Showing 9001 words to 12000 words out of 30436 words

Chapter 4 - Amani Book 3 Hausa Novel Complete

Takori   

13 Dec 2024

159

dan uwan ta Maina ya dawo gida, ta ce sai ta haihu zata zo daga baya, tana cikin watan aifuwa.
Tunda aka soma shagulgulan bikin nan wanda zaa kwashe kwana bakwai ana yi Amani bata saka Mukhy a idon ta ba ko daga nesa, rabon ta da shi tun washegarin zuwan su Diffa, wato ranar da suka gana da iyayen sa, yana can cikin sarakuna abokan Baban sa da yayayen su saannin sa, wadanda iyayen ke kokarin kulla abota da zumunci mai karfi tsakanin yayan nasu, kamar yadda nasu iyayen suka yi masu.
Ba iya masarautun Nijar kadai Sarki ya gayyato ba har daga bangarorin masarautun Songhai, Mali, Gao, da Kanem-Bornu. Haka ya gayyato aminin sa Sarkin Burkina-Faso, wuri yayi wuri, taro yayi taro sai Rakuma ake kayarwa ana gashewa ana kyafewa. Abinci kuwa duk iya diban ka haka zaka gaji da diba ka bari.
Umami tasa an yi wa Amani kwalliya irin tasu, da kaya na shudin karen miski da sarkokin zinare har a hancin ta, an dorata akan kujerar Mowar Diffa, wato kujerar da Ummami take zama a kai koyaushe, abin gwanin ban shaawa, shagalin sai wanda ya gani.
Kwana bakwai aka kwashe ana wadannan shagulgulan na ban mamakia Al-Imaraat Al-Diffa, an nadawa Mukhtar rawanin sarautar jiran gadon mahaifin sa Mainan Diffa, wato dan sarki mai jiran gado.
**** **** ****

