Showing 54001 words to 54710 words out of 54710 words

Chapter 19 - Jarababben Namiji Book 1 Hausa Novel Complete

15 Dec 2024

348

kina son ki gane kwai mai kyau sai ki zuba su acikin ruwa zakiga masu kyau din suna kasan ruwan mara kyau kuma zasu tashi a saman ruwan.

***yanada kyau idan zakiyi masa bayan kinyi hadin sai kisa hannunki aciki ki juya shi hakan nasa shi ya tashi mai kyau.

***idan gishiri ya yawa miki a miya ki fere dankaki kasi aciki.

***Idan zaki yanka red pepper dinki ki shafa hannunki da man gyada yin hakan zai hanake jin zafin shi

***Idan zaki yanka albasa kuma kina tsoron zafinshi a ido to bayan kin bare bayan kisa a fridge zuwa minti biyar ko kina yanka albasan acikin ruwa hakan zai hana zafi a ido.

***anfani da cray fish a abinci yana da balain kyau

**idan zakiyi ajiyan madara bayan kinyi anfani dashi kuma kina gudun kar ya bace ko ya changer teste to kidan sa gishiri aciki.

Yanada kyau kina anfani da curry leave da scent leave a abinci musamman a pepper soup.


~YOGHURT~

*Ingrediants*
Madarar gari rabin kwano
Nono mara tsami small cup
Ruwa

*METHOD*
Dafarko zaki samu tukunyarki mai kyau kizuba ruwa kidora kan wuta su tafasa saiki barshi ya huce kadan idan sun huce saiki douko madara kirinqa barbadawa kina damawa harya danyi kauri (karki bari yayi gudaji)saiki dauko nonon mai kauri kuma mara tsami shima kirinqa zubawa kina motsawa idan kingama saiki rufe ki ajiye wuri mai dan dumi kibarshi kamar 4hr after 4hr saiki bude madarar zakiga tayi kauri saiki zuba sugar da flavour ki motsa ya motsu saiki zuzzuba acikin mini roba kisa a fridge yayi sanyi

 PIZZA 

Kayan Hadi

• Filawa

• Gishiri

• Yis

• Man zaitun

• Manshanun kanti (Cheese)

• Mayonnaise

• Kayan kamshi

• Tumatir da farar albasa da koren tattasai

• Tsokar\ kaza

Yadda ake yi:-

 

Da farko za a jika yis da ruwan dumi kamar tsawon minti 10, sai ki zuba gishiri da man zaitun. Sannan sai ki kara filawa a cikin wannan ruwan yis din ki kwaba har sai ya yi tauri. Idan ma kika ji shi ya yi ruwa ko lauashi sosai sai ki kara fulawa don yayi tauri. Daga nan sai ki rufe ki bar shi ya hau zuwa mintina 30. Idan ya hau (kumbura) sai ki sami farantin gashi ki juye filawar a ciki sannan ki sanya a cikin oben ki gasa ki bar shi tsawon mintuna biyar. Ana sai ki yanka tumatir da farar albasa da koren tattasai kanana. Sai ki koma wurin fulawarki ki duba idan ta gasu sai ki fito da ita. Sannan ki dauko kayan tumatir din da kika yanka sai ki zuzzuba akai da dan garin kayan kamshi ki barbada. Sai ki sami tsokar naman kazarki da kika yanka kanana tare ki zuzzuba akai. Sannan sai ki kawo mayonnaise ki yaryada akai. Sai ki zo ki rufe samansa da manshanun kanti (chease). Sanann ki mayar cikin abin gashin (oben) don ya kara gasuwa. Za ki ji yana kamshi sosai sai ki fito da shi daga ciki shi ke nan Pizza ta yi sai ci.







*FRIED CABBAGE*

ingredient
-Cabbage
-Dankali (5)
-karas (5)
-Nama (yadda kikeso)
-Kwai (7 or 8)
-Maggi
-Albasa
-Soy souce
-Mai


*METHOD*
-Dafa nama da maggi da albasa da 'yar citta yadda zaiyi d'and'ano, idan yadafu ki yanyankashi k'anana.


-Fera dankali da karas, dafasu sai ki soya ammah daban-daban, sai ki ajiyesu gefe.

-Yanka cabbage irin girman da kikeso ammah yakasance girma, d'an tafasashi, idan ya tafasa safkeshi ki tsane, yanka albasa a ciki.
Kawo sauran kayan da kika ajiye ki zuba a ciki.

-Zuba soy souce dan k'arin d'and'ano, maggi, curry da d'an gishiri.

-Zuba mai a kasko kamar cokali hud'u (tea spoon) kiyi ta juyawa har ya had'e, zaki ga k'wan ya had'e a jikinsu sai ki safke.
Zaki iya ci da d'an lemunki.


*CAKE 'DIN WAINAR KWAI DA DANKALI*

Ingredient
-Fulawa
-Kwai
-Dankalin Turawa
-Attaruhu
-Albasa
-Maggi
-Kifi
-Curry
-Gishiri

*METHOD*
-Fera, kidafa dankalinki ki yanyankashi gutsin gutsin.
Ki jajjaga attaruhu da albasa ki cakud'a cikin dankalin kisa maggi shima sai ki ajiye a gefe.

Ki fasa k'wai, ki soya manya-manya da fad'i kar abari yak'one, ki yanyanka ki zuba cikin dankalin nan.

-Ki k'waba fulawarki kamar zakiyi meat-pie already daman kin dafa kifin ki kin cire k'ayar tas kin marmasashi, sai ki zuba cikin k'wa'ba'b'biyar fulawar nan, kiyi irin shape d'in da kikeso, kisa a oven ki gasa ko kisoya a mai.









_OUM APHNAN NAMUKU SO FISABILILLAH,09065990265 PLZ ,DON ALLAH MASOYANA JARABABBEN NAMIJI,MAI LITTAFIN NAN DAGA FARKO YA TURO MUN IN HADA MAKU DOCUMENTS PLZZZZZZZZZ🤟🤟🤟🤟_





Maassalam , ina kewarku😭😭😭
09065990265

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login