Showing 24001 words to 27000 words out of 30436 words
da na tangaran ne ba abinda zai hana su fashewa su yanke su sabida yadda suka subuce daga rikon ta ba zaton ta, amma hakan bai sa Mukhy fasa abinda yake yi ba, ta fahimci bat un yau ba, babu kamshin da Mukhy yake matukar so a jikin ta irin kamshin tsakiyar gashin kan ta, wanda ya fahimci turaren gashi na musamman ne take amfani da shi a cikin gashin ta, wanda iyayen ta Jalan da Aisata dake bata shi kadai suka san sirrin da ke cikin sa.
Kamshin gashin nan ya tsokano abubuwa da yawa da yake ta kokarin dannewa tun dazu, kuma dai dama ko ta ina aka je aka dawo Mukhtar ya san yayi kewar Tafisu, ba ita kadai ba har tsiwar tata, kidifiri da rashin kunyar duk ya yi kewa yadda ba ya zato, a kwanaki goma sha hudun da ya yi a Burkina Faso.
Sai kawai ya jirkito Amani bakidaya ta fado masa ya soma kissing din ta gently, wani abu data tabbatar ya matukar kwarewa a kai fiye da komai watau gentle kiss, duk ta kara daburcewa kafin kisses din Mukkhy ya soma shigar ta yadda ya kamata. Gangar jikin ta kuma ta soma responding.
Tafiya ta soma yin tafiya, Mukhtar na kara birkita Amani da duk wani nauI na romancing na miji ga matar da yake matukar so, yana kara sanya mata son amsa kiran sa ta koina da sumbar nan tasa mai shiga rai, a kowacce gaba mai bukatar hakan a jikin ta, wannan karon ma kamar wadancan karon, Amani ta gama sakarwa Mukhy komai, da dukkan zuciyar ta da sahalewar ruhin ta, gabban jikin ta sun gama nuna amincewar ta, ta shirya welcoming din sa (as a husband), har addua take a ran ta koma meye zai faru ya faru a yau, kuma a yanzu. Zata jure, in dai hakan zai faranta ran Mukhy ya daina rikon ta a ran sa ya bari su zauna lafiya.
Lokaci daya Mukhtar ya tuna Amani fa ba wai son shi take yi ba har yanzu, kada yar canzawar nan da ta yi ya rudar da shi ga sanin ainahin wacece Amanin sa, Tafisu wadda tafi sauran mata tinkaho, yanzu haka tana da dalilin ta na wannan dan canjin da ya gani a tare da ita. Maiyuwuwa wani abun take so yayi mata, amma a sanin da yayi mata, Amani bata da kirki, kuma bata kirki domin Allah. Sai tana neman wata alfarma a gare ka.
And he will not be selfish anan, duk inda ya kai da son ta, da son kasancewa tare da ita don bayyana wannan son da tabbatar da shi, yafi karfin yayi auratayya da macen da baya ran ta kwata-kwata, bata kuma yi masa irin son da yake yi mata, sai dai ta amince da shi bisa dole don ba yadda zata yi da auren sa, tunda iyaye suka hada shi bisa karfin ikon su a kanta kuma sun fi karfin ta. A yanzu kam baya jin akwai abunda ba zai iya hakura da shi ya zauna lafiya ba a rayuwar sa, ya hakura da iyayen sa ma shekaru sha biyar, kuma ya rayu da numfashin sa balle soyayyar mace, alhalin yana karkashin gatan sa?
Amani sai gani tayi Mukhtar ya sake ta ya ja da baya cikin mutuwar jiki, yatsun sa ya saka cikin tarin sumar kan sa, ya ce Im so sorry for that, I know you dont love me Amani, and I will not force you to love me or to sleep with me, because I will not be selfish! In na yi hakan na so kai na.
Ya dauki dankwalin ta da ya sabule ya dora mata saman kujera, yana fadin Sorry for making you to regret this again, I just couldnt resist your changes for today, I like this new you. Ina ma wannan sabuwar Amani tawa ta dore!
Ya sumbaci goshin ta ya ce by Allah! You will be the death of me Amani, je ki kada ki sa in kasa controlling kai na kuma, in yi abinda zai zo ya dame ni, kema ya dame ki, tunda har gobe na kwana da sanin ba kya so na. Dole aka yi miki a kai na.
