Showing 18001 words to 21000 words out of 30436 words

Chapter 7 - Amani Book 3 Hausa Novel Complete

Takori   

13 Dec 2024

157

bai damu ba ya cigaba da gudanar da harkokin mulkin sa rai kwance hankali kwance.
A kan idanuna babu irin gatan da bai yi wa yan uwan sa mata Sayluba da Saadiyya ba. Tun ba lokacin auren su ba. ya zaba musu mazaje na fita tsara ya kuma yi musu auren gata.
Kema kin san kafin uwa ta jure wannan kin san akwai wuya, meye laifin Maina don kawai ya zo a namiji? Amma haka na jure don farantawa miji na bisa raayin sa, ban taba kalubalantar sa ba tunda aka ce abinda babba ya hango yaro ko ya hau rimi ba zai hango ba.
Kullum jakadiya ta kawo min shi don in shayar da shi, nuna mata nake bana so, in ta isheni da roko sai in karbe shi, amma kuryar daki nake tafiya da shi ina shayar da shi ina kallon shi ina kuka. Ya kan kura min ido kamar yana tambaya ta dalilin mu na yi masa haka.???
Ummami ta share hawayen da suka kawo a idon ta, itama Amani zuwa lokacin nata idon ya ciko da kwallah, ta cigaba da cewa na san yana leken mu a shigifar sarki ko wajen hutawar sa da yamma a yawancin lokuta, wanda ba komai ke kawo shi ba sai bond din nan na soyayyar iyaye, wannan yasa na ke yawan zuwa wajen da Mai yake hutawar yammaci, dan mu yi sallar laasar tare, in mun idar in yanke masa akaifa ko in taya shi hira yana daga zaune bida karagar sa ina daga kasan kafafun sa cikin ladabi mai yawa, ba don komai ba sai don in ya zo leken namu nima ina samun damar ganin sa a sace.
Ranar da aka ce min ya gudu ni na san dalilin sa, na kuma yarda da hujjar sa, tunda bamu taba zama da shi mun masa bayani, wanda zai gamsu da hujjar mu ba, don haka duk abinda zuciyar sa ta gaya masa ko ta fassara masa a kan mu a wancan lokacin a wurin sa shine dai dai. Suma na dinga yi ba tare da kowa ya san dalili ba, ana zuba min ruwa ina farfadowa. Daga ranar kuma ban kara sallah na tashi ban yi masa doguwar addua ba, kan cewa duk inda ya shiga Allah ya zama gatan sa, ya kare mun shi da karewar sa da kiyayewar sa, ya kuma kula da shi. Domin na yarda kulawar Ubangiji tafi tamu ta iyaye, kuma itace ta kawo Mukhtar yau inda yake.
Ya yi rashin duk wata soyayya ta iyaye a kuruciyar sa, ina jin damuwa idan na tuna hakan. Da wannan nake rokon ki, a kan ki dubi girman Allah ki kula min da Mukhtar kin ji AMINA! Ko da a kasan ran ki babu soyayyar.
Amani sai ta saka kukan data ke rikewa tun dazu a bakin ta, kuka mai sauti sosai, ta rasa abinda zata ce da Ummami wanda zai sa ta gamsu ba ta kin Mukhy yanzu, its true Mukhy had a traumatic childhood, and he deserve happiness a yanzu. Matsalar ta da shi riko. Ya ki sakin ran sa da ita su mori auren da kuruciyar su sai tsananin rikon ta da laifukan na baya da ya bari suka yiwa ran sa kaka-gida. Ko yayi kokarin sakin ran sa da jikin sa da ita wani time din, rikon dake zuciyar sa sai ya hana shi. Bayan rayuwar bakidayan ta sai ana ma juna afuwa, saboda rashin tsayin ta da rashin tabbas din ta. Life is very short and transient. Amma ai Allah ya san ta yi nadama, wadda ba lallai wanda ya santa a baya ya karba ba, zaa ce ne don ta gan shi da gata ne a yanzu.
Don haka ta hadiye duk wani tunani a ran ta, nadamar ta da damuwar ta a kan Mukhy bata iya ta cewa Ummami komai ba, sai sheshshekar kuka take tana hadawa da ajiyar zuciya.
Ummami ta ce to yanzu meye abin kuka daga magana? Ni labara kawai na baki don ki tausaya masa. Ba don in saka ki kuka ba. Koda yake Jalan ma haka take da saurin kuka, da abinda ya isa a yiwa kuka da wanda bai isa ba duk abin kuka ne a wurin ta tana karama, kin yi gado. Ni dai na baki amanar Mukhtar don dai gashi ya dawo gare mu ne, amma rayuwar sa zata fi yawa tare da ke, ke ce silar duk wani farin ciki da zai iya samu ko akasin sa, domin sai kin faranta masa daga gida ne zai fito cikin jamaar sa cikin annashuwa, ya ji dadin tafiyar da alummar sa da mulkin gidan su da tarin responsibilities din talakawa da ke kan sa, tun da dai kin ga shi Maina ne wato (Mai jiran gado).
