Showing 12001 words to 15000 words out of 45946 words

Chapter 5 - Dacewa Book One Complete Hausa Novel

Mamuhgee   

31 Oct 2025

120

a fusace tace,

Ka fitarmin a mota before I decide to do sumtin crazy.

Hannuwanta biyu ya kamo da sauri daidai Jamaal ya bude motar.

Saurin sakin hannuwanta yayi cikin sigar tsoro yana qoqarin fita daga motar.

Duk da bata tsoron Jamaal sosai ta firgita da yanayin daya samesu saidai batajin zata nuna masa hakan yaji 'dadi saita 'daure fuska tamau zatai magana ya fixgota waje tareda jefa mata key 'din motar ummi da handbag 'dinta yashiga motarsa harya fara tafiya saiya tsaya tareda qarewa Habib kallo tacikin glass yaja motar da mugun speed yabar gurin.








Mamuh馃拫



馃尣 *R H F W F*馃悇



_Don't forget to vote, follow and comments_
[3:21AM, 4/1/2018] 鈥�+234 816 253 8316鈥�: _*DACEWA*_
_(when east meets west)_



_By_
_Mamuh geee_


*Viawattpad@mamuhgee*



*24-25*
Tunda take arayuwarta ba'a ta6a wulaqantata kamar yauba.,

Yau ita neesar da kowa ke rububice qaninta Jamaal ya wulaqnta cikin dubban mutane,

'Dagowa tayi zuciyarta kamar zata qone takalli Habib dake tsaye gefe yana sakar mata murmushin mugunta sbd buqatars data biya na yanda Jamaal yagansu.


Zeey ce ta qaraso da sauri takamata a kidime tana cewa,

Lpia neesah?
Ina motar?

Har lokacin kallon Habib take sbd wata sabuwar tsanarsa da qiyayyarsa datakeji.


Kuka takeson yi sbd zuciyarta dake mata zafi sosai amma tsabar taurin rai taqiyi sbd gani take taci baya idan tayiwa Jamaal kuka.


Tsabar baqin cikin ko motar ummi daya bar mata bata kallaba ta hau drop ta nufi gida tanajin tsanarsa shima nashiga ranta.


Harta isa gida tsanar Habib da Jamaal na kai kawo cikin ranta

A harabar gidan ta tarar dashi yana waya har lokacin fuskar nasa a ha'de take.

Kai tsaye shi ta nufa itama fuska a murtuqe.


Sarai ya lura da gurinsa ta nufo ya qara ha'de fuskarsa sosai.


Zata fara mgna ya 'dora mata oily eyes 'dinsa cikin tsuke fuska yace,

What?

Rantane yakuma 6aci tama rasa abinda zatai masa sai kawai ta juya a fusace tai cikin Palo.

Siririn tsaki yaja yanajin tsantsar takaicinta tareda qyanqyaminta na shigarsa cox yanxu yafara tunanin abinda yasa aka fasa aurenta shine shi aka maqala masa,.
Motarsa yafada yafice daga gidan.


Khadija dake tsaye qofar parlor tana kallonsu jitayi qirjinta yayi mata nauyi tayi 'dakinta da gudu tana danne hawayenta.

Neesah ta ganta taja tsaki tareda fadawa 'daki itama sbd kukan dake qoqarin zuwar mata itama tana dannewa.


Baki ummi dake zaune Palo tasaki tana bin qofofin 'dakunan nasu da kallo cikin mamakin abinda ke damun kowaccensu.


Tana shiga 'dakin ta sulale qasa tareda sakin kukan baqin ciki,
Tabbas yau taqara tabbatarda bazata iya Rayuwa da Jamaal ba sbd bazata iya 'daukar wulaqancinsa ba.



Da safe ummi hankalinta tashi yayi matuqa sbd da wani mugun zazza6i su duka suka tashi bama kamar neesah da har lokacin bata daina tsiyayar hawaye ba.


Khadija kuwa duk zazza6in dake cinta hakanan ta shirya ta gudu school sbd ganin neesah zai iya 'Dora mata hawan jini.


