Showing 42001 words to 45000 words out of 45946 words
saka dogon wandon bacci kawai batareda Riga ba.
Order abinci yayi ana knocking tana farkawa ta miqe zaune tsakar gadon tana mitsitsika ido sbd wata muguwar wahalalliyar yunwace ta tada ita.
Tasowa yayi daga kujera yazo kusada ita ya zauna tareda riqo hannunta 'daya yana kallonta.
Abincin da aka aje take kallo hanjinta har wani kuka sukeyi.
Zamewa tayi ta sauko gadon ta zauna gaban abincin tafara dubawa taga gasashen kifine sai chips da plantain da ketchup saikuma ruwan coffee da toasted bread yanka hudu.
Chips 'din tahauci saidata cinye tas taji bata qoshiba ta cinye slice uku na toasted bread 'din ana hu'dun ne taji zuciyarta tafara tashi amai na qoqarin zuwar mata ta miqe da gudu ta nufi qofar data tabbatar ta toilet ce.
Binta toilet 'din yayi cikeda mamakinta danshi ba qaramin mamakin cin abincin nata yayiba.
Amai tayi sosai harta galabaita
Daqyar ya lalla6ata tayi wanka bayan yafito toilet 'din,
'Daure da towel iya cinya ta fito tanajin jirin aman datagama yi,
Riqota yayi tareda ha'data da jikinsa yana cewa,
Baby sorry kinji..
Zamewa tayi ta zauna bakin gado tareda kallonsa idonta na kawo hawaye tace,
Nifa wlh wata yunwar nakeji sosai bazan iya bacci ba,
Zama yayi kusada ita tareda shigarda ita jikinsa ransa na ayyana masa wani abu yace,
Don't worry I will order something for you again...
No ni furar Habib nakeson sha sbd ita zatafi qosar dani.,
Rungumota jikinsa yayi tareda saka hannunsa 'daya ya 'dau wayarsa daya kashe ya kunna ya danna kiran Yusuf yayi masa bayanin abinda sukeso batareda ya tsaya sauraron shaqiyancin dayakeson yimasaba ya kashe wayarsa.
Wani qaninsa Yusuf yakira yafada masa tareda tura masa number Jamaal da hotel 'din dayake.
Lafewa tayi cikin jikinsa dan dama gangar jiki nasone zuciya ta hana.
Shafa gyararen gashinta yake ahankali yana kallon wani program a tashar cwtv,,
Kiransa yaron yayi yafada masa room number saigashi yakawo har roba biyar Jamaal yabasa ku'di masu 'dan yawa ya wuce yana godia.
Zama tayi tsakiyar gadon tafara sha har wani lumshe idanuwanta takeyi tana murmushi.
Zama yayi yana kallonta yanda takesha har ya gangaro da idanuwansa kan qirjinta dasuka cicciko sai sheqi suke duk da 'daure takeda towel yana iya ganin sama.
Roba biyu ta shanye tas ta sauko tayi miqa tanajin wani farin cikin samun furar,
Rigar baccin daya siyo mata ta 'daga zata saka taga ikon Allah bawai dan bazata iya sakata ba hasalima tafison irinsu saidai batajin zata iya sakata yagani dan da ita da babu duk 'daya.
'Dauke kansa yayi yazuba coffee 'dinsa yana sha harya gama yayi shirin kwanciya tana tsaye da rigar a hannu tana ayyana rainin wayo irin nasa tana yayarsa yasiyo mata irin wannan sexy nightgown 'din tasaka masa.
Rage wutar 'dakin yayi tareda isowa bayanta ya jawota jikinsa ya 'dora zuro kansa ta wuyanta cikin muryar kashe mata jiki yace,
Kina kunyan sakamin itane?
Ok I will do it myself...
Zame towel "dinta yahau qoqarin yi tayi saurin juyowa ta shige jikinsa sbd towel 'din harya zame daga qirjinta.
'Daukarta yayi suka haye gado yana qara shigar da ita jikinsa duk da hannunsa 'daya na kan nonuwanta da suka matuqar 'daga hankalinsa..
