Showing 9001 words to 12000 words out of 45946 words
zata siya to saidai a babban mall bare sauran kayan amfani shiyasa kusan kullum suna hanya.
Ga ummi data 'dau wani sabon so da tattali ta'daura mata
Hakama tana tsananin so da qaunar khadija itama saidai son neesah dabam yake aranta sbd 'dan uwanta yayanta wato abban neesah.
Abin duniya yataru yayiwa khadija yawa dan yanxu ko lectures bata ganewa sbd ba kullum take zuwaba ga wata uwar rama data sanyota gaba duk ta rasa sukuni kullum saitayi kuka kafin tayi bacci sbd kullum rayuwar neesah qara haskaka takeeyi,
Ummi tayi lallashinta akan tafada mata damuwarta saidai tace ba komai inna Rabi ma tayi lallashinta amma duk abanxa baqin ciki da hassadar neesah na Neman sadata da kushewarta.
Yau ansamu ta'dan saki jikinta ta fito palo suna zaune suna fira,
Ummi da inna Rabi sai neesah dake kwance kanta a cinyar ummi tana chatting da amirah akan binciken data sakata akan tahir da Habib.
Kallon neesah dake kwance jikin ummi tayi ta danne hawayenta tana gaida ummi.
Khadija Yaya ciwon kan naki?
Kodai wai asibiti zamuje ne ni naga sai rama kike koda wata matsalar ne uhumm?
Zama tayi tana maida hawayenta tadan saki fuska tace,
Bakomai ummi Kaine kuma yadaina insha Allah.
To Allah ya qara sauwaqewa.
Inna Rabi ta kalla tace,
�? �? Inna abani abinci naci ka'dan.
Yawwa khadija kokefa bara na hadamiki yanxu kuwa.
Danne duk wata damuwarta tayi ta 'dan kalli neesah tace,
�? �? 聽聽 Anty neesah ina wuni?
Qyaleta tayi taci gaba da chatting 'dinta saida takuma cewa,
�? 聽聽 Anty neesah sannu da hutawa.
Daqyar ta bude baki tace,
�? 聽聽 Uhummm.
Neesah Sam ta tsani mutum mai 6oye 6oye sbd ita kai tsaye take abinta bata 6oyo ko tauye kai sbd tanason rayuwar cikakken 'yanci saidai Sam bata shiga ko kallon duk wani Abu dabai dametaba.,
Tun bayanxu ba ta fahimci khadija Nada abinda take 6oyewa amma takasa fa'da Ai mata magani saidai taita duhun rai wanda ita agurinta ba dalili bane ka 6oye damuwa shiyasa Sam ita khadija batai mataba.
Wayar ummi ce tayi qara tana dubawa taga Jamaal ne tasaki murmushin farin ciki tace,
�? �? �? 聽聽
�? �? �? �? Jamaal kan....
Ummi kadakice komai dan nasan�? abinda zakice.,
To bani dalilinka na 'daga tafiyar?
Ummina pls kadaki tambayeni dalilin coz kinsan bazai wuce work,work, work ba.
Ok then yanxu fadamin when are you coming son?
Ummi ina nan tafe ranar Wednesday Insha Allah sbd wani dalilin da sainazo zan fada miki.
Cikin farin ciki tace,
聽聽 Ok son Allah yakawoka lpia.
Ameen ummi na.
Koda tagama wayar ta kalli fuskar neesah taganta a tamke ba walwala saita saki 'dan guntun murmushi kawai.
Khadija kuwa wani farin cikine ya dirar mata Wanda rabonta dashi tun zuwan neesah gidan.
Kar6ar abincinta tayi tafaraci cikin farin ciki Wanda yabawa ummi da inna Rabi mamaki matuqa.
Mamuh.