Zama ummi tayi tana kallon neesah jiki asanyaye tace,

Baby kidaina kukan nan ki sanar dani matsalarki nayi alqawarin magance miki ita muddin batafi qarfina ba.


Lumshe rinanun idanuwanta tayi hawayen dake ciki suka gangaro batareda ta bu'desu ba murya a karye tace,

Ummi in gaf da rasa numfashina,
Ummi rayuwata bazan ta6a samun farin cikiba muddin ina zaune da auren Jamaal akaina,

Ummi bazan iya Rayuwa da Jamaal ba sbd halayenmu sun nesa da juna,

Bu'de idanuwanta tayi ta 'dorawa ummi murya na rawa tace,

Ummi kisa araba aurena da Jamaal wlh bazan iya rayuwar aure dashiba.


Sosai jikin ummi yayi sanyi takalli neesah jikinta na tsananta sanyi tana karanto iya gskia neesah ke fadar zancen.


Baby tabbas yau da inada dama dana rabaki da Jamaal amma kasancewata mace na rasa wannan damar saidai ina miki alqawarin samun farin ciki matuqar kikayi hkr kikai biyayya.


Rintse idanuwanta tayi tareda zamewa takoma kwance.
Ummi ma jiki amace ta miqe ta fice.



Jamaal kuwa a ranar ya tunkari dady da zancen auren ayeesha kai tsaye dadyn yace ba yanxu ba.

Bai tsaya 6ata time 'dinsaba ya kira abban neesah yafada masa kai tsaye,

Abban neesah kuwa babu wani shamaki ya amince tareda alqawarin zuwa wani sati sbd ganawa da iyayen ayeesha.


Mamy dataji sosai tashiga damuwa sbd sanin halin neesah na girman kai bazai ta6a bari taji 'dadin rayuwar aureba gashi har za'ayi mata kishiya da wuri haka batareda tasan wani da'din aurenba.

Abba bayan yakira dady sunyi mgn shima dadyn ya amince ummice ta tsaya tsayin daka akan bata aminceba.


Sam Jamaal yanxu baicika zama gidanba sosai sbd Fushun da ummin keyi dashi akan mgnar.



Yau zaune suke Palo ummi na lalla6a neesah akan tasha magani inna rabi kuwa sai dariyarsu take.

Khadija Ce tafito 'dakinta tazo ta zauna kusada ummi duk ta hargitse ga wata uwar rama datai.

Kallo ummi tabita dashi cikin damuwa da tausayinta zatai magana inna Rabi tarigata da fadin,

Ummi 'yayanki dai lpia tayi musu qaranci musamman ma khadija duk tabi ta rame.

Hmmmn inna Rabi wlh ita khadija nama kasa sanin damuwarta har gwara baby ita nasan matsalar aurentane da jamaal....

Wata mummunar qwarewa khadija tayi wadda ta haddasa mata wani yunqurin amai ta sbd jin maganar ummi ta qarshe wai Jamaal mijin neesah.

Ummi dake zancen Sam bata luraba sbd hankalinta nakan neesah sake shan magani taci gaba da fadin,

Sannan yanxu dan tsabar rigima yace wani auren zaiyi kafin yakom......


Kusan atare neesah da khadija suka aware gaba 'daya ruwan dake hannunta suka xube had glass cup 'din nafashewa itakuwa khadija miqewa tayi ta nufi janyar bedroom ko gani batayi sai kawai su ummi ganin sukai ta yanke jiki ta fadi asume.




Mamuh馃拫



馃尣 *R H F W F*馃悇



_Don't forget to vote, follow and comments_
[3:21AM, 4/1/2018] 鈥�+234 816 253 8316鈥�: _*DACEWA*_
_(when east meets west)_



_By_
_Mamuh geee_


*Viawattpad@mamuhgee*



*26-27*

A rikice sukayo kanta ummi na kiran sunanta da qarfi amma Sam ko numfashi babu alamar yana tareda ita.