MATAR MAINA

Kuma shikenan don ya zama Maina ganin sa ma ya zama jan aiki? Amani ta tambayi Baba Sahura babu ko kunya, koda yake dama kunyar ta mata karanci ai, ranar da suka cika sati biyu a Diffa bata sanya Mukhtar a idanun ta ba. Kai ko daga nesa bata hango shi ba. Don ko yana son magana da Ummami baya shigowa sassan ta, don ma kada ya hadu da Amani, can a turakar Mai Diffa suke haduwa da mahaifiyar tasa su yi duk maganar da zasu yi.
Baba Sahura ta bantari farin goro sal, sannan ta fashe da wata shashashar dariya, ta dubi Amani tana mamakin rashin kunyar ta, wai yau ta murje ido tana cigiyar Mukhy a gicciye da idanu, ta ce,
ki na so ki gan shi fa kika ce? To kewar sa kike ko yaya abin yake? A dan yimin bayani?
Baba Sahura bana son irin wannan rainin hankalin naki, daga magana sai kimin wata fassara daban, na ga dai mutumin nan tare muka zo, kuma don shi muka zo, ai ya kamata ya dinga zuwa ganin lafiyar mu, in bai zo don ni da ya raina ba ya zo saboda ku da yake ganin girman ku
ni kike cewa na raina miki hankali? Wato har yanzu bazaki gyara halshen ki ga na gaba ba ko? To lafiyar ku ke da wa? Aa Uwa, ki cire mu cikin lissafin ki da rashin kunyar ki, mu kam ai muna gaisawa da shi a waya, bai banzatar da mu a kasar sa ba, ko dazun nan ya kira Jalan, yace ko tana son wani abu, ta ce cukui take so sabon yi, a kawo mata, kuma yasa an kawo shi faranti guda mai laushi.
Haushi ya kara turnike Amani, ita din dai ita kadai Mukhtar ya raina, kuma baya son ganin ta ko jin yadda take rayuwa a garin su mai shegen zafi, ta tashi ta bar mata wajen cikin kunan rai. Baba Sahura na kara kyakyatawa kyal-kyal-kyal don ta gano damuwa sosai a tare da ita.
Tun daga ranar kuwa duk sanda Baba Sahura ta ga Amani ta yi tagumi sai ta fashe da muguwar dariya.
Ummami kuwa, yanzu ta mayar da hankalin ta ne kacokam! Ga shirin tariyar diyar ta Amani, shiri na musamman take yi wa Amani, shiri irin wanda ake yi wa yayan sarakai in zasu dakin miji, masu yi mata gyaran jiki daga Maine-Saroa har su biyu ta kirawo ta ce daga yau har sati daya su gyara amaryar Maina, gyara na musamman fiye da wanda suke yi matai ta Ummamin, Sarki kuma ya saka ana ginin bangaren su a gefen nasa, wani irin kasaitaccen gini shiyasa har zuwa lokacin basu tare ba.
Amani a daya daga dakunan sassan Ummami take zaune, an bata bayi mata masu kula da komai nata har su biyar, amma in suka nemi yi mata wata hidima ma korar su take yi saboda haushi, haushin kowa take ji, saboda Mukhy bai neme ta ba ko sau daya, mai hali dai da baya fasa halin sa.
Sahura da Mamma ma dakin su guda, Sarki ya hana su komawa Katsina yace sai sun raka Amani ta tare a dakin ta tukunna.
Ginin Maina zai dauki sati biyu ana yi don gini ake ba na wasa ba wanda duk masarautar Diffa babu ginin da ya zanu, ya kuma zamanantu kamar sa.
Duk da rashin ta idon Amani sosai ta samu kan ta da jin kunyar Ummami, bata sani ba ko sabida yadda take jan ta a jiki ne, ta ce kuma ita ya take da ita ba suruka ba, don haka ba karamin tanadi take yi wa tariyar ta ba. Da nata, ya tata, komai tuwon ta man ta, farin cikin hakan har ya so yayi mata yawa. Shi yasa take yin komai da karsashi.
To amma yadda Mukhtar ya share Amani tun zuwan su, ko zancen ta bai kara yi ba ya damu Mamma Jalan a kasan ran ta, bata dai nuna ba, don ta san yayi hakuri iya hakuri da Amani, yanzun lokacin sa ne, amma bata fatan ya ce zai rama wulakancin Amani gare shi, don ko babu komi yar uwar sa ce, ta san idan ma Amani ta ce tana son sa yanzu, ai wata fassara zai yi mata daban, don hankali ba zai kama ba.
Don haka ta shiga rokon Allah a boye a kan ya daidaita tsakanin su ba tare da sauran mutuncin Amani ya zube daga idanun Mukhtar ba.
Ita kuwa Ummami yawan sabgogin dake kan ta na mijin ta da bayi da tariyar Amani yasa bata fahimci cewa Maina ko gaisawa baya yi da Amani ba. ba kuma ya zuwa inda ya san a can take.
Allah kadai ya san me ke zuciyar Mukhy a kan Amani, don har zuciyar sa baya mararin sake ganin ta, duk da cewa hes absolutey busy kuma busy din da yake ciki da jamaa da iyaye da yan uwan sa ne ya hana shi zuwa inda suke, amma yana kiran Mamma Jalan a waya akai akai, har Baba Sahura ma, kuma dai duk da hakan Amani tana nan a like a ran sa, yana tuna ta a yawancin lokuta in ya kadaice domin kwanciya barci, amma bai damu ya gan ta ko ya neme ta don ya gan ta ba, duk a kan kalaman ta na Saliyo, da har zuwa lokacin ya kasa manta su, ya kasa yafe su, ya kasa share effect din su daga ran sa, kuma in ya tuna suna masa maqaqi a rai, amma ba don wai ya dawo cikin gatan sa da take masa gori bane ko don halayen ta da ya riga ya sani bane ya sa bai neme ta ba.
