Showing 12001 words to 15000 words out of 30436 words
ji a kasan dogon wuyan ta yana sunsunar ta, kafin ya saki wani wahalallen kiss, a asan wuyan nata ba tare da shi kan sa ya shirya ba, ya gangaro a hankali ya saka fuskar shi saman kirjin ta, bai san lokacin da yayi hakan ba domin tun dazu yake kokawa da kan sa a kan yin hakan, amma zuwa yanzu duk wata dauriya da duk wani azanci da ya san ya mallaka ya kwace masa, jaruntaka da ego da pride din sun subuce masa, wannan yasa ya yarda hakan wani miracle ne da Amani ke da shi a kan sa.
Wato duk irin fushin da yake da ita baya jin zai kasa kusanta kan shi da ita, in har sun kebe.
Mukhy ya tafi da yawa, Hajiyar kuwa da ke guilty na damun ta yanzu bata yi wani hobbasa na hanawa ba, ya manta cewa a dakin Ummami suke sai faman wannan smooth lallausar fatar da taji wankan madara dana lalle yake yi, yana hadawa da sunsunar ta kamar ba zai daina ba, sai dai kamar wancan karon, yanzun ma sai da kwakwalwar sa ta tuna masa AMANI FASKARI ce fa! Sarkin rashin mutuncin duk duniya, har yanzu bata yi hankalin da zai sake mata ba irin haka, balle yanzu da take matsayin kanwa a gare, shi tana bukatar ya bar ta ta kara hankali har zuwa lokacin da zata kara sanin ciwon kan ta afin ya soma irin wannan rayuwar da ita.
Mukhtar ya saki Amani ta hanyar komawa bisa sofa din da ya tashi, ya kama kan sa da dukkan hannayen sa yana jin haushin kan sa, ya nutsa yatsun sa cikin tarin sumar kan sa ya runtse idon sa, ya tuna abinda ta gaya masa ana I gobe zasu taho nan, cewa tana regretting abunda ya shiga tsakanin su a Saliyo, me yasa yake bari ajin sa ke barewa muddin ya kebanta da Amani? Me yasa yake kasa controlling emotions din sa a kan ta, a irin wadannan lokutan???
Amsar da baya son samu daga kasan zuciyar sa dole ita ta soma pumping a cikin kan sa, wato duk da halaye da dabiun Amani Usman Faskari marassa kyau da baya so, wadanda a yawancin lokuta suke saka masa tsanar ta, ya fahimci duk da hakan still yana matukar son ta da kaunar ta.
So kuma kwakkwara guda daya, mara algus, wanda ya san daga Allah ne ba don Alhaji ba.
Shi kawai tun sanin sa da ita a gidan su yake da wani extra feeling a kan ta, ko ganin ta yayi daga nesa sai gaban sa ya fadi duk da kasancewar ta maras tarbiyya maras mutunta mutane. Idan kuwa ta matso kusa da shi, to kuwa sai ya ji hakan a dukkan jikin sa.
Kunya ta sa Amani sanya doguwar rigar Ummami a baibai, wadda ta yayibo daga wardrove din ta, tana jin wata irin kunyar Mukhy, wadda a baya bata da ita a kan sa, tana zuwa tana baibaye ta. Da kyar Mukhtar ya samu ya koma daidai, ya mike yana faman daure fuska kamar yadda ya saba, ya ce,
na tambaye ki kin min banza, nace wai ina Ummami na ta shiga ne?
A kokarin ta na son adopting kyawawan dabiu daga yanzu, wadanda ta fahimci gaisuwa ga miji na cikin su a gidan sarautar Diffa, kamar yadda suka dauke ta a matsayin kyakkyawar alada, sai ta yi kasa da murya duk da har zuwa lokacin jikin ta bari yake yi, ta ce.
Yaya Mukhy ina wuni?
Bai amsa ba, don ko kyau ladabin bai mata ba, da yake bata saba ba, sai ma cewa da yayi a dan tsawace. Nace ina Ummami?
Amma a kasan ran sa yana mamakin gaisuwar data yi masan, wadda ya ji ta kamar daga sama, ko kuwa kamar wadda aka tursasa sai tayi, ta yi gaisuwar ne ta hanyar kokarin danne girman kan ta, wanda har zuwa lokacin akwai burbushin sa tare da ita, bai bar ta gabadaya ba, duk da ta yi wa kan ta alkawarin dainawa,
Ummami ta tai gun Mai ta bashi amsa murya na rawa da irin hausar gidan, bata gun Mai shima ya bata amsa, to ina jin tana dakin Mammah. Karo na farko a rayuwar su, da Amani ta yi masa Magana cikin kwanciyar jankali. Hakan yasa ya taso ya kara matsowa inda ta ke cikin son tabbatar da canjin da aka samu a tare da ita, na gaske ne ko gizo idon sa ke mata? Ya ce na zo in gay mata ne zamu yi tafiya Burkina-Faso, zamu kai Alhaji wajen mai magani, ko zamu jima, ban sani ba.