Shigowar Ahmed yasa ummi kallonsa a kidime tana nuna masa khadijar sunkutarta kawai yayi yafito su ummin suka biyosa zuwa asibiti.


Har suka fice neesah na zaune bata motsaba sbd baqin ciki da takaicin datake ciki na zancen auren na ummi tace zaiyi,
Imagine ace ita qaninta zaiwa kishiya dan ya rainata,
Baqin cikinta 'daya da auren nasa shine friends da sauran mutanen dasuka santa amatsayinta na babbar yarinya yanxu zasu riqa ganin itadin ma ba kowa bace a gun Jamaal 'din data raina,,,wato yafita zama 'dan rainin wayo,
To wlh bari ummi tadawo bazaiyi auren nan ba saiya saketa.


A zafafe ta miqe ta nufi hanyar bedroom taji an fixgota harsaidata fa'do masa cikeda tsoro ta 'dago idanuwanta suka shiga cikin nasa daya kafeta dasu,

'Daure fuska tayi tareda fixgewa da qarfi itama tana watsa masa irin kallon rainin dayake watso mata tace,

Karka kuma ta6ani dan ni ba sa'ar ta6awankace ba so better stay within your limits and karkayi tunanin 'dan na hakura nadawo nan yana nufin na amince da zama da wannan auren sunan....

Fixgota yakumayi ta fado jikinsa ya matseta tareda kallon tsakiyar idanuwanta cikin ra'da yace,

Banajin kinada jikinda yakai matsayin ta6awa a guna cox na girmi tunaninki sbd ni mutum ne mai qyanqyami and I don't like wat is common to people especially downgrade pple and you see this body of urs is like a common market tomatoes,
And maganan zuwanki nan I think its your problem not mine.

Tureta yayi daga jikinsa ta fa'di qasa kan hannunta ya bugu,
Magan ganunsa sun qona ranta matuqa kamar ita ya kalleta yace kamar tomatoes take a kasuwa.

Cikin qunan rai ta 'dago da idanuwanta dasuka ka'da zatai mgn ya tamke fuska tareda watsa mata kallon zallar qyama ya fice daga palon batareda tasamu ta fadi 6acin rantaba.


Hawayen baqin ciki da tsanarsa suka gangaro mata ta miqe ta fa'da bedroom tana jin kamar zuciyarta zata qone.



A asibiti saida khadija ta share 5hours kafin ta farfado kuma tunda ta farfado take hawaye ummi tayi lallashi da tambayar harta gaji amma ko magana khadijar taqiyi.

Sallamarsu Dr yayi bayan ya tabbatar musu da damuwa ce tayi mata yawa kuma tana gab da illatata matuqar ba 'a dau matakin rabata da itaba dan haka suje gida su rarrasheta ta fa'di damuwarta.


Har suka iso gida hawayen khadija sun kasa tsayawa gashi xuwa lokacin idanuwanta da duskarta tayi mugun kumbura sbd kuka amma takasa daina hawayen.

Hankalin ummi sosai ya tashi gashi suna dawowa sun tarar da itama neesah ta rufe kanta a 'daki tana kuka.

Zama ummi tayi bakin gadon bedroom 'din khadija tana kallon khadijar dake kwance ta rufe idanuwanta ga hawaye na gangarowa cikinsu jiki a sanyaye tace,

Khadija na roqeki ki fadamin damuwarki sbd haryanxu zuciyata takasa yarda da cewarki ta wai karatu ne yayi miki yawa a school.


Bu'de idanuwanta tayi daqyar sbd kumburinsu murya a dashe tace,

Ummi Ki yarda dani Allah karatune yamun nauyi a school,
Ummi da inada wata matsalar bayan wannan dana fa'da miki sbd banda wata uwar data wuceki a yanxu.

Ajiyar zuciya ummi tasake tana shafo kan khadijar cikeda kulawa tace,
Idan kuwa karatu ne khadija saidai kiyi hkr dan kuwa kinbarsa kenan sai zuwa nan gaba qila dan banga amfanin karatunba matuqar yana barazana ga lafiyarki da rayuwarki saiki haqura kawai.


