Showing 15001 words to 18000 words out of 30436 words
Allah ya raba su a yanzu.
Sayluba kuwa sun hadu tun a wajen bikin auren su data zo, har ta koma Tahoa tun kafin a kammala bikin, halayen yayan Sarki Issouffou mata kwata-kwata bai yi kama dana iyayen su mata ba. Suna da saukin kai sosai da son mahaifin su, don bai raga musu komai na soyayyar Uba ba.
Sannan tasa aka kai Amani gun amaryar Sarki ta yanzu wadda ita daga Somaliya ya auro ta.
A daren Mukhy ya kira Mai Diffa, ya gaya masa in sha Allahu akwai alamun nasara a maganin da akewa Alhaji, don haka Sarki ya gayawa Ummami, inda ya ce ta gayawa Amani ta cigaba da yi wa mahaifin ta adduar neman lafiya mai dorewa.
**** **** ****
MALAMA BA SURUKA BA!
W
annan tafiyar da su Alhaji suka yi suka bar Amani tare da Ummami, shi ya haifar da wata kyakkyawar shakuwa a tsakanin su, kuma Ummami ma kamar kowa ta soma noticing rashin wadatar ilmin addini da rashin ingancin dabiun Amani, sakalcin ta, doloncin ta da sauran su. Amma ita ba kamar Jalan ba, bata duka bata hantara, sai tayi amfani da tafiyar su Mukhy Burkina Faso ta ja Amani a jikin ta, babu tsawa, babu duka ta soma koyar da ita muhimman abubuwa da ya kamata matar aure ta sani na addini, Ummami tun daga alwalah, sunnoni da farillan sallah dana alwallah da wankan janaba ta soma koya mata, domin ta sha mamaki da ta ce ta yi mata bayanin yadda ake yi ta ga ta hau kame kame, ko kuma kai tsaye ta ce bata sani ba, ko ta ce ta manta.
Sannnan hatta yadda akewa sarakuna magana cikin ladabi da kwantar da murya sai da Ummami ta soma aikin koya mata, da yadda ake rayuwar aure da masu mulki, wani abun Amani ta ji kunya, wani abun ta gode har cikin ran ta.
Ummami dai ta zamewa Amani malama ba suruka ba, shakuwar su ta kai ga cewa Ummami ta fahimci akwai rashin jituwa da rashin kakkarfar soyayya tsakanin Amani da Mukhtar, kuma auren hadin Alhaji ne ba wai su suka hada kan su ba, amma ta fannin dan ta Mukhtar dai ta san ko makaho ya shafa zai gane yana matukar son Amani a cikin idanun sa ma kadai, amma abinda ya fada ranar da zai tafi, ya dan tsaya mata a rai, da ya ce Amani bata son sa, auren dole Alhaji ya yi mata da shi, ta sunsuni akwai babbar matsala a kan hakan a tsakanin su.
Ummami bata san cewa daga tafiyar Mukhtar zuwa yanzu an samu positive improvement wato canji mai yawa ba, a tare da Amina-Amani. Ta kasance cikin kewar Mukhtar, yadda bata zato, ba tare da ita kan ta ta san cewa tana kewar tasa ke damun ta ba, gabadaya tayi sanyi, duk ta zama wata irin shiru-shiru ba tsiwa, ba gayu ba cokala daurin kallabi. Mukhtar ya bar ta da kewar sa mai yawa a ranar da zai tafi, in ta tuna memories na abinda ya faru ranar da zai tafi kai mahaifin ta gidan magani, wato (sweet sensation) na lokacin ya ki barin ran ta, taji tana so ma ya dawo, ko ganin sa ne ta yi daga nesa, koda yake yace ba zai kara kiss ba, umh. Amma ita yanzu ne ma ta fara so da shaawar kiss din nan nasa, ta samu kan ta da son yayi maza ya dawo a maimaita sumbar, ko da cikin cokali ne wato wadda bata kai ta tsayin mintinan na ranar tafiyar sa ba.
A wannan lokacin da wannan tunanin ya zo mata, Amani sai da ta tura kan ta cikin filo tana jin kunyar kan ta da kan ta, zuciya mai abun mamaki, zuciya tsokar naman kirjin dan adam mai yawan dawurwura (rashin tsugunawa a wuri guda), wai yau kuma Mukhtar take kewa, da bege haka, kai har ma da mararin gani, dan adam kenan mai saurin manta baya. Gaskiya ne da aka ce (no condition is permanent). Gaskiyar Balewa da ta taba cewa ta taka a sannu akan wannan bawan Allah bata san inda rana zata fadi ba.