Ga dukkan mamakin Mukhtar tashin hankali da tsantsar damuwa ne suka bayyana a fuskar ta, ta ce har wata kasa? Amma ai Daddy is doing well a hakan da yake, not like before, tunda yana motsa komai nasa tafiya ce kawai baya iyawa.
Mukhy, ya kara matsowa jikin Amani yana jin dan sanyi a ransa na canjawar ta, ya ce,
Wa ya gaya miki tafiya ce kawai baya iyawa? Ai Mamma Jalan bata yi tsufan da zata yi zaman zuba ruwa a buta da da daga ruwan wanka da kika zabar mata ba, kin gane?
Kunya mai tsanani ta kama Amani ta harari Mukhy ba tare da ta sani ba, hararar da ta kara kunna shi dama ba wai ya zama satisfied bane yana so ko yaya ya sumbaci bakin nan nata na tsiwa kafin ya bar dakin, zuciya da ego da pride din sa na hana shi, tasa kai zata wuce shi don bata son cigaba da tsayuwa tare da Mukhy, kafafun ta rawa suke yi sakamakon kallon kurillar da yake bin ta da shi, sai Mukhtar ya riko hannun ta tana kokarin wucewa ta gaban sa.
Na gaya miki zan yi tafiya, amma ba wani fatan alkhairi ba komai, me ya kamata kice min ko ki bani? Allah ya kiyaye hanya kawai zan ce. Ni me nake da shi da zan baka Yaya Mukhy? Ya ce abunda zai mantar da ni kalolin rashin kunyar ki, da kamanni na da shegu. Ai Amani kamar jira take sai ta saka kuka tana cewa.
Allah ya gani ban san yaushe zaka bar maganar nan tabi ruwa ba Yaya Mukhtar, wai shi dan adam ba zai taba yin subutar baki ya hadiye ya ce ya mayar da su inda suka fito, a karbi tuban sa ba?
Yace in dai ke ce baki san tuba ba, tubanki shi ake kira tuban muzuru, baya taba cika sharuddan tuba na addini, don ko bayan wannan din da kika fada a Freetown, bayan mun dawo Katsina me kika ce min a dakin ki???
Wane cin mutuncin ne baki yi min ba ana I gobe zamu taho nan?
Ta gane ya koma neman rikici kuma, ya saki layin soyayyar da ke rinjayar sa da farko, tana kokarin cewa ta tuba tabi alah ta bi shi ego din ta na rinjayar ta, yana gaya mata kada Mukhtar ya ce don ta gan shi da matsayin sa na yanzu ne ta bashi hakuri.
Don haka ta hadiye bada hakurin data so yi a cikin zuciyar ta. Amma hakika Amani tayi nadama mai yawa, just bata san hanyoyin da zata bi ta yi expressing hakan wa mijin ya gamsu ba, da kuma yadda zata yi repenting kura-kuran ta, amma ai darasin rayuwa da karatun ta nutsu da duniya ta gama daukar sa ita kam! Da a ce tana da wayewa a shaanin aure, da tuni ta saukewa Mukhy hadda, musamman da ya kasance mai rauni wajen yawan son (body contact) da ita. To bata da wannan exposure din sai na iya rashin kunya.
Cikin rikici irin nasa kuma ya sake riko ta, wannan karon bakin sa ya hade da nata yana kissing, da wani irin zafin rai, kamar ta hakan ne zafin sheganta shi din data yi zai fita daga zuciyar sa, shi kadai ya san irin pleasure din yake samu daga irin wannan kiss din da yake yi wa bakin ta a karo na biyu kenan bayan wanda ya faru a Saliyo, wanda yake jin zakin sa ya fi na zuma, gardin sa ya fi na madara. Watakila kuma hakan ne kadai zai sa ya samu rangwame a zuciyar sa da gangar jikin sa na tasirin soyayyar ta mai zafi da ke damun sa, da kuma jin zafin maganar ta ta baya ta da yake yi akan maganar shege, yawan sumbatar ta na sakawa ya manta duk wannan, wani sako na zuciyar sa ya yarda cewa Amani masifa ce a gare shi.