Da zata iya da ta gayawa Ummami cewa ta daina bata amanar MUKHY don Allah, don ita Uwar sa ce kuma bata san halin sa ba, amma shi ma ai takadarin kan sa ne na gani kashe ni, wanda baya bari ko da wasa a taka shi, ko a danne hakkin sa da ya rataya a wuyan mutane. Sai ya kwaci abinsa ko ta karfi ne.
Kamar misali in tayi masa kwauron gaisuwa kasancewar shi mutum ne mai so a bashi girman da ya cancanta, da son kowacce mace ta kasance da halaye da dabiu na kwarai na girmama miji kwatankwacin irin na Ummamin sa, to fa ba zai hakura ba sai ya nemi gaisuwar nan ko ta karfin tsiya ne da bakin sa, haka in tayi masa rashin kunyar nata mai lasisi, Mukhy ramawa yake yi babu jinkiri babu bata lokaci, wani lokacin da mai zafin da yafi nata zafi, wanda sai ta kwana tana hadidiye bakar maganar sa.
Amma tayi relating da labarin da Ummami ta bata na kuruciyar Mukhy, sai ta ga cewa ita kam, duk da babu Jalan, kuruciya ta gata da yanci kuma mai dadi ta yi, har ma da jin dadin tafi kowa gatan uba, he really deserves happiness ko yaya ne a rayuwar girman sa ta yanzu, kamar yadda mahaifiyar sa ta ce. Kuma ba daga kowa wannan farin cikin zai fara samuwa gare shi ba sai daga cikin gidan sa, wato daga hannun ita matar sa.
Can cikin kanta ta jiyo sassanyar muryar Ummami, kasancewar ta yi nisa a tunani.
Kin min alkawarin kula da Mukhtar da bashi soyayya da farin ciki a rayuwar girman sa AMINA? Ni kuma in kika yi min hakan, na yi miki alkawarin ba dai kiyi kuka akan Da namiji ba, zan tabbatar na zame miki garkuwa a wurin sa, daga duk mai son shiga gaban ki. Fata na kawai shine Mukhtar ya samu kwanciyar hankali a rayuwar girman sa, wadda bai samu ko kadan a kuruciyar sa ba.
Ni da ke, babu hijabin surukuta ko yaya a tsakanin mu, sakamakon cewa ke din ya ta ce ta halali, wadda ko babu Mukhy a tsakanin mu zamu kashe mu rufe tare, ba tare da ko Jalan data yi nakudar ki ta ji ba. Hakika Allah Subhana na so na da kwanciyar hankali a tsufa na, wanda ban samu a kuruciya ta ba cikin gidannan, shiyassa ya bani ke wato ya sallado min ke a matsayin suruka ba tare da dabara ta ba, ke da kika kasance ya ta halali a gare ni, bai yi min suruka da wata daga waje ba, wadda zata sa Mukhtar ya sha wuya a hannun ta, don kawai yana son ta, shi yassa na bude miki ciki na yau mu fahimci juna mu tallafawa juna ta hanyar bashi kulawa a farin ciki ni da ke, ki sa a ran ki ni na haife ki ba Jalan ba.
Amani ta share yan kananan hawayen da suke ta tsatstsafo mata a kowanne furuci na Ummami, wadanda ta san ba na komai bane na tausayin Mukhy da Mahaifiyar sa ne, duk Ummami ta gama kasha mata jiki da kuzari. A hankali ta gyadawa Ummami kai, wato ta yi wannan alkawarin, na kula da Mukhtar, da sanya shi farin ciki da bashi soyayya.
Kuma har cikin ranta ta yi din, domin jikin ta yayi wani irin sanyi, ta yi lakwas kamar jikaakken tsumma, jijiyoyin rashin kunya, na girman kai, na alfahari dana dolonci suka shiga tssitstsinkewa suna farkewa da kan su, hankali da nutsuwa har ma da tsoron Allah ya soma ratsa Amani a kusufa-kusufa daban-daban na kwakwalwar ta.
Ta gamawa Ummami kitson cikin matsanancin mutuwar jiki, kuma dare ya yi, don haka ta ce mata zata je ta kwanta, kan ta na sarawa sabida kukan data yi mai tsanani.