A wannan lokacin Hamida ta fado mata a rai, hakika bata kyauta ba, tun zuwan ta bata kira Hamida ba, akawari bai ce haka ba, gashi zata so ta bata labarin abubuwa da yawa da suka faru da ita dinnan a bayan rabuwar su din nan, masu dadi da marassa dadin, koda yake masu dadin kamar haduwar ta da Maman ta da dawowar Mukhy cikin nasa iyayen su suka fi yawa cikin labarin da zata baiwa Balewa, to amma wace irin fassara Balewa kan ta zata yi mata in ta ce mata yau gata dumu-dumu cikin kewar Dirty Human Being? Cikin mararin ganin Smart Ass da begen sumumu-kasau? In reality, Hamidah ta fi kowa gaya mata ta taka a hankali a kan Mukhy, ta ji tsoron kaddara, ta rage kiyayyar ta ga Mukhy, har ce mata ta taba yi bata san inda rana zata fadi ba, yau ga rana ta fadi da ita a gabas! Inda wanda ya san kin da ta yi wa Mukhtar da tijarar data zuba masa don wai yana matsayin yaron baban ta babu kamar Hamidah Balewa, ina ma dai da a ce Hamida zata zo har Diffa, ta ga yadda rayuwa ta yi kuli-kulin kubra da ita, iyakaci dai tayi mata dariya da shegantakar da bata san karshen su ba.
Anyway, ya kamata ta kira Balewa, ta labarta mata duk abubuwan da suka faru a bayan ta, don abokin kuka baa boye masa mutuwa, shakiyanci ne dai ta san zata yi mata har sai ta gaji ta bari don kan ta.
Amani ta kira wayar Hamida, cikin saa ba jimawa layin ya shiga, duk da ba koyaushe suke amun network mai kyau na yin kira Nigeria ba, saboda rashin kyawun network na yankin su. Hamida ta daga da hamzari, tana fadin. Sahibah, ke ce kuwa a kan layin? In da alkawari ruwa baya dafa kifi ba, kin makale a Saliyo, kin manta da ni Bestien ki? Anya alkawari ya ce haka?
Amani tayi ajiyar zuciya ta ce da farko dai zan fara da baki hakuri Bestie, ki yi hakuri Hamdy, na shiga harkalla mai yawan gaske data sa ban samu damar kiran ki ba, sai yanzu da na samu nutsuwa.
Kawata I have a lot to gist you with, muhimmi a ciki, ina mai farin cikin shaida miki cewa na hadu da Mama na Haj. Jalan a Saliyo, har an mayar da auren ta da Mahaifi na mun taho tare da ita, ki taya ni hango irin farin cikin dana ke ciki a sanadin hakan, amma a halin yanzu bama Katsina muna can yankin Diffa.
Da tsananin mamaki Hamida ta ce Sahibah Diffa kuma? Wajen wa? Inane haka? Amani ta nisa tana fadin Bestie, wato labarin nan mai yawa ne, mai matukar ban alajabi, har ma da ban tsoro a cikin sa, na so a ce ga ni ga ki ne, in kwantar da kai a kafadun ki in yi kukan nadama, in kuma yi dariyar farin ciki as well, amma dai in takaice miki, na kwashi kashi na a hannun nadama, na kuma nade tabarmar kunya ta na yi gammo da ita a kai na. Abinda kika dade kina tunasar dani cewa in taka a sannu, kada watarana in zo ina nadama ya tabbata.
Ashe Mukhtar da nake rainawa dan sarkin Diffa ne, mai jiran gadon sarautar gidan su, da daya kwal da Sarki Issouffou ya mallaka, wanda inda an bi ta nasabar da nake masa gori ne, ba zai aure ni ba.
Diffa na daya daga cikin manyan biranen kasar Nijar, sannan kuma ashe dan uwana ne na jini, dan Yayar mahaifiya ta ne Haj. Aisata, wadda ke aure a can tun da jimawa.
Hamida ta yi kabbara, ta sake yi, ji ta yi kamar ta shigo cikin wayar ta tadda Amani sabida zaquwa ga abinda take ji, ta ce ki bari Sahibah, bana so, bana son irin wannan zolayar kamar ta hikaya Amani ta yi rantsuwa tace babu zancen wasa a cikin magana ta. Ashe duk jini na na yiwa wannan tijarar, yau gani dumu-dumu cikin kogin nadama da wani sabon yanayi Sahibah, wanda nake so ki fidda ni a duhun sa.