Eh masifa fa, tunda maganganun ta na Saliyo kadai sun isa su sa ya tsane ta, ya shata babban layi a tsakanin su amma ina! Kullum sai in bai gan ta ba, yana iya jurewa rashin ganin ta na wani lokaci amma da zarar ya ganta din shikkenan ya rasa duk wani control na kan sa.
Ya cigaba da sakin zazzafan kiss din sa idanun sa a rufe, a kasan ran sa yana rokon Allah ya canza masa Amani, (from evil to good, and from devilish to saint), cikin wannna halin suka jiyo takun Ummami tana kokarin shigowa don suna jiyo kirarin da bayin ta ke mata daga waje.
Da sauri Amani ta hankade Mukhy, ya ce ta baya ta rago bayan duk kin gama tsotse mata Dan ta, na kan manta ke kanwata ce nake wannan aikin zubar da girman da ke, in sha Allah ta yi kai, daga yau ba zan kara ba. Ya dauki wayar sa a kan sofa ya nufi kofar fita, ya bar Amani da budadden bakin mamakin sa.
Mutum kamar mai iskokai, ya gama yamutsata yadda yake so har dakin uwar ta, kuma ya bita da wannan maganar, wai itace ta tsotse shi, ta yi dan murmushi tana cewa a ran ta Mukhy-Mukhy case ne shi wallahi, ko yaya ne dai, ni di kujera ce, dole a zo inda nake a zauna a kai na, duk da gorin hali da ake yi min din!.
Yana saka kai zai fita daga dakin Ummami na shigowa, sun kusa karo, ya yi maza ya ja baya ya bata hanya, ta ce to kai kana nan ashe, ana can ana ta neman ka, duk sun fito kai suke jira zaku tafi airport Ummami ke na zo nema ni, bamu yi sallama ba aah ka dai zo yin sallama da matar ka, to gani me zaka bani? Mukhy sai ya riko hannun Ummami, ya sumbaci saman hannun nata ya ce wannan sallamar zamu yi. Kunya irin na rashin sabo ya kama Ummami, amma ta yarda Mukhtar yayi rashin wannan soyayyar tata, bata nadama, amma tana tausayawa faruwar hakan a tare da shi, yau gashi ai Allah ya raya musu shi, ya zama magidanci cikin koshin lafiya.
Tabbas ka ki naka ne duniya ta so shi, amma mutanen duniyar ma ba kowadanne ne irin Alhaji Usman Faskari ba. masu maida dan kowa nasu, kodayake shima din saar sa aka ci don a baya halin mutanen duniya gare shi.
Da wannan tunanin take so itama ta kwatanta, wajen rike masa tilon yar sa da amana duk da cewa itama yar ta ce. To Amani zata ci tudun alfarma har biyu kenan a wurin su.
Ta dubi Amani dake ta sunkuye-sunkuyen kai, rashin gaskiya duk ya bayyana a tare da ita, da kyar in Ummami bata ga abin da ta gani ba, ta ce,
ina fatan kun yi sallama, zasu wuce Burkina-Faso ne. Yace Ummami wace irin sallama ce tsakanina da ita? Baki san Amani bata so na bane?
A firgice Amani ta dago ta kalle shi a tsorace, ya kuwa tsare ta da kyawawan idanun sa ya ce ko zaki ce karya nayi miki? Ba auren dole Alhaji yayi miki ba? Ko in gaya mata me kika ce da ni a Freetown gidan Faytoory?.
Idanun sa suka kada, suka kuma tsaya a kan ta, kamar yanzu ta fadi maganar, ita dai ta shiga uku ta lalace da Mukhy a kan wannan maganar, mana daya ya ki yafe ta. Amani ta hadiyi miyau da kyar, ta girgiza kai, idanun ta fal hawaye, ga mamakin ta tafiyar da zai yi Burkina-Faso har tsayin sati biyu shi ya fi damun ta da daga mata hankali a yanzu, ba wannan tone-tonen nasa da neman rigimar tasa ba.
Ummami duk da maganar ta buge ta kuma bata yi mata dadi ba amma ta waske, ta ce ta yaya zaayi hakan? Dole kanwa ta so Yayan ta yace banda wannan Ummami, ita bata son kowa daga kan ta sai kan ta da Amani ta ga zai tona mata asiri a gun Ummamin dake ganin mutuncin ta, sai ta saki kukan da dole zai dakatar da shi, kuka shiga yi riii-riii sosai, nan kuwa ba na komai bane na damuwar tafiyar sa ne.
