Showing 1 words to 3000 words out of 30436 words

Chapter 1 - Amani Book 3 Hausa Novel Complete

Takori   

13 Dec 2024

151

 AMANI

3



Littafin

SUMAYYAH ABDULKADIR
(TAKORI)
[email protected]
07030137870
TAFIYA ZUWA DIFFA
M
asu iya magana suka ce tafiya mabudin ilmi, wasu kuma suka ce tafiya yankin azaba. To duka dai Alhaji da iyalin sa da yan uwan sa babu wanda basu fuskanta ba a hanyar su ta zuwa jihar Diffa ta kasar Nijar. Ga Karin ilmi suna ta samu a kan garuruwa da Baba Idi ke musu bayani kasancewar ya taba zuwa fatauci Nguigmi daga Maiduguri tun yana saurayi, ga kuma yanayi na wahalar zafin ranar sahara wadda tasa hatta A/c din motar daina bada sanyi ta ke yi lokaci-lokaci saboda zafin rana da zafin rairayi irin na sahara. A hakan ma don sun yi zagaye ne ta Maine-Soroa da Nguigmi basu bi ta cikin Bama din Maiduguri ba.
Kasancewar sun fito tun asubah, tafiya non-stop, kuma mota lafiyayya, zuwa yamma sai gasu a cikin Maine-Soroa, makwabtan Diffa, anan ne suka tsaya suka yi sallah azahar da laasar da ta riske su a hanya, suka sayi gasashshen naman rakumi da madarar rakumi mai dumi sabuwar tatsa da sabon cukui a nan cikin garin Maine-Saroa suka ci, suka sha, Mukhy har Shayin su na Tubawa ya saya ya sha, dama kuma dai sun yo guzurin su yadda ya dace na abinci da abin sha, wanda tun dare Rakiya ta shirya musu suka taho da su, wadanda ba masu lalacewa ba, snacks ne da soyayyun kaji (pepper chicken), don haka basa tare da yunwa har suka shiga jihar Diffa.
Shigar su garin ke da wuya komai ya soma kwancewa Mukhtar, (his in-born character) ya soma aiki a kan sa, ta yadda hatta gashin jikin sa dana kan sa sai da ya mimmike da duk wani gashi da ke jikin sa. Amani da ke gefen sa yana tuki, ta lura da yadda Mukhtar ke canzawa a yanayin sa da halittar sa, wata irin kamala da nutsuwa suka bayyana a tare da shi, suka lullube ainahin Mukhy saurayi nan dan gaye suka maida shi cikakken MOUKHTAR din sa, tsigar jikin sa har wani tashi take yi kamar mai jin sanyi. Jinin Issouffou Massaoudou ya soma circulating yana kurdawa a cikin jikin sa, yana sauya shi daga normal Mukhtar din sa da kowa ya sani zuwa Mainan Diffa na asali. Amani bata san me Mukhy yake kwancewa daga leda ba ta ga dai Mukhtar ya saka hannu ya janyo wani farin kyakkyawan tsohon amawali (rawani) daga cikin leda, ya kashe motar su a gefen titi.
Rawanin nan ya hau nannadawa cikin iyawa da kwarewa, saida ya nade kyakkyawar fuskar sa tsaf, sai tsinin karan hancin sa da manyan idon sa ne kadai ya bayyana, kwatankwacin yadda taga nadi a fuskar mafi yawancin jamaar garin maza, wato nadin rawani irin na buzayen asali ko kuwa Tubawa, ko kuwa a kira su da yadda aka san su da shi wato Larabawan Diffa. Sai bata yi mamaki ba, don kuwa ta san cewa baa canzawa tuwo suna, Mukhtar duk dadewar sa tare dasu, idan aka taho gida, shi buzu ne na hakika.
Ya ja motar suka cigaba da tafiya. Baba Idi na tsokanar sa wato kowa ya bar gida-gida ya bar shi, kyawun kowanne tsuntsu yayi kukan gidan su. Mukhtar yayi dan murmushin miskilanci ta cikin amawalin sa, bai ce komai ba. Amma ya yarda da maganar Baba Idrisu cewa kukan gidan su har da kururuwar gidan su yake yi yanzu.
Zuwa lokacin sun shiga tsakiyar gari, Amani ta bude hanci da ido tana shan kallon alummar wannan jiha dake cikin janhuriyyar Nijar, ta fahimci cewa sittiru, kamanni na halitta da dukkan aladar su ta barranta da ta inda ta fito, suna ta gudanar da harkokin su na yau da kullum cikin sukuni da godiyar Ubangiji, domin kuwa alummar wannan yanki na Diffa mafi yawa talakawa ne likis, masu abin yi daga kiwon dabbobi (livestock production), kasuwancin waje (export trade), jimar fatar rakumi da sauran su. Sun kuma kasance maabota biyayya ga shuwagabannin su, wato sarakunan yankin Diffa.
Shiga nan fita can Muktar bai manta hanya ba, bai manta koina ba, kamar wanda ake bankado komai daga cikin kwakwalwar sa ana nuna masa, kamar jiyan nan ya tafi daga Diffa. Haka yake ji yanzu da ya dawo cikin ta kamar ba shekara goma sha biyar ba, haka rayuwar sa ta baya ke rewinding kamar kaset din video a cikin kan sa, tana tuna masa duk abinda ya faru a baya.
Sai suka hau wani mikakken titi dodar mai nisa, wanda daga shi Amani ta soma hango wani dogon kasaitaccen gini, wanda tsahon sa da fadin sa ya kai daidai da kilomeita (2,988), wani katafaren gini suke dosa wanda daga can sama aka rubuta da harshen larabci Al-iimaarat-al Diffa wato Diffa Emirate da harshen turanci. Suka cigaba da tafiya Amani na cewa a ran ta wato in ka zo garin, sai ka fara kaiwa sarki gaisuwa dole, kafin a bar ka ka tafi cikin gari inda ka zo.
Can kuma ta ce Watakila kuma Baban sa bawan sarki ne, shi yasa ya tura shi birni neman kudi maimakon ya makale abin sa su yi bauta tare.
Ai kuwa ta kasa shiru, ta kasa barin tunanin ta a ran ta, lokacin da ta ga sun hau titi fetal wanda ya mika har cikin fadar Diffa. Masu tsaron babbar kofar masarauta ta farko suka tare su a kofar shiga, amma da Mukhtar ya sauke tagar sa, suka ga wannan nadin dake kansa da wannan amawalin da kuma tambarin da ke jikin rawanin, sai kawai suka daga musu kofa suka wuce ciki. Gasunan gasu nan har gate na biyu, shima kamar na farko daga ya sauke glass sun ga irin nadin sa da amawalin sa sai suka daga masa kofar masarauta suka nausa ciki.
Daga nan sai gate na karshe, wanda shine na uku kuma daga shi sai fada.
Anan ne aka dan takura da binciken bayan motar su kafin Mukhtar ya sauke glass, Amani na cewa Daddy ashe dan naka bawan sarki ne? Ko ko dan bayi ne ka ga duk sun san shi. Mamma Jalan ta kusa zagin ta, don ita jikin ta ya fara bata abubuwa masu yawa, amma Amani tana haukan ta irin wanda bata san ranar shiryuwar ta ba. Baba Idi ne ya ce mata shi dan bayi ba mutum bane? Jaira marar mutunci. Sai tayi dif!