Ta dan yi shiru, domin ita kan tabtana jin kunyar abinda zata fada, kewar Mukhtar nake Hamdy, son ganin sa nake, matukar son ya sake kusanta ta na ke, sabida baya gari yanzu haka, ya kai Alhaji Burkina Faso tun satin da ya wuce ta tusa kanta cikin filo rike da wayar tana cewa na shiga uku Balewa, don ji nake abinda nake fada kamar sabo nake, amma gaskiyar abinda ke zuciya ta kenan, mararin ganin sa da dawowar sa daga Burkina Faso nake yi kamar in yi tsuntsuwa in cimmasa.
Me yasa a da bana jin hakan ban da kiyayyar sa?
Hamida bana so ya kasance sai da ya taka wani matsayi ne hakan ta faru da ni, don ban san fassarar da shi kan sa da alummar da ke zagaye da mu zasu yi min ba!
Hamida ta yi kabbara ta sake yi, sannan ta fadi ta yi wa Allah sujjadah a dakin ta, ko babu komai ya karbi adduar da ta dade tana yiwa aminiyar ta, yau matsalolin ta sun warware ta kowanne bangare, jin abubuwan da take fada mata take kamar almara ko tatsuniya, tace Amani (sunan da ba kasafai take kiran ta da shi ba), are you sure duk wadannan abubuwan da kike gayamin daga bakin ki suke fitowa?
Amani sai ta soma share hawaye cikin karaya da tsoron kada ya zamanto Balewa ce farkon wadda zata karyata ta, ta ce what are friends for? Shi yasa na gaya miki. Shi ya ce tuba na na karya ne, kada kema ki ce haka don Allah, in na boye miki ai bazan boyewa Allah ba cewa na yi nadama, Allah ya ga zuciya ta tayi wani irin damuwa da shi yanzu, ta share hawayen ta sannan ta ce,
amma wa zan gayawa ya yarda da ni in ba ke ba?
Ko cigiyar sa nayi cikin kuskure Baba Sahura mahaukaciya take maida ni, shin dan adam baya taba iya gyara kuskuren sa ne a karbi tuban sa?
Don na tabbata in kowa zai yarda dani banda shi Mukhtar din, sabida wata bakar magana dana gaya masa cikin kuskure da ya kasa mantawa, da sauri Hamida ta ce kada ki gaya min, na san zaki aikata, ni na yarda da ke in kowa bazai yarda da ke cewa kina son Mukhtar ba Sahibah, ni na yarda kina son sa ba tun yau ba, wauta ce ta hanaki ganewa tun can kin damu da Mukhy, kin damu da duk wani takun sa a rayuwa ta hanyar yawan yin maganar sa with utmost hatred, and too much hatred so ne yake kawo shi. Haka yawan yin zancen mutum.
Don haka yar uwa bamu makara ba zamu samo kan Yaya Mukhy din mu, ke dai ki tabbatar kin canza din da gaske kuma da zuciya daya, ki kuma tabbatar masa da canjin naki ta hanyar nagartattun halaye sababbi da zaki yafa yanzo, ki koyi bayyana soyayyar dake zuciyar ki a gaban sa da ladabi da biyayya, Sahibah ki nuna kulawa koda zai miki wata fassarar, to na dan lokaci ne, don na tabbata Mukhtar na son ki.
Da sauri Amani ta damke wayar ta sosai a kunnen ta, hawayen farin cikin kalaman Balewa ya tsirgo mata ta ce da gaske kike Hamida Mukhtar yana so na? Kuma zai cigaba da son nawa bayan duk abubuwan batanci da tozarci da na yi masa? Zai cigaba da son nawa bayan ya dawo cikin gatan sa, ba zai fassara ni da wata fassarar ta daban ba? Hamida har ce masa na yi yana kama da.. Astagfirullah bana so in maimaita don na koyi sakawa harshe na linzami.
Maganar ta yi wa Hamida gingiringin, amma ta san Amani neman wanda zai kwantar mata da hankali ta a ke yanzu, shi yasa har ta neme ta, tana neman mai bata support da assurance na cewa in ta gyara kurakuran ta zaa yafe mata, tunda ta ce ta koyi sarrafa harshen ta ta hanyar yin furuci mai kyau ga kowa, ance matar na tuba bata rasa miji.