_don't forget to vote#follow#and comments viawattpad@mamuhgee._
[3:20AM, 4/1/2018] 鈥�+234 816 253 8316鈥�: _*DACEWA*_
_(when east meets west)_
_By_
_Mamuh geee_
*Viawattpad@mamuhgee*
*18-19*
Tunda neesah taji maganar dawowar Jamaal ta rage zama sosai a gidan
Kullum tana school sai yamma sosai take dawowa data dawo kuma zatai shigewarta 'daki.
Ummi na lure ta qyaleta gudun rigimarta,
Ahmed ne kawai yake samun ganin fara'arta harsuyi fira.
Khadija kuwa sosai take al'amuranta cikin tsananin farin ciki.
Kowa yayi mamakin sabon yanayin nata amma sukai shiru itama batareda sunce komaiba.
Ranar Wednesday tun guraren 8:00 ta tafi school sbd Sam takasa samun sukuni cikin gidan,.
Duk wata hidimar tarbonsa inna Rabi da khadija ne suka yita.
A da inna Rabi ke gyara 6angarensa idan zai dawo amma wannan karon khadija ce taje ta gyare komai ta kunna aircon tareda kunna fridge 'din dake palonsa bayan taje ta 'dauko ruwan Eva katon 'daya da drinks ta jera aciki.
Rufo qofar tayi takoma 'dakinta tayi wanka tareda zaunawa gaban mirror har zatai kwalliya saikuma ta fasa gudun kada agano manufarta,
Riga da skirt na maroon atampa tasaka tareda 'daura 'dan siririn gyale akanta tadawo Palo tazauna tana charting da wayanta cikin walwala sbd tuni Ahmed yatafi airport 'daukosa.
A nutse yake tafiya hannunsa 'daya na cikin aljihun black fanfuego trousers 'dinsa sai 'dayan hannun yana waya da ayeesha dayake dakatarwa akan kadatazo 'daukarsa Ahmed yazo daukarsa.
Kyakkyawar fatarsa dake sheqin Hutu da kyau Ahmed ya tsaya kallo harya iso gabansa daidai gama wayarsa da ayeesha ya kalli Ahmed 'din yana saka 'dayan hannunsa cikin pocket 'din wandonsa.
Murmushi Ahmed yasaki yana cewa,
Gskia Yaya zanzo na nemi Hutu kwanan nan natafi gurinka sbd nima nasamu lafiyar fata kodan nima na riqa jawa husna aji.
Murmushi kawai yasaki batareda yace masa komai akan abinda yafadaba yace,
Idan ka gama shirmenka kasaka kayan a mota ka kaini gida coz I desperately wanah see my mummy.
Shigewa yayi motan shikuma Ahmed yayi saurin
Saka kayan mota suka nufi gida.
Tun a mota ya kashe wayarsa sbd yasan Sam yanxu ba Hutu ayeesha ta dinga kiransa kenan..
Suna isa gida Ahmed ya nufi part 'dinsa kai masa kayansa shikuma ya nufi palonsu ummi kai tsaye.
Cikeda tsananin farin ciki ummi ta tarbesa zama yayi kusada ita yana riqo hannunta yace,
Ummi da fatan na sameku lpia?
Lpia klau Jamaal,
Ya hanya?
Kasalallen murmushi yasaki yana cewa,
Alhamdulillah.
A ladafce khadija ta taso har gabansa cikin sanyin murya tace,
Ya Jamaal barka da dawowa.
Batareda ya kalletaba ya qaqalo murmushi yace,
Yawwa khadija,
Ya studies naki?
Tana 'dan qaqalo fara'a itama tace,
Alhadulillah.
Da haka ta juya tabar palon jiki a mace sbd rashin ganin fuska a gunsa Wanda dama hakan suke tun farkon fari.
Inna Rabi kam kasa zama tayi sai hidimar kawo masa abubuwan sha take cikin farin ciki dan har cikin ranta Allah yadora mata qaunar Jamaal tun yarintarsa.
Murmushi yasaki har fararen haqoransa suka bayyana cikin kulawa sosai yace,
Innah,
Inna kibarshi hakanan bana buqatar ci ko shan komai yanxu Am ok,
Saidai zuwa anjima may b.
