Showing 6001 words to 9000 words out of 45946 words
Jamaal ya damesu ya shanye a fagen class da duk wata wayewa da girma dasuke ganin sunada shi uwa uba ga kyau da naira.
Neesah dan Allah kidaina 'daga hankalinki domin kuwa tashin hankalin nan bazai baki abinda kikeso ba saima lalata abubuwa dazaiyi.
Koba komai kiduba yanda ummi ke tsananin qaunarki duk tabi ta damu akanki amma ba kunya kike dagewa da bakya qaunar 'danta a gabanta,
Ni aganina ma dakinbi abin a tausashe to saiki ga ummin da kanta tabi bayanki kin samu abinda kikeso.
Kallon amirah tayi da kumburarrin idanuwanta tana qoqarin danne takaicinta tace,
Wlh bazan iya Rayuwa da wannan baqin cikinba,
Yanxu kamarni a kallen ace wai anhadani auren da mutumin danake masa kallon qani agurina,
Cutatuwa zamuyi mu duka dan wlh bazan kwantar da kaina nayi biyayyaba gun qanina
Haka shima yanda nasan shegen girman kansa bazai ta6a kwantarmin da kaiba,
Kinga kenan antarwatsa min burin rayuwar danaso tsarawa a gidana na aure,meyasa taheer ya cuceni ya fasa aurena alhalin munyi alqawarin gina kyakkyawar Rayuwa a tare.
Su siyams ne suka shigo dukkaninsu fuska qunshe da daria sbd sanin a kwai qura agun neesah.
Fahimtar zasu iya kawo mata rainin wayo yasa ta miqewarta ta shige toilet.
Cikin kanne daria amirah tace,
Allah kukai mata daria fada zakuyi dan gskia she seems very serious akan zancenta na bazata yarda da aurenba.
Asmy na tu6e doguwar rigarta tace,
Neesah is different, dan nikam hundred percent captain Jamaal yayimin koba komai ai ba kowa yasan itace ta girmesaba sbd yanayin jikinsu ma ba 'dayaba.
Cikin daria siyama tace,
Koba komai da gani zai iya haukata mace a fagen making love sbd yanayin qirarsa ta ingarman namiji.
Daria suka sheqe da ita gaba dayansu.
*******
Zaune take bakin gadon 'dakinta idanuwanta sunyi jajir sbd kukan data kwana ta yini tana sha.
Kallon wayarta tayi a karo na ba adadi tana jiran kiransa amma shiru.
Miqewa tayi ta isa bakin window ta tsaya cikin sabon takaicin halin ko inkula irin na Jamaal.
Jamaal kayi babbar sa'a zuciyata ta riga tayi mugun nisa akan sonka da wlh saina zamar maka masifa da bala'in da bazakaga tahowarsaba
Amma ko ayanxu saika 'dan'dani mugun baqin dafina dayafi na kunama zafi,
Ko wacece ka aura saina zamar mata baqin macijin da bataji bare tagani saidai taita jin dafina acikin jininta.
Toilet ta fada tayo wanka tana fitowa ta shirya cikin doguwar riga ta fito palon inda ta tarar da umman ta nata faman fira da aminiyarta haj shema'u.
Kwanciya tayi a two seaters tareda danna kiran wayarsa.
Shiru number bata shiga saita kira ta qasar wajensa.
Ringin tafara harta katse bai daukaba.
Qara kira tayi harta kusa katsewa ya 'daga.
Taso yimasa rigima amma yanayin muryarsa dake a 'daure yasa ta fasa dan gudun 6ata ransa,
cikeda kissa a kasalance tace,
Captain ka koma without informing me?
Shiru yayi mata,tasake cewa,
Lafiya kuwa captain or.....
For god sake ayeesha how many times zan fada miki banason yawan tambaya just tell me dalilin kiranan.
Siririn kuka tasaki a hankali harda shesheka.
Shiru yayi yana sauraronta duk saiyaji tabasa tausayi sbd yasan dole ne tadamu akan aurensa kai tsaye.