Daren ranar duk abinda ya wakana tsakaninsu ya sanya musu wani tsantsar farin ciki da nishadi dan tuni ta manta da alqawarinta na rabuwa dashi duk da haka ta murxu matuqa dan tun datai sallah takoma ta kwanta wani wahalallen bacci ya 'dauketa sallarma a zaune tayita..
Haryayi shirin 'daurin aure bacci takeyi ya kalleta tareda sakin lallausan murmushi ya duqa ya manna mata light kiss a baki da goshi ya fice.
Mamuh?
RHFWF
*_DACEWA_*
_(when east meets west)_
_By_
_Mamuh geee_
*_Viawattpad@mamuhgee_*
*70*
Gurin 'daurin auren Yusuf yayita yimasa iskanci yayi banxa dashi dan shi yamatsu a 'daura yakoma dan jiyake fatarsa na ra'dadin son kasancewa da tata fatar.
Sha biyu aka 'daura auren gurin reception ne ma ya'dan jima sbd tsayawa dayayi yabada komai na tafiyarsu dan so yake su wuce daganan.
Zaune take tana kallon wata diramar India a zeetv tanashan robar qarshe data rage mata ta furarta dan ta shanye biyu da safe.
Sanye takeda purple handless gown iya cinya Wanda itacema mai sauqi cikin kayan daya siyo mata.
Kallonta yayi tareda sakin murmushi ya ware mata hannuwa
Ta 'dauke kai taci gaba dashan furarta.
Qarasowa yayi ya zauna kusada ita tareda jawota jikinsa ta 'dago ta kallesa ya 'daga mata gira yana cewa,
How is my gorgeous doing?..
Lumshe ido tayi batareda ta amsa tana qara lafewa cikin jikinsa.
**********
Kwanansu uku a Kaduna suka wuce UK bayan yayi waya ya sanardasu ummi da mamy,
Soyayya da shaquwa ce mai qarfi tashiga tsakaninsu duk da kumbure kumbure da 'daure 'dauren fusriga
a yana nan saiyaci maganinta ya iya bida ita yanda takeso duk da ya lura da kawai rigimarta kesata yin hakan dan wasu lokutan mantawa take ta sake suyita soyayyarsu duk da taqi yarda da son mijinta yakamata.
Rayuwar jin da'di da wayewa suke a qasar dan dama irin rayuwar takeso wadda ko a ina mijinta zai iya nuna mata soyayya ba takura.,
Gashi ashe dama duk wayewa da ajin Jamaal acan bakomai suka ganiba sai anan take ganin mamaki dan kusan kowane time fita yawo suke ko a ina suka maqale da juna tana cikin jikinsa
Nan take suka canza su duka dan harwata qasunbar kyau da kwanciyar hankali ya tara taqara masa wani kyau da kamala.
Ahankali cikinta ya'dan fito kadan duk da har lokacin bai gama tantace cikine da itaba..
Yau tun safe ya fita aiki dan anyi masa wayar ana nemansa prison 'dinsu inda aka kawo su zeey aka rufe 'daurin rai da rai.
Sai 6 yadawo gida,
Zaune take tanashan milkshake sbd shi yayi mata replacing furarta.
Blue jins mini skirt ne a ajikinta wanda iyakacinsa qwatan cinyarta da farar handless rubber top ta kame gashinta gefen kanta ta nabba'a tana kallon wani series _the originals_ a tashar cwtv.
Qaran doorbell yasata miqe ta nufi qofar da cup a hannunta.
Jawota jikinsa yayi yana cewa,
God I love this gorgeous so much..
Zamewa tayi tareda juyowa ta kallesa tace,
Ina kaje kafita so early and you came back late.?
Kiss yakai mata abaki kafin ya nufi bedroom yana cewa,
Work.
Zamanta tayi a Palo taqi binsa taci gaba da kallonta..
Wayarsa daya bari a palon ta'dau ringing harta share ta amma ringing 'din ya dameta duk da bamai hayaniya bane.