Wani tsohon bafade tukuf, ya dogaro cikin kayan dogarai na jikin sarki sosai ya zo bakin tagar da Muktar yake, yace Samari, na gan ka da Amawalin gidan nan, Amawalin dana baiwa Mainan Diffa, amma ban shaida ka ba, ko zaka bude amawalin in gan ka sosai, kafin mu yi muku iznin yin parking a kofar fada?
Sai kawai Mukhtar ya sa hannu yana warware rawanin kan sa, yanayi wa tsohon nan murmushi idanun sa fal hawaye. A hankali ya ce Baba na Katchalla! Tsoho Bafaden nan sai ya fadi kasa, yana fadin Allah ya taimaki Mainan Diffa, barka da dawowa hasken Diffa!
Wannan batu da wannan tsohon bafade ke yi shi ya janyo hankalin sauran fadawa duk suka taho da gudun gaske, wajen hannu goma ne ya budewa Mukhtar kofa a gigice, suna faduwa suna tashi suna fadin Hasken Diffa ya dawo, barka da dawowa hasken Diffa, barka da dawowa tauraron Diffa, Maina ka sauka lafiya ka taka a hankali.
Allah ya kare tauraron Diffa, haske maganin duhu, hadari malafar duniya.
Daga nan aka bude musu kofa a ka bazawa Mukhtar babbar riga aka kareshi ya sauko daga motar.
Tuni har wani ya sheka labari cikin gida wai ana tsammanin Mainan Diffa ya dawo, zancen nan nan da nan ya isa kunnen Sarki Issouffou Massaoudou, wanda ke kwance a turakar sa a lokacin bayan ya sha magani, ya soma shirin dan mikewa ya kwanta kafin lokacin da zai fita fada. Sai ga wayar sarkin fada wanda ya manta shekaru nawa rabon da ya kira shi a waya, don a kaida fadawa basa kiran sa a waya.
Kamar bazai dauka ba amma sai yayi tunanin banza bata kai zomo kasuwa haka kawai Katchalla ba zai kira shi ba, sai ya daga. Yana dagawa kuwa sarkin fada ya fashe da kuka yana fadin nayi rantsuwa da Allah ga Maina ya dawo, ka san dai cikin kowanne hali bazan kasa gane shi ba ko da bai zo da rawanin sa ba.
Sarki Issouffou Massaoudou a kwance yake, amma sai ganin sa yayi a bakin kofa ya manta cewa jar hula ce da ake kira Dara da rigar shan iska mara hannu kadai a jikin sa, ya kama hanyar kofar da zata sada shi da hanyar fada.
Fadawan da ke tsaron kofa sun kidima da ganin fitowar Sarki a haka yana ta surfa uban sauri, aka kuma rasa wanda zai tare shi ya tuna masa babu amawali da alkyabbar sa a tare da shi. Farin dattijo amma ba tukuf ba, kyakkyawan Balaraben Diffa na gaske wanda yawan shekarun sa bai boye kyawun surar sa na lokacin kuruciya da tsananin kamannin sa da Mukhtar ba.
A lokacin har an shigar dasu Mukhtar fada, baka jin komai sai tashin kirarin da fadawa ke zubewa a kasa suna yi masa.
Hadari malafar duniya, hadari sa gaban ka inda kake so, gaba salamun, baya salamun, haske maganin duhu Zaki dan Zaki, Majina gishirin yaro, tsawa mai ratsa gidan arna. Kunun bagaruwa cika ciki har makogaro. Dan Sarki jikan Sarki kuma sarki mai jiran gado.
(Wannan kirari ba da hausa suke yin sa ba, suna yin sa ne da vernacular language din su wato Chadian Arabic daya daga cikin yaren Diffa Arab). Wani babban bafaden kuma yace Zakin duniya makiyanka fadawan ka, ana kin ka ana rusuna maka, ba yin kan ka bane yardar Allah ne da adduar iyaye ya dawo mana da kai. Allah Ubangaji ga Mukhtar dan Issouffou Massaoudou ya dawo gida. Hasken Diffa ya dawo, duhu ya yaye!.