Jingina yayi da kujerar palonsa dayake zaune ahankali cikin cool voice dinsa yace,
Eshaah,
Eshaah meyasa kikeson kuka akoda yaushe bayan kinsan babason kuka.
Cikin muryar kuka tace,
Koyaushe kukana akanka ne captain sbd soyayyarka dake azabtar dani.
Yanxu gashi kayi aure ni yanxu banida stand akan.....
Ok naji daina kukan sai muyi magana.
Share hawayenta tayi cikin son qara samunsa tace,
Pls captain don't leave me, I promise I can wait har time 'din daka shirya kar6ana.
Tausayinta ya qara shigarsa sbd hakurinta yasa koda yaushe yake qara sonta.
Naji ammadai yanxu kidaina kuka I will call anjima sainaji idan kin daina kukan saina fada miki sumtin sweet OK?
'Daga kai tayi kamar yana kusa da ita.
Tana aje wayar ta kalli Umma data nutsu tana kallonta cikin farin cikin yau tasake tadaina kuka.
Ita kuwa murmushin fara samun nasara tayi cikin shirinta na tarwatsa rayuwar neesah datayi.
*********
Zaune take a palo tana waya da asmy mamy na asibiti burin aiki Anty mamy ma takoma,ummi kuwa tana 'dakin mamy waya takeda Jamaal.
Abba ne yashigo palon ta datse wayar datake ta gaidasa tareda cewa,
Abba dama inason gobe zan koma makaranta kuma gashi motana taqi tashi.
Neesah keda zaki bar gari wace makaranta kuma,
Kibari idan kinje can saiki dora.
Cikin dakewa tace,
Abba ni anan nafison na qarasa karatuna Kuma dan Allah Abba kabarni nayi zamana anan.
Kallonta yayi ganin da gaske take yace,
Naji amma nama fasa abinda nayi niyya na barinki anan har Jamaal ya dawo tashi jeki ki hada kayan gobe zakibi ummi Ku koma can kafin Jamaal 'din yadawo.
Magana zatayi ya daka mata tsawa tayi dakinta cikin baqin ciki da takaici.
*R H F W F*
Mamuh馃拫
[3:20AM, 4/1/2018] 鈥�+234 816 253 8316鈥�: *_DACEWA_*
_(when east meets west)_
_By_
_Mamuh geee_
*_Viawattpad@mamuhgee_*
*Balkeey Shuwerh I sincerely heart you*鉂�
*14-15*
Tun acikin daren take kuka shiyasa koda ta tashi da safe idanuwanta sun kumbura.
Fushi take da kowa a gidan dan haka ko breakfast bata fitoba.
Ummi taso zuwa ta rarrasota amma mamy ta dakatar da ita ta hanyar miqewa ta nufi 'dakin.
Zaune ta tarar da ita gaban mirror 'daure da towel alamun wanka ta fito.
Akwatinanta mamy tajawo ta bude wardrobe ta kashe kayan ciki tsaf ta jere matasu a akwati ta rufe akwatinan ta matsar gefe tareda zama bakin gado ta fuskanci neesah.
Hawayen datake dannewa suka gangaro mata ta 'dauke kai daga kallon 6angaren mamy.
Neesah,
Neesah hakan dakike qoqarin yi baida banbanci da abinda su taheer sukai mana na fasa auren 'yarmu a ranar 'daurin aure.
Mune iyayenki dasukafi duk wani mai sonki qaunarki amma kike qoqarin bijirewa buqatarmu akan wani dalilinki na banza,
Shi Jamaal 'din da kike rainawa kina masa kallon wanda kikafi qarfi tabban idan bakiyi ahankiba wataran saikin zubar da hawaye akansa illaima na sonsa illaima na qaunarsa.
Jajayen idanuwanta ta kalli mamyn dasu murya a karye tace,
Mamy dan Allah Ku tausayamin kadaku yankemin hukuncin dazai lalata farin cikina wlh ba laifina bane dana kasa sonsa,
Nayi iya qoqarin dannewa amma na kasa kodan sbd ummi amma wlh mamy bana son ko sunansa naji ana fada amatsayin mijin danake aure.