Aka fara yima amarya Hamam Hallawa daga shi aka yi mata Dilka Gomage irin na matan Diffa, washegari aka yi mata wankan madara da wankan lalle. Sai kunshi, wanda ya zama shine na karshe a gyaran amarci da aka yi wa Amani a Diffa.
Yau da yamma da aka gama kunshin, aka cire ya kama radau, kamar ka sace kafar da hannun ka gudu, mai gyaran jiki ta ce ta je ta yi wanka da ruwan turaren data sirka mata a toilet din Ummami, sun gama gyaran yau kenan sai kuma na gobe in Allah ya kai mu.
Mukhtar yana son ganin Ummami ya duba inda suka saba haduwa bai gan ta ba, dole ya shig sassanta har addua yake Allah yasa kada ya hadu da Hajjajun nasa.
Mukhy ya shigo dakin Ummami ne don ya gaya mata zasu tafi Burkina Faso yau, domin kai Daddy wajen wani mai maganin shanyewar barin jiki na gargajiya da Sarki ya ce a kai shi. Bisa umarnin abokin sa sarkin Burkina Faso da ya tambaay ko akwai masu irin wannan maganin na wannan lalurar ta shanyewar barin jiki a kasar shi bayan na asibiti? Shi kuma yace tabbas akwai, kuma shi zai dauki nauyin maganin, da duk masu raka Alhaji har sai ya samu lafiya. Don haka suka gama shirya tafiyar Alhaji Usman da yan rakiyar sa karkashin jagorancin dan sa kuma surukin sa Maina Mukhtar.
Da sallama ya shiga har kuryar dakin Ummami don bai gan ta a falon data fi zama ba, sai hadimanta suna ta ayyuka a falon wajen tsaftace shi da turare shi, bayan an gama kunshin amarya, ya duba duk inda zai gan ta har turakar Mai bata can, kuma dole yana so yayi mata sallama saboda zasu kai sati biyu a Burkina Faso in sun tafi gobe ana yi wa Daddy gashin kashi na gargajiya, don har Mamma Jalan zasu tafi, kuma ya gay mata ta waya cewa ta shirya, don ta dinga kula da Alhajin sosai da daddare.
Bai ga Ummami a dakin ba, sai wani fitinannen kamshi da ya baibaye dakin ta koina, can kuma sai ya jiyo karar ruwa a shaya, daga toilet din Ummamin, nan ya gayawa kan sa Ummami tana wanka ne, don haka ya samu kujerar sofa kwalli daya dake dakin barcin Ummami ya zauna yana jiran fitowar ta, hankalin sa bakidaya a kan wayar sa da wannan kamshi da yake ji yana fitowa ta toilet ne ko ta falo ne dun sun bi sun rikita gidan, da wani turare mai tada hankalin yan maza.
Zuwa can Mukhy yaji an bude kofar toilet din, sannan a hankali ta fito daure da faffadan tawul, gashin ganta ya sha wanki don kitso zaa yarfa mata gobe, dagowar nan da zai yi sai ga Hajiyar tasa ce tana fitowa daga wankan turare data shiga, ta zama tamkar hurul-eenin larabawan Diffa. Mukhtar ya samu kan sa da fara tazbihi a cikin ran sa da sauri da sauri. Gabadaya iskar dakin ta debi kamshin sihirtaccen turaren da Ummami ta sa aka hada musamman saboda Amani, yau kwana bakwai da shi take wanka, wanda Ummami tun daga TChad ta aika aka kawo mata shi, daga ita sai dan faffadan towel wanda ko guiwar ta bai kai ba, tayi wani irin sumul ta yi jazur kai har wata yar kyakkyawar kiba ya ga ta yi kamar ba Amanin da ya sani kamar a bushe ta ta fadi ba don rashin kauri. Yo kam ta ci Dawisun Diffa ta koshi.
Da farko ita bata gan shi a dakin ba sam, har rausaya take tana rera wani baiti cikin wakar mutuniyar ta wato Nancy Agram, da harshen larabci, a haka ta isa ga mudubi domin ta sharce jikakakken gashin kan ta data wanke, nan ta hango Alhajin nata zaune yana kare mata kallo, ta cikin mudubin ta hangoshi, sosai ta tsorata duk ta firgice, don bata san da shi a dakin ba. Mukhy ya dan rikice da kama shi da tayi yana mata kallon kurillah, duk ya zama wani upset don bai taba ganin real Amani irin yadda ya gan ta yau ba, ita ma ta diririce don bata san tana da kunya ba sai yau, tana kokarin komawa bandakin don suturta jikin ta ya daure fuska sosai ya ce ke da Allah malaam! Tsaya, tambayar ki zan yi, ina Ummami? Ba wajen ki na zo ba balle ki yi min yanga idon Mukhy na walainiyar da basu san suna yi ba a kan kirjin ta wanda ya dago sosai kamar an an kara hura mata shi ya zama kamar balloon, sai zagin idanun sa suke ta cikin kakkauran towel, da zara-zaran hannayen ta da suka sha jan lalle da hallam hallawa, suka zamar da fatar ta tamkar na jaririya don taushi, wadannan abubuwan guda biyu, gabadaya sun gama tada nutsuwar Mainan Diffa, ya kasa dauke ido a kan ta tsayin lokaci, Amani ta juya don komawa toilet ba tare da ta amsa masa ba. Mukhtar bai san lokacin da ya mike ya soma taku zuwa gaban Amani ba, ya sha gaban ta yana cewa ba tambayar ki nake ba?