'Daukar wayar tayi da niyyar kai masa taga sunan Yusuf ne saita 'daga kafin tayi magana yarigata da magana cikin dan takaici.
"" Jamaal how can you meet with that crazy ayeesha bayan nafada maka karkaje inanan zuwa cikin week 'dinnan I know how to handle yan iska irinsu now gashinan tafara blabbing nonsense wai she thinks she's 4 months pregnant and u are the fathe.....
Wurgi tayi da wayar batareda tajira yakai
Qarshen maganarsaba dan mummunar faduwar gaba da jikinta daya 'dau rawa,,
Dararewa tayi tayi ta zauna a kujera tuni wani kallo ya gushe a qwaqwalwarta,
Takaici,baqin ciki da zafine suka rufeta lokaci 'daya,,
Fitowa yayi daga bedroom sanyeda three quarter trouser black da da black armless riga
Zama yayi kusada ita tareda 'daukar cup 'din data aje yana kur6an milkshake 'din ya kai hannu zai jawota jikinsa ta miqe tareda nufar bedroom tashige yabita da kallo duk da yasan tana hakan idan rigimarta ta motsa amma yanxu she seems so serious.
Har dare qin fitowa bedroom tayi qarshema kwanciya tayi tace zazza6i takeji kafin kace me sai kuka.
H��r tsakar dare kuka take gabaki 'daya ta 'dagamai hankali duk yabi ya hargitse cikin daren.
Kafin safe fuskarta da idanuwanta sunyi suntum kuma har safen takasa daina kukan dan tuni taji ta tsanesa da cikin jikintama gabaki 'daya banda taji cikin yabar jikinta ba abinda takeso saikuma taganta gida dan har qasar gabaki 'daya ta isheta.
Kasa gane kanta yayi danko abinci taqici ga yunwa tanaji kamar ta kasheta amma tsabar taurin rai taqici.
Badan yasoba yafita office sbd kiran gaggawar da akayi masa yafita da niyyar yaje yadawo yanxu yanxu.
Yana fita ta'dau key 'din motarsa 'daya ta fita.
Magani tasiyo tana shigowa ko zama batayiba ta 'dauko ruwa ta shanyesa tas ko qaida batabi ba sbd baqin cikin datake ciki idan ba ganin tayi cikin yafitaba bazata samu sukuniba.
Sulalewa tayi qasa ta zauna qasa saikuma wani sabon kuka yazo mata dan har lokacin bata daina jin zafin datakeji a zuciyarta ba.
Sannu ahankali taji mararta qulle tafara mata ciwo amma ta dake ko motsi taqiyi.
Tun tana danne ciwon tuni azabar ta wuce tunaninta ta dafe ciki tana nishi hawaye nabin fuskarta.
Zubewa kwance tayi tana juye juye da kuka.
Ahankali taji kamar jini ya 6alle mata cikin qarfin hali tasa hannu ta shafo taga jinine kuwa nan kuma tasaki wani sabon kuka cikin azaba dan tuni ciwon ya gigita tunaninta nan tafara ficewa hayyacinta.
Dishi dishi tafara gani numfashinta na fita ahankali daidainan tashiga palon ganin ta kwance a qasa kamarma ba rai jikinta yasa ya qaraso jikinsa harwani kyarma yake ya tallafota jikinsa yakira sunanta da qarfi amma ko motsi..
Idonsa ne yakai kan jinin daya 6ata jikinta gabansa yabuga da qarfi ya ha'diye wani yawu mai 'daci da fargaba ya sunkuceta zai fita da ita sauran maganin datasha da takardar sunansa suka fa'do daga jikinta.
Kallon maganin yayi gabansa na tsananta fa'duwa amma rashin sanin ko maganin meyene yasa ya 'dauka ya nufi asibiti dasu gabaki 'daya.
Wata ha'daddiyar hospital 'din friend 'din Dr Vincent yakawota aka shiga gyne emergency da ita,,
Tsowon awa 'daya suka yi akanta kafin suka samu jinin ya tsaya bayan cikin ya fita gabaki 'daya.
