Showing 3001 words to 6000 words out of 30436 words

Chapter 2 - Amani Book 3 Hausa Novel Complete

Takori   

13 Dec 2024

152

suna jin ta, Sahura na yagar cinyar Dawisu ta ce ah to ai duniya makaranta ce, ta ishi kowa riga da wando har da hula. Allah da kan sa yayi hani da girman kai, ya bada misali da Shaidan da Annabi Adamu Alaihissalamu,
Ubangiji da ya halicci dan adam ya karrama shi akan dukkan halittun sa, kai dan adam waye da zaka kaskanta dan adam dan uwan ka, don kawai kana tunanin ka fi shi arziki? Ai ko hausawa sun ce rabon bawa da arziki mutuwa ce.
Baba Idrisu ya ce kwarai da gaske, baka debewa bawa tsammani da arziki sai ya mutu! Uwa ki ji tsoron Allah ki gyara halayen ki na raina mutane, kiyi karatun ta nutsu, nan dai kin gani gidan sarauta ne babu ta yadda zaayi su dauki halayen ki na banza da wofi, idan ma bamu koma tare ba kenan, tunda ke din ba yar sarauta bace, na san kuma yayan sarakuna yayan sarakuna ya uwan su kawai suke aure.
Mamma Jalan ta ce da ta fi gane shayi ruwa ne. Don in ba Mukhtar din ba sarkin hakuri da girmama iyayen ta wa zai iya kwasar ta? Ai Amani an rako mata!
Yau dai gaki gidan sarautar Diffa, ko ki iya takun ki, ko ki ji ki a kofar masarauta, ko kuma ki kare karkashin azaba da mulkin kishiyoyi.

Idanun Amani suka wani irin raina fata, zuciyar ta ta tsinke, wai bata san tana da kishi ba sai yau da Mamma ta yi mata fatan kishiya, to ta Allah ba tasu ba su duka, ta san Mukhtar yana son ta ko bai fada ba, ta ga hakan muraran ranar su ta karshe da shi a Saliyo gidan Mamma, ta san ko saboda Alhaji ba zai wulakantata ba balle yayi mata kishiya. Ta san ta yi kuskure ba kadan ba amma a bata dama zata gyara. Ba wai a bita da mugun fata ba. Sai ta saka kuka tana cewa.
Mamma ke uwa ta ce, duk abinda kika fada zai iya kama ni, ki fadi alkhairi a kaina da Mukhy ko kiyi shuru. Ta yaya zaki yi min fatan kora ko kuma na kishiya? Baba Sahura ta fashe da dariya tana fadin yau kuma? Lallai Amale ya ga Zaki. Yarinya wa ya gaya miki Bornu gabas take, miji irin wannan ake cewa baa so banda wauta da hauka?
Daddy ne kawai ya ji tausayin ta, yadda suka taru suka yi mata caaa! Ganin yadda duk ta bi ta muzanta. Yanzu kam ta gama saddaqarwa Mukhy ya fi karfin ta, idan bata yi saa bama tare da iyayenta zata koma Katsina a matsayin sakakkiyar bazawara. Sunan ta ya koma bazawara. Irin iskancin da ta tata masa da kaskanci da rainin hankali da kyar zai iya yafe mata tunda ya dawo cikin gatan sa.
Na tuba Ya Ubangiji na tuba! Amani ta fada a fili tana hawaye. Alhaji daga zaune ya mika mata hannu ya ce zo nan Uwata, rabu da su kin ji! Bakin su ya sari danyen kashi. In dai Mukhtar dina ne dana sani wallahi zai yafe miki, kuma shi mutum ne kaifi daya bana jin rashin hankalin ki na damun sa, tunda yace ya amshe ki to da gaske ya amshe ki, bana jin dawowar sa gida zata sa ya canza magana. Ke dai ki yi kokari daga rana irin ta yau ki canza halayen ki, ta hanyar komawa AMINA ba AMANI ba.
Aminatu Mamar Manzo maaobociyar ilmi da hankali da iya zama da mutane, kin ji?
Ya shiga bubbuga bayan ta yana lallashin ta domin kukan nadama take yi tukuru. Tana mai adduar kada Allah ya kama ta da laifukan ta a kan mijin ta Mukhtar.
Daddy kai kadai ne ka yi min fatan alkhairi, na gode Daddy har abada na san inada kai, na san ba zaka bari a wulakantani ba, wai don nayi laifi na kuma gane na yi laifi na tuba.
Mamma don Allah ki hyi hakuri ki sa min albarka.
Mamma ta kora ruwan tataccen inibi a tambulan na tangaran mai garai garai ta dube ta yanzu da rahma a idanun ta, ta ce idan da gaske kike kin tuba, Shi Ubangiji mai afuwa ne kuma yana son masu yawan tuba daga laifin da suka san sun aikata.
Ni kuma zan taya ki da adddua a kan Allah ya huwwace miki zuciyar sa, ya baki dukkan soyayyar da ke zuciyar sa, ya kade fitina a zaman ku, ya baku zuria mai albarka.
Amani ta ruga da gudu ta rungume Maman ta tana na gode Mamma, na gode sosai.
Sun kwana suna tattauna alamarin nan cikin tuajjibi da mamaki iri-iri, Mukhtar dan baiwa ne hakika, wanda bai taba alaqanta kan sa da wata daukaka irin haka ba a inda ya tabbatar baa san ko shi waye ba, amma hakika wasu attributes nasa da yawancin personality din sa masu tsinkaye a cikin su irin Mamma, sun ce sun sha alaqanta shi da babbar sarauta ko babbar nasaba.
Suka kwana hira da tsarkake tsarkin mulkin Ubangiji.
**** **** *****