Nan da nan ta fara rawar jiki don dadin ganin sa da ta ji, ga kuma kunyar yadda ya gan ta, sannan a gaban ta ya tsaya yana fadin, shin sai yaushe zaki yi hankali ne ke? Ko gaisuwa ga miji har yau baki iya ba, gaida miji ma sai an ce ki yi? Ni kam anya Alhaji ya san irin shashashar matar da ya bani?
Mukhy yana maganar nan cikin takaici mai yawa, muryar sa na canzawa cikin yar inina, ta dalilin tasowar wani kwantaccen feelings daga kasan ran sa, duk kuwa da cewa gashi korafi yake akan halin ta, ya yarda yana son Amani har gobe, duk da pretending din nasa, amma baya son halayen ta ko kadan, don haka yanzu ma kokawa yake da kan sa na kada ya sake kai hannun sa gare ta, komai zai faru da shi gara ya faru amma ba zai kara sake mata ba.
Mukhtar ya kara taku ya tsaya a gaban Amani hannayen sa biyu cikin aljihun Caftan din jikin sa, ya ce Hajjaju ina fatan zafin kasar mu ta talakawa bai saka ki ciwo ba? Na san yayan Qaruna basa son zafi da rana da sauro. A yanzun yana maganar ne fuskar shi dab, da nata, a fakaice yana sunsunar wannan sihirtaccen kamshin ne dake neman bugar da shit un dazu, wanda yanzu ya gane daga jikin ta ya samo asali, mai neman bugar da numfashin sa, ya rasa inda suka same shi. In bai manta ba irin sa ne tayi amfani da shi a Saliyo ya kusa mutuwa a kan ta ba don kwanan sa yana gaba ba.
Ta rasa me zata ce da shi, don kamar bakar magana ce ya gaya mata, shi kuwa tsakanin sa da Allah ya san garin akwai zafi, akwai Sauron ma at times, tana rokon Allah a ran ta yasa kada yau ma Mukhy ya tada zancen Shege! Har yayi abinda zai yi bar dakin nan.
Zuwa wannan lokacin Mukhy ya kusan hade dan space din da ya saura tsakanin su, ban da makyarkyata ba abunda Amani take yi daga tsaye. Yace cikin tsananin takaici wai ashe ke kanwa ta ce duk wanan lokacin ban sani ba, na tsaya kika yi ta yi min rashin kunya a banza a wofi, kina kunsa min bakin ciki kina cin bulus, kina tada kai da bulus, to daga yanzu kika kara yi min rashin kunya ko hararar nan taki ta raini, na rantse da mai samada mai kasa gwabje bakin ki zan yi sai jini ya fito ta yi wani sunkuye da kai, sannan ta yi kasa da idanun ta bata ce komai ba, jikin takanwa y agama yin laasar.
Mukhtar ya kara matsowa jikin ta don kamar wani magnet ya ji yana jan sa zuwa gare ta, abinda bai tsara bane yake neman zuwa da kankanuwar murya ya ce ba zaki koyi gaisuwa ba? Ya kara nacin fade, wannan karon cikin shakakkiyar murya, Amani sai ta soma kokarin gocewa kusancin su, ta yi gaba zuwa wardrobe don ta saka kaya a jikin ta, tana cewa cikin ran ta,
Allah yasa kai ne Sarkin kasar Nijar bakidaya, ba mai jiran gado ba, ba zan gaishekan ba, tunda ta karfi ake saka gaisuwar, ayi mutum ba maganar arziki tsakanin sa da wadda yake kira matar sa amma babu lallashi a bakin sa kullum. An yi sati biyu ma baa hadu ba, yau an hadu tana mararin ganin sa amma ba maganar arziki, ai kuwa bata isa ga wardrove din ba ta ji Mukhtar ya riko gefen tawul din, sai ganin tawul din ta tayi a hannun sa ya rataya a wuyan sa, ta bude baki domin yin ihu, yayi maza ya toshe bakin da hannun sa yana zaro manyan idon sa, ya ce,
baki da hankali zaki yi min ihu ki tara min mutane? Meye haka sai kace yanka ki nayi? Zaki jawo a zaci wani abun nake miki? Daga kawai na zare tawul?
Amani ta rufe dukkan idanunta kamkam, cikin matsananciyar kunya da gigita, tana ambaton Allah a ran ta, domin Mukhtar ya damke bakin da kyau da hannun daman sa yadda bazata iya ihun da ta yi niyyar yi ba don Ummami ta kawo mata agaji. Shi kuma rufe idon da ta yi sai ya bashi damar karewa kyakkyawar halittar matar ta shi kallo, yana tazbihi a ran sa har ya fito fili.
Amani bata san yaya aka yi ba daga nan, don idanun ta suna rufe, gara mata rufe idon da ta hada ido da shi cikin wannan situation din, ta san dai Mukhy ya tallafe bayan ta ya hanata kai wa kasa daga nauyin jikin ta da da kafafun ta suka gaza dauka, daga nan kuma sai saukar bakin shi ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login