Kallonsa dr vin yayi yace,
I'm really sorry captain we couldn't save the baby because the pills she has taken are very strong and....
Miqa masa maganin Jamaal yayi jikinsa a matuqar sanyaye.
Kar6a Dr yayi ya duba tareda girgiza kai yace,
Ths are not good to pregnants women atall because....
A zuciye ya katse Dr da cewa,
Just clear things to me vin,,she terminated the pregnancy by taking this...
Pls don't take things to harsh may be she has her own rea...
Tsaki mai qarfi yaja tareda miqewa yabar office 'din a fusace zuciyarsa harwani rawa take sbd baqin ciki da 6acin rai..
Ko room 'din datake bai komaba yabar asibitin tsabar baqin ciki daya isa gida har hawaye saida yayi cox she shattered all his dreams..
Taci wuya sosai kafin suka sallamota bayan kwana 'daya kuma tunda ta farfa'do bata saka shi a idoba.
Dr vin da kansa yakaita gidan bayan yayi waya da Jamaal dan ko wane time Jamaal nakiransa ya tambayeta amma baisake zuwa asibitinba.
Baya gida dan haka ko shigowa Dr baiyiba yajuya Yakoma asibiti.
Wanka tayo taxo Palo ta zauna tareda qurawa tv ido amma sam hankalinta ba'anan yakeba tunani da fargaba take sbd dai tasan yarigada yasan komai yanxu sbd yanayin yanda Dr yayi mata 'yar nasiha tagane yasan komai kenan shiyasa yaqi komawa dubota.
Shafo cikinta tayi saitaji Hawayen kewar babynta sun gangaro mata akaro na farko.
Sorry bby, pls forgive mummy but it's daddys fault he hurts mummy that's why mummy over reacted and did sumtin stupid out of rage.
Har 8 na dare bai dawoba tashige bedroom 'dinta ta kwanta bayan tagama komai na shirin bacci.
Sai 9 yadawo kuma har lokacin batai bacci ba ta lafe tana jiran yashigo dubata amma shiru har bacci ya 'dauketa.
Tana 'daukar alamarin wasa saigata kullum da hawaye take yini dasu take kwana dan ko ganinsa bata samun damaryi,
Ta 'dauka bazataji komaiba akan duk wani mataki ko hukunci dazai 'dauka akanta saigashi tarasa nutsuwarta da sukuninta dan yayi mata mugun sabo na zama cikin jikinsa koda yaushe ga zuciyarta dake azalzala dason ganinsa koda baxai mata maganaba.
Sosai ya shareta ya tattarata yafita sha'aninta dan ta qona ransa matuqa.
Sati uku ahaka saiga Yusuf da amryarsa amirah sun 'diro qasar.
Koda suka iso bayanan sosai tayi murna da zuwansu hardai dataga amirah kamarta rushe da kuka suna shiga 'daki tun amirah bata tambayeta dalilin ramartaba tafara gayamata dan tagaji matuqa mafita take nema.
Cikin jin haushin abinda tayin amirah tace,
Qasqantarda kanki zakiyi kiyita lalla6asa kinabasa hkr harya sauka.
Yawu ta hade tareda 'dan tsuke fuska tace,
Hkr kuma?
Nice zan basa hkr gskia bazan iyaba shine dai zai hkr yadawo da kansa tunda yana cewa sona yake fiyeda komai dan haka nidai yazo rarrasheni zan hkr da wuri wlh.
Dariyar rainin wayo amirah tasaki tana cewa,
Lallai kuwa kin 'debo da zafi amma ai bakinki zaki kai zakiji..
Waya Yusuf yayi da Jamaal 'din yafita suka tafi gurin alamuransu.
Abinci mai kyau da da'di suka shirya duk da dai duk rabi snacks ne sai kaji da kifi da pasta.