Takaicin neesar ne yafara kama mamy amma sbd son ta rarrasheta saita dake tace,
Neesah ki daure kiyiwa iyayenki biyayya kodan yanda dadyn Jamaal yayi saving 'din abbanki daga humiliation 'din dasu taheer suka tanadar mana a idon mutane,
A 6angare 'daya haka zaki sakawa ummi da tsantsar soyayyar datake yi miki tun kina qanqanuwa,
Neesah ko kunyarta bakyaji na yanda kika fito kai tsaye kika nuna bakya qaunar 'danta datake matuqar so.
Hawaye suka gangaro a fuskar neesah batareda ta gogeba murya a qarye tace,
Mamy har abada bazan qi jinin ummi ba amma wlh mamy bana sonsa amatsayin abokin Rayuwa.
Tsuke fuska mamy tayi tareda miqewa tsaye tace,
Tunda lallashi baya yimiki sai ayimiki yanda zakifi ganewa,
Ki tashi ki saka kayanki 10:00 flight 'dinku zai tashi zuwa Lagos.
Kuma wallahi a matsayina na mahaifiyarki ban yafe ki ce komai ba akan tafiyar nan.
Ficewa tayi a fusace takoma Palo.
Baqin ciki da takaicin datake ciki bamai faduwa bane ta danne abinta cikin ranta tareda 'daukarwa kanta mugayen alqawaririka akan Jamaal dabaimasan tanayiba danshi tuni ya aje zancen auren a gefe ya maida hankali akan alamuran gabansa.
Abba sosai yayi mata nasiha hakama mamy duk da tana fushi da ita.
Nasir ma na gida a ranar sbd Saturday ce ba school
Sosai yashiga damuwar tafiyar antynsa duk da kullum sai sunyi fada sbd shegen son girmanta da rainasa datayi Wanda shi kuma bayason hakan dan yace so yake shima Idan ya qara girma yazama handsome cool guy kaman Jamaal.
Har suka iso Lagos batace qalaba hakama batai ko guntun hawayeba sbd alqawarin datai na bazata qara zubar da hawayenta a banxa ba.
Ahmed yazo 'daukarsu daga airport danshi tuni suka dawo tareda dady.
Anty nee ya hanya?
Qin kulasa tayi sbd akwai 'yar tsokana a tsakaninsu itada Ahmed 'din sbd shi ya iya bi da ita a yanda takeso.
Murmushi ummi tayi tace,
Ahmed kadaka dami baby bata cikin yanayin tsokana yanxu.
Tofa ummi yanxu fa sai kowa ya kama kansa sbd 'yar gaban goshi tazo kowama yanzu mai laifine Idan ya ta6ata.
Harara neesah ta 6alla masa duk da tana cikin damuwa.
Daria yayi dan yaga hararar yace,
Sorry Anty babba kada idon su juye.
Koda suka iso gida dady baya nan mai aikin ummin ce inna rabi ta iso tana musu barka da zuwa cikin farin ciki.
Babban gidane mai 'daukeda part uku,
First one na Jamaal ne mai 'daukeda parlour da qaton bedroom aciki,
Second one 'din kuma na Ahmed ne kusan irin na Jamaal shima,
The third and last one 'din shine babba sosai na iyayensu,
Babban Palo ne a qasa da 3 bedrooms kowanne da toilet,
'Daya shine na Ummy sai 'dayan na khadija ne 'yar qanwar dady da ummin ke Riqo.
'Dayan kuma na saukar manyan baqin ummin ne,.
Sama kuma gaba 'dayansa na dady ne.
Ko'ina acikin gidan ka kalla abin burgewa ne gashi koyaushe qyal qyal a tsaftace sbd dukkanin 'yan gidan masu tsaftane uwa uba inna Rabi datake kula da tsaftarsa dan a yini zatai gyara ba adadi duk da bawai wata 'daudar yayiba.
