo daf dashi tai saurin matsawa baya tana ha'de rai dan mugun zafinsa takeji haka kawai.
Murmushin gefen baki yasaki tareda aje book 'din ya miqe tsaye yana kallon 'daurariyar fuskarta yace,
Well tunda naga bakiyi murna dazuwana ba I think qofa itace hanyana yanxu so saki fuskanki ni kaina inada abinyi agabana.
Ra6ata yayi ya fice batareda ya ko waiwayotaba sbd Sam ya tsani halayenta na ko inkula da girman kan da bazai bari tayiwa mutum kallon arkiqi ba koda so 'dayane.
Ranta ne ya qara 6aci tabi qofar daya fita da kallo yazo nan be kawai dan ya ca6amin maganar 6acin rai ya fita.
Zubewa tayi bakin gado tana jinjina alamarin cikin matarsa dan tasan ko ummi zata iya yin komai akan cikin sbd yanda take hango tsananin soyayyar datakewa cikin sbd soyayyar Jamaal data shafesa.
Tundaga ranar ya daina shiga harkarta sbd ganin ta kama kanta da kowa a gidan qarshema bata yini a gidan sai school shiyasa shima ya shareta ya maida hankalinsa gurin kulada ayeesha da kullum yanxu ke fama da ciwon mara kadan kadan.
Yau tun safe ayeesha tafita da cewar gidansu zata ta yini.
Shine yakaita bayan yashiga ya gaida ummanta da dadynta ya fito
Daf dazai bar layin gidan motar Ahmed tashigo layin ya qurawa motar ido sbd ganin mace aciki,
Daf dazasu giftasa yaga qawar neesah ce zeey zaune gaban motar.
Mamakine yakamasa sosai na ganinsu atare batareda neesah ba kuma a layinsu ayeesha.
Tafiyarsa yayi tareda sanya hakan cikin tattalin bincikensa akan Ahmed.
Suna pakawa zeey takira ayeesha a waya saigata ta fito tashigo motar tazauna tareda rufewa ta kalli Ahmed a gaggauce sukayi mgna ta fita sukuma suka wuce.
Da maraice ti6is tadawo tareda zeey data biyota zata kwana a gidan.
Bayan sunci abincin dare harsunyi wanka zeey tace,
Neesah pls kiban aron wayarki mana zan 'dan kira mumy naji kosun isa kano lpia.
Duba wayar tayi har cikin hand bag 'dinta bata gantaba tace,
Inajinfa nabarota a mota.
Lah kinga natuna ba Ahmed naga ya kar6aba dazu,,,
Yes hakane bari na karbo sbd kinmaga natuna zanyi waya da mamy.
Miqewa tayi itama tana cewa muje na rakaki.
Ayeesha dake zaune tareda Jamaal a balcony tana hango fitowarsu ta miqe tareda zuwa 'daki ta dauko ledar kaya tace,
My captain yaudai ga Anty neesah can nasamu gani bari nakai mata tsarabar danayo mata.
Batareda ya 'dago daga aikin dayake a iPad 'din hannunsaba yace,
Ummhhn.
Ko palonsa basu shigaba saigasa ya fito da wayar a hannunsa zai kaimata.
Kar6a tayi tana cewa,
Let's go zeey,.
Ayeesha ce tai saurin qarasowa ta hawo stairs hu'du dake qofar palon tareda miqawa neesah ledar hannunta fuska a sake tace,
Inatason ganinki nabaki wannan tsarabace.
Tamke fuska tayi tareda 'fagowa zatai mgn idanuwanta suka sauka akansa yana tsaye yana kallonsu.
Wata 'yar kwalba Ahmed ya bude batareda neesah ta luraba bare Jamaal dake nesa yayi saurin zazzage mattacen baqin macijin dake ciki ya juya ya shige palonsa yana cewa,
Antynah gud night dan ni barci nakeji.
Murya a shaqe tace,
Tnx amma ki aje kayanki bana buqata.
OK tace tareda juya zatabar gurin a tsorace da qarfi zeey takira sunan neesah tana nuna mata qaton baqin macijin daidai ayeesha zata 'dora qafarta
a tsorace cikeda firgici neesah tasa hannuwa biyu ta ture ayeesha da qarfi sbd gudun karta taka ya sareta
Wani mahaukacin ihu ayeeshar tasaki sbd muguwar faduwar datayi nantake jini ya 6alle mata.
Wani iri mugun gudu dabai ta6a sanin yanadashiba ya fito aguje ya tallafota yana kiran sunanta da qarfi nanma su ummi suka fito a ru'de sbd sun jiyo ihun
Ahmed ma a ru'den yafito yana tambayar lpia,
Khadija dake zaune cikin rumfar shaqatawar kusada qofar palon Ahmed taga komai kuma sai ayau ta tabbatarda qiyayayyarta lami ce akan wainnan.
Mamuh💋
🌲 *R H F W F*🐄
_Don't forget to vote, follow and comments_
[8:31AM, 4/9/2018] �?+234 703 593 2228�?: *_DACEWA_*
_(when east meets west)_
_By_
_Mamuh geee_
*_Viawattpad@mamuhgee_*
*46-47*
*_I sincerely heart you labibah lawal thank you for all the care_*
*_page 'din na yau naki me_*..
Jinin dake zubane sosai ya tsananta tashin hankali da fargabarsu tuni ummi tafara kiran innalillah sbd tarigada ta saddaqar da cikin ya 6are.
