Showing 45001 words to 45946 words out of 45946 words

Chapter 16 - Dacewa Book One Complete Hausa Novel

Mamuhgee   

31 Oct 2025

113

tafadawa mama abinda tayo bataji da'diba amma saita canza salo tafara gyaran neesah 'din ciki da waje tareda iya kissa kala kala da abubuwan Jan hankali,,


Cikin qanqanin lokaci neesah ta masifar canxawa tayi wani yellow yellow har wani qyalli take ga uwa uba salon Jan hankalin miji data iya yanxu.


Baidawoba saida tayi wata uku da dawowa.

Part 'din Ahmed aka gyara musu bayan ancire komai ancanza
Part 'din yayi masifar kyau yakoma na amare sbd dama girmansa 'daya Dana Jamaal Palo da two bedroom sai kitchen store da dining area.

Abinci ta girka da kanta ta jera masa a dining 'din sashen ummi.

Dakinta tashiga tayo wanka da ha'daddiyar kwalliyar Riga da skirt na wani drylace ja dayayi mata kyau saita zubo gashinta ko 'dankwali taqi daurawa.


Fitowa tayi Palo ta kwanta kusada ummi tareda 'dora kanta qafafun ummi Rana chatting da wayarta.

Sabon direban ummi ne yaje ya 'daukosa daga airport,,

Da sallam yashigo palon fatarnan tasa taqara wani haske sai sheqi takeyi yayi wani sahallen kyau daya sa takasa 'dauke idonta akansa saida mama ta'dan zungureta da qafa tai saurin 'dauke idonta tareda cigaba da ta6a wayarta.

Kusada ummi ya zauna bayan ya gaida mama da inna Rabi.

Cikin tsananin son 'danta ummin tace,

Jamaal ya hanya?

Wani lallausan murmushi yasaki dayasa wayarta su6uce mata ta miqe dan barin gurin sbd zuciyarta zata iya bada ita.

Saidata miqe tsaye ya 'dago fararen idanuwansa ya 'dora akanta qirjinsa yayi masa wani mugun nauyi aransa yace,

_son yarinyar nan zai kashenifa sbd a buge nake marus da soyayyarta gata ita kuma yar rainin wayo_..

Wata tafimiyar 'daukar hankali yaga tanayi ya ha'diye wani mugun yawu tareda miqewa yace,

Ummi bari naje na 'dan huta kafin nazo naci abinci.


Wanka yayi ya kwanta amma yakasa bacci.

Sai yamma yashigo Palon cikin qananun kaya baqaqe sai qamshi yake ahankali.

Mama ce kawai a palon ummi tafita inna rabi kuma na kicin tana aikin abincin dare.

Dining ya nufa mama tace,

Bari nakira neesah tazo tayi serving naka tunda bata komai....

Fitowar neesah ce cikin wani three quarter red jins da farar vest tana waya ya katse zancen mama.


'Dauke kansa yayi daga gefen datake yana dubbba wayarsa.

Neesah kije mijinki zaici abinci ki zuba masa.

Kallon fuskarsa tayi taganta a 'daure gabanta na faduwa ta nufi dining 'din tazuba masa hartabar gurin bai 'dagoba..

Bayanta yabi da kallo qasa qasa tareda lumshe idanu.


Kwanansa biyu da dawowa amma har lokacin fuska nan a 'daure take bareta sakaran zai aje fushin ya dubeta.


Yau da maraice zaune suke a palon suna kallo itada mama nashan fruit's salad a bowl 'daya kan dining ummi na kan kujera zaune inna kuma na zaune qasa.


Shigowa yayi yaci ado cikin wata lallausan Australian shadda coffee brown sai qamshi yake yaci yau harya gaji fuskarsan har wanni annuri ke fita acikinta.

Kallonsa tayi taji gabaki 'daya jikinta ya mutu.

Kusada ummi ya zauna ummi tace,

Ina zuwa haka Jamaal da maraicen nan?

Murmushin gefen baki yasaki ahankali yace,

Zanje gidan alh mansur ne abokin dady yace naje nadubo 'yarsa data dawo daga Sudan karatu yabani idan harna amince zan aureta.


