Showing 27001 words to 30000 words out of 30436 words
zasu so ni a yadda nake ba?
Ke da yake yar Qaruna ce kin ki yarda mu daidaita kan mu har yanzu, sabida baki son yaron Alhaji, ni kuma iyaye na na na son ganin yaya na da wuri, Maimartaba kuma na son gani na cikin nutsuwar data dace da kowanne dan gata.
Kullum in naje fada bani da nutsuwa in na ga babu yayan Mai ko daya bayan ni, ina son samun yara wa iyaye na yara masu yawa, tun da su Allah bai basu yaya masu yawa ba.
Ki fada min yanzu da lafiya ta da komai, an yi mana aure ya kusa rufa watanni nawa amma har yanzu ban san irin nawa ba, Tafisu zina kike so in je in yi in ban karbi kyautar sadakoki ba?
Ko kuma durkusa miki zan yi in roki alfaramr ki so ni, ki kuma bani hakki na? Ai gara sa-dakan, ko ba su nake wa Son da nake yi miki ba, a kalla zan dinga rage zafin da kike kunsa min dasu.
Amani ta zuba masa jikakkun idanun ta da ke zuba cikin tashin hankali, bata ko kyaftawa, bata taba zaton Mukhtar zai iya wadannan maganganun ba, Mukhy mai kawaici da kamewa. Mukhy ya kalle ta yana murmushin tura haushi, ya kara guma mata da cewa.
Kuma banda abun ki, banda shirme irin naki Sadaka ai ba matan aure bane na hakika a wurin sarakuna, da zaki yi kishi da su, kada ki damu ababen hutawa ne ga sarakuna kadai.
Amani na neman zaucewa yanzu ta ce au, bama daya bane har nawa ne ka roko? Yace na roka ko aka bani kyauta? Su biyu ne kawai aka kawomin daga Sultanate of Damagaram.
A wannan gabar Amani ta kusa dawowa tsohuwar Amanin ta yanzu, domin jijiyoyin rashin kunya sun mimmike, tsigar jikin ta har tashi take, manyan idanun ta suka firfito waje, ta ce.
Mukhtar! To kai din wane irin jarababbe ne da zaa kawo maka mata biyu a lokaci daya? Plus me, three? Kwatakwata shekarun ka nawa?.
Mukhtar ya buda hannuwa irin na (ba matsalar ki bace) ya ce har goma in ina so zan hada a lokaci guda, in kika bani dama ko yanzu sai ki ga irin jarabar tawa.
Ya soma tunkaro ta, idanuwan sa na nuna yau ba mai raba shi da Amani sai Allah yana balle botirin wuya da links din hannun farar shaddar jikin shi, ta ce.
Allah ya suwake in hada miji da wasu, wallahi sai ka maida ni gidan Uba na, kafin ka karbo su, ai ba kai kadai ne dan gata ba, nima nan da kake gani na TAFISU ce har yanzu har gobe, bar ganin na yi sanyi, ina nan a Tafisu na da ka sani in aka tabo ni.
In banda mugunta na taba cewa kada ka kusance ni? Ko kuwa ba kai kake dakatawa don radin kan ka ba da son saka ni a damuwa Ya Mukhy? Za dai ka karba ne don ka sanya ni a bacin rai, don ka ga na fara son ka Mukhtar ba don komai ba!
To idan so cuta ne to hakuri magani ne! na barwa sadakoki kai, ka maida ni inda ka dauko ni gobe goben nan. Ta rushe da kuka, ta ce wallahi Katsina zan koma wajen iyaye na, sai dai ka zaba ko ni ko sadakoki, ai da aka bar ni a nan ba wai an ce gata na ya kare bane.
Mukhy, yau ji yayi kamar yayi juyi a gaban ta don dadi, murmushin da ke kan fuskar sa sai karuwa yake, for the first time ya fahimci Amani ta fara son sa don radin kan ta, ba abinda yafi dadi ga da namiji irin ya fahimci matar sa na tsananin kishin sa irin haka, yau ga Tafisu na kukan kishi a kan sa kamar ta shide.
Niyyar sa da farko shine ya rungume ta, ya lallashe ta ya sumbace ta son ran sa daga nan koma me zai faru ya faru yau, in yaso gobe yace a bar sadakokin baya so, ya yi amfani da wannan damar ya gaya mata cewa son da yake mata mai yawa ne da ya isa cike gurbin mata hudu! Ba wata mace da zai iya yi wa irin son da yake mata.