Lumshe idanuwanta tayi cikin tausayin kanta dan ko ummi batace tabar karatuba batasa ran idanma taci gaba dayi zata fahimcesa sbd halinda take ciki.


( _hassada mugun ciwo ce 'yan uwa dan Allah Ku tsarkake zukatanku_)



Neesah ma duk yanda ummi tasojin dalilin kukanta kasa fa'da tayi sbd har lokacin bata daina hawayen baqin cikin maganganunsa.




*******
Kallon maganin hannun husnah tayi ta yamutsa fuska tace,

Do u know wat husna I don't think I can use this dan gskia nima inada qyanqyami bare Wanda zanbawa duk da basani zaiyiba amma ina fargabar yaji warinsa a cikin koma mai zan saka masa aciki.


Harararta husnah tayi tace,

Wannan kuma matsalarki ce dan nidai nasan irin su Jamaal masu shegen girmankai da jan ajin tsiya sai an hada musu da asiri suke lanqwasuwa..

No no no, zeey tafada tana saukowa daga gado tace,

Samun kyakkyawan matsuguni a zuciyar irinsu captain hanyar 'dayace,
Wato amfani da kirsa tareda kwantar da kai ka nuna biyayyarka.

Yes zeey nima I prefer that akan wannan 'din sbd wannan zai sakashi ya soni ne kawai nikuma nafison qiyayyarta tafi soyayyata a zuciyarsa duk da nasan ba wai yana sonta bane hasalima yanxu tsanarta da qyamarta yake tun ranar da ya kamata da Habib.,

Zeey dake shafa lips stick gaban mirror ta juyo tace,

Nakuma tabbatarda saita gwammace Rayuwa a baqin kabari da zama dashi sbd muguwar tsanarta dazamu saka masa just kwantar da hankalinki qawata luck is on our side.


Shu'umin murmushi tasaki tareda 'daga wayarta ta danna kiransa..

Fira tashiga jansa cikin kwantar da kai duk da ita kadai ke firar iyakacinsa sauraronta sbd baya iyawa da surutun ayeesha.



....lectures suka fito ta lura da yau miskilancin yafi na kullum ta kalleta cikin nuna kulawa tace,

Neesah akwai abinda yake damunki ne? You look pale.

Yamutsa fuska tayi batareda tace komaiba har suka isa mota kafin sushiga amirah takirata tana 'daukar wayar tasaki ajiyar zuciya tana cewa,

Thank god amirah you called ina tsananin buqatan magana dake.

To inajinki''amirah tafada daga can 6angaren.

Amirah asmy tazo lagos tun jia ina buqatan magana da ita since dukkanku bakwa kusa tace she's coming over today and now I can't reach her number so jst send me aunt fateema's Address I can't wait.

Zan turo miki address 'din yanxu idan kin isa ki kirani nima inason mgn da ita before su wuce Paris tomorrow.

Ok bye.


Duk wayan datake hankalin zeey nakai amma a kallo bazakai tunanin hankalinta na gunba.


Sai gaf da magrib suka fito school duk da gajiyar dasuka kwaso neesah tace bazata gidaba harsaitaje taga asmy sbd gobe zasu wuce Paris da iyayenta gurin checkup nata na ciwon heart datakeda shi.


Sbd nisan anguwar da hold up yasa har akai magrib suna hanya.

Kallon zeey tayi a fakaice sbd ganin tunda suka fito take exchanging texts a waya.

Suna gaf da isa gidan text yashigo wayanta tai banxa dashi,
Zeey ta kalli wayar takalli neesah cikin tsokana tace,

Neesah kamar anyi miki text ko?

Lumshe fararen idanuwanta tayi tana cewa,
Ummn anjima zan duba idan nasamu time.

Qaqalo murmushi tayi tace,

Inaga kiduba cox may be wani mahimmin saqone qilama amirah ce.

Juyowa neesah tayi ta kalleta sbd ganin damuwarta nason ta bude saqon.