Haka suma Uba da dan da mahaifiyar sa, sun kwana tare a turakar Sarkin Diffa, kamar su maida dan nasu Mukhtar cikin su. Wani abu ne da Mukhtar bai taba samu tare da su ba tun haihuwar sa, wato closeness sai yau. Don haka (he cant control his tears).
Maina ina ka je? Maina ina ka shiga? Maina ka bar mu, shekara goma sha biyar ba kwana goma ba Maina in ji Ummami, tana share hawaye da gefen laffayar ta.
Ummami I thought kun fi son hakan, kun fi son in yi nisa da ku din, ba kwa so in rabe ku, kamar ba ku kuka haife ni ba.
Na yi kokari na jure hakan tun haihuwa ta amma dana fara girma sai abun yake neman zame min ciwo a zuciya ta, dole na zabi in tafi in yi rayuwa a inda bazaku ko samu labari na ba, tunda zamana tare da ku bai da wani amfani a gare ku.
Daga baya kuma kullum na yi kokarin juyowa gida bana iyawa sakamakon dabaibayin dake zuciya ta.
Rana daya Allah ya yaye min wannan dabaibayi, naji hankali na ya yo gida, Im so sorry Ummami, har aure na yi babu jimawa bada sani da yardar ku ba, but I have no choice, saboda mahaifin ta has been my savior, my shelter for a very long time.
Nan ya gaya musu cewa bayan ya karbi kwalin kammala karatun sakandire tare da yayan bayin gidan a makarantar gwamnatin Diffa da yayi ya kasa cigaba da zaman kasar Nijar, ya yanke shawarar shiga duniya ya nemi ilmin da zai taimaka masa ya dogara da kan sa. Tunda sun nuna basa bukatar shi a rayuwar su sun bar shi a bangaren bayi yana rayuwa tare da yayan bayi, karkashin kulawar Jakadiya da mijin ta Sarkin fada, wato Bafade Katchalla wanda shi ya fara gane shi yanzu ma da ya dawo.
Ya ce tunda na taso na ganni a hannun jakadiyar Ummami, ita ta raine ni, saidai lokaci lokaci ta kaini gun Ummami ta kuma dawo dani bangaren da take wato bangaren bayi.
Dana fara girma, ma sai ta rage kai ni gun Ummami, itama ba koyaushe take wuni da ni ba tafi wuni a cikin gida, sai dai in yi ta wasa da yaranta maza guda biyu saanni na, sai na dauka ma su suka haife ni wato ni dan jakadiya da Baba Katchalla ne, musamman da suka saka ni a makaranta tare da Shettima da Ari, wato yayan su, muke zuwa tare kullum muna dawowa.
A hakan sai na fara mantawa da Ummami, wadda nake gani lokaci lokaci, kai kuwa Maimartaba dama ba a zancen ka, don tsakani na da kai sai dai in hango ka a turakar ka ko a fada, ko a kan Rakumi idan ana wani festivities din kamar misali bikin sallah ko na aure ko na nadin sarauta.
A baya Baba Katchalla na zuwa da ni fada mu zauna a gefe nida shi, bazan manta ranar da kayi masa tsawa ba, ka ce kada ya kara kawo ni fada, mai bakin baya ne ni, tunda ga kai na ko batan wata baa kara yi a gidan ka ba.
A ranar ne ma wasu a fada suka san ni dan Sarki ne. Nan ne aka yi ta kuskus a gari wai ashe Sarki yana da Da namiji amma baya son yaron. Ya barwa bayi shi.
Wannan zance har a makaranta an yi min gorin sa, lokacin ina karatun sakandire. A wani dare na tsuye jakadiya ina tambayar ta da gaske ni dan sarki ne? Kuma Mowar Sarki wato Ummami da muke zuwa wajen ta lokaci lokaci har wani lokaci ta bani apple ita ce mahaifiya ta? Jakadiya ta tabbatar min haka ne, amma bata san dalilin ku na ajiye ni tare da su ba, kodayake tace Sarki da Mowar gida basu da trusted servants a cikin bayin su kamar ita da Katchalla.
