Showing 6001 words to 9000 words out of 30436 words
ka a jikin ta, nida kaina na ce ta fidda kai daga ran ta, Allah zai raya mana kai. Ba zaka taba zama sarki ba idan ka samu gatan da yayan sarakuna ke samu, kasancewar kai din daban ne, zagaye nake da makiya haka mahaifiyar ka zagayeta ke da kaidin mata yan uwan ta iri iri musamman da ta haife ka, kasancewar ni mutum ne mai yawan aure-aure, amma tunda muka watsar da kai sai duk hankalin su ya bar kan ka, ya koma kan yadda zasu yi su samu nasu yayan suma, don na nuna bana kaunar ka ban damu da rayuwar ka ba.
Mukhar dauriya iya dauriya irin wadda ba duka iyaye zasu iya ba a kan dan da suka haifa kwalli daya muka yi a kan ka, domin mu tseratar da rayuwar ka, amma duk halin da kake ciki a gidan Katchalla wallahi mun sani. Kuma muna kulawa da komai naka.
Hatta tafiyar ka Farisa mun san da ita, nine kuma na sa aka baka scholarship daga ofishin Baare Mainasara (shugaban kasar Nijar na wancan karnin).
Haka daga sanda ka bar Farisa ne muka daina samun labarin ka sannan bamu san ina ka koma ba.
Malamai na daban-daban na cikin gida kullum gayamin suke in kwantar da hankali na domin kana raye, kuma a kyakkyawan hannu mai tsafta, amma na kasa kwantar da hankalin nawa.
Kullum (blaming) kaina nake yi kan ko dai hukuncin dana yi wa rayuwar ka ba dabara bace karbabbiya? Ko dai kuskure na yi maimakon (saving life) din ka?
Wannan tunanin da wannan nadamar su suka taru suka kwantar da ni na lokaci mai tsaho. Musamman da aka tabbatar min ka bar Farisa baa san inda ka shiga ba kuma. Har gobe a kan treatment nake, mahaifiyar ka kuwa ka gan ta yanzu bata gani sai da Gilashi, sabida yawan kukan tafiyar ka Maina.
In mun yi kuskure cikin abinda muka aikata muna rokon Allah ya yafe mana, kai ma ka yafe mana. Sannan madallah da jin cewa kayi aure, lokaci ya yi da zan bayyana ka ga duniya.
Zan maka bikin aure irin wanda baa taba yin irin sa a masarautar Diffa ba, zan gayyato duk sarakunan jamhuriyyyar Nijar, in gabatar da kai gare su, sannan zan baka sarautar Diffa tun ina raye. Kafin nan zan maka nadin sarautar Mainan Diffa ka fara zama a fada tare da ni don ka koyi shaanin mulki na lokaci mai tsaho.
Duk wadannan abubuwa da ke faruwa yau, Mukhtar couldnt believe them, don ya dauka mafarki yake yi, ire-iren mafarkan da dan adam in yana yin ba ya so ya farka, yana rokon Allah da dai ya farka daga wannan mafarkin, gara ya zarce a cikin niimar sa, wato ya karasa mutuwa a cikin dadin sa..
***** ***** *****
WASHEGARIN RANAR
Da wayewar gari, Sarki Issouffou Massaoudou ya aiko a tafi da su Alhaji cikin masarauta, yasa aka kai su dakin da yake ganawa da manyan bakin sa, sannan aka shirya musu karin kumallo tare da Sarki da Ummami. Wanda ya kai su shigifar ya ce su jira kadan, Mai Diffa na zuwa tare da Mowa.
A lokacin Mukhtar na can yana ramuwar barcin gajiya bai ko tashi ba, don kwanan zaune suka yi da iyayen sa, tun bayan da suka dawo masallaci sallar asubahi aka bude masa wata shigifa da ke kusa da na mahaifin sa, yake barci har zuwa lokacin, barci na kwanciyar hankali irin wanda bai taba samu ba.
Su Jalan sun nutsu suna kallon sarautar Allah, domin ko a cikin masarautun Nijar Diffa na sahun farko, komai na masarautar mai ban shaawa ne da ban mamaki kuma irin ancient dinnan amma aka zamanantar da shi, suna kalle kalle suna jiran isowar Mai Diffa da Maidakin sa, wadda suka ji an kira Ummami (Mowa).