To Jamaal amma mutum yayo tafiya yace ko ruwa bazaisha ba.
Inna kadaki damu anjima zanci kuma ke zaki bani da kanki dan nasan yanxu ummi ta canzani batada time 'dina.
Cikin so da qaunarsa ummi tace,
Jamaal bani kadai na ajekaba kowama har inna 'din sbd kanada mata yanzu and all kulawanka da 'dawainiyanka yana kanta yanzu.
'Dauke wuta yayi fuskarsa na 'dan canzawa sbd gaba 'daya ya manta da zancen auren da neesah.
Anyways baida matsala da ita tunda bason auren takeba afterall bayajin zai iya zama da duk macen da bazata iya respecting 'dinsaba tabasa girman daya kamacesa amatsayinsa na mijintaba koba komai baida time 'din mata irinta.
Miqewa yayi daidai shigowar Ahmed bai kallesaba yana ficewa yace,
Ahmed take my car out to man-u car wash I have important place to go anjima.
Sashensa ya shiga kai tsaye bedroom ya nufa saidaya kunna wayarsa yakira dady sun 'dan 'dau time suna mgn kafin ya kashe yafada toilet yayo wanka.
Koda yafito dogon wandon Judhench black yasaka tareda rigar blue rugbay shirt sbd shi mutum ne mai yawan jin sanyi komai qanqantarsa.
Kwantawa yayi sbd sosai yakeda buqatar hutawa.
Bata dawoba saida maraice shi 'dinma sbd kawai ta gaji ne sosai hutu kawai take buqata.
A galabaice tashigo gidan tana parking ta fito motar riqeda handbag dinta,
Doguwar rigar turkey straight gown ce ajikinta databi jikinta ta kwanta kalar ja sai 'dan siririn red Vail data yane kanta dashi.
Sam bata lura dashiba shiyasa kai tsaye take tafiyar kamar wadda kwai ya fashewa aciki.
Kamar ance ta 'dago takalli gefenta
Tsaye yake a varandan qofar palonsa ya zuba hannayensa cikin aljihun dogon wandonsa daya canza ga alama wani wankan yayi bayan yatashi bacci,
Kafeta yayi da ido batareda wani sabon yanayi ya sauka a fuskarsaba Wanda hakan ya tabbatar mata da kallon raini ne da tsantsar wulaqanci yake mata.
Ranta ne yai tsananin 6aci ta 'dauke kai a fusace taqarasa cikin Palo ko inna Rabi dake jera abincin 'dare a dining bata kallaba tawuce 'daki tana fadin,
Wlh bazan yarda da kallon wulaqanci ba bari ummi tazo.
馃尣 *R H F W F* 馃悇
Mamuh馃拫
_Dont forget to#vote#follow#and comments via wattpad@mamuhgee_
[3:21AM, 4/1/2018] 鈥�+234 816 253 8316鈥�: _*DACEWA*_
_(when east meets west)_
_By_
_Mamuh geee_
*Viawattpad@mamuhgee*
*20-21*
Wani sahirtaccen murmushi yasaki yana cewa,
She is unbelievable.
Fitowar dady ce tasashi qarasowa gurinsa suka nufi masallacin jikin gidan nasu dan sallar magrib da ake qoqarin tayarwa.
'Dakin ummi tashiga dan gabatarda sallah sai ganinta tayi zaune gaban mirror tana Shafa mai tafito wanka fuska a hade.
Cikin kulawa tace,
Baby yaushe kika dawo?
Kuma maiya sameki naga duk ranki kamar a 6ace.
Danne takaicinta da 6acin ranta tayi tace,
Ummi nidai ki tara kowa na gidan nan kice kowama ya fita harkata dan gskia ummi bazan yarda anai mini kallon wulaqanci ba idan ba hakaba zan tattara nakoma hostel da zama.