Tace Sarkin Diffa ba mai yawan haihuwa bane, shiyasa yake ta aure daga kasa-kasa don ya samu haihuwa, a irin haka ne ya auro mahaifiya ta daga wata kasa cikin kasashen Afrika, yayan sa biyu kacal kuma duk mata ne tare da matar sa ta lalle wato uwargidan sa da mai bi mata wato mata ta biyu. Daga kan su bai kara samun haihuwa ba sai da ya auri Ummami, kuma tun haihuwa ta suka bata ni, shayarwa ma a boye Ummami ta shayar da ni don sai ta bita cikin sirri ta roke ta.
Bayan ta yaye ni ma kuwa bata bukatar a kai mata ni inda take. Ni ne dai dana yi hankali na ji ba wanda nake so a duniya irin ki Ummami, sai nake satar jiki ina zuwa inda kuke, wani lokacin inna leka inda kuke zama da laasar zan same ku kuna sallah tare ke da Sarki, ko kina zuba masa abinci ko kina masa yankar farce, har rannan wani bafade ya kama ni ina leken ku ya taska min mari, shine fa ban kara leken ku ba daga ranar.
Watarana Baba Katchalla yace muje ana bikin Yaya ta a cikin gida, nan na bishi muka je har fada naga irin auren gata da aka yi wa yar uwata, akan taguwa aka kai ta Tahoa inda ta auri dan sarkin Tahoa, ni kuwa inna shiga cikin gidan na hau rabe-rabe kenan kamar mara gaskiya, hatta sittiru na tare ake din ka mana da Ari da Shettima, babu wani banbanci tsakanina da su. A makaranta ma ajin mu daya da su.
Dana fara hankali sai nake tambayar kaina to meye dalilin hakan da sarki da Ummami suka zabarwa rayuwa ta? Na sa a raina bakin bayan da ya taba ambata min ne dalili, wato daga kaina ko batan wata wata matar sa bata kara yi ba har ita Ummamin. Amma ai wannan bai isa dalilin da zasu sarayar da rayuwa ta a hannun bayin su ba, sai ma dai yayi dalilin da zasu daukaka daraja ta fiye data kowa a masarautar.
Bani da wata shakuwa ko kusanci da ku da zai sa na iya yi muku wannan tambayar. Ban ma isa in je inda kuke kai tsaye ba.
Na yarda iyaye na kun haife ni ne da gaske, amma kuma baku kauna ta!
In na tuna hakan sai wani irin bakin ciki ya murde ni, har ya zame min habit, daga baya bayan na kammala sakandire na ji bazan iya cigaba da zama a Diffa ba, gara in tafi inda bazaku kara jin labari na ba, tunda kun haife ni bisa kuskure amma bakwa kaunata ko miskala zarratin.
Wannan abu ya cigaba da bakanta min dare da rana, har na koma tamkar depressed, na daina walwala, na daina shiga cikin saanni na, na yarda bakin baya na zai iya shafar kowanne yaro iyayen sa su tsane shi.
Duk da babu abinda Baba Katchalla da Jakadiya suka raga min, suna ma kula da ni ne har fiye da yadda suke kula da yayan su Ari da Shettima. Rana daya na yanke shawarar barin Diffa, to amma ina zani bani da ko sisi?
A hakan ne aka ce sakamakon mu na sakandire ya fito, kuma na ci jarrabawa ta da sakamako mai kyau wanda yafi na kowa, don haka gwannatin kasar Nijar ta dauki nauyin karatun mu ni da wasu dalibai zakakurai iri na zuwa kasar goyon mu wato Faransa. Aka damka min admission dina da tikitin jirgi, na so in gayawa Baba Katchalla amma zuciya ta ta kwabe ni, kan cewa zai iya hana ni tafiya, ku kuwa dama na san ba damuwar ku bace rayuwa ta ce, baku da matsala da wannan, hasalima na yi amanna farin ciki zaku yi in yau aka ce na bar Diffa.
Hatta malaman makarantar mu basu san cewa ni Maina ne ba, sun dauka ni dan bawa Katchalla ne wanda kusan kullum shi yake kawo mu makaranta ya kuma zo ya dauke mu.
Don haka da aka fara jigilar daliban da suka samu scholarship na sulale na tafi Agadez tare da sauran dalibai yan uwa na, inda daga can jirgin mu ya daga zuwa France. Acan ne aka rarraba mu zuwa jamioI daban daban a cikin Faransa, ni aka bar ni a Jamiar Paris Saclay University.
***** **** ****