Kuyangin ta da aka bata su suka raka ta har dakin barcin ta, don har zuwa lokacin suna can suna jiran ta a inda suka saba zama su jira ta in ta zo gun Ummami, da suka dawo bangaren ta daya daga cikinsu ta hada mata tea mai kamshin nanaa bisa umarnin ta, ta sha a gefen gadon ta, sannan ta kawo mata Panadol ta hadiya, suka yi mata duk abubuwan da suke yi mata kafin ta kwanta kamar kashe kayan wuta, kunna A/C da kunna mata karatun Alqurani a radion bakin gadon ta cikin kiraar Mahmoud Khalil bisa umarnin Ummami, na kullum su kunna mata in zata kwanta daga kanan surori don ta kara iyawa da gyara karatun sallahr ta. Tahira da Sugra kenan, wadanda su tafi sanyawa aiki da ja a jikin ta cikin hadiman nata guda biyar da Sarki yasa aka bata tun zuwan ta, sauran biyun suna kula da girki da kitchen din ta ne, daya kuma sharar bangaren ta da goge-goge da wankin toilets, ta zabi Sugra daTahira su dinga zama a jikin ta ne don su ba yara bane kamar sauran ukun, suna da hankali da nutsuwa, kuma suna da aure har da yara. Koina zata shiga cikin gidan suna tare da ita.
Tahira da Sugra suna bada baya, bayan sun mata light off da sai da safe, sun bar mata dim light shudiya, kukan ta cigaba da yi, mara sauti, da alama dai Amani Faskari, most at times, finds pleasure and comfort in crying, tana yi tana yin wannan kukan ne don tausayin Mukhy tana comparing rayuwar sa da nata. Sai ta ga cewa, ratar gatan da ta samu da wanda ya samu mai tsananin girma da fadi ne. bama zaa kwatanta ba. Da gaske kamar yadda Ummami tace ne Mukhtar yana bukatar kulawar su su duka yanzu, amma ta yaya? Ta ina zata fara tata kulawar? Ko ta yi kokarin hakan ba zai bata dama ba, saboda ya rike ta da yawa a ran sa.
Wata zuciyar ta ce da Amani Ai kema Amani mace ce, ko da ake cewa kin rako mata! Ki yi tunanin hanyoyin dadadawa mutum, musamman mijin auren ka, ta yadda zai ji dadi, ya manta da laifukan ka komai girman su, ya sakar maka fuska da zuciyar sa gabadaya koda baya so, albarkacin kulawar ka gare shi. Tunda an ce zuciya na son mai kyautata mata.
Sai ki hada da abubuwan da Balewa ta koyar da ke na kissa mai kyau ta waya, da kuma naki yan dabarun da bazaki rasa ba, da wadanda Ummami ma ta koyar da ke na tafiyar da Saraki.
Daddyn ta ya fado mata a rai shima zai iya taimakawa wajen sayo mata yardarm Mukhy a yanzu, ta tuna tun tafiyar Daddy basu yi way aba sai ta dauko wayar ta, ta kuwa same shi online a kan whtsp. Sai ta yi masa kira ta cikin whtsp call.
Yana dagawa ya ce Tafisu! Me kike yi har yanzu baki yi barci ba?
Amani ta yi ajiyar zuciya mai nauyi, ta ce yanzu nake shiri ai Daddy, so nake in tambaye ka yaya jikin ka? Kuma Yaya Mukhy yana lafiya?
Dadi mai yawa ya kama Alhaji, y ace na samu lafiya sosai Uwata, kuma ina iya mikewa ma yanzu, Mukhtar sai dai in ce Allah ya saka shi a aljannah y araba shi da iyayen shi lafiya, ko ke da na Haifa iyakar abinda zaki yi min kenan a rayuwa.
Uwa in har baki bi Mukhtar sau da kafa ba wallahi sai Allah yayi mana hisabi ni da ke, na hore ki da ki bi shi ki nemi aljannar ki babu ruwa na dake duk ranar da Mukhtar ya kawo min karar ki.
Amani ta saki kukan da ke cin ran ta, ta ce Daddy! Kuna ta dora min abinda yafi karfi na, bayan ba daga gareni bane matsalar yanzu, na riga na gane kuskure na, shine dai ya ki ya yarda da ni ya kuma saki zuciyar sa da ni. Hakika na yi kuskure, ina so na gyara in zai bani dama, ka roke shi ya karbi tuba na ya kuma bani damar gyarawa. Na yi alkawarin canzawa daga yadda kowa ya sanni dinnan, amma hakan ba zai yiwu ba sai ya yarda da ni.
Yardar miji kuma yardar Allah ba! In sha Allahu Mukhtar zai karbi tuban ki musamman in kin ajiye girman kai. Nima kuma zan taimaka wajen ganar da shi halayen ki ba laifin ki bane, nawa ne. Musamman a yanzu da muke da lokaci ni da shi kullum muna tare barci kadai ke raba mu.
Ina rokon Allah yayi wa rayuwar ku albarka bakidayan ku, ya kuma albarkaci auren ku da zuriar da zamu yi alfahari da ita mai yawa mai albarka.
Ta tambayi Maman ta yace ta yi barci tun dazu.
Sun dade suna hira irin tasu ta Tafisu da Daddyn ta.