Can suka jiyo takun sa ya durkako inda suke. Cikin taku na haiba da kamala. Yana shigowa duk suka mike domin girmamawa. Haske da kwarjinin addinin Musulunci ya bayyana sosai a tare da farin balaraben dattijon. A nitse ya zauna a kujerar da ita kadai ce kujerar mulki a dakin, wanda yafi dacewa a kira shi palace, ba jimawa da zaman sa sai wata kofar ta kara budewa. Doguwar matar cikin kyakkyawar laffaya da farin gilashi a idanun ta, ta shigo, ita kadai ba tare da kowa ya rako ta ba.
Ta nemi guri gefen maigidan ta ta zauna kasan kafafun sa, fuskar su fal annuri da maraba dasu. Kafin kowannen su ya ce komai aka ji Mamma Jalan ta tsinke da salati ta ce Yaya AISATA!
A firgice Ummami ta juyo, jin muryar kanwar ta, Jalan. Da gudu Jalan ta sheka ta isa gareta ta rungume ta. Sai kuma ta saka kukan farin ciki. Da kyar Aisata ta banbarota daga jikin ta. Ta ce Jalan, ke ce koko ido na ne? Aah ke zan tambaya da gaske ke ce? Kuma Mukhtar dan ki ne kenan? Aisata (burst into tears) tace ban taba gaya miki cewa na haihu ba, sabida bamu kara haduwa ba tun rabuwar mu sai aike ne a tsakanin mu, sabida a kaida matan gidannan basa fita, ko asibiti bama zuwa saidai likita mace ta zo har daki ta duba mu, sannan da matsalolin da suka biyo bayan haihuwar tasa, da muka fara waya dake bayan kin yi aure na biyu kenan, ni ban san meyasa na kasa gaya miki ina da Da ba, kodayake bana maganar sa sam, balle irin wannan a muhimmiyar magana ta hada mu da wani nawa ta waya, daga baya kuma bama tare dashi ma, daidai lokacin rasuwar Abbu sanda na aiko dan aike na wajen ku, aike na na farko gida Kenema, lokacin Maina ya riga ya gudu.
Me ya kai ki Najeriya yanzu? Na dauka kun rabu da mijin ki na can tun su Abbu na raye, har kin yi wani auren da Lukman kin samu yara? Daga baya kika gaya min a waya ya rasu, ta ina kika hadu da yan Najeriya bayan na san kina Kenema?
Suka rungume juna ana ta mamakin wannan ikon Allah, Jalan ta gaya mata Alh. Usman shine mijin ta na fari wanda aka aura mata a kasar Katsina, suka rabu bayan ta haihu, itama rabon ta da yar tun lokacin, sai yanzu da kaddara ta sake hada su. Ta nuna mata Amani dake ta sakin fitsari a kai-a kai daga zaune ta cikin wandon ta a lokacin, sabida yadda ta kara firgicewa da alamarin Ubangiji, wato Mukhy Yayan ta ne na jini kuma?! Bayan nadamar data sha jiya bata ko gama fita daga cikin ta ba, yau ga gagarumar nadamar data fi ta jiya ta kara samun ta. Jalan ta nunowa Aisata ita da hannun ta manuni.
Kin gan ta itace yar da na haifa na baro a Najeriya sunan ta Amina, sai da girman ta na gan ta, kuma ita ce matar Mukhtar a halin yanzu, domin a hannun mahaifin ta ya zauna a gidan su duk tsayin wannan lokacin.
Ummami sai ta mikawa Amani dukkan hannuwan ta tana hawaye tana fadin Ya ki nan diya ta, ta kaina! Amma Amani ta kasa tashi sabida yadda ta jika jikin ta da fitsari a zaune, sai da Sahura ta ciccibata, ta isa ga Aysata, ita kuma ta saka dukkan hannuwa ta rungume ta a ciki, tana fadin dukkan godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai, mai rahma mai jin kai, mai yawan hikima ga rayuwar bayin sa.
Sai lokacin Sarki yayi gyaran murya ya ce hakika Ubangiji mai hikima ne, madallah da ku, madallah da kariman mutane irin ku, masu mayar da dan kowa nasu.
Ya dubi Daddyn Amani yana murmushi ya ce yadda ka rike min Mukhtar da amana ba tareda ka san komai a kan sa ba, haka nake fatan in rike Amina daga nan har karshen rayuwar mu, ko da bata kasance yar uwar sa ba. Allah ya saka maka da alkhairi ya kuma baka lafiya.
Sai ga Mukhtar ya shigo dakin daga shi sai farar jallabiyya kal da bakar hular larabawa a kan sa, kallo ya koma gare shi suna mamakin yadda cikin kwana daya tal ya canza ya koma tamkar ba shi ba, yayi kyau, yayi wani irin fresh tamkar balaraben Madina. Kamar da ka latsa shi jini zai yi tsartuwa. Nan aka gaya masa ko me ke akwai, wato Jalan kanwar Ummami ne ta jini, uwa daya uba daya.