Na rasa me yasa? Komai na kudurta a raina don tsira da mutunci na daga fitinar ki, in kika zo gaba na sai kin san yadda kika yi kika rusa min shi. Amani, why? Why are you playing with my heart? Me yasa bazaki bar ni in zauna lafiya ba? Ko don kin ga bani da juriya a wannan bangaren Im very fragile? Kullum sai kin san yadda kika yi kika tsokano ni wato ko? Do you know how Im suffering after touching you? Na rasa ko ke wace irin mai halin hawainiya ce, yau ki zama fari gobe baki. Kasancewar kin san ni mutum ne mai son a kyautata min, a kuma yi min ladabi shiyasa kika bullo min ta nan ba don kina so na ba?
Na bi ladabin ki da gudu na tattake ba takalmi a kafa ta in dai da shi zaki yaudare ni yau Amani!
Ya sake ta ya kama hanyar ficewa daga falon, ta karfin hali da bin karfin zuciya da kuma bravity na son kiyaye pride irin nasa domin hakika yanayin da fuskar ta ya koma yayi tsananin bashi tausayi, ya bar Amani a wani yanayi na rashin jin dadi da takurar zuciya wanda har a fuskar ta ya nuna nadama, ta cigaba da tsayuwa a wurin kamar an kafe ta. Kafin kuka mai tsananin karfi na nadama da dana sani ya kwace mata.
Ta riga ta san it will not be easy for him and for her, ya yarda da ita, ya amince da tuban ta farat daya, amma bata zaci har haka ya rike abun a ran sa ba. Duk kuwa da cewa ta san yana da riko.
Haka ta wuni sukuku a cikin gidan ta, cikin rashin jin dadin abinda ya faru tsakanin su ranar, it made her whole day black! At the same time, ta wuni tana takaicin dandani haukacin nan da Mukhtar ke yawan yi mata. Sai ta sakankance yau zata zama matar sa sai kawai ya fasa, yana nufin, this is his punishment a gare ta ko me? Ko ya fahimci tana son sa ne yanzu, tun kafin ta bayyana hakan da bakin ta gare shi, shi yasa yake faman yi mata dandani haukaci wanda yafi ramuwar gayya ci mata rai?
Bayan wannan dan romance din na Mukhy da ya hana Amani barci daren yau bakidaya, tunda ya fita lokacin bata kara ganin sa ba sai washegari da safe a sassan Ummami. Don sanda ya dawo gidan ta riga ta yi barci, kuma bai yarda ya kwana a dakin ta ba. ya dai leko ya gan ganta tana barci ya wuce dakin sa.
Ta shiga kenan domin ta gaishe da Ummami, sai ta samu Uwar da Dan suna magana, wato suna magana shi da Ummami amma maganar da ta dan ja hankalin ta, don ji tayi Ummami na gaya masa Sarki ya karba masa kyautar sadakoki wato kwarkwara guda biyu na yammata daga Sultanate of Damagaram.
Amani ta yi sallama a shigifar Mowar Sarki, saidai kuma cikin rashin saa ta riga ta ji magana ta karshe da Ummamin ta gama fadi wa Maina yanzun, sai ta samu wuri gefen kafar Ummami ta zauna, kamar ta ji Ummami tana fadin Sarki ya ce an baiwa Maina kyautar Sadaka, Ummami din tana tambayar sa ko yana da bukatar amsar su? Yara ne masu matsakaitan shekaru yanmata, lafiyayyu. Ummami ta kara bayani. Kamar da gayya don Amani ta ji.
Amani wadda ta ji zancen alhalin tana shigowa, amma bata gane sosai ba, don haka sai ta tambayi Ummami cikin rashin fahimta bayan ta samu wuri ta zauna a gefen ta.
Ummami meye kuma Sa-daka?
Ta tambaya ne ganin kamar Mukhy bai so ta ji abinda suke tattaunawa ba, ya zama kamar mara gaskiya daga shigowar ta, kuma fuskar sa ta ki karantuwa duk ya bi ya daure fuska. Sannan bai ce komai a kan kyautar da Ummamin ta ce an yi masa ba, sai faman hade giran sama dana kasa yake yi yana Harare-harare. Ummami ta ce cikin kwantar da murya.
Sadaka yana nufin kwarkwara (concubines).
A dan rikice Amani ta ce kwarkwara kuma Ummami? Me yasa aka bashi? Kwarkwara a wannan zamanin? Shi din ne ya ce a bashi ko shi ya ce yana son su?