Amma ko me Mukhtar ya tuna? Sai ya fasa rungumeta din da yayi niyya ko ya lallashe ta, ya sa kai zai wuce ta gaban ta ba tare da ya tsinka mata ba, amma a ran sa yana mamaki yana karawa, wato duk shakiyanci ne abun nata, Amani ta san SO.
Yau wace irin ranar saa ce a gare shi?
Amani ganin zai tafi ya bar ta a wurin, wato bashi da lokacin sauraron ta, don bai dauke ta mai cikakken hankali ba, bata san sanda ta sha gaban sa ba. Ba inda zaka je Mukhy, na rantse sai ka zaba ko ni ko sa-dakoki.
Kai tsaye Mukhtar ya wani irin dago, ya zuba mata fusatattun idanun nan nasa masu kama da an diga musu zaiba, ya ce bani hanya in wuce kafin in yi huce kan dami a kan ki, me zaki iya idan na ce na zabi sadakokin, tunda zasu bani abinda Amani-Tafisu bata bani, zasu so ni su kaunace ni, son da Amani-Tafisu bata yi min, zasu so ni duk rashin asali na da rashin kowa nawa.
Amma Amani fa? Wadda kyawun Mukhy da ake fadi bai taba bugar da ita ta So shi ba, saboda Mukhtar bai isa komai ba a idanun ta tunda ni hadimin gidan su ne! Amani wadda da ta aure ni, ni da bani da asali, kuma ba dan kowa bane gara ta auri tsohon mai kudi saan Baban ta Alhaji Sadisu Talle?
Ni kuwa me zai hana ni karbar sadaka, idan har ba maza na rako duniya ba kamar yadda Tafisu ta rako mata? Kamar wani wani wanda bai san gatan iyaye ba irin wanda Amani ke tutiya da shi a koda yaushe?
Kullum ki saka a ran ki a wurin Alhaji ne kadai kike amsa sunan TAFISU, amma baa wurin Mukhtar da sauran mutane ba, tun da ni ban yarda Amani ta fi sauran mata komai ba sai iya sai rashin kunya da rashin daa, duk halin banza shi ta fi su iyawa!.
Maganganun sa sun ratsa ta, domin ta fahimci ya fidda tsatsar duka maganganun ta ne dake kwance a ran sa, duk tsayin lokacin data yi masa su, tana fatan tunda ya furta su yanzu, bayan ta jima da gasa masa su, daga yau ya samu sanyin su daga ran sa, ko ta samu su bar zuciyar sa gabadaya.
Ta sunkuyar da kai. Guilty conscience na aikin sa ta koina yana nunawa a fuskar ta. Jikin ta duk yayi dan sanyi musamman da ta ji a jikin ta Mukhy ya kafe ta da kyawawan idanun sa, yana karantar reactions din nata, amma Amani-Amani ce har gobe, sai in baka tabo ta ba, masu iya Magana suka ce. A bar hali a ci me? to hakan yake ga Amani yau ma.
Domin kuwa share tasirin maganganun sa ta yi gefe ko ince ta hadiye tasirin da suka yi mata ta ce.
Tunda ban fi su ba, shine na hakura na bar musu Mukhtar din, tunda a duniyar ka mutum ba ya taba yin kuskure ya dawo ya tuba.
Ko mai yasa? Ita kan ta Amani bata sani ba. Amma ta san bata taba jin faduwa da karaya sun same ta ba irin yau, duk da dai Mukhy yau cikin subutar baki yayi gangancin gaya mata YANA SON TA, son da baya iya kwatanta shi dana kowacce mace. Sai hawaye ya kara tsinkewa Amani, ji take gabadaya yau tata ta kare.
Ta samu kanta kawai da kifa kai a kirjin Mukhtar ta shiga sakin kuka wiwi, tana rera shi cikin zaki muryar ta kamar sarewa.