Inna Rabi dattijuwa ce datake aiki a gidan tun Jamaal na yaro Wanda yanxu ta zama tamkar 'yar uwa a gidan sbd sabo da yarda dasukai da ita bama kamar Jamaal da yake qaunarta har ransa sbd yanda take tsananin qaunarsa tun yana yaro haryanxu daya girma muddin yana gari to duk hidimarta tasace.
'Dakin ummi neesah tashige dan dama ko zuwa tayi anan take sauka dan haka yanxuma anan zata zauna.
Tsabar karma ayi mata maganar zama inda ba nan 'dinba ta bude 'dayar wardrobe 'din Ummy ta Jere kayanta.
Tu6ewa tayi ta shiga toilet tayo wanka tana fitowa tayi sallah kafin ta zauna gaban mirror ta 'dan shafa mai sbd yanayin garin da sanyi.
Doguwar rigar shaking material tasaka mai yankaken wuya da qaramin hannu ta zari wayarta ta fito Palo sbd yunwa datakeji.
Daidai qofa sukai kusan karo da khadija dazata shigo bedroom 'din sbd dawowarta kenan daga schools ta tarar dasu ummin sun dawo shine takeson mata barka da dawowa cikin farin ciki.
Cak ta tsaya ganin neesah batareda ta tsammata ba,babban abin mamakinta neesah dasu ummin sukaje aurenta itace tafara fita harta biyosu.
Jiki a sanyaye tace,
Anty neesah barka da zuwa.
Daqyar neesah ta amsa tana qaqalo murmushi kafin ta wuce zuwa palon tana kiran inna Rabi.
Khadija kasa qarasawa 'dakin tayi ta juya 'dakinta jikinta a matuqar sanyaye ga hawayen datake qoqarin maidawa.
Tana shiga 'daki tai wurgi da handbag 'dinta tareda zama bakin gado zuciyarta kamar zata qone.
Khadija ba mummuna bace hakama bazaka kirata da kyakkyawa sosaiba saidai tanada diri mai matuqar kyau da 'daukar hankali,
Khadija tun tashinta ta taso da tsananin hassadar aneesah sbd ganin gata,kyau,dukiya,wayewa duk neesah tasamu uwa uba tsananin soyayyar da kowa ke mata bama kamar ummin wadda ita bata samu koda rabinta agurin ummin ba.,
Duk wa'innan abubuwan kanta tasowa sbd babban burinta ne tazama rich,
Pure natural Beauty,
Classy and popular,
Sbd kawai tasamu damar zama matar Jamaal data reni sonsa tun batasan kantaba,
Amma duk neesah ce tasamu wannan,
Babban abinda yasama take jin sauqin damuwarta shine babu alamar so ko kusa atsakanin Jamaal da neesah saima rashin kula da ko oho da juna dabatasan yazatai da rantaba,
Halin khadija ne hassadar duk Wanda yafita saidai takasance mai dannewa da 6oyewa sai dai abin yayita cinta arai,
Neesah Sam khadijar bata gabanta kodama can,
Duk ranar data aje baqin halinta zata saki jiki suyi fira harda ummi,
Idan kuwa hassadar ta taso to ranar ko abinci bataci saita wuni ta kwana tana duhun rai,.
Shiyasa ko yanzu sarai ta lura da batai farin cikin zuwantaba.
Ita kuwa khadija ranar 'daki kasa fitowa tayi bare cin wani abinci,
Babban baqin cikinta kyawu da burgewa dataga neesah ta qara kuma yanxu ummi batada time 'din kowa saina neesah da abinda takeso.
Abu 'daya ta qullace a ranta bazata ta6a bari jituwa ko wani shiri bare soyayya yashiga tsakanin Jamaal da neesah ba sbd Jamaal natane ita khadija.