'Daukar wayar tayi ta bude massage 'din.

""" _hey neesah itz me asmy ga address 'din dazaki sameni nan sbd ba gidan Anty fateema na saukaba_""

Sake maimaita karantasa tayi kafin tasaki 'dan qaramin tsaki tana juya kan motar zuwa address din da asmyn ta turo mata yanxu.


Ajiyar zuciya zeey tayi a 6oye tareda turawa Ayeesha saqo ta maida wayar cikin Jakarta.



Zaune yake a palonsa yana kallon news dawowarsa daga masallaci kenan sallar magrib..

Wayarsace tayi ringing ganin unknown number yasa bai damu da daukaba.

Cigaba akai da kira yaqi 'dauka saiga kira da number ayeesha.

Saida yasaki qaramin tsaki ya 'daga wayar tareda ha'de fuska sosai sbd muryar namiji dayaji.

A ki'dime mutumin yake fadin,
Bawan Allah koma ya kake dame wayarnan kazo yanxu da gaggawa a waffroad sbd tana ana gaf da lalata mata rayuwarta.

Kallon wayar yayi tareda zarar key yafito da mugun speed.




Suna isa address 'din lokacin ana sallar ishai ga anguwar tsit babu mutane da yawa.

Parking tayi tareda 'daukar handbag 'dinta tafito ta nufi cikingidan tana mamakin maiya kawo asmy irin wannan mataccen gidan sbd gidanma is like uncompleted building.

Ihun mace taji a 'dakin dake farkon shigowa gabanta na faduwa ta nufi 'dakin ta tura qofar 'dakin da sauri taja baya sbd ganin ayeesah a kwance kayanta duk a 6arke ga bakinta na jini alamar bugu sai maza hudu tsaye akanta.



Koda ya parker bai lura da motar ta agurinba ya nufi cikin gidan da saurayin yayi masa kwatance daidai nan qartin suka fito da gudu jikinsa har rawa yake ya nufi 'dakin

Kuka take tana kakkama jikinta tana cewa,

Na roqeki kadakisa su keta haddina ki taimaki rayuwata kiji tausayina koma mainayi miki ki.....

Cikeda mugun tausayinta da sabuwar soyayyarta ya nufeta tareda rungumota jikinsa idanuwansa na ka'dawa zuwa jajaye .

Rintse idanu neeesah dake tsaye tayi.

Bude idanuwansa yayi akanta cikeda xafin rai ya taso ya yarfa mata wani lafiyayyen marin daya 'dauke ganinta na daqiqu...






Mamuh馃拫



馃尣 *R H F W F*馃悇



_Don't forget to vote, follow and comments_
[3:22AM, 4/1/2018] 鈥�+234 816 253 8316鈥�: _*DACEWA*_
_(when east meets west)_



_By_
_Mamuh geee_


*Viawattpad@mamuhgee*




*28-29*

Zafin marin yasata zubewa qasa kan gwiwowinta idanuwanta suka ka'da jajir amma Sam taqi yarda hawaye zubowa fuskarta
Kallonsa take ido cikin ido zuciyarta na quna,
Ji take kamar numfashinta zai bar qirjinta sbd mummunan baqin cikin Marin daya sharara mata.


Fixgota yayi tareda jefar da ita qasa idanuwansa sun rufe sosai da 6acin rai ya nufota tareda kamo wuyan rigarta ya 6arka da qarfi yace,

Kinason kisa ayi mata fyade sbd bakisan ya baqin cikinsa yakeba to yau zan 'dandana miki baqin cikinsa.

Yaga rigarta yayi qirjinta ya bayyana yakai mata wata muguwar cafkar da zafinta yasa hawayen datake dannewa suka gangaro hakama idanuwanta a rintse suke tsabar baqin ciki ko qoqarin hanasa bataiba sbd gangar jikinta data daina aiki.