Ba kasafai kukan Amani ke bashi tausayi ba, saboda ya riga ya san ita zuma ce sai da wuta, ta hakan ne kawai zai iya rama kadan daga abinda ta dade tana yi masa, hakika Amani ta dade tana cutar da shi da kalaman fatar bakin ta, yana shanyewa yana hadiyewa albarkar mahaifin ta. Amma ganin irin karayar data same ta yau, ga ta kuma kwance akan kirjin sa sai ya ji shima rauni ya shige shi, ya kuma san lallai dagaske Amani ta canza, ko a ce ta fara canzawa, domin a irin zafin kan ta, babu karaya ko kadan a tare da ita cikin tsarin ta. A ajandar halayen ta duka babu given up, ba zai ce saboda sa-daka bane ta fara canzawa, ya dade yana karantar ta, ya san tun kafin maganar sadaka ta samu canji a kan sa a zuciyar ta, haka ya san baka taba kishin mijin da baka so har haka.
Zame ta yayi daga jikin sa cikin karfin hali, domin ta saka masa kasala ba yar kadan ba, ya juya zai fita, cikin mutuwar jiki, ba tare da ya kara cewa komai ba.
Amani ta sake ruko shi da karfi, murya na karkarwa ta ce,
Mukhy! Will you believe me, if I said I LOVE YOU?
Sai ya juyo da dukkan idanun sa yana mata wani kallo, kamar na warning din ta daina rike shi, amma kuma ya firgita da jin kalaman, domin sun zo masa a bazata, a cikin idanun sa soyayya da kaunar ta ne tsantsa, haka nata jikakkun idanun abinda ke kwance cikin su kenan, kallon da sukema juna ya shiga tado wata irin shaawar juna ta shiga tarnaki a zukatan su, ta shiga ruruwa tun daga kwakwalen su har yatsar kafafun su, in bai yi kuskure ba kamar yau ya taba jin sunan sa a bakin ta.
A yanayin da fuskar ta ta koma yanzu, kamar ta rasa duk wani gatan ta sai shi kadai, a irin kallon data ke masa yanzu, kamar shi kadai ya rage mata a fadin duniya, hawaye na zubar mata wasu na korar wasu ta zame daga jikin sa ta durkusa masa, ta rike kafafun shi tanaci gaba da kukan sosai, tana rokon sa da murya mai ban tausayi ya yi hakuri da duka halayen ta, daga yau ta yi alkawari ta daina!
Ya Mukhy, na yarda ka yi min komai don ka huce hali na na banza, na yarda hali na da yawa mara kyau ne, na yarda zan canza daga Amanin da baka so, zuwa Aminar da kake so, na yarda zan zama matar Maina Mukhtar daga daren yau, abokiyar rayuwar sa ta har abada kuma abar hutawar sa karkashin inuwar aure.
Amma ka yi min rai! Banda kishiya ko sadaka, saboda bana son su, zuciyata baza ta iya dauka ba Ya Mukhy. Saboda bazan iya sharing Mukhy dina da wasu matan ba. Hakan zai iya manna min ciwon hauka da ciwon damuwa.
Ya Mukhy don Allah ka yi hakuri, ka yi min rai, kada ka karba!
Kaga ni tun fil azal ba Maina na aura ba Mukhtar na aura, ban san da wadannan traditions din naku ba, na roke ka kada ka bari kokarin tabbatar da culture and tradition na gidan ku da basu zama dole ba a addidni su rusa kyakkyawar dangantakar mu, da rayuwar dana yi mana tanadi daga yau.
Amani ta russuna ta sumbaci babban yatsan kafar sa cikin roko, duk hawayen idon ta ya koma diga akan kafar sa.
Zuwa yanzun kam hes touched, extremely touched! Kuma ya yarda abinda take fada daga zuciyar ta yake fitowa, ba daga fatar bakin ta ba, mamakin hakan da birbishin tausayin da so ke kimsa masa, suka taru suka soma rinjayar dakiyar sa da pretending din sa, suka hana shi magana suka hana shi motsin kirki, ita kuma ta kai sumba yatsan kafafun shi, Mukhtar yayi mutuwar tsaye, amma dai yana gargadin kan sa a kan yayi taka-tsa-tsan da nadamar Amani don akwai gaggawa a cikin ta, kuma sadaka da bata so ne sila, yaushe har Amani ta fara son sa irin haka, da har ta shirya rayuwa da shi haka?
Komai aka ce masa mace zata iya, in dai a kan kada a yi mata kishiya ne yau kam zai iya yarda.