Lokacinda Yusuf yayiwa amirah wayar gasunan dawowa neesah shiru tayi idanuwanta na narkewa sbd kusan wannan shine kiran na goma sha wani Abu da Yusuf 'din yayi mata bayan fitarsu.,
Ada har gajiya take ta kashe wayarta sbd kiran Jamaal idan yafita amma saiya koma kiran landline amma yanxu....
Miqewa tayi tashiga toilet tayo wanka ta'dan zana simple makeup tasaka doguwar rigar 'yan Turkey _Turkey gown_ mai A shape da dogon hannu sai adon crystal stones,
Dark maroon ce rigar saitayi mata masifar kyau tasaki gashinta har qasan kafadunta bayan tagyarasa sbd haka Jamaal yafison gashin a gwance.
'Dan qaramin Vail 'din rigar tasaka itadai amirah dariyama alamarin yaringa bata na qarfin halin neesah na anaso Girman kai ya hana.
Saida sukayi sallar isha'i suka shigo gidan ba kunya Yusuf ya riqo hannun matarsa yana cewa,
Precious you look so tired?
Jujuya idanuwanta tayi cikin sigar shagwa6a tace,
Munyi aikine that's all.
Juyowa tayi suka gaisada Jamaal ya sake sosai kamar ba abinda ke damunsa.
Ahankali ta fito daga bedroom tashigo palon gefensa takalla tana qara gaisawa da Yusuf
Ko 'dagowa baiyiba qarshema miqewa yayi yashige bedroom 'dinsa.
Binsa da ido tayi tareda turo baki dan wlh ita tagaji idan yadaina sontane ya maidata gida mana.
Sunci abinci cikin jin dadi saidai fuskarnan tasa a tsuke take har gabanta faduwa yake idanta kallesa.
Sai dare sosai su Yusuf suka tafi masaukinsu.
Suna komawa amirah tafada masa komai akan yayiwa Jamaal 'din maganar yayi hkr ya sassautawa neesah.
Washe gari dasuka fita bayan yakawo amirah gurin neesah yayiwa Jamaal maganar Jamaal 'din yayi banxa dashi sbd haushima abin yaqara basa wai sbd kishin banxa akan abinda bata tabbatarba ta xubar masa da ciki.
Satinsu Yusuf 'daya suka baro bayan yayi duk yanda zaiyi yaga Jamaal 'din ya sauka amma ina sbd koshi ya jinjina alamarin dan shima zai iya fiyema da hakan idan shine saidai tsananin son da Jamaal 'din kewa neesah yasa yaqi korota gida.
Bayan tafiyarsu amirah komai ya qara jagule dan har tafiya ma yayi sydney auren abokinsa tsawon three days.
Yau kam tanajin fitowarsa ta fito palon daga ita sai qaramin towel ko ida ha'dewama baiyiba sbd fitowarta wanka kenan taji motsinsa batason yafita batai magana dashiba.
Gabansa ta tsaya fuska a 'daure tace,
Inason nasan matsayina a gidannan?
Wani mummunan kallo ya watsa mata
Duk da gabanta ya fa'di qara tsuke fuska tayi tace,
Idanma dan cikine kake wannan naga ai mahaukaciyar matarka nacan da wani ko?
Takaicin zancenta da baqin ciki yasashi kallonta yana 'daure fuska yace,
Meye banbancin haukarki da tata haukar? Ba gwara itaba tayine dan cimma wani buri kefa meye naki burin?
Baki tasake tana kallonsa hawaye na 6alle mata sbd takaici da baqin cikin zafin zancensa a qule tace,
Dama bance gwarani ba akanta indai agurinkane kuma wlh ni gida zani saikuje can ku qarata da ita wadda kakeso dan wlh bazan zauna da mijin wataba gwara nima naje na nemi nawa ni kadai.
Kai tsaye yace,
Shikenan pack all your things and get ready tunda gida zaki shike nan.
Ficewa yayi yabarta tsaye sakeda baki sai kawai ta saki kuka tana cewa,
Wlh sai ummi ta 'daumin fansar wannan wulaqancin.