Amani ta jero tambayoyin cikin rudewa, rikicewa da da karkarwar murya, ba tare da ta san lokacin da ta jero su din ba, tsakanin Mukhy da Ummami, sai ka rasa wa ta jefawa tambayoyin, sai zare ido take a tsakanin su su biyun, tana jiran dayan su ya bata amsa. Amma duk suka yi mata shiru. Tsabar rudewa ta ma manta da wacece Ummami a gare ta. Haka ta kafawa Mukhtar ido cikin tuhuma da tashin hankali. Mukhtar sai ya tashi zai fice daga dakin, yana mamakin dalilin gigicewar ta da rikicewar ta haka don kawai an ce an bashi kwarkwara, ba dai zai ce Amani kishi take ba, saboda ya sha jin ana cewa sai da SO mata ke kishin mazajen su. Shi kuwa ai baida wannan gatan da wannan alfarmar a wajen Amina-Amani.
Ta soma harzuka, tana kokarin komawa Amani Faskarin ta da kowa ya sani wadda bata barin ko ta kwana, ganin ta rasa mai bata amsa a cikin su. Gashi yana kokarin ficewa daga dakin ba tare da ya bata amsa ba.
Ya Mukhy! Magana nake yi. Yaya zaka fita baka bani amsa ba? Kai kace a baka sadakan, me na yi maka? Am I not enough?
Mukhy har ya kai bakin kofa zai fita, sai ya juyo ya dube ta da warning look a idanun sa, wato ta san a gaban wa take, da irin maganar da zata furta, da alama ta manta Ummami na wajen, ya ce cikin fushi.
Are questioning or accusing me? Na yi kama da saan wasan ki da zaki jefa min query? To ban sani ba din, sai kin matse baki na zaki ji amsar tambayar taki.
Yayi tsaki ya fice ya bar musu dakin.
Rudewar da take ciki ya sa ta mancewa ko wacece Ummami gare ta, ta ce don Allah Ummami shi ya roka? Ko shi ya ce muku yana son sadaka?
Ummami sai ta fito mata a mutum sak! Itama, ta dube ta ido cikin ido ta ce, Amani! Kin ga na lura tun zuwan ku kallon juna kuke kamar ba aure ne a tsakanin ku ba, alamu kuma sun nuna min tun a Nigeria ma haka kuke zaune, Mukhtar in ya je fada Baban sa ya lura baya iya komai sai damuwa, in an yi Magana sai yace naam wato sai an maimaita, shi kuma Mukhtar da kike gani, Yarima ne maana (Maina ne) Sarki mai jiran gado, shine wanda ake fatan ya gaji mahaifin sa a komai, bazai yiwu a kyale shi haka babu kulawar mata ba, ko da sadakan ne don samun nutsuwar sa.
Shi yasa muka ga gara a bashi sadakan ko ba yawa kafin ku daidaita kan ku, da sabanin da ke tsakanin ku, ki sani Mukhtar Sarki ne, halittar su daban da ta sauran maza da kika sani a kan mata, kusan in ce miki, duk yawancin sarakuna. A shekarun Mukhtar yayi hakurin da ya zarce kima babu mace, gara kada a kure hakurin a bashi karin wasu matan na hutawa, su kuma yi muku hidima ke da shi har zuwa ku daidaita.
Ko ita dakikiya ce zuwa yanzu ta fahimci me Ummami ke nufi yanzu, tunda dai ta shiga aji, ba wai bata taba shiga aji ba.
Gata suke nufin zasu yi wa dan su, don sun gane bata bashi kulawar data dace mace ta baiwa mijin ta na auratayya.
Kasa magana tayi, tayi kokarin rike hawayen ta bata bari sun zubo a gaban Ummami ba, don kada a ga rashin juriyar ta da raunin ta, sannan ta mike ta koma sassan su cikin sanyin jiki, sai Kuyangar ta mai kula da kitchen wato Ramu ce ta biyo ta da wayar ta, don a can dakin Ummami ta manto ta tsabar ta shiga rudu mai yawa, kuma Ummami bata sake bi ta kan ta ba, bayan bayanin da ta yi mata. Ta san ta ahada mata bom yadda take so ya tashi.
Duk da sanyin AC mai karfi da ke aiki a falon ta. Amma Amani zufa take yi in ta tuno zancen nan. Idanun ta ba abunda suke hararo mata sai kyawawan yammata abzinawan usli tare da Mukhtar, cikin irin yanayin su da suka kasance jiya shi da ita, wannan alamari ba karamin daga hankalin Tafisu ya yi ba.