Kusan atare neesah da mama suka sarqe jin wannan mummunan batu ummi kuwa tsuke fuska tayi tace,

Kaikuma ka amince 'dinne?

Eh ummi..

Sake tsuke fuska tayi tace,

Idan kai ka amince matarka ta amince ne.....

Tun kan ummi taqarasa ta taso harta tuntu6e mama na riqeta tace,

Na rantse da Allah ummi ban amince ba kuma wlh ba amincewa zanyiba
Ni wlh ma fushi yake dani ummi dan allah kice ya aje fushin wlh nagaji.

Daria abin yaso basa sosai amma ya fuske
Ummi da inna kuwa dariya sukayi sosai mama ta kalleta alamar kin kwafsa,,

Qasa tayi da murya cikin rasa abinyi tana 'dan sosa kai tace,

Mama wlh mantawa nayi sbd tashin hankali yanxu shikenan ajina ya zube ko?

Daria mamar tayi tace,

Wannan bazai faruba har abada neesah.

Miqewa yayi zai fice sbd dariya da mamakin dayake fuskewa karsu fito.

Ummi ce tace,

Allah Jamaal tunda tace tagaji ta tuba karna kumajin labarin wata 'yar alh mansur.


Kunya tasata shigewa 'daki bata fitoba sai dare hartayi shirin kwanciya mama tace tafito taje takaiwa Jamaal coffee 'din da yasa inna ta dafa masa.

Badan tasoba taje sbd sai yanxune takejin kunyar abinda tayi 'dazu dan idontane ya rufe Sam ta manta da wani aji da kunya.


A palo ta aje ta juya zatabar sashen saigasa ya fito daga bedroom dagashi sai dogon wandon rigar bacci fari qal.

Harzata juya yace,

Meyasa zaki sako ummi cikin zancen nan?

Turo baki tayi tace,

Nifa su6utar bakine.

OK tunda su6utar bakine kenan naje na cigaba da Neman aurena k.....

Da gudu ta fa'da jikinsa ta rungumesa qanqam batareda tabari yakai qarsheba.

Ajiyar zuciya yasaki ahankali dan yafita azabtuwa da rashinta.

'Dagota yayi yakalli fuskarta batareda yasaki tasaba yace,

Gwara tun wuri ki hkr dan maganar aure ba fash.....

'Daga qafafuwanta sama tayi takai fuskarta setin tasa ta rufe bakinsa da nata..

Zaro ido yayi cikin mamaki amma salon datake masa yasa idanuwansa lumshewa.

Kasa shareta yayi ya tallafota jikinsa tareda kar6ar ragamar sauran aikin duk da salonta yatafi dashi matuqa.

Ba kunya anan takwana amma da wurwuri takoma duk da haka saidata hadudasu ummi a Palo.


Tun lokacin gurin mijinta take kwana suci soyayyarsu ganin abin nasu ba kunya ummi ta garga'data takoma can gabaki 'daya kafin daga baya suka wuce abuja dagacan suka koma uk.


Tunda suka koma suka bu'de babin sabuwar Rayuwa harsaida takuma samun wani cikin suka dawo gida haihuwa

Cikin yardar Allah ta haihu aka samu junior Ahmed.





*_ALHAMDULILLAH_*
*_ALHAMDULILLAH_*


_*Anan nakawo qarshen wannan labari duk da dai labarin Nada tsawo na gutsureshine sbd lokaci daya kawo na azumi dan haka ina fatar zamu amfana da fadakarwar dake cikinesa sa6aninsa kuwa Allah ya tsarkakemu*_


*_Nagode Allah daya bani ikon kammala wannan labari cikin amincinsa,Kuma ina godia ga dukkanin masoyana Dana littafaina wainda nasanin da wainda bansaniba_*..


*_godiata ina miqata ga kowa da kowane sbd tsayawa rubutasu jan lokacine dan haka nagode qwarai da gaske.._*




????????
*_HAPPY BIRTHDAY MEELA ADEEL_*?
_(nacika alqa....)_?




_*MAMUH GEEE*_?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login