Murmushi tasaki ahankali domin ta fahimci inda zancen ya dosa idan ba kuskure tayiba to lallai Jamaal ne ya ta6a ta,
Sarai tasan Jamaal zai iya hardai idan ya fahimci bataso ta tabbas ya dingi yi mata kenan harsai yaga tana neman zaucewa kan masifa.
Shafa kanta tayi tana cewa,
Baby kyale koma wayene ni zanyuwa tufkar hanci saki ranki babu Wanda ya isa ya 6ata ranki a gidan nan indai ina nan.
********
Washe gari tunda safe ta shirya ko breakfast bataiba ta fito cikin adon Riga da skirt na coffee atampha da 'dan qaramin gyalenta kitchen ta leqa tacewa inna Rabi tabata Apple biyu.
Riqeda apple 'din da handbg 'dinta ta fito ta nufi part 'din Ahmed.
Zatai knocking saigasha yafito a gaggauce shima tace,
Na 'dauka baka tashiba oya bani key 'din motana ina saurine.
Zaiyi magana wayarsa tai qara yaduba da sauri ya 'daga yana cewa,
Ya Jamaal wlh inada test ne yanxu da safen nan amma idan nadawo zan kaima.,
Ok to ngd.
Kallonta yayi yace,
Sorry Anty neesah wlh bankai wankin motar takiba amma muje atawa mana.
Harara ta sakar masa tareda cewa wlh bazan bika ba sbd daga can akwai inda zani.
Juyawa tayi a fusace takoma cikin gida tana qoqarin shigewa 'daki ta hango key 'din mota a saman center table batai wani dogon tunaniba ta 'dauka ta fito dan duk tunaninta motar ummi ce.
Kodata fito tuni Ahmed ya wuce dan haka kai tsaye ha'daddiyar sabuwar motar ta nufa dan dama tayita kwadayin hawanta amma anqi wanketa sai yanxu dataji ummin na maganar zata bikin auren 'yar qawarta.
Da mugun speed tabar gidan dan saura mintota ka'dan su shiga test 'din.
Baki maigadi yasaki yana mamakin yau wani yahau motar Jamaal akaro na farko bayan Ahmed dashima sai idan zai kaita wanki yake hawa.
Guraren 11 yafito cikin shirinsa na qananan kaya sai qamshin turaren oriflame signature dake tashi ajikinsa.
Palon yashiga cikin siririyar sallama.
Ummi ce kawai zaune a palon tana kallon tashar TLC entertainment.
Kallonsa tayi tana amsa gaisuwarsa kafin tace,
Dadynku yayita jiranka baka fitoba and you switch off your phone harya fita.
Na manta ne ban kunna wayana ba bayan sallar asuba I will call him yanxu idan na fita.
Khadija ce taqaraso palon 'daukeda breakfast 'dinsa jere a babban tray ta aje gabansa tana gaidasa cikin girmamawa.
Yana duba wayarsa ya amsa mata batareda ya kalli gefen datakeba.
Tea kawai yasha ya miqe yana cewa ummi zai fita.
A tsarge ta kallesa tace,
Jamaal ina zakane naga kabawa fitar mahimmanci.
Kallonta yayi yana da kyau dan son fahimto mai yasa tayi tambayar.,
Dawowa yayi ya zauna kusa da tareda riqo hannunta yace,
Ummi meyasa kikai tambayar bayan baki ta6a tambayataba idan zan fita?
To yanxu nayi tambayar kuma inason nasani.
Ummi nasan tunanin dakike kuma tunaninki gaskia ne ummi sbd Inda kike tunanin zani can zani.
'Daure fuska tayi kafin tayi magana ya miqe yabar palon.
Dawowa yayi yana cewa,
Ummi pls Ahmed yace yabar miki key 'din motana jia da dare ko.
Eh bari naji ina inna Rabi ta aje.
Khadija kira inna Rabi.
