Showing 21001 words to 24000 words out of 30436 words

Chapter 8 - Amani Book 3 Hausa Novel Complete

Takori   

13 Dec 2024

158

tayi kiran ta, don haka ta rike hannun Daddy tana hawaye ta rufa tafukan sa a kan fuskar ta, ta ce to yanzu Daddy ni da ku sai yaushe? Kai tsaye Alh. Usman yace sai kin haihu zamu zo, in kin min aboki ko sabuwar amarya, ki sa himma shekara mai zuwa sai ki gan mu gabadaya mun dawo radin suna, har Balewa zamu dauko miki da su Laure, da Kamilu.
Kunyar da bai san Amanin shi da ita ba ya gani ta zo ta lullube ta, harda kare fuska da hannayen ta cikin jin kunyar Daddy yau.
Jakadiya da kuyangin ta suka maida Amani wajen Ummami, aka soma shirya ta don wucewa nata bangaren, wanda ke can gefen dama na masarautar Diffa. Da ka wuce sassan Sultan Issouffou Massaoudou.
An kawata ginin a zamanance, hakanan ya tafi da zubin sarautar Al Imaraat Al-Diffa duk da haka. Daga ciki ne aka zuba abubuwa na zamani.

Bangaren Maina Mukhtar Bn Issouffou Massaoudou dake ciki Al Imaraat Al Diffa wato masarautar Diffa, zan iya kwatanta shi da Palace din da babu kamar shi a duk cikin fadin masarautar, in ka cire sassan Sarkin Diffa.
An shirya musu dakunan barci har shidda, da shigifu (faluka) na alfarma wadanda aka yi wa design da furnitures kala daban-daban, wasu an yi musu zubin royal parlors, wasu kuwa English parlors ne, da kuma Francaise.
Jalan na cikin hada kayan ta don gobe da asubah zasu kama hanya, Mai ya basu driver wanda zai kai su har Katsina sannnan ya dawo, Jalan ta ki yarda su yi sallama da Amani ta ce da Ummami a wuce da ita gidan ta kawai, ita bata son koke-koken banza na Amani, sannan duk wani abunda uwa zata fada mata ta san Ummami ta gama gaya mata, don haka Ummami tayi abunda baa taba yi ba a masarautar Diffa, inda tace da kan ta zata kai Amani har dakin ta.