Ganin idanuwansa a rufe suke da 6acin rai zai iya abinda yace 'din tayi saurin sakin wani sabon kuka mai ta6a zuciya tareda rungumosa ta baya cikin kuka take fadin,

Captain ba halinka bane karkayi na yafe mata koma wacece ita,,

Juyowa yayi ya rungumeta cikin jikinsa yana daidaita numfashinsa kafin ya dauketa ya fice gurin da ita.


Suna fita zeey ta qaraso gurin da sauri tana kallon neesah cikin mamaki da kulawa tace,

Neesah?

Jajayen idanuwanta ta bude zeey tai saurin ja baya cikin zatana sbd tsantsar fushi,6acin rai tareda qiyayya data gani kwance a fuskar neesah.

Murmushi tayi aranta dan tasan wannan qiyayyar ta Jamaal datake gani a idon neesah bamai gushewa bace koda zata gushe to tabbas ba yanxuba.

A fili kuwa rungumo neesah tayi tana fashewa da kuka tace,

Neesah dan Allah karki cemin abinda nake zargi shi ya sameki?
Neesah dana sani da bazan bari kishigo ke 'daya ba.

Rintse idanuwa takuma yi ta jinjina tarin qiyayyarsa dake bin jini da jijiyoyinta.

Gyale zeey tajawo tareda rufawa neesar takamota suka fito har lokacin idanuwanta a lumshe suke.

Seat 'din gaba ta zaunar da ita kafin tazagaya ita taja motar.


Allah yasa koda suka isa gida ba kowa a Palo ta kaita har bedroom 'dinta tayi saurin fitowa ta nufi gida dan Sam ba yanxu take buqatar Jamaal ya Santa ba sai zuwa gaba.


Gaban mirror ta tsaya tana kallon jikonta da duk rabi yake waje sbd 6arkar da Jamaal yayiwa rigarta,.

Ihu tasaki mai qarfi tareda 'daukar qwalbar turare dake gaban mirror ta fasa madubin tana fashewa da wani irin kuka mai qarfi da ciwo dan wannan abin da Jamaal yayi mata baida bambanci da fyade.

A rikice ummi da inna Rabi suka nufo 'dakin amma gam suka jishi a rufe.

Bugawa ummi tahauyi tana kiran sunanta amma ko jinsu batayi sbd kukan datake tana dukan madubin.


Ahmed daya shigo palon yayi saurin qarasowa yana tamvayar lapia.

Ahmed bude qofar nan tun kafin ta illata ko kashe kanta.

Palon dady ya nufa da gudunsa ya 'dauko keys masu yawa yafara gwadawa jikinsa na rawa danko keys 'din da qyar suke tsayawa a hannunsa.


Jan jikinta data farfasa da kwalba ga gashinta duk a hargitse ta fa'da toilet tareda tu6ewa ta shiga bathtub dake cikeda ruwa ta kwanta tareda nitse kanta sbd bazata ta6a iya Rayuwa da wannan tsananin baqin cikinba da tarin tsanar datakeji tana yiwa duk wani Wanda ya danganci Jamaal 'din bare shi kansa dan gwara mata mutuwa da rayuwa.


Da qyar yasamu key 'din daya bu'de dakin har ture ture suke wajen shiga 'dakin
A tsorace ummi tace,
Nashiga uku ni ayshatu me zangani?

Toilet 'din ta nufa da sauri ba wani 6ata lokaci ta fada ai da gudu ta qarasa bakin tub 'din tareda sakin salatinda ba qarashe da qarfi tana kiran sunanta.

Inna Rabi ma qarasowa tayi cikin tashin hankali tasaki kuka tana cewa,

Allah yasa ba mutuwa 'yar nan tayi,

Ahmed da duk a ru'de yake ji yake kamar ya fa'da toilet 'din murya a qage yace,

Ummi Ku kamota Ku fito da ita mana sai Ai asibiti da gaggawa.

Qoqarin kamota suke amma sun kasa sbd jikinsu dake matuqar rawa sbd tashin hankali gata ba kaya bare Ahmed 'din ya 'dauketa,

Cikin kuka ummi tace,
Ahmed maza kiramin Jamaal yazo da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login