RAYUWA TA A FARANSA
R
ayuwa ta a matsayin dalibi a birnin Paris, rayuwa ce irin ta kowanne dalibi mara gata sai na gwamnati, mai fafutuka da neman ilmi da gumin sa, gwamnatin kasar mu na bamu alawus wanda da shi muke rike kan mu. Na yi wani dogon rashin lafiya bayan tahowa ta kamar bazan rayu ba, don sai da na kwashe watanni biyu a asibiti bansan inda kaina yake ba, bayan na farfado da kyar, na ji a cikin kaina bani da buri irin na kara nesanta kaina da gida, kuma har Paris din ji nake ta min kusa da Nijar amma hakika ina son samun kwalin degree dinnan, shiyasa na tsaya. Da kyar na samu na hada karatun domin banida cikakkiyar lafiya kuma likitocin kasar duk kwarewar su sun kasa gano takamaimai me ke damu na.
Akwai wani abokin karatuna Musulmi, Faiq, da ya zo daga kasar Masar, shi ya bani laqanin kullum in karanta ayatul kursiiyu kafa bakwai in tofa a ruwa da safe in sha kafin in ci komai. Da wannan lakanin na fara samun lafiya har na kammala karatu na da kyakkyawan sakamako.
Daga wannan lokacin ne tallafin da kasar mu ke bamu ya yanke mana, wato dama scholarship din mu iya degree ne, sai na shiga tunanin hanyar da zan bi in yi sponsoring karatu na na gaba wato masters, duk dai don in samu damar cigaba da zama a Paris kada in koma gida.
Ayyuka na neman rufin asirin dalibi iri-iri babu wadanda ban yi ba, tun daga wanke-wanke da share-share a hotel, direban bus, jiran shago, zaman library da kuma receptionist, da haka na kukkulla na kukkula na dinga biyan kudin karatun masters dina in instalments (a rarrabe) har Allah ya taimake ni na samu shaidar kammala degree na biyu, daga nan na dukufa neman aiki kwakkwara amma ban samu ba, ko in ce ban dace ba, ina tunanin fallewa zuwa Hong-Kong again, don neman aikin yi, Allah ya hada ni da Ubangida na na yanzu, wato Alhaji Usman Faskari.
Nan ya labarta musu komai na irin haduwar da suka yi da Alhaji, ya biyo shi Najeriya ya bashi gida da aiki ya kuma ja shi jikin sa da amana irin yadda ko yan uwan sa bai yi wa ba, duk tarin alkhairin Alhaji gare shi sai da ya fada musu har zuwa lalurar data same shi wadda tayi sanadin bashi auren AMANI da Alhaji Usman yayi. Yadda a rana daya yaji duk wani dabaibayi da ke zuciyar sa a kan Diffa ya yaye, da kuma karfin zuciyar da ya samu na dawowa gida karkashin umarnin Alhaji duk ya fada musu.
Tun kafin Mukhtar yayi nisa da labarin nan daga Maimartaba Sultan Issoffou Massaoudou har maidakin sa Ummami kuka suke yi sosai.
Sarki Issoufoou ya janyo Mukhtar jikin sa ya rungume shi yana kuka sosai da hawayen sa, yana rokon sa ya yafe masa, ya ce da Mukhy (cikin vernacular language din su).
Moukhtar, duk abinda muka yi dinnnan muna sane, we did it to protect you from envy, hatred, evil eyes, bad luck, and to save you, as the only male child that I have, to make sure you get the throne of Diffa Emirate at an appropriate time.
Ni da kaina na hana mahaifiyar ka jan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login