## *_Neesah_*
## *_Ayeesha_*
## *_khadija_*
馃尣 *R H F W F*馃悇
_Don't forget to follow,vote and comments@mamuhgee#*via wattpad.._
Mamuh馃拫
[3:20AM, 4/1/2018] 鈥�+234 816 253 8316鈥�: *_DACEWA_*
�? �? �? _(when east meets west)_
_By_
_Mamuh geee_
*_Viawattpad@mamuhgee_*
*Thanks mum AbdulAhat,,,*
*16-17*
Da safe qin fitowa khadija tayi koda ummi ta tambayi lafiya sai cewa tayi kantane ke ciwo kuma yau batada lectures a school.
Neesah kuwa lafiya lau tai baccinta dan kusan rabin 6acin ran datazo dashi ya tafi sbd anan ne tasan ummi zatai mata duk abinda takeso bamai hanawa ciki kuwa harda raba wannan qaddararren auren zubar mata da girma.
Kodata fito Palon guraren 11 bakowa sai inna Rabi dake kaida kawon ayyukanta.
Zama tayi a sofa suna gaisawa da inna Rabin ta'dora da cewa,
�? �? �? Inna ummi fa?
Ummi takoma sama bayan fitar alhaji.
Ok, to Ahmed fa shima yafita ne?
Aa bai fitaba tukun dan baima shigoba yayi karin safe,
Yau alhaji da ummi kawai sukai kari,
Ke,
Ahmed da khadija duk kun musu tawaye yau.
Murmushi tadanyi tana duba kiran daya shigo wayarta tace,
�? �? 聽聽
�? �? 聽聽 Ammnnnn Inna pls kibani breakfast 'dina a 'daki Idan kuma Ahmed yashigo kice yasameni ina nemansa.
Tana gama fada ta miqe tai bedroom tareda amsa wayarta.
Sunkuyar da kai khadija tayi cikin nauyin zuciya sbd fitowarta kenan ta tarar da neesah da innar a palon suna magana.
Bayan shigewar neesah bedroom kasa qarasawa palon khadija tayi sbd 'dan guntun qarfin zuciyarta da ganin neesah ya wargaza.,
Juyawa tayi batareda taje taci nata breakfast 'dinba takoma 'daki tana danne hawayen dake qoqarin gangaro mata ba.
Koda Ahmed yashigo palon saida yaci abinci kafin ya nufi 'dakin ummi gurin neesah,
Zaune take gaban mirror har lokacin waya take dasu amirah.
Katse wayar tayi tajuyo gurinsa tace,
聽聽
�? �? Ahmed so nake ka kaini gurin da zan samu lafiyayyen gyaran kai a garin nan.
Ajiyar zuciya ya sauke yana cewa,
I thought wani laifin nayi danaji kiran nan.,
Ok to kishirya nan da 50 minutes zan dawo nakaiki yanxu zan kar6o saqo wani urgent saqo ne.
Dan Siririn tsaki tasaki tana 'daure fuska tace,
�? �? �? Karka kuskura ka shanyani.
Daria yasaki yana ficewa yace,
�? �? �? Insha Allah Anty neesah.
Ko 50 minutes 'din bai cikaba yadawo har lokacin ummi na sama sai kawai sukai ficewarsu.
A wani babban saloon daya hadu matuqa suka Parker ta fito tashiga tana yaba gurin ba laifi yayi.
Kasancewar weekdays ne babu mutane agurin sbd aiki
Mutum 'daya ta tarar a gurin ana mata gyaran kai itama.
Kallo 'daya neesah taiwa gurin ta 'dauke kai tareda kallon 'daya daga cikin 'yan matan shagon tayi�? mata bayanin abinda za'ayi mata.
Kusan atare atare suka miqe bayan an kammalawa ko waccensu abinda yakawosu.
Tsaye suke gaban tangamemen mirror 'din gurin..
Siririn gyalen data yafo batareda 'dankwaliba neesah ke gyarawa,
Ita kuwa 'dayar powder ta qara shafawa tana gyara zaman hot red jambakin dake lips 'dinta.
Idanuwansu ne suka shiga cikin na juna ta cikin mirror gaban ko waccensu saidaya buga da qarfi.