Amani da iyayen ta da ke kallon abinda ke faruwa kamar a majigi, sun kasa ko motsin kirki. Amani ta lura hatta tafiyar Mukhtar ta canza kan ta da kan ta, ba irin wadda yake yi a baya bace. Me ke faruwa ne haka a gaban idon ta? Wanene wannan Mukhtar din? Wane alamari ne tattare da shi haka?
Jalan, wadda ke tura Alhaji cikin wheelchair zamu iya cewa mamakin ta ragagge ne, ko dama a tunanin ta tun ganin ta da shi na farko, bai yi mata kama da komai ba sai dan sarauta maabocin kyakkyawar nasaba, duk wasu attributes na sarauta sun bayyana kan su a tare da shi da halayen sa.
Baba Idi da Baba Sahura sai zare ido suke don kuwa Sahura har fitsari ta yi a wando data ga wani katon Zaki mai rai a zaune, amma bai ci kowa ba, sai daga baya ta gane zane ne da aka yi da ceramic (architect) amma kamar real image na zaki mai rai, tambarin Issouffou Massaoudou Kenan, wato Zaki dan Zaki, zakin Diffa.
Alhaji Usman dai hawaye yake sharewa a fakaice, ba tare da ya bari an gane kuka yake ba, Mukhtar ya shammace shi yadda baya zato, ashe dan sarkin Diffa ne mai jiran gado yake masa bauta iya bauta shekaru kusan goma!
Dadin abun ya kyautata masa ya kaunace shi, irin yadda ko yan wan sa na jini bai yiwa hakan ba. Allah ne ya hada shi da Mukhy amma bai taba kawowa ran sa wai dan sarki bane mai jiran gado. Yafi dangantawa ma da cewa bashi da kowa a duniya shiyasa baya ko so a yi masa zancen ya je ganin gida.
Karyar ku makiya da mahassada, karyar ku ta kare mahainta, yau Allah ya maido Mainan Diffa gida (Maina na nufin Yarima mai jiran gado a Diffa, kamar yadda Biyamaradi yake a Maradi).
Ire-iren kirarin da ake ta yi wa Mukhtar kenan har aka bashi kujera kusa data Sarkin Diffa, amma sai ya ki zama ya zube a kasa yana kukan farin ciki da godiya ga Allah.
A haka Sarki ya fado fadar, sarkin fada ya biyo shi da Alkyabbar sa da amawalin sa suka rufe kofar fadar aka hana kowa shiga bayan shigewar Sarki.
Yana zuwa da Mukhtar ya fara tozali, ya ce Mon pils (Da na) Mukhtar da gaske nake gani? Koko ire-iren mafarkai na ne? Sai yayi baya luuu! Zai fadi, kasancewar dama yana fama da hawan jini tun tafiyar Mukhtar wanda ake treating din sa tun lokacin, cikin zafin nama Mukhtar ya tare mahaifin sa ya rungumo shi a kirjin sa, (for the first time) a rayuwar sa da jikin sa ya shafi na mahaifin sa, suka zube a kasa tare.
Nan fadawa suka kare scene din da hannayen manyan rigunan su aka umarci kowa ya fita sai manyan fada kadai. Mukhtar sai firfita yake ma sarki da rawanin sa yana fadin ka yafe ni Ya Abiy, na dawo kenan babu inda zan kara zuwa, koda zan cigaba da rayuwa yadda kake so.
Da kyar aka samu Sarki Issoufou ya zauna a kujerar sa, sannan ya yi umarni da ayi wa wadanda suka kawo Mukhtar sauka ta alfarma a babban masaukin bakin sa.