Mukhtar ya san tsakanin sa da Ubangiji yana matukar son Amani, halayen ta da dabiun ta ne dama baya so. Ganin ta tana neman shidewa a gaban sa yau a kan kishin kada wasu matan su rabe shi ya yi matukar tasiri a tare da shi ba kadan ba, ya kara masa son ta da jin tausayin ta, ya rage masa kuzarin muzanta mata.
Duk da haka wani devilish bangare na zuciyar sa bai yarda da ingancin nadamar tata da soyayyar tata ba, ya fi dangana yanayin ta na yau da KISHI. Amma a irin kukan da take yi rike da kafafun sa harda sumbata, sai ta soma saka masa rauni, wato ta soma samun weakness din sa, sabida baya son ganin kukan mace balle matar sa AMANI-AMANAR ALHAJI.
Domin ji yake sumbar da take ma yatsun sa na neman sumar da shi daga tsaye, duk wasu tsofaffin feelings din sa a kan Amani na sake dawowa sabbi kar, suna sake sakin sabuwar yabanya ta korran ganyayyaki a fadin zuciyar sa.
Yau Ga TAFISU a kwance a kan kafar sa, tana neman gafara da jin kan sa, daga soyayyar sa da kin kishiya, a irin yanayin da yau ko me ya nema zai samu har mafiyin sa, ba tare da ya yi hurting feeling din ta ba.
Amma duk da haka taurine rai irin nasa ya ki bari ya dago ta, yana gayawa kan sa kada ya yarda ya bada kai yanzu, sai ya tabbatar da ingancin wannan nadamar tata da canzawar tata, aka ce kowa ya tuba don wuya ba lada, duk da cewa a cikin idanun ta ya ga nadama da soyayya tsantsa, sai dai ya san wasu mata ko basa son miji suna kishin sa, tunda aure ne a tsakanin su.
Sai kawai ya janye kafafun sa daga rikon ta a hankali, cikin karfin hali ya taka ya fice ya bar ta a falon, zuciyar sa kamar ta fashe da son Tafisu, da ke kara tumbatsa a kowanne sako na cikin ta. Yana gayawa kan sa Amani Zuma ce sai da wuta, gara ya kara rike shaawar sa a kan ta komai karfin ta, zuwa lokacin da ya dace da ya amshi nadamar tata, amma ba yanzu da tsoron sadaka ne yafi rinjaye a ran ta ba, ba soyayyar sa ba (a ganin sa).
**** **** ****
AMANI
A
wajen da Mukhy ya bar ta ta ci kukan ta ta koshi, tana gayawa kan ta Mukhtar baya ta tata yanzu tunda ya zo cikin gatan sa, ko dama can yaya lafiyar Kura? Dubi dai irin lallashi da roko da bada kan ta data yi amma yayi funfurus! Itama kawai gara ta koyawa zuciyar ta hakuri da shi ta yi zaman Ummami cikin gidan nan, tunda uwar ta ce ko ba Mukhtar a tsakani, tunda in tace ta barwa sadakoki Mukhtar din, ita a maida ta Katsina ba sauraron ta zaayi ba, ba kuma maida ta zaa yin ba, ta san ta shigo gidannan kenan har abada ba saki ba yaji, sunan auren nan mutuka raba in ji Ummami, zata koyawa kan ta juriya ta rabu da shi ya auro ko goma ne ta koma gefe ta yi kallon su.
Tunda shi baya amsar tuban dan adam, baa kuskure a nemi gyarawa ya yarda ya bada second chance, Allah da kan sa mai afuwa ne, kuma yana son bayin sa masu afuwa, yana amsar tuban bayin sa idan sun yi repenting, sun tsarkake zukatan su daga sake aikata wannan kuskure, then why not him?
Wanda shima ba sama yake da aikata kuskure ba, tunda ba maasumi bane ba kuma Annabi b.
Ai bari kawai ta nuna masa har gobe tana nan a Tafisun ta, ajin ta bai tsinke ba, halin ta na banza na girman kai da raina mutane da wulakanta su kawai ta bari.
Tana wannan sake-saken tana hadiyar zuciya sabida kukan data ci, daga bisani ta wuce uwar dakin ta ta kwanta bisa gado, da tunanin Mukhy barcin wahala ya sure ta a wajen.
Cikin barcin ta, tsabar yadda ta saka Mukhy a ran ta, da son ya lallashe ta koda da kalaman fatar baki ne, amma ya saka kafa ya fice ya yi banza da kukan ta,