Sunkutarta yayi duk da jinin dake 6ata masa jiki suka nufi mota ummi da inna rabi suka shiga yabar gidan da mugun speed.
Qoqarin zubewa takeyi zeey tai saurin tarota sbd sosai take cikin tashin hankali dan Sam ta manta da cikin da ayeeshar take dashi yanxu shikenan tayi kisa tunda ta 6arar mata da ciki.
Hawayene suka gangaro mata na tausayin ummi yanxu shikenan ta rusa musu farin cikinsu dasuka kasa samu daga gareta sun samu daga wata tayi musu hasararsa.
Zubewa tayi gurin tareda sakin siririn kuka ahankali sbd har cikin ranta taji baqin cikin itace silar rasa farin cikinsu.
Ganin tana kukan datake mai tsima rai yasa jikin Ahmed yayi mugun sanyi ya matso zai kamata yaji an riqe hannunsa a tsorace ya 'dago.,
Khadija ce tsaye idanuwanta taf da hawayen tausayin kanta dana neesah a karo na farko ta kallesa cikin ido murya a sanyaye tace,
Ahmed karka shiga hurumin Allah sosai sbd samun sassaucin sauran lefukan da ka jima kana aikatawa.
'Dauke numfashinta tayi tareda kama neesah suka bar gurin.
Kallonsa zeey tayi zatai magana ya watsa mata idanuwansa dasuka kada rai a 6ace yace,
Tabbas danasan haka abin zai kasance dana qi biyewa kafirar baqar zuciyarku saidai na reni sonta a zuciyata na mutu dashi koba komai zan zama masoyi na haqiqa ko bayan raina zatai alfahari da ni amatsayin masoyi na haqiqa.
Wani kallon tsana da wulaqanci ta watsa masa kafin tace,
Ko yanxu ma lokaci bai qure maka ba saidai ka shirya kai da neesah ne zaku 'dandani 6acin ran Jamaal kun 6arar masa da ciki.
Qoqarin damqota yayi tai baya tace,
Don't waste your energy tun yanxu
Save it you gonna need it later,
Da kana nufin ka dakemu ne ka daki banxa to bari kaji lokacin da kake zazzage qaton macijin a kusada qafar ayeesha kana tunanin ta kareka kar Jamaal ya hango to abinda baka saniba shine sosai tai seti da yanda ya hangoka tsaf dan haka saika shirya fuskantar 'dan uwanka da iyayenka.
Wucewa tayi tareda sakin dogon tsuki tana cewa,
Dama bakasan dawa kake wasaba.
Kasa komawa bedroom 'dinsa yayi sbd jirin dake neman 'dibarsa sai kawai ya durqushe agurin hawayen da baisan dasuba suka fara gangaro masa na tausayin neesah dakuma mummunan tashin hankalin da gidan zasu fuskanta ta rarrabewar kawuna.
Khadija nakaita 'dakinta ta fice zuwa nata 'dakin ta zube a qasa tana kuka Mara sauti sbd wannan abun datake gani su ayeesha nayi to tabbas bazata samu Jamaal ba har abada.
Zama zeey tayi kusada ita tareda rintse ido ta dafa hannun neesah dake zaune quryar gado idanuwanta jajir.
Koda suka isa asibiti aka kar6eta batareda 6ata lokaciba aka tabbatarmusu da cikin ya xube gaba 'daya dan haka basai anyi wankin Mara bama shiyasa aka kasa gano magani tasha cikin tuni dama yafara zuba.
Duk iya yanda ummi taso daurewa saida tayi hawayen tausayin Jamaal sbd yanda idanuwansa suka ka'da jajir ko magana yakasayi sai zama yayi bakin gadon da ayeeshar ke kwance ya riqo hannunta da wannuwansa biyu ya rintse ido yanajin wani irin zafi a zuciyarsa.
Bata wani jimaba ta farka tana bude ido ta fashe da wani irin kuka.
Bude idonsa yayi tareda riqota yana qoqarin lallashinta
Ummi ma matsowa tayi tana cewa,
Ki kwantar da hankinki ayeesha Allah zai kawo miki wani insha Allah.
Ihu ta qwalla jin abinda ummin ke fada takallesa tace,
Na rasa babyna ko yananan?
Girgiza mata kai yayi yana qoqarin kamota jikinsa ta fasa ihu tana kuka cikin tashin hankali tareda fusge drip da canola dake jikinta tana rusa kukan daya masifar 'daga hankalinsu.
Qoqarin kamota yake tana turjewa kuka take sosai tana cewa,
Babyna,babynah inason babynah.
Tsuru inna rabi tayi tana kallonta cikeda mamakin kukan datake akan ta rasa cikin fari kuma agaban uwar mijinta.
Ummi kuwa tausayin ayeeshan da baqin cikin rasa cikin yasa itama hawayen take.
Daqyar ya qanqameta ajikinsa sbd ko magana baya iyayi
tsit 'dakin yayi banda kukanta dake fita ahankali bakajin komai tuni idanuwanta da fuskarta suka kumbura tsabar kuka kallo 'daya zaka mata tabaka tausayi idanbakasan komaiba.
Har gari ya waye suna zazzaune kuma har lokacin kukan take saidai qarfinta daya qare hawayene kawai ke tsiyayowa ahankali.
Dr na shigowa da safe ya sallamesu shida ummi ne suka