Kamar wasa washe gari tana zaune palo waya takeda amirah dake fa'da mata ciki gareta duk sai jikinta yayi sanyi.
Fuska a tsuke yashigo yana waya bai kalletaba yace,
Idan kinshirya muje jirgi zai tashi zuwa 7.
Kallonsa tayi fuska cikeda mamaki kafin ta kalli qaton agogon dake maqale a palon taga 6:15,
Wuceta yayi yashiga bedroom 'dinsa yana cigaba da wayarsa
Qofar tabi da kallo hawayen baqin ciki na taruwa a idonta.
Shiga 'daki tayi ta ha'do kayanta a akwati ta canxa kaya zuwa doguwar Riga baqa da golden Vail qarami sai handbag 'dinta tafito.
Har suka kai airport waya yake dan karma tasamu damar yimasa wata magana.
Lokacinda yagama mata komai ya miqa mata ticket da passport 'dinta alamar ita ka'dai zata bada shiba gabanta faduwa yayi ta kallesa tareda murtuqe fuska zata ca6a masa baqar magana ya juya yabar gurin batareda yace mata qalaba bare ya saurareta.
Tsabar baqin cikinda tashiga har jirginsu ya sauka abuja bata daina tunaniba dan har wata bugawa zuciyarta keyi.
Naseer yazo 'daukar sbd Jamaal 'din yakirasa ya fada masa tana tafe,.
Cikeda murna da farin ciki mamy ta tarbi 'yarta saidai ganin ba komai gaban neesah yasata kallonta bayan taci abinci tayi wanka da sallah ta huta tace,
Neesah lafiya kuwa naganki duk a sanyaye kuma ina cikin da kikaje dashi?
Da sauri ta kalli mamy cikin mamaki gabanta na faduwa sbd batasan ina mamy tasanda maganar ciki ba.
Cikin son jin bayani mamy tace,
Eh nasan dashine bawai wani yafadamin ba niga alamominsa da kaina.
Girgixa kai tayi cikin son 6oye firgicinta tace,
Mamy babu wani ciki kawai dai qila kinyi tunanine.
Tsuke fuska mamy tayi tace,
Karki rainamin wayo dan ko ba uwace niba karki manta ni Dr ce..
Zubewa yayi kome?
Tana dan basarda zancen tace,
Eh..
Garin Yaya?
Zaro ido tayi tace,
Mamy haka nan fa ya zube.
Kallon mintuna mamy ta tsareta dashi ta gyara zama tace,
Zaki fadamin ne kona kira Jamaal 'din.
Tsuke fuska tayi jin sunansa tana 'dan tura baki tace,
Mamy nina zubar amma wlh nayi nadama dan Allah karki fadawa Abba.
A zafafe take kallonta tace,
Wlh dama tun farko na zargi hakan saidai yamin daidai daya koroki kuma wlh abbanki yagamajin wannan zancen.
Lokacin da Abba yaji taga bala'i dan harcewa yayi a ranar saita bar gidan takoma gurin Jamaal 'din yacigaba da gasata.
Daqyar mamy ta rarrashesa ganin abin na Neman zama wani babban alamari.
Zaman gidan yakaimata intaha sbd Sam ba fuska daga gurin mamy har abban gashi tunda taje gidan amirah so biyu Abba ya hanata fita saidai su amirah suxo mata Jamaal kuwa ko waya saidai taga alert na kudi masu yawa daya turo mata.
Satinta biyu ta harha'da kayanta tace itadai Lagos zata koma gurin ummi basu hanata ta tafi.
Tundata dawo Lagos hankalinta ya 'dan kwanta dan gata da soyayyarta da ummi ke mata tananan saima abinda ya qaru
Ga mama itama jitake da ita sosai sun 'dinke kamar wasu sa'anni sbd mama wayayiyar mace ce data iya kirsa dajan hankali matuqa saita fara koyawa neesah dan ummi yanxu ko sirrinsu bataji saidai taita tsokanarsu tace,
Uwa da sirika anzama qawaye.
Lokacinda