Mukhtar sai kamar bai yi wani mamaki ba, cewa yayi ai ni naso in gane hakan tuntuni, kawai ban san komai akan Ummami bane ko dangin ta, wanda zai karfafa zargin nawa, amma tabbas na ga alamu, tun sanda na ga cindo Ummami a hannun ta da wasu attributes da dama, sannan jiki na ya bani, son da na samu kaina ina ma Mamma, kamar na Ummami ne, musamman da ita ta sake da ni sosai ba kamar Ummami ba cikin yan kwanakin da nayi tare da ita.
Nan aka shiga mayar da zance, aka dauko tarihi tun daga farkon sa, tarihin masarautar Diffa da yadda kakan sa Sultan Oumarou ya bada sarautar ga dan sa Sultan Massaoudou tun yana raye, bayan rasuwar sa Sarki Issouffou ya gaji sarautar daga hannun mahahifin sa Sarki Massaoudou. Ya ce sun kasance su masu karancin haihuwa ne a jinin su, shiyasa suke aure-aure daga kasashen Africa daban daban daga kyawawan matan Africa, wadanda suke saye suna sa-daka dasu (concubines) basu cika maida su matan aure ba.
Ya ce amma ita tunda aka kawo ta gaban mahaifiya ta ta ganta da tabon sujjadah a goshin ta, sannan aka gaya mata daga Saliyo take sai tace aure zaa daura mana bata yarda in yi sa-daka da ita ba.
Marigayiya mahaifiya ta tace matan Saliyo mata ne na musamman, daban suke a halitta da sauran matan Africa, Allah yayi musu baiwa ta auren manyan mutane, tace sanda zata kwace Mowar Diffa daga hannun Ummu Aymana, bazan sani ba.
Sarki yayi murmushi yace and thats exactly what happened today, Aisata Mowar Diffa! Kafin ita ina da matan aure guda biyu, uwargida Ummu Aymana yar sarkin Zinder tana da ya daya; Sayluba. Sai Tarha diyar sarkin Agadaz wadda itama na samu haihuwar diya mace da ita. Sai aka daura mana aure na Sunnah da Aisata, na bata dakin mace ta uku a gidan sarautar Diffa.
Kasancewar duk matan da ake kawomin matsayin sa-daka nake basu, wannan ya tada hankalin mata na; Ummu Aymana da Tarha. Musamman da ya kasance har zuwa lokacin babu wadda ta samu haihuwar Maina cikin su. Suka daga hankalin su a kan Ummami nima suka daga min, sanda ta samu cikin Mukhtar kuwa ina wuta su saka ta, aka hanamu aure ta hanyar saka min tsanar ta a shimfida, aka saka mata warin gaba, aka saka mata kurarraji kai matsaloli marassa dadin ji iri-iri a dalilin wannan ciki kamar ba zai kai labari ba.
Don daga baya ko dokin haihuwar tata na daina. Na koma ganin abinda zata haifa min din a matsayin matsala.
Sai malaman fada ne suka saka ta gaba da addua don kowa yana so Diffa ta samu Maina, basa so sarautar ta bar gida na, don ina da yan uwa a raye, amma ni ko a jiki na. Uwargida na da bakin ta ta gayamin cewa muddin Aisata ta haifi Da namiji sai ta salwantar da rayuwar sa, na kuma san zata iya, a yadda ta cika zuciyar ta da burin ita zata haifa mun Maina.
Sai bayan an haife shi an kawo min shi hannu na zuciyata ta cika da kaunar sa, gashi cikin yan uwa na ma da suke da yara maza basu so na samu Maina ba, sun so ya kasance na mutu babu magaji don sarautar Diffa ta koma hannun yayan su. Don haka na san ta koina Mukhtar yana cikin hadarin makiya musamman da ya kasance kamar an tsaga kara ni da shi a kamanni. Sai na shiga tunanin ta hanyar da zan bi in kare rayuwar sa.
Nan na zaunar da Aysata, na ce wannan yaro kin haife shi dai ko? To ki godewa Allah komin runtsi sunan sa dan ki, amma ki nema masa kariya ta hanyar rashin nuna kauna da kulawa a gare shi.
Ta yi min kallon rashin fahimta nan na wayar mata da kai, na ce mata na barshi karkashin kulawar bayin mahaifi na na tun tali-tali, wadanda nima gadar su nayi a gun mahaifa na saboda amanar su, wato Katchalla sarkin fada da Jakadiyar dana bata. Na ce ta runtse idon ta daga kan yaron nan, ta bar shi ya rayu a hannnun su. Zasu kula da shi kamar yadda zasu kula da yayan su amma rayuwa irin ta yayan su.