Jiki a sanyaye ta miqe sbd sosai zancen Jamaal ya daketa dan tuni taji ciwon zuciya na neman kamata na nan take akan baqin cikin dake neman ruguzo mata muddin da gaske Jamaal neman auren wata yake.
Duk inda ake tunanin ganin key 'din anduba amma ba'a gansaba saida khadija ta fito harabar gidan ta lurada babu motar tayi tunanin Ahmed ne yafita da motar saitaga babu tasa hakama iya saninta jiya motar neesah ba gida ta kwanaba kenan ita tafita da motar,
Baqin cikinta da takaicinta ne suka ninku hawaye suka ciko idanuwanta ta juyo palon jiki a sanyaye hawayenta na qoqarin zubowa.
Bedroom 'dinta ta nufa batareda tabari kowa ya lura da yanayintaba.
Harzata shige tajuyo ahankali kai 'duqe tace,
Ya Jamaal motarfa Anty neesah ce tafita da ita.
Tunda yake rayuwarsa baitaba yimata kallon second biyar bama shiyasa bawani kamanninta yasaniba amma jin abinda tafada yasatashi 'dagowa ya kalleta da oily eyes 'dinsa dasukai masifar yi mata kwarjini da razanata da hanzari ta fa'da 'dakinta ta rufo qofa tana sakin siririn kukan baqin cikin kullum neesah ce agabanta.
Duk iya yanda yaso 6oye 6acin ransa saida ummi tagane sbd tafi kowa sanin halinsa.
Ita kanta tasan neesah bata kyautaba....
Miqewa yayi tareda komawa bedroom 'dinsa ransa a matuqar 6ace amma zata dawo tasamesa he don't think he can tolarate her nonsense and stupidity coz yafitajin duk wani abunda takeji dashi infact he will put her to her place.
Zama yake qoqarin yi wayarsa tayi qara yana dubawa yaga ayeesha ce,
Banza yayi da wayar saidayaji batada alamar hakura da kiran ya 'daga yana cewa they are all dsame#ladies.
Ranta a tsananin 6ace yake amma yana 'dauka ta tattaro nutsuwa ta danne 6acin ran tace,
Captain my Luv ba yanxu zakazo bane naga motanka yanxu a Royallunch hotel.
Ure mistaken,,, yafada kai tsaye yana lumshe idanuwansa dasukai jan 6acin rai.
Qaqalo murmushi tayi tace,
Yes my Luv nima at first dana gani na 'dauka mistake ne but wat confuse me is the lady who is driving the looks familiar,
I think I once saw her wit Ahmed.
Bu'de idanuwansa yayi a hankali zuwa lokacin sun rine sosai yace,
She and who?
Su biyu ne my love may be is her boy friend kasan yanxu wasu na 'daukan rayuwar banxa tsakanin namiji da mace shine wayewa but ni....
Quite pls ayeesha.
Sosai ta ankaro 6acin rai a muryarsa tasaki wani shu'umin murmushin samun nasara tace,
Sorry my Luv if I said sumtin wrong.
Kashe wayar yayi tareda kiran Ahmed yana 'dagawa yace,
Where are you?
Ina school,
Tun yaushe kake school 'din?
Tun safe.,
Da problem ne ya Jamaal?
Bai masa amsaba ya kashe wayar tareda miqewa ya nufi palon ummi.
Yanda tagansa itama saidata tsorata sbd tsantsar 6acin rai da masifar data hango a idanuwansa.
Key 'din motarta ya kar6a yafita da mugun speed.
Royallunch ya nufa yana ganin kiran ayeesha amma yaqi 'dauka sbd yanda ransa ke 6ace zai iya sakata kuka da bacin rai.
Hannu ayeesha tasa ta 'dau kwalbar champaign 'din dake gabanta ta zuba a cup ta kur6a tana kallon Habib tace,
Trust me sweetheart our victories days just started from today.