A daren Mukhtar yana tare da Mai, suna cin abinci a kwano guda, yana masa hirar abubuwan da suka faru dasu a Burkina Faso da yadda aka magance lalurar Alhaji Usman ta suga da shanyewar jiki ta hanyar maganin gargajiya ziryan. Mai cikin gamsuwa da taimakon da aminin sa sarkin Burkina Faso yayi masa ya ce da Mukhy, ya saka an warewa Alhaji Usman Rakuma hamsin, a fara yi masa kiwon su anan cikin bargar Rakuman sa, in kuma yana so a kai masa su Nijeriya ne duk zai iya sawa akai masa har can, sannan ya bashi sittiru irin nashi na alfarma da rawanin sarautar Diffa akwati guda, har da zoben azurfa mai matukar daraja.
Mukhy ya taya Alhaji godiya sai ya ce Uwa ta fa? Me aka tanadar mata? I mean ita me zaa bata? (yana nufin Mamma Jalan).
Mai ya ce ya bada bracelet na zinare a bata, har Baba Idi ma ya samu kyautar Rakuma goma daga Mai Diffa, Baba Sahura kuma Sarki yace Ummami ta ce a nan shiyyar Amani zata zauna tare da ita har sai ta saba da gidan da mutanen cikin sa koda zata koma Katsina. Duk da dai an bata wadatattun kuyangi da masu hidimar ta. amma zaman Sahura zai mata amfani.
Mukhtar yana can suna wannan tattaunawar da mahaifin sa, ba tare da ya sani ba Ummami da Baba Sahura suka kai masa Amani dakin ta, bai san hakan ba don tun dawowar su bai nemi ganin Amani ba, kuma ko a hanya basu hadu ba, tunda yayi alkawarin daina kebewa da ita sai ta yi hankali ta kuma koyi son shi don radin kan ta, ya fahimci sai sun kebe ne take warware masa lissafi, da haka yake so ya koyawa kan sa hakuri daga shiga lamarin ta yanzu, ya fuskanci muhimman alamuran da ke gaban shi na taimakawa mahaifin sa kan shaanin mulkin sadon sauke nauyin alummah dake kan su.
Don haka yayi gefe da Amani daga ran sa (for the mean time) na yana so ta koyi son shi domin Allah ba don wasu material attachements, ko nasabar da take goranta masa ba.
Daga wajen Mai, sai ya wuce suka yi sallama da su Daddy, yana jin wata irin kewar Alhajin nasa, Mukhy har da hawaye ya yi, ya fiddo wayar shi ya yi ma Alhaji hoto, yace Alhaji duk tsayin lokacin nan wai ace bani da hoton ka a waya ta. Dariya Hon. Ya yi ya ce to gashinan ka samu, sai ka ajiye in ka tuno ni ka dauko ka duba. Tunda ni da Uwa bama kama balle take tuna maka ni, Jalan da yake ta fini karfin jini ta kwace wannan. Da kyar suka iya rabuwa don dare ya fara yi, daga wajen su sai ya wuce sassan Ummami.
Ya same ta tana shirin kwanciya, sai ta ce Maina tun dazu nake jiran shigowar ka in kwanta don na gaji da yawa, hidima kan hidima yau na sha ta har na gode Allah. Alhamdulillah tunda komai ya nabbaa yanzu yadda na tsara Mukhtar ya samu kujerar sofa din ta ya zauna, ya ce ai ga ni yanzu, Sweet Mum, me zaki bani Ummami na?
Budar bakin Ummami sai cewa tayi.
Amanar diya ta Amina mana!.
Maina ka sani daga yau zaka soma rayuwar manyantaka, ka kasance mai hakuri da yi wa matar ka adalci da rangwame a kan duk wani ajizancin ta, kai ne babba sama da ita, don haka babba juji, bayan kasancewar ta matar ka yar uwar ka ce, jinin ka ce, da ta fi karfin kowanne uzuri a wurin ka.
Haka Ummami ta zaunar da Mukhy wajen awa guda tana masa wata irin nasiha mai ratsa zuciya, ta gaya masa ta kai masa Amani gidan sa yanzu haka.
Ya dan yi shiru na yan sakanni, ya rasa a yanayin da yake ciki, finally, shi da Amani yanzu! A gida daya, daki daya, kuma gado daya. Tsakanin farin ciki ko akasin sa, bai san wane ne yake nukurkusar sa a kasan ran sa ba, a can wani sako na zuciyar sa yayi kewar ta, a wadannan sati biyun da bai sanya ta a ido ba kuma bai ji muryar ta ba, duk da yake busy da kula da Alhaji, amma kullum sai Alhaji ya masa zancen ta, mai nuna yay aye mat aba don halin ta ba, mai nuna tsanannin kaunar da shimahaifin nata yake yi mata, wanda ke sawa ya kara mannata a zuciyar sa shima ko ya ki Allah balle yana son ta, albarkar Alhaji sai son yake ninkuwa kullum. Amma ba don ita ba, ba kuma don halin ta ba, sai don an jarrabce shi da son ta da kaunar ta tun kafin haka, (no matter how worse her behaviours are).
A haka suka yi sallama shi da Ummami, yana jin kan sa kamar wani sabon mutum yau da ya mallaki matar aure a cikin gidan sa, kuma yar Alhajin sa, Amani Tafisu da zuciyar sa ke matukar so fisabilillah, ya shiga ratsa falillukan Ummami ya wuce zuwa sassan nasu, dogarai na faduwa suna gaida shi a duk kofar da ya wuce.
Tunda Ummami ta ajiye ta a bakin gado bata sauya wajen zama ba, dan irin kukan nan na amare babu shi a idon Amani Faskari, idanun kemadagas, kamar soyayyar gyada marau-marau, amma damuwa da taraddadin haduwa da Mukhy yau, ta mayar dasu yan kanana, data gaji da lullubin ta sauke shi saman kafadun ta, ta daga kai tana kallon irin wannan dukiya da aka zuba musu a wannan daki don su biyu rak, ta dade a zaune tana godiya wa sarki Allah akan komai ma, musamman a kan iyayen ta da suka koma auren su, sai kuma ta tuna bata yi sallahr isha ba, don haka ta tashi da sauri ta shiga inda take tunanin toilet ne, don yanzu bata wasa da lokacin sallah ko kadan sabida nasihun Ummami.
Ta idar da sallahr tana addua ta ji motsin shigar sa dakin da ke kallon nata.
Kamar ta je, kamar kada ta je, ta tunawa kan ta cewa ita fa amarya ce no matter how, Mukhtar shi ya kamata ya zo inda take duk mulkin sa.
Don haka ta daure ta cigaba da zama akan dardumar da tayi sallah, daga baya tun tana addua a kan Allah ya gyara mata halayen ta da kowa ke kuka da su, har barci ya dauke ta a kan sallayar.