Da yake Aysata mai fahimta ce, mai kuma bani hadin kai akan duk abinda na zo mata da shi sai ta yarda. Amma ta roke ni in bar ta ta shayar da shi ko a boye ne, ko na tsayin shekara daya ne, na amince mata. Don na san muhimmancin nonon uwa, kuma inaso ya tsotso irin kwakwalwarta da kyawawan dabiun ta.
A takaice wannan ne dalilin da yasa muka yi wa Mukhtar rainon da muka yi masa, yau gashi Allah ya raya shi yadda nake fata, duk wani da ya nufe shi da sharri na tabbata ya ga abun sa a kwaryar shan sa, domin koda aka gaya min kurciya aka yi masa daga baya ni ban damu ba, na bar shi ya je ya koyi rayuwa har zuwa lokacin da ni da kai na nasa malaman fada suka karya sihirin, tun a daren ne kuma aka gaya min Ummu Aymana ta fita daga gidan nan, ta tafi har Zinder a kafa, ita ba mahaukaciya ba, ita ba mai hankali ba, ta dai koma kamar tababbiya, kuma kalamanta kullum.
Mainan Diffa dana yi wa kurciya zai dawo yanzu ya karbi Diffa.
A halin yanzu tana can hannun iyayen ta ana mata magani amma tace bazata dawo gida na ba in dai Mukhtar na cikin sa.
Don haka a jiya na datse igiyar aure na da ita na aikawa mahaifin ta sarkin Zinder. Diyar da muka haifa nida ita (Sayluba) na dade da aurar da ita a Tahoa, tana da yaya basu fi uku ba itama ta gado rashin yawan haihuwa ta, sai kanwar ta yar wajen Tarha (Saadiyya) itama tana aure a kasar Guinea kusa da Liberia ga Amabasadan Nijar a Guinea.
Bayan Aisata ta haifi Mukhtar shiru shiru babu karin haihuwa a gida na, sai na kara aure da Balqissa, wadda aka kawo min ita daga kasar Abidjan. Har yau itama bata haihu ba, Mukhtar mai bakin baya ka hana ni samun ko yaya matan ne sabida alhakin ka Ubangiji ya hana ni..
Ya karasa fadi cikin zolayar Mukhtar. Sai da kowa a wajen yayi dariya Ummami ta ce kada ka damu MAI DIFFA! Ba da jimawa ba in sha Allah diyata Aminatu zata cika maka gida da yaya. Jalan ta ce ni nafi so a kara mishi da sadakoki yadda yaran zasu fi saurin taruwa dariya kowa yayi, amma banda Amani da Mukhtar, wadanda duk suka bi suka daddaure fuska, kuma kowanne yaki yarda ya kalli inda dan uwan sa yake. A zuciyar ta cewa take ta Allah ba taki ba Mamma.
Ga dukkan jin dadin ta sai Ummami tace in har ba ya zama (Mai) din Diffa ba (Sarkin Diffa) babu mai bashi sa-daka a halin yanzu. Yanzun Maina ne kawai, ku bar su su mori kurucciyar su don Allah.
Sai Amani ta hau addua a cikin ran ta;
Ya Allah kasa kada a taba baiwa Mukhtar sarautar gidan su, Allah ka kara nisan kwanan mahaifin sa, yayi ta zama a muhallin sa na Mainan Diffa.
(Ta manta Sarki ya ce tun da ran sa zai baiwa Mukhtar kujerar sa).
Sarki yayi umarni da su Jalan su koma bangaren Ummami da zama har Amani. Gobe-goben nan zaa saka tubulin ginin bangaren matar Maina.
Ya kuma ce a yau dinnan zai soma aika takardar gayyata zuwa ga sarakunan jamhuriyyar Nijar, wato gayyatar bikin auren Maina da nadin sarautar sa ta (MAINAN DIFFA).
**** ****** ******
MOUKHTAR ISSOUFFOU MASSAOUDOU
(MAINAN DIFFA)
B
aka jin komai sai tashin bushe-bushen algaita da kade kaden ganguna irin na masautar Diffa, a yau Asabar, wadda ta kasance ranar bikin auren Maina da nadin sarautar sa.
Cikin wadanda suka halarci wannan kasaitaccen biki har da Yayar shi gimbiya Sayluba daga Tahoa, mai bi mata da yake tana Guinea, bata samu zuwa ba don tayi nisa sosai, mahaifin ta ya aika mata kan ta zo ga