Showing 30001 words to 30436 words out of 30436 words

Chapter 11 - Amani Book 3 Hausa Novel Complete

Takori   

13 Dec 2024

225

ba tare da ya ce ya fasa amsar sadakokin da aka yi masa tayi ba wadanda tunanin su kadai neman haukatata yake.
Ta tsinci kan ta a duniyar mafarkin ta tare da MOUKHTAR ISSOUFFOU MASSAOUDOU cikin wani nauI na soyayyar auratayya mai shiga jiki da zuciya, tare da dan Issouffou jikan Massaoudou Balaraben Diffa mai abun mamaki, ta gan su cikin mafarkin Mukhtar yana sumbatar ta iya sumbata, yana juya ta duk ta yadda yake so, daga hakan sai kawai ta ji ya dauke ta suna tafiya zuwa turakar sa, yana rada mata cikin kunnuwan ta cewa.
Tafisu kin fi sauran mata a zuciya ta!.

Irin mafarkin da in dan adam yana yi baya so ko sauro ya cije shi ya farka.
Sai kawai Amani taji muryar Baba Sahura a cikin kwanyar ta.
Uwa Uwa, Uwa, ke wai lafiya kike barci haka a kasa, ko fadowa kika yi daga gadon, da baki na faman motsi kamar kina cin tsutsa, ga hawaye kina faman yi, kuma a bakin kofar daki kamar wata wadda uwa ta yi wa baki?
Sai lokacin ta ankara wai ashe duk wannan a mafarki ne, kenan ita tata soyayyar bata zo da wasa ba, Mukhtar har a cikin mafarki neman zautata yake don ya ga ta gama mika wuya ga soyayyar sa.
Ta mike zaune, bata san yaushe ta fado daga gadon har ta mirgina kofar daki ba, ita dai ta gan su suna mirginawa a cikin korran ciyayi ita da Mukkhy, sannan ta dubi Baba Sahura, ta tabbatar mafarki take hakan bai faru ba, Mukhtar tunda yasa kafa ya fice bai dawo gidan bama, ta kama Babar ta Sahura ta rungume jikin ta na kyarma, sai ta fashe da kuka, ta ce Baba Sahura wai kin ji sadaka zaa bashi? Sahura ta ce,
Au! Shine kike neman haukata kan ki Uwa? Yo in dai a kan zancen sadaka ne Uban ki ma ya auri mata yana saki sun fi goma, shi a kan me zaki hana shi cika alada? Gaki ke ban ga alamar kina masa wani amfani ba sai shegen kaudi da rashin kunya da kika fi kowacce mace iyawa.
**** **** ****

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login