Mukhtar na nasa dakin har washegari yana barcin gajiya, haka kawai zuciyar sa bata amince ya je ga Amani ba, ko ya so hakan zuciyar ta ki amincewa, haka kawai ya koyi juriya daga shiga alamarin ta.
Basu suka hadu cikin gida ba sai da safe a falon sa na farko, ta fito cikin sassaukar shiga ta atamfa Holland, ta yi daurin kai dai-dai misali ba irin daurin ta na baya da ta saba yi ba wato Ture ka ga Tsiya yau daurin Amani kan sa ya russuna, kamar yadda zuciyar ta ta russuna, musamman da ta ga sun kwana gida daya da Mukhy amma ko da wasa bai neme ta ba. Jikin ta duk ya yi laasar ya jikakken tsumma.
Mukhtar na kwance cikin kujerar zaman mutum daya a falon nasa ta shigo ba tare da ta san yana ciki ba, don ta duba abinda suka shirya musu na Karin kumallo, ya yi wata irin kwanciya kamar mai barci amma a zahiri ba barcin yake ba, yana tuna maganar da suka yi da Mai ne, na cewa Mai Diffa yana so ya karbi sarautar Diffa tun yanzu, sabida shi tsufa ya cimmasa abubuwa da yawa baya iyawa yanzu, sabida rashin karfin jiki.
Ya tuna amsar da ya baiwa Mai a lokacin.
Allah ya taimaki Mai Diffa, ina rokon a bari zuwa gaba kadan, tunda Allah ya hore maka lafiya da koshin lafiya da abinda lafiya zata amfana, ina so in kara samun nutsuwar da zan kara fuskantar yadda shaanin mulkin yake daga gare ka.