Washegarin ranar, a darussan su na yau, ita da Ummami, har yadda uwargida ke zama a gaban Sarki sai da Ummami ta koyawa Amani, da yanayin yin magana da Sarakuna cikin kankan da harshe da tausasa furuci, da hadawa da kirari na kambamawa da nuna soyayya.
Wani abun har sai Amani ta rufe ido don kunya. Da gaske Ummami ta janye hijabin surukuta bakidayan sa. Tasaka na malunta.

***** ***** *****

BAKIN BURKINA FASO
R
anar da su Mukhy suka dawo Diffa daga Burkina Faso ana zabga wani irin ruwan sama kamar da bakin kwarya har da kankara. Labari ya isko su cewa Maina ya dawo lafiya tare da jamaar sa, suna fada wajen Mai Diffa.
Tsakanin Mukhtar da Alhaji bata san wa tafi dokin gani ba, don an ce da su Alhaji na tafiya yanzu a kan kafafun sa. Wannan ya kusa saka ta shekawa da gudu don ta cimma Daddy har fadar sarki.
Don haka ta roki Ummami Allah Annabi tana son zuwa masaukin su Alhaji. Ummami tasa kuyangin ta wato Sugra da Tahira suka raka ta har inda aka sauki su Alhajin, da gudu ta karasa shiga dakin tana kwarara kiran sunan Alhaji Daddy, Daddy na!
Alhajin kuwa ta fara yin tozali da shi yana tsaye a kan kafafun sa yana waya da Matawalle da ke Katsina, da gudu Amani ta karasa ta rungume shi, tana kukan farin ciki, da godiyar Allah. Mamma ce ta hau ta da fada tana cewa ta yi masa a hankali, bashi da kwari, jiya ba yau bace, kuma da da yanzu ba daya bane a gareta ita kan ta, ta daina wannan haukan da take yi a jikin Alhaji. Ita matar gida ce yanzu
Ta dube su duk sun murje sun yi gwanin kyau, tsufa duk ya bace, Alhaji yayi kiba yayi haske, ta hau dariya ta ce ai kawai Mamma ki ce honeymoon kika tafi kai Alhaji Burkina Faso ba jinya ba, wannan irin murjewa haka?
Jalan uwar saurin hannu nan da nan ta kai mata duka. Amani ta goce tana tana ta dariya, Jalan na fadin na ga alama kin maida ni saar wasan ki, ni kike cewa na je honeymoon? Alhaji ya kammala wayar da yake yi ya rufe yasa a aljihu, yace Ya ki nan Uwa ta, kyale ta, sannan ya hau Jalan da fada, ni tunda nake ban taba ganin Uwa mai saurin dukan Da irin ki ba, to in bata yi wasa da ke ba da wa zata yi? Yar guda daya ita kenan Allah ya bani bazaki taya ni tattalin ta ba don ke kina da wasu ko?
Amani tayi dariya ta ce aah Daddy, daina mata fada haka, kada ta yi zuciya taki yi min wasu kannen, biyu sun min kadan. Duk suka fashe da dariya har Mamman. Alhaji ya ce ta tashi ta koma cikin gida haka, don mai Martaba ya ce masa an gama ginin su, an saka komai, yau zaa kai ta bangaren ta kafin wucewar su gida Katsina. Su kuma in sha Allahu gobe zasu wuce Nigeria.
Tuni jikin Amani ya mutu, yar farar data shigo da ita ta koma ciki, aure da rabuwa da iyaye ba wasa bane ba kuma sauki gare shi ba, damuwa da kewa suka bayyana a fuskar ta tun ma yanzu kenan, ta soma tunanin irin kewar su da zata yi tun basu tafin ba, musammamn Alhaji.
Zata soma kukan tun kafin gobe ta yi, Ummami ta aiko jakadiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login