Ko har yaushe Mukhy ya soma samun matsuguni irin wannan a ran ta, da har take jin damuwar tafiyar sa matuka gaya haka a kasan ran ta? ita kan ta bata sani ba! Ummami ta hau shi da fadan girma, inda take cewa cikin fada-fada kada ya kara gaya mata wani abu da ya shafe su, tunda ita bai shafe ta ba.
Sannan ta hau lallashin Amani, tace rabu da shi diya ta kin ji, gidan zai bari ki samu ki huta sosai Amani kamar ta cewa Ummami ita so take ma ta bi shi, babu wani hutu a nesantar ta shi sai karin damuwa da hakan zai zame mata, hakika yau ta samu kan ta a sabon yanayi, wato ta samu kan ta da enjoying dan short kiss din da yayi mata fiercely (a zafafe) fiye da wanda ya faru a gidan Mamma a Kenema, ita bata san ana soyayya cikin zafin rai ba sai yau.
Memories din hakan, dana sumbatar da ya yiwa kirjin ta, ya like a kasan ran ta, kamar har zuwa lokacin Mukhy sumbatar nata yake ke cigaba da yi, don har zuwa lokacin tsigar jikin ta da Mukhtar yayi sanadin tashin ta bai koma normal ba.
Ya saci kallon ta, kamar ya karanci situation din da ya bar ta a ciki, shima hakan take, ji yayi kamar ya ce da Mamma a tafi da ita su dan zauna tare, amma sai kawai ya share, yayi wa Ummami sallama sannan ya bar dakin ba tare da ya sake bi ta kan ta ba, yana so ya koma Mukhtar din sa na baya, mai daurarriyar fuska, rashin walwala, da cin magani, amma ina! Idan yana gaban Ummami yanzu, sai ya ji kan shi kamar yaron goye, farin ciki ya cika zuciyar sa, rayuwar sa ta haskaka ta zama cikakkiya, soyayyar da bai samu a kuruciyar sa ba ita yake samu yanzu wadda take yawan saka shi a nishadin da yake sawa ya manta previous situation din nasa.
Wannan yanayin nasa na rashin walwala da bacin rai a yanzu ya zama tarihi a tare da shi.
Ya gane hakan ne da ya ga har ya ga Amani duk da fushi da yake da ita amma kuma ya kasa ignoring din ta, karshe sai gashi ya bige da sumbatar ta, wanda ya jima da hana kan sa sake bari wani abu makamancin wannan ya shiga tsakanin su, sabida abubuwan data faffada masa ana I gobe zasu taho Diffa a dakin ta na gidan su sun kara kwaba waccan maganar ta farko.
Duk da cewa ya rama da mai zafi har fiye da nata tun a lokacin, daidai da yadda yake so ya rama din, amma tsatsar maganganun har yanzu bata bar ran sa ba.
Mukhtar, Alhaji, Mamma, Baba Idi da wadanda sarki ya wakilta su raka su har mutum biyar, sun tashi a jirgin sama zuwa makwabtan su wato Burkina Faso, ya zama sai ita da Ummami da Sahura da tarin bayi mata da ke shige da fice suna ayyukan su a bangaren Ummami.
Tunda Mukhy ya kira Ummami yace sun sauka lafiya bai kira Amani ba, hakan yana cikin sababbin techniques da ya dauka don yana so ya koyawa kan sa tolerance a kanta, ita kuma ya koya mata sanin darajar sa, har zuwa lokacin da zata koyi son shi don radin kan ta, irin son da ya samu kan sa yana yi mata, ba wai so na tursasawa ba ko na cin alfarma, ko don idanun iyayen sa da take tunanin bashi da su a baya, ko na dangantakar jini da ke tsakanin su.
Ummami tasa aka shirya musu zuwa wajen kishiyar ta wato Hajja Tarha domin Amani ta gaishe ta, an musu karba ta musamman a sassan Tarha ta kuma kira yar ta Saadiyya dake Guinea a waya ta hada su suka gaisa da Amani. Ummami ta yi haka ne don samar da sanayya tsakanin Amani da yayan Sarki guda biyu mata, wato Sayluba da kanwar ta Saadiya kasancewar su yan uwa biyu kacal da Maina ya mallaka a duniya. Kuma dai dama tsakanin ta da Tarha babu muguwar gaba ta azo a gani sai kishi, wanda baa iya kaucemawa, wannan sai Ummu Aymana, wadda