Takun sawun Tafisu da kamshin turaren ta ne ya ankarar da shi isowar ta, a daidai kafafun Mukhy Amani ta zauna, har yanzu gajiyar tafiya bata sake shi ba, shiyasa yake ta kwanciya tun jiya ya kasa fita yau, ya bita da kallo tana zama a daidai kafafun nasa, har ta zauna fuskar ta ba yabo ba fallasa sai damuwa da kulawa, ga dukkan mamakin Mukhtar sai cewa ta yi.
An dawo lafiya Ya Mukhy?
Sai kuma ta tuna zaman da Ummami ta ce irin shi zata dinga yi in tana gaban Maina, ai kuwa ta gyara zaman nata da irin zaman Ummami din, kamar zata shige cikin jikin sa russunawa da kulawa kamar baiwa a gaban Sarki, shi dai Mukhy kallon ta yake daga kwance yana cewa cikin ran sa wannan canjin nata ba na kalau bane, don ganin abun yake banbarakwai, wai namiji da suna Hajara.
Haka nan dai ya daure ya amsa mata (with straight face), sai kuma ta ce masa ka ci abinci? I mean breakfast? Ya dan kalle ta da wutsiyar ido yana mamaki, sai ya biye mata da yadda ta zo, ya ce aah ban ci ba tukunna, wani abu ne ya faru? Tashi na kenan daga barcin da na koma bayan sallahr asubahi, shine na zo nan nake hutawa, kafin lokacin fita ta ya yi.
Mukhtar yayi bayani, don ya kasa gane inda ta dosa da sabon canjin, yafi sawa a ran sa wani abun take so shiyasa, don bai saba da concern din da yake gani yau daga gareta ba. Amani ta karya kai, Allah ya taimaki Maina to ai ga abincin can sun shirya shi tun dazu a kan dining-table, Maina ko zaka taso mu je mu karya tare?
Mukhtar ya kasa hadiye mamakin sa har ma da dariyar sa, ya ce Amani ce kuwa?
Don hatta lafuzzan ta da wani irin taushi da rangwada suke fito masa.
Tayi murmushin jan hankalin miji, sannan ta ce ko a kawo maka abincin nan ne Ya Mukhy? Idan ba ka son tashi daga nan din?. Sai ya ce umh kawai, ya koma yadda ta zo ta same shi a kwance, ya sake maida hankalin sa kan wayar sa, don ya kasa gasgata abunda yake gani daga gare ta dinnan. Maiyuwuwa gizo idaun sa ke masa.
Amani sai ta tashi ta tafi ta kawo abincin daya bayan daya, ta shimfida ledar cin abinci a gaban sa, ta hau hadawa Mukhy black tea mai kamshin kanimfari da citta, don Ummami ta ce mata lallai su duka su dinga yawan shan kaninfari, tana cewa ni bana shan tea da madara fa, ban sani ba ko kai ma haka?
Mukhy ya tashi zaune sosai, sannan ya harde hannuwa a kirji, ya kuma harde kafafun sa, ya zuba mata kyawawan idanun sa, ya sake cewa umh, kawai, yana ta mamaki dai, don still ya kasa yarda ita ce, sai ta mika masa kofin shayin da ta kammala juyawa da Zuma maimakon sugar, ta bashi cikin girmamawa.
Mukhtar sai ya karba, ba tare da ya ce komai ba, ya kuma kai bakin sa ya kurba, kamshin kanimfarin ya masa dadi a makoshi, bai ce aah ba, amma bai yi wata kwakkwarar magana ba har yanzu.
Amani ta cigaba da zama a yanda take, abin ki da rashin sabo da kyakkyawar muamalar data ke son assasawa, duk ta kasa sakewa da zaman da tayi din, shi kuma ya cigaba da sipping shayin sa ko a jikin sa. Ganin ya karba ba tare da ya gwale ta ba har yana sha, sai ta samu karfin guiwar zuba masa farfesun naman kaza, ta sa spoon a ciki ta mika masa.
Ya karba again, ya soma shan romon da cokali, yana yi yana daga ido yana kallon ta, ta kara da zuba masa chips and fried egg wanda ya ji albasa da koren tattasai, ta sake mika masa, ya karba babu musu, don yana jin yunwar sosai, rabon shi da abinci tun jiya, amma kuma babu magana a tsakanin su sannan babu nagode.
Ta zauna ta cigaba da latsa wayar hannun ta wanda chatting ne suke yi da Balewa, ta ce Bestie, Im done with step one, but he seemed careless da kokari na. Balewa ta turo mata Emoji na jinjina da kwanji, ta ce, dont worry, keep up the good work, saura kwashe kwanukan da ya gama cin abinci, ki tabbatar rigar ta zazzago gaba kuma a saitin idanun sa kin masa flashing.
Dariya ce ta kama Amani ta yi yar sheshshekar dariya ba shiri, ta ce Balewa ba dama! Sai da Mukhtar ya dago daga cin abincin sa ya dube ta, ke da wa Hajjaju? Ya tambaya cike da tsegumi, don kuwa Amani ba mutum ce mai yawan fara ba balle a je ga dariya a iya sanin da ya yi mata.
Yau kuwa sai fara take kamar gonar auduga. Yanzu kuma har da kyakyatawa.
Ya Mukhy ni da Balewa ne.
Oh I see! Ki ce Your role model!. Ta yi murmushi, domin bata yarda da abinda yace din ba, hakika da aboki yana maida abokin sa role model din sa, da tuni Balewa ta dade da zame mata role model tuntuni ba sai yanzu ba da duniya da kan ta ke koya mata hankali. Domin iyakar hankali da sanin ya kamata, mutunci da sanin ciwon kai da rikon addini suna tattare da HAMIDAH HASHIM BALEWA, ita din ce a baya bata yarda ta yi copying halaye da dabiun Hamida Balewa ba, don a nata tunanin, a sanda take kan ganiyar ta it ace wayayya Balewa bata waye ba, shi yasa take yin simple life duk da kasancewar ta yar gata, kuma a nata ganin simplicity din Hamida yayi yawa, zai sa kowa ya raina ta.
Sai yanzu ne ta san Balewa ce wayayya ba ita ba. Ita shirme da kidifiri da girman kan banza kawai ta sani, ta kuma kware a kai.
Mukhy ya ci ya koshi, ta tashi don ta kwashe plates da bowl din farfesun, ta yi yadda Balewa ta ce ta yi, kuma cikin saa Mukhtar dagowar sa kenan idon sa ya fada kai, ba zato ta ji ya mike shima, zata tafi da kwanukan sai ya dan rungumo ta ta baya, ya ce.
Na gode da kulawar nan, nagode da dan canjin nan dana gani, honestly I cant resist it!.
Sannan ya dora karan hancin sa saman gashin kan ta yana rike da ita daga bayan ta, ya mannota sosai zuwa jikin sa, yana sunsuna gashin ta yana cusa dogon karan hancin sa a ciki, wanda hakan ya sa dankwalin Amani ya sabule ya fadi kasa ta baya.
Gabadaya gashin da ya shag yara ya zubo bisa kafadun ta. Ya Ilahee! in ji Mukhy. Yadda Mukhtar ya shiga goga tsinin karan hancin sa cikin gashin kan ta ya haifar mata da yar rudewa, daburcewa da bakuwar kasala, duk ta san cewa ita ta tsokano shi, hakan yasa kwanukan dake rike a hannun ta subucewa suka zube a kasa,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login