Hamida tayi ajiyar zuciya. Sun tattauna extensively kuma heart to heart yadda ya kamata aminai na kwarai su magantu, a kan wata masala data sha kan dayan su. Hamida ta gaya mata cewa har abada Mukhtar ba zai guje ta ba, ta gaya mata dalilan ta; inda tace bayan soyayya ta jini akwai soyayya gangariya a zuciyar sa a kan ta. Sannan ta gaya mata wasu maganganu na sirri na yadda zata nunawa Mukhtar cewa da gaske ta canza da zarar sun tare a gidan su.
Amani da Hamida yau sun raba dare suna tattaunawa kuma Hamida ta taya ta murnar duk abubuwan da suka faru din. Kuma ta ce zata zo har dakin ta a Diffa watarana idan Allah ya nufa.
Tun daga ranar dokin ta ga son dawowar Mukhy ya karu, har practicing/rehersing yadda zata yi masa sannu da dawowa take yi, da irin kallon da zata ke masa mai nuna kunya da ladabi ba irin na baya ba da take ware idanuwa ta zuba masa harara, yadda dai Hamida ta gaya mata, ya zama duk dare da tunanin Mukhtar ta ke iya barci, ta kuma gan shi cikin mafarkin ta, a yanayin da take kwadayin ganin nasu.
Ummami bata san hakan ba ita, domin ta koma fara yi wa dan ta yakin neman soyayya, a fakaice (kamfen). Daga ranar data fara koyar da Amani karatu, in suka yi karatun addini suka gaji don ko wajen Mai bata zuwa sosai yanzu kullum tana like da Amani, don ta fahimci itama irin Mukhy ce ba soyayyar uwa ta tashi, gara ita ta samu ta uban shi kuwa fa?
A kokarin ta na son kara cusa soyayyar tilon dan ta a zuciyar yar uwar sa kuma matar sa, tunda ta ji yaa ce bata son sa duk da ta musanta hakan, sai ta ga bari tayi amfani da damar wajen fayyacewa Aman tarihin Mukhy wataila hakan yasa ta tausaya masa a matsayin ta na yar uwar sa, tausayi da fahimta ta sani suna tasiri sosai wajen kimsa SO. Don haka rannan bayan sun gama karatu na addini da Karin Alqurani da take mata kullum sai Ummami ta sako zancen Mukhtar.
Tace Aminatu kin san labarin mijin ki Maina?
Cikin jin yar kunyar gaske da ta fara samun muhalli a tare da Amani yanzu, ko da yake in bata kunyar kowa tana kunyar Ummami, ta sunkuyar da kai, a lokacin tana taje ma Ummami dogon gashin kan ta da furfura ta soma samun muhalli, Ummami ta ce ta raba shi gida biyu ta yi mata tufka biyu ta gaji da shi a tsefe, mai kitson ta ta yi tafiya. Amani ta ce.
Aah Ummami, ni dai kawai na tashi na gan shi karkashin kulawar Alhaji na, ban san inda ya samo shi ba kuma ban taba tambayar Daddy ba don bama jituwa ni da Yaya Mukhy ko kankani, shi baya son hali na nima bana son nasa, shi yasa kika ji yana cewa wai bana son sa!.
Ta karasa fadi cikin karamar murya mai nuna kunyar idon uwa, amma gara ta gaya mata gaskiya a kan ta ci gaba da rikon ta a ran ta a kan bata son Mukhy, ba uwar da zata so a ce dan ta na auren macen da bata son sa sai dai ta yi kawaici, idan mai kawaicin ce irin Ummami kenan.
Ummami ta gyada kai ta ce wato Amani, a duniyar Subhana ina tsananin tausayin Mukhtar Amani, shi yasa nake so kema ki tausaya masa, ki bashi soyayya wadda ban bashi ba, ki jiyar da shi dadin da mata hudu zasu jiyar da shi a lokaci daya, ki kuma kula da shi da rayuwar sa yadda nake kokari akan mahaifin sa ba don bai da wasu matan ba.
Ummami ta nisa, sannan ta cigaba da cewa kin ga yadda ya bar gida duk gatan shi a shekarun balaga, a shekarun da ya dace a ce yana kusa da mahaifin sa a fadar sa yana koyar da shi shaanin mulki, amma ya zabi ya tafi uwa duniya sabida rashin samun kulawar iyaye. A hakan ma don baki san irin rayuwar da yayi tare da yayan bayi, a kuma sassan bayi ba.
Idanun ta ya ciko da hawaye ta ce shi da ni sai dai leke daga nesa, ban taba goya shi a baya na ba, duk hakan bai isa ba aka zo aka bi shi da mugun asiri wai kurciya ya kara yin nesa da gida, kuma Baban sa