Mamuh馃拫
馃尣 *R H F W F*馃悇
_Don't forget to vote, follow and comments_
[3:21AM, 4/1/2018] 鈥�+234 816 253 8316鈥�: _*DACEWA*_
_(when east meets west)_
_By_
_Mamuh geee_
*Viawattpad@mamuhgee*
*22-23*
Neesah na fitowa test suka fito makarantar tareda sabuwar friend 'dinta datai a school 'din mai suna zeey.,
A kasalance take driving sbd yunwar datakeji.
Kallonta zee tayi tace,
Yaya ne naga kamar bakyason driving 'din?
Tana kallon titi tace,
Yes wlh yunwa nakeji kamar naje gida.
Cikin murmushin samun sauqin aiki zeey tace,
Why not muje na kaiki wani babban gurin cin abinci na manyan ladies kamarki I knw u will love it and d place is so calm da quiet.
Kamar bazataba saikuma tace,
Ok then muje inane gurin?
ROYALLUNCH.,,ta fada kai tsaye.
Suna isa gurin taji Sam gurin baimata ba bawai dan bai haduba hasalima gurin ya hadu matuqa dan gurin na manyane kawai dai kasancewarsa hotel ne yasa taji Sam bazata iya shiga ciki ba.
Zeey taso tashiga amma ganin neesah ta hade fuska saita share tareda bude motar tace,
Bari nayo mana take away saimu tafi school muci nima gurin naga bai kamacemu ba sbd mutumci da qimarmu muna matsayin mata.
Ok kawai neesah tace tana qoqarin duba wayarta.
Zeey na fita ta nufi wata mota qirar camry217 modl baqa batareda neesah ta luraba sbd hankalinta nakan wayarta datake daddanawa gashi dama bata kashe motarba Ac takesha abinta.
Zuge glass 'din motar akayi zeey ta watsawa ayeesha harara tana cewa,
Wlh hkr na yakusa qarewa sbd waccan miskilar kishiyar taki,
Ke banda abinki ma wannan ai bazatai wuyar kishiba sbd shegen Jan aji da girman kai bazai barta tabi miji ba.
Habib ne ya katse zancen da cewa,
Shiyasa nake masifar son babe 'din I like her ego and personality hmmnnn.
Kallon takaici ayeesha tasakar masa tana cewa,
Can you pls stop that right now before I change my mind nasa ayimin raping 'dinta once and for all nayi maganin matsalata na huta.
Wani 'dan iskan kallo ya watsa mata yana cewa,
Wlh nafiki zama 'dan iska muddin kikai ganganci ta6ata zakiga tsantsar tantirancina so gwara ki tabbatar kin tsaya a yanda muka tsara plan,
Neesah is mine alone and captain is urs.
Bude motar yayi yafito ya nufi motar neesah cikin farin ciki yana gyara agogon hannunsa.
Harara ayeesha tabisa da ita sbd Sam takasa samun yanda takeso akan neesah sbd wata stupid soyayyarsa.
Murmushi zeey tayi tace,
Kibarsa eshaa,idan munsamu buqatarmu tabiya akan neesah ni nasan yanda zamuyi dashi yanda ko sunanmu yaji saiya suma wlh.
Qaramin tsaki ayeesha tasaki batareda tace komaiba tsabar takaici ita yanxu duk ba wannanba tasamu ta zamo matar Jamaal 'din tukuna.
Shigarsa motar yayi daidai da isowar Jamaal gurin tsaf ya hango shigarsa motar
abinda yafi 6ata ransa kenan ta 'daukar masa maza a mota infact ace wai motarsa a hotel.
A fusace ya fito mota ya nufi motar
Idan ba Wanda yasansa ba Sam bazakace ransa a tsananin 6ace yakeba.
A zabure ta kalli Wanda yashigo motar..
Rantane yayi mummunan 6aci baqin ciki da takaici suka taso mata
Batasan sanda ta 'daga hannu ta wanka masa lafiyayyen mari ba
Amma ga mamakinta saitaga ya shafa wajen data maresa yana wani shu'umin murmushi.
Rantane yakuma 6aci ta kallesa