Ummami na can cikin gida amma tuni labari ya kai mata ta bakin Jakadiyar Sarki marikiya ga Mukhtar, wadda ta shiga turakar ta kai tsaye ba tareda ta jira an mata iso ba, ta same ta tana haki, tana cewa yanzu wani bafade ya gaya mata wai Maina yana cikin fada bata san ko da gaske bane don yace an kulle fada, an hana kowa shiga.
Mowar Sarki, sai ta mike ba tareda rakiyar kowa ba aka ga ta kama hanyar fita, akwai wata boyayyar kofa ta cikin turakar Sarki wadda yakan shiga fada ta cikin ta wani lokacin, ta can Mowar Sarki ta bi ta isa fada, Mukhtar sai ganin Ummami yayi a gaban sa, ta dubi Mukhtar shima ya dube ta ta taba shi ta tabbatar dan ta ne kwalli daya a duniya Mukhtar dan Issouffou Massaoudou, wanda ya bar su yau shekaru goma sha biyar! Kafin Mukhtar ya ambaci sunanta wanda ya kakare a makogaron sa ya kasa fita, Ummami ta fado jikin sa luuu! A sume.
Mukhtar yana fadin Ummami kada ki yi min haka.. kada ki mutu bamu gana ba, bamu fayyacewa juna zuciyar mu ba. Na yi nadamar tafiya ba tareda na fayyace muku abinda ke rai na ba, kuma kun bani uzurin ku! Yanzu da girma ya same ni na san kuna da uzuri fiye da nawa. Aka yayyafawa Ummami ruwa ta farfado sai ta rike Mukhtar ta fashe da kuka.
A lokacin an fita dasu Amani da Mamma da Daddy da su Baba Idi zuwa masaukin da Sarki yayi umarnin a kai su. Wani hamshakin gini ne na sarauta da yaji kujeru royal chairs na alfarma, da dakunan barci da aka kawata da gadaje na kasaita, babu abinda babu a wannan guest house din ga dakunan barci rututu. Aka shiga sauke musu kabakin abinci har da naman Dawisu, aka ce su kintsa kafin washegari Sarki ya gama ganawa da Maina zai neme su.
In ka ga fuskar Amani a cikin guest room dinnan ta koma kamar jikakken tsumma, sabida yadda tayi cooling, tana ambaton Ya Salaamu sallim, a cikin ran ta, harda su istighfari, tana neman wanda zasu hada ido ko karin bayani ne ta samu, amma ina! Mamma Jalan ko kallon ta taki yi, sai hidima take da mara lafiyan mijin ta. Wata irin nadama da dana sani suka zo suka lullube Amani, mutumin data raina ta ke wulakantawa, ta cewa shege, ta cewa bawan gidan su, kai babu irin sunan kaskancin da bata kira Mukhtar da shi ba shekara da shekaru ashe ya fi ta kyawun nasaba, dan Sarki ne jikan sarki mai jiran gado, wanda in nasaba zaa bi ba ikon Allah ba, da bata isa zama matar sa ba.
Ta daga ido tana kallon wannan kasaitattar hamshakiyar masarauta wadda ko masarautar Katsina bakidaya data sani bata kama kafar ta a kasaita da shaharar mulki ba.
Kada dai Allah ne yake yi mata talala da laifukan ta, kalaman ta marasa Tauhidi da girman kan ta? Yanzu wace izza zata kara yiwa Mukhtar da gorin nasaba? Dama Jalan ta ce mata ta guji ranar dana sani.
Ya Ilahal alaameena na tuba! Na tuba Ya Ubangiji na tuba, daga yau baki na ya daina fadar abinda ba alkhairi bane a kan kowanne dan adam, na daina raina kowa, na daina tunain nafi kowa gata!
Ita kadai take furta wadannan kalaman kamar zautatta sabon kamu, cikin kidima, Mamma da Daddy duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login