Neesah ta fara 'dauke fararen idanuwanta cikin 'dan tamke fuska zuciyarta na tsananta nauyi.
Ita kuwa budurwar kafe neesah tayi da ido tunani kala kala na shigota.
Atare suka fito neesah ta nufi mota tashiga tana qara 'daure fuska
Ahmed kuwa harzai tada motar ya hangota ta nufo motarsa
Saurin kallon neesah yayi yaga fuskarta a tamke tana duba wayarta.
Fita motar yayi ya qarasa batareda yabari taqarasoba ya sakar mata fuska sosai.
Lafiyayyen murmushi tasaki tana kallonsa tace,
�? 聽聽 Ahmed kaima tunda yayanka ya jonamin hawan jini yayi aure ka ajeni ko?
Dariya yayi yana cewa,
�? �? �? Ayeesha me zai sakaki hawan jini tunda na tabbatarda captain bazai gujekiba kinyi masa mugun kamu da sanyin halinki alhalin kuma ba sanyin halin ne dakeba.
Dariyar data qara fitar da zallar wayonta da budewar idonta tace,
�? 聽聽 Ahmed ina jinjina maka ako yaushe da kai kadai ke iya ganoni akoda yaushe,
Amma to ai ba laifina bane sbd captain Idan bada sanyin halina da biyayyar danake masa ba aida tuni nabi sahun sauran matan dayaqi jininsu.,
Dan haka kadakaga laifina soyayyar yayanka ce,
Kuma akansa zanmayi fiyeda hakan.
Jutawa tayi ta nufi motarta tana wani shu'umin murmushi tace,
Saimun sake haduwa brother Ahmed..
Shima murmushin yasaki mai ma'a noni ya koma mota sukabar wajen.
Ayeesha kabir 'yace 'daya tilo a gurin alh kabir zaki tsohon Senator anan Lagos,
Ayeesah tun tana yarinyarta ta iya kirsa da 6oye qiyayyarta ga maqiyinta,
Ta iya kwantar da kai da biyayya akan Abu muddin zata samesa sai dai Sam bata yafiya ko mantuwa akan Abu hakama Sam,
Ayeesha batada tarbiya ko kadan sbd gata da rashin kwa6a data taso cikinsa,
Kyakkyawace sosai hakama akwai wayewa da ilimi amma na boko kawai bana addini.
Tayi karatunta ne a qasar us inda acan ta hadu da Jamaal da farko Sam bata gabansa data lura da hakan saita ringa canza halayenta agabansa sbd ta lura shi mutum ne mai sanyi saita ringa nuna juriya,hakuri da biyayya harta samu tausayinta da soyayyarta ta shiga ransa batareda ya shedar da ainihin halintaba.
Ba wasu shekaru yabata ba saidai suzo mate amma yanda take kwantar da kai ta nuna masa girmansa sosai shiyafi burgesa da ita sbd shimafa akwai son a girmamasa.
Ahmed da ayeesha sun San juna sosai sbd aminiyarta husna da�? Ahmed 'din yake tsananin so.
Jamaal kawai ayeesha ke boyewa halayenta sbd batada mutumci ko kadan uban kowa bata tsoro shiyasa Ahmed yasan halinta tsaf kuma yayi iya qoqarin fahimtar da Jamaal amma yakasa sbd Sam baimaga fuska ba.
Amma tabbas shi yasan ayeesha guba ce dazata iya tarwatsa gidansu gabaki 'daya bama kamar neesah dake basa tausayi da takaici gurin son girmanta da girman kanta tareda daukar kanta ayeesha ta lalata mata rayuwa.
*******
Kusan watanta uku kenan a Lagos ba laifi rayuwar garin ta'danyi mata saidaima miskilanci daya qaru dady ya nemar mata admission university 'din nan tafara karatunta ka sabuwar motar daya siya mata duk da haka wani lokacin tareda Ahmed suke zuwa dama can shima yake karatu kuma yanxu shine abokin yawonta kusan kullum suna gurin yawon shopping dan ita qa'idarta ne ko Biro or bathroom slippers