Fisabilillah me yasa baa yi ma Mukhtar aure tun sanda ta tsane shi ba sai yanzu da ta soma saka shi a ran ta, ta soma tsara musu rayuwa ta soyayya mai tsafta a cikin zuciyar ta, kiris ya rage mata ta samu dama ta bayyana masa son da take masa? Mafarkin ta na haifa ma Ummami da Mai Diffa jikoki daga Mukhy ita kadai ran ta, ya tashi a banza Kenan muddin aka bashi wasu matan suka riga ta shiga jikin sa?
A hankali ta soma sheshekar kuka, bata san cewa Mukhy yana cikin dakin da ta jingina da kofar sa ba. Sautin kukan ta ya dame shi, yana ci masa rai, don bilhaqqi take yin sa, hakan ya fiddo Mukhy daga dakin barcin nasa, ya bude kofar saura kadan ta fadi, don a jikin kofar ta jigina duka jikin ta, tunda ya baro su ita da Ummami gidan sa ya dawo, ya kwanta a daki ya rufe kan sa yana tunanin karbar tayin mahaifin sa ne ko aah?
Ita bata ma san yana ciki ba, ya zo kan ta cikin fushi dama kuma ran sa a bace yake da abinda ta yi masa gaban Ummami mai kama da raini, cikin tsawa ya ce ke lafiya zaki zo ki daga min hankali da kuka haka ina kokarin samun barci? Me aka yi miki? Wani aka ce ya mutu? Koko rashin hankalin ki da kika saba?
Amani ta daga jikakkun idanun ta ta galla masa hararar nan tata da ta dade bata yi masa irin ta ba. Sai yau da ji take gabadaya ta tsane shi bata ko son ganin shi a idon ta. Sannan ta juya tana share hawayen ta don bata so ya kama ta tana kukan nan ba, ko don tsira da sauran ajin ta, ta yi masa banza ta cigaba da share hawayen ta da habar laffayar ta.
Ba gara mutuwa ba ta san kowanne mai rai mamaci ne. Wannan kuwa tashin hankali ne na har abada ya same ta, in har ta bari ya faru, kishiya daga zuwan ta gidan miji! Mijin ma Mukhy dan uwan ta da ta soma kallafawa a ran ta bada jimawa ba, wanda bata kwatantashi da komai a yanzu, son sa take bilhaqqi.
Mukhtar ya sassauta murya ganin cewa fada da daure fuska bazasuyi tasiri a gare ta ba, har ya samu ta gaya masa kukan me take yi, ya ce pls Amani! Na hadaki da Allah ki yi shiru, ki gaya min abinda ya yi sanadin wannan kukan babu gaira babu dalili.
Don sosai ta firgita shi, don kukan nata ba na wasa bane yau, ko na sakarci irin wanda ta saba a yawancin lokuta, aah wannan kuka ne mai fita daga kasan zuciyar matar da ke tsananin son mijin ta, kuma dare daya ya zo ba zato ya ce zai mata kishiyoyi, kuka ne take yi bilhaqqi, baka da zuci, mai nuna tsananin kishin ta akan abinda take so da zuciya daya.
A matukar fusace Amani ta dago, idanun ta sun yi jawur, hawaye ya hade da majina ta ce ina rokon ka Allah Annabi ka bace min da gani Ya Mukhy, sabida bana son ganin fuskar ka, ka tafi gun sadakan da ka je ka roka a baka sabida na gaza, ka tambaye su kukan me nake yi, tunda kai baka da hakuri, baka da bin komai a sannu. Son da na samu kaina da fara yi maka, ina rokon Allah ya sa ya koma inda ya fito, kada Allah ya bar ni da koshin wahala.
Mukhtar ya hadiye mamakin sa da dariyar data zo masa nan take, sai yanzu ya gane musabbabin kukan, wanda bai taba ganin Amani na yin mai zafi da cin ran sa ba, ya ce.
Tafisu yau ni kike kira mara hakuri? Shin a duniya akwai miji mai hakuri ma iri na? Ni da aka kira bawan Alhaji, mara galihu, mara nasaba kai har mai kama da shegu an ce min kuma na yi hakuri na Manzon Allah, ban taba kallon ki da kalaman bakin ki ba, sai matsayin diyar ubangida na mai daraja a idanu na. Ni tsintacce a bola, ke komai ma na batanci da rashin galihu ni ne. To ki gayamin ya kike